Free chapter · Read without an account
THE DEADLINE
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
NURI'S POV
Tana zaune akan abin sallah tana addu'a ammn absent-minded don hankalinta yana wani wurin totally. She was thinking about deadline din da Inna ta basu, it was tomorrow, Friday.
She can't even imagine Inna ta koresu, tasan bata sonsu amman bata taba kawowa tsanar ya kai har haka ba. Ko a yanzun gani take kamar zata iya jin tausayinsu idan ta koresu taga babu inda zasuje. Tana bawa kanta hope kamar zata tausaya musu duk da ita shaida ce Inna sam bata da mutunci, don ko Abba lokacin da yake nan idan rashin kudinta ya ciyota sauke masa bala'i take. Ita kawai bata son taga bata da kudi sam, burinta kudi kawai.
Kiran sallahr Isha ne ya dawo da ita daga tunanin data fada hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya ahankali. Sai da Azan ya kammala kiran sallar tsaf bayan tayi addu'a ta miqe taje ta sake dauro alwala don akwai lada sosai acikin sabunta alwala. Isha, shafa'i da wuturi tayi a lokacin sai dai ba tayi dadewar da tayi tana addu'a irin na Maghrib ba ta miqe tana nade abin sallar ta ajiye a gefe ta fita.
Kitchen dinsu ta nufa kai tsaye don yunwa take ji dazu murnar Afif bai barta taci abincin kirki ba sam. Tana dubawa taga abincin saura kadan bai da wani yawa sosai. Tukunyar tabi da kallo kawai tana tuna sanda Abba yake nan. Abincin gidan nasu ya kare gaba daya yanzu aunowa suke abinda sam da ba haka suke ba. Every month Abba yana ajiye abincin da zai kai wani watan. Is hard kayan abincinsu ya kare kamin karshen wata yazo, Abba yana mugun kokari don sam bai son yaga ana zama da yunwa.
Rufe tukunyar tayi tana fita daga kitchen din ta bari suci da Mami don idan ta diba zata galgalta musu shine kawai. Wayarta data ajiye kan centre table tun kamin Maghrib ta dauka tana zama akan sofa dake parlourn. Number din Zara tayi dialing tana jin kewarta tun ba'a je koina ba.
Ringing biyu kacal Zara tayi picking call din ko sallama ba tayi ba tace "Friendy kina raina ina shirin kira kin rigani."
Murmushi Nuri tayi tana gyara zamanta tace "Allah ko? Ba wani nan. Kedai kinje Lagos kin manta dani best."
"Who am I dazan manta dake friendy? Haba Allah ya kiyaye. Kawai kinsan sabon gida ne so har yanzu bamu gama saita kan gidan ba. Ga Mummy da jajibowa mutum aiki."
"Ga best da kiwa kuma ba." Dariya sukayi a tare. "So how is Kano without me Friendy?"
Dan lumshe kyawawan oily eyes dinta Nuri tayi tana cewa "Uhmmm Kano without best is the best..."
"A'ah fa, fadi gaskiya ga naira goma." Nuri na murmushi tace "come on, Yah Mummy, ya sabon gida, in fact ya Lagos?"
"Ba dadi garin na fada miki. Lallaba daddy zanyi wallahi na dawo nan."
"Ki zauna dawa?"
"Hostel hajiyata."
"Eh lallai dadina dake kanki sha tara wataran yake bugawa." Sun jima sosai suna hira kamar sun dade basa nan haka. Fitowar Mami yasa suka yi sallama. A kusa da ita Mami ta zauna tana cewa "yaushe zaki ware wannan kalabar kan naki duk, yama ware kanshi." Kanta da hularta ya zame ta shafa tana cewa "Mami I don't have time. Gobe ne ranar da Inna zata dawo, wanne halin muke ciki Mami?"
"Allah is all seeing and hearing Nuri." Bata sake magana ba sai da Mami tace taje ta zubo musu abinci sannan ta miqe. Agaban Mami ta ajiye plate din abincin Mami tabi dan abincin da kallo tana cewa "are we playing or eating Nuriyya?"
"That's all fa Mami." Shiru Mamin tayi tana cewa "ok is like I'm full ma. Bana jin yunwa. Eat."
Baki Nuri ta saki tana kallon Mami da mamaki, tasan yunwa take ji that's why tace a zubo abincin and now an zubo ta ganshi kadan tace ta koshi.
"Ni daman ba yunwa nake ji ba ko kadan..." Kallon da Mami keyi mata yasa bata karasa maganrta ba tayi shiru kawai tana zama agaban abincin. Sai dai zaman kawai tayi ta zuba tagumi ta kafe Mami da kallo. Tun Mami na pretending bata san tana yi ba har dai ta kalleta tana cewa "dole Afif yake kiranki da mayya, you're acting like one."
Baki ta turo cike da shagwaba "Mami Allah abincin nan zai ishemu. Kinsan dai ba ci ne dani ba."
Banza Mami tayi mata tana fara danna waya, dole Nuri ta fara cin abincin amman ta ragewa Mami, wanda sai da kyar Mamin ta yadda taci sauran data rage mata.
Basu dade da gamawa ba sai ga kiran Afif, Nuri har kamar zata fadi wajen amsa kiran. "Ka riqa dai cika alqawari." Ta fada masa immediately tana amsa kiran.
"Kinga dan bawa me wayar, ita na kira." Harararsa tayi kamar yana gani kamin ta miqawa Mami wayar tana zama agefenta.
Basu jima suna wayar ba kasancewar karatu Afif din yake kawai yana son ya sake jin muryarsu ne shi yasa ya kira.
WASHEGARI
Dukkansu da fargabar Inna suka tashi, aikin gidan ma babu wani kuzari haka suke yinsa don suna expecting dinta ko yaushe. Ganin har rana tayi bata zo ba yasa Mami kiran carpenter din da yayi musu kayan daki don sunyi yau zaizo suyi ciniki daman. Sun rabu ana idar da jumu'ah zai qaraso don babu nisa da inda yake da unguwar.
Sunyi waya da Afif ranar tun da safe hakan yasa babu wanda ya sake bi takan wayar don yace musu sai dare zai sake kira.
Cefanen kayan abinci Nuri ta fita yi musu sanye cikin dogon hijabi wine colour daya yi mata kyau sosai duk da bata sakashi don kyau ba. Kasancewar inda za tayi siyayyar babu nisa hakan yasa bata wani dade ba ta dawo. Ita za tayi girkin don haka ta fara hada kayan girkin ta dora.
Jin bugun kofa daga waje yasa ta fito tana zura hijab dinta ta karasa ta bude kofar tana fatan ba Inna ce ba and it was not Inna, carpenter da Mami ke jirane yazo.
Ciki ta koma tana kiran Mami dake zaune a parlour doing nothing, bata san me za tayi ba banda tunani. Miqewa Mami tayi tana zura hijab ta fito Nuri kuma ta koma kitchen.
Gaisawa suka yi don kamar akwai sabo kadan atsakaninsu. "Hajiya ina kayan?"
"Suna ciki Idris, ka sansu ai, tunda kai kayi aikin. So don Allah kar kayi musu siyan wulaqanci."
Kai ya gyada mata yana cewa "karkiji komai hajiya bazanyi ba kodan darajar mai gidan da baya nan, mutumin kirki."
Kai kawai Mami ta gyada tana yin shiru, Idris din ya tabo mata mikin da yaqi warke mata watanni biyar kenan.
Ciki ta nuna masa tana cewa "bismillah." Kai ya girgiza yana cewa "nifa inaga ba sai na gansu ba hajiya, ki fadamin kawai nawa zaki siyar na baki kudin."
"Me za'a siyar?" Muryar Inna ta cika bakin gate din gidan da Mami da Idris suke tsaye. Wani faduwar gaba ya riski Mami tana jin kamar ta sallami Idris kawai to amman she's in need of the money. Kudin take so, musamman da Inna tazo, tason korarsu tazo yi ba wani abu ba.
Idris ya kalli Inna daya santa a matsayin mahaifiyar Abba don dan gadon dakinta ma shine yayi mata da kujerar dakin.
"Wasu daga cikin kayan dakin zata siyar hajiya Inna." Ya bata amsar da yasa Mami saurin kallonsa ganin kai tsaye ya bada amsar da ba shine yake da hurumin bada ita ba.
"Uban waye ya bada izinin sai da kayan dakin gidan nan?"
Yadda Inna take daga murya ya jawo hankalin Nuri da kadan daga cikin masu wucewa da suke jiran kiris suka tsaya suna kallo.
Danasani Mami ta shiga yayi don ta tabbatar Inna zata kwance mata zani a kasuwa ne. Nuri na zuwa ta tarar da Inna ta wani riqe kugu kamar mai jiran dambe duk da tsufanta kuwa.
"Tambaya nake Bintu, waye ya baki izinin sai da kayan dakin da ba naki bane?"
Hannu biyu Mami ta hade da sigar roqo tana kallon Inna tace "kiyi haquri Inna don Allah mu shiga daga ciki sai muyu maganar."
Harara ta banka mata tana sake gyara tsaiwarta cike da jin fada tace "ba shiga ciki ne ya kawoni ba Bintu, sam banzo nan don na shiga ciki ba. Ke ki bani amsata malama da za'a kawoki gidan nan kinzo da kaya ne da kike shirin siyar dasu?"
Anzo wajen, anzo wajen da Mami ke gudu tun dazu. Tasan bazasu taba rabuwa da Inna bata ci mata mutunci ba. Yes tabbas ba akai Mami da kayan daki ba, Abba ne yayi mata don bata da mai yi mata a lokacin, shi kuma Abba yana fama da soyayyarta hakan yasa yayi mata kayan daki gwargwadon karfinsa a wancan lokacin.
Kai Mami ta girgizawa Inna tana cewa "don Allah Inna ki shigo ciki." Tsaki Inna ta ja tana cewa "dalla can, to bude kunnenki da kyau kiji abinda zan fada miki." Ta karashe tana riqe kunneta daya alamar gargadi.
"Wallahi, billahillazi la'ilaha Illa huwa idan kika kuskura kika siyar da kayan dakin nan mai rabani dake sai Allah. Kaya dai na Audu ne, Audu kuma dana ne ni Laure. Tunda bake kika tsugunna kika haifominshi ba baki da hurumin siyar da kayan da yake nasa ne."
Sai ta sauke kallonta akan Idris da yayi tsuru tsuru yana kallonta tace "Kai kuma, bace daga nan. Algungunmi ai kasan ba nata bane tunda kai da kanka kayi su kazo zaka wani siye munafiki baqar haihuwa." Salin alin ya kada kansa ya tafi don Inna ba dai masifa da jaraba ba. Yawanci 'yan unguwarsu jarabatu suke ce mata don bata bar kowa ba. Baka shiga gonarta ba ta yanka maka rashin mutunci bare ka shiga. Itafa akan kudinta, to babu abinda ba za tayi ba idan ka cire kisa.
Nuri dake a rakube agefen Mami Innar ta harara tana cewa "ke kuma me idon mayu, kina bina dasu kamar zaki lashe to kurwata kur dai maye yaci kansa." Nuri bata kulata ba sai Jan hannun Mami data farayi tana cewa "Mami mu koma ciki nan duk rana."
Caraf Inna ta cafe da cewa "wacce cikin zaku koma Nuratu?" Shiru duk suka yi suna kallon yadda Inna take magana cike da daga murya kowa yana ji.
"Ya muka yi daku wancan satin?"
"Amman Inna a addinance ba haka ya dace ayi ba." Mami ta fada tana rusunar da muryarta wai ko Innar zata tausaya musu.
"Sannu uwar addini, nace sannu uwar addini. Kinga bani da isasshen lokacinku wallahi. Gida na siyar dashi har naci kudi. Kuma na siyar dashi ne tare da kayan dakin da kike shirin saidawa, don haka ba ruwanki da tabasu." Ki tattara komatsanki keda wannan mayyar yarinyar taki mai zubi da mayun farkon zamani kusan inda dare yayi muku kuma. Masu gida suna son fara gyara gidansu. Eh a koma inda aka fito."
Sai Inna ta matsa kusa da Mami sosai tana mata wani kallo tace "matsa ko." Babu wani musu Mami ta matsa mata ta shige ciki tana cewa "ku zo ku kwashe kayan kawai zan jira har zuwa sanda zaku tattara ku tafi. Yau dai baku kwana agidan nan aradu."
Babu wanda zai kalli Mami da Nuri basu bashi tausayi a lokacin ba. Yadda suka takure ajikin juna shine abin tausayin. Inna sam bata da kirki kona misqala zarratin. Agaban mutanen da suka taru kallon bala'inta tayi musu wannan tozarcin. Suma mutanen unguwar da tsegumi babu wanda ya iya bata haquri ko da yake wasu sun san wace Laure, ba'a shiga gonarta.
Ahankali Mami ta raba Nuriyya da jikinta cike da sanyin jiki ta jawota suka bi bayan Inna da ta hakimce akan katuwar 3 seater dake parlourn ta daura kafa daya kan daya tana hura hanci. Kallo ta kare musu tsaf lokacin da suke shigowa musamman Nuri da yau ne karon farko da taga tana mata dan kama da Abba. Don daga Nuri har Afif duk da Mami suke kama that's why Inna sam bata wani sonsu. Amman yau karon farko taga wata fisgar kama da suke yi hakan yasa ta kafeta da idanu tana tuna Abdullahi.........
To be continued.....
#like
#share
#comment