Free chapter · Read without an account
EVICTED
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
"Zonan Nuratu." Da wannan sanyin jikin da naturally take dashi plus halin da Inna ta sake jefasu ta waiwayo ta kalli Inna kamin ta sake kallon Mami data fada nata dakin ko ba'a fada mata ba tasan kayanta zata hado. Kamar bata so haka ta fara takawa zuwa inda Inna take cike da fargabar abinda za tayi mata. A qasa daga dan gefe da ita ta zauna tana sadda kanta qasa don ko fuskar Inna bata son gani don babu wani rahama a fuskar nata.
"Zanyi muku sassauci guda daya Nuratu." Da sauri ta kalli Inna da mamaki don this is not what she expected.
"Eh shima darajar Audu zaku ci Allah dai ya jiqansa kawai don nasan ya mutu wallahi wannan dadewa haka" sai ta fara matsar kwallar karya tana jan hanci. Nuri dai dauke kanta tayi daga kallonta without saying anything.
"Gida dai na riga da na siyar dashi Nuratu, karewa ma kudin na kashesu gaba daya..." Sai ta dan dakata tana sake karewa Nurin kallo kamin ta dora da "kije ki fadawa waccan uwar taki..."
Da dan qarfi Nuri ta runtse idonta tana jin zafin yadda tayi addressing Maminta. "Ku dawo gidana da zama amman da sharadin...." Shiru Innar ta sake tana sake tunanin abinda take shirin yin kuwa anya zata samu karuwa, don itafa idan ba zata karu ba sam ba za tayi abu ba.
"Sharadin shine kuzo ku kama haya a daya dakin da yake gidana wanda babu kowa aciki!"
Da wani irin madaukakin mamaki Nuri ta dago ta kalli Inna she was like what the hell, wacce irin mata ce Inna? Su din fa jininta ne amman look at how she was treating them. A bayan babu mahaifinsu bata kasance mai taimaka musu ba sai kuntata musu. Maganar ringing kawai yake akan Nuri da mamaki sosai. Haya! Agidan Inna. Gidan da mahaifinsu ne ya siyeshi duk kuwa da Innar ya bawa. Ya Rabbi, yau ta gama tabbatar d ba qaramin rashi suka yi ba.
"Idan ba zaku iya biya ba kuma gaskiya ku nemi wani wurin kawai." Ahankali Nuri ta miqe ba tare da ta sake kallon Innar ba ta juya ta shiga dakin Mami. Tarar da ita tayi ta fito da kayanta duka tana hadawa a akwati cikin sauri wasu ma cusasu kawai takeyi. Kallon Nuri data shigo Mami tayi, da kamar ta dauke kanta amman yanayin data shigo da wannan sanyin fiye da asalin nata data santa dashi yasa ta tsaya tana binta da idanu har ta karaso inda Mamin take a tsaye.
Fadawa jikin Mami kawai Nuri tayi tana fashewa da kuka sosai har da shessheqa. Patting bayanta Mami ta fara yi without asking her abinda Inna tace da ita, ta bata lokaci har zuwa sanda tayi shiru don kanta. Zaunar da ita agefen gado Mami tayi tana zama agefe da ita "me tace dake Nuriyya?"
Ajiyar zuciya Nuri ta sauke "Wai zata bamu hayar dakin nan na gidanta da yake rufe." Shiru Mami tayi tana rasa abin cewa har fin minti biyar. Sai da Nuri ta dago ta kalleta sannan ta riqe hannunta tana cewa "ya zamu yi Nuri?"
Kai ta girgiza mata tana cewa "the say is with you Mami." Wani shirun Mami ta sake yi kamin ta dago Nuri data kwantar da kanta ajinkinta tana cewa "i think yadda tace din zamuyi Nuri. Kama haya da tsada agarin nan, ni ba wani kudi nake dashi mai yawa ba."
"Ni wallahi muje wani wurin bana son gidan Inna." Kai Mami ta girgiza tana cewa "Nuri wannan kamar shine mafitar da muke da ita. By next week zaki koma makaranta to da wanne kike so naji fisabilillahi..." Tausayin Mami Nuri taji kawai tayi shiru amman billah bata son zama gidan Inna.
Miqewa Mami tayi tana cewa da ita "karasa hadamin kayan ina zuwa." Da kallo Nuri tabi Mamin har ta fice before ta miqe ta fara hada mata kayan accordingly.
A zaune yadda Nuri ta bar Inna haka Mami ta fito ta tarar da ita. Wurinta ta nufa kanta a kasa taje ta zauna akasa tana dagowa ta kalleta "Inna mun yadda!"
Murmushin gefen baki Inna tayi irin ai dama ta sani basu da wani option rather than this. Tana hura hanci tace da ita "yo ai shikenan ku hada kayan naku kozo mu koma tare" Kai Mami ta gyada mata tana cewa "nawa zamu ke baki to Inna?"
"Uhmmmm...." Sai tayi shiru tana tunanin nawa zata saka musu tasan Mami na sana'a yanzu hakan yasa tace "Ku bada dubu 70 kawai duk wata!!!!"
Da sauri Mami ta dago tana kallon Inna, dubu saba'in as in how! "Inna beyi yawa ba?"
"Ke babu dole Bintu, zuciyar musuluncin nan ba dole, an fasa tausaya mukun ku san inda dare yayi muku kawai." Da sauri Mami tace "kiyi haquru Inna zamu biya, amman don Allah ki bari sai zuwa wani watan...."
"Abun da bazaiyu ba kenan Bintu....zaku zauna zaku biya...baku biya ba babu zama shikenan."
"Inna kudin ne.."
"Kina sana'a Bintu."
"Zan baki rabi to sai na cika miki." Nan ma kai Inna ta girgiza tana cewa "ke bafa zan yadda ba yawwa." Shiru Mami tayi tana lissafa sauran kudin dake wurinta da baifi dubu hamsin ba. "Don Allah Inna in baki rabi, bamu da abinci siya muke kinga..."
Wani Dan banzan kallo Inna tayi mata tana cewa "wannan ke ya shafa Bintu." Miqewa Mami tayi ta juya zata shiga dakin nata Inna tace "ku kawo rabin amman wallahi ki tabbatr wani watan kin hadamin da ragowar wannan dana sabon wata." Kai kawai Mami ta gyada mata tana shigewa dakinta ta tarar da Nuri ta kwanta akan gadonta bayan ta kammala hada mata kayan. Alokacin Mami ji tayi kamar ta daki Nuri, just look at yadda ta wani kwanta bayan ko nata kayan bata hada ba dana Afif kuma sarai tasan halin Inna. Bata kulata ba kawai ta fita ta nufi dakin nata da kanta ta hado mata dukkan kayanta a nata akwatin sannan ta shiga dakin Afif ta tattare masa nasa shima a nasa akwatin daban ta fito dasu. Sauran abubuwan amfaninta tadan tattara tana kallon Inna tace "fridge din Inna har shi kika siyar?"
"Kin bada kudi kin siya ne?" Kai Mami ta girgiza tana yi mata shiru kawai ta shiga kitchen 'yan abubuwan data san dole zata buqata na amfani ta diba wanda tasan ta siya da kudinta da Abba yake bata every month ciki harda tukunya da kurfetu da wasu kitchen appliances din duk ta zuba a buhu. Da kallo Inna ta bita dashi sanda take fito dasu, da har za tayi mata magana sai kuma ta fasa tayi mata shiru kawai.
Dakinta Mami ta sake komawa making sure ta dauki duk wani abu da yake da amfani awurinta sannan ta kalli Nuri dake kwance kamar ma barci ya dauketa. Takaici ya sake kule Mami that makes her beat Nuri this time. A firgice Nuri ta farka tana sosa inda Mami ta daketa fuskarta kamar za tayi kuka. "You're somehow stupid Nuriyya, you're really sleeping after all what we're facing?"
Shiru tayi ba ta iya cewa komai ba tana kallon Mami na harararta amman tayi kaman bata gani ba ta miqe tsaye da nufin fita ta hada nata kayan.
"Kije ki fito da akwatinki dana Biyayyenki na hada muku kayan." Kai kawai ta gyada tana fita da wannan tafiyar nata mai kama da bata son taka kasa. Kayan nasu ta jawo ta kawo bakin kofa tana turo baki gaba ita a dole Inna bata kyauta musu ba. Bata jima ba Mami ta fito sanye cikin dogon hijabi blue black daya haska farar fatarta.
"Bani mukullin gidan." Miqa mata Mami tayi without saying anything taja gefe ta tsaya Inna ta kare mata kallo tsaf don kyau Mami akwai kyau ita kawai asalinta da ba'a sani ba shine damuwarta. Ita kuwa ba zata so ta hada jini da mara asali ba, ko da yake ta dade da hada jinin dasu.
"Muje ko?" Ta fada musu tana nufar hanyar waje, hijab dinta wine dake jikin kofa kawai ta zaro tana zurawa ta riga Mami fita tana jan akwatunan har waje daya bayan daya Mami ta tayata da kwaso sauran shirgin nasu.
Suna fita Inna ta hau rufe kofofin gidan tsaf har na can gate din. "To ku muje, ko kinga Nuratu samo wani almajirin ya dauki kayan nan don akwai yawa ba iyawa zakuyi ba da wannan dan jikin." Ba tayi mata musu ba sanin ba iyawar zata yi ba. Bata sha wahala ba ta samu wasu yaran maqotansu suka kama musu kayan har bakin gidan Inna da baya da nisa da nasu gidan.
Da kallo Nuri tabi layin su Innar ganin wani katon tamfatsetsen gini daya kusa cin rabin layin ta opposite din su Inna da akeyi, lokacin da suka zo ita da Afif babu ginin sai filin kawai. Tun kamin a kammala ginin ya mugun daukar hankalinta don yadda aka tsarashi is worth watching ga ma'aikata nan sanye da kayan construction da aka rubuta NOVEBUILD LTD a baya suna ta hada-hadar aikinsu.
Daya bayan daya suka shigar da kayan nasu bayan Inna ta bude gidan nata ta bawa Nuri keyn dakin da yake daga farkon soron gidan. Kana wuce soron gidan shi zaka fara tararwa, yana nan baida wani girma na azo a gani. Adalci daya data yi musu shine ta basu wata tsohuwar katifar da Salama tayi amfani da ita kamin bikinta tace su saka a dakin. Duk wannan abinda take Nuri takewa magana babu ruwanta da Mami, itama Mamin bata damu ba. Aganin Mami Innan ma tayi musu mutunci for the first time don har kayan da zasu gyara dakin duk ta basu kamin ta kada kai tayi ficewarta.
Shiga dakin suka yi da yake nan cike da kura, bin dakin da kallo Mami tayi tana tuna lokacin da aka kaita gidan Abba, daga ita sai Baba talatu da wasu munafukan refugee camp dinsu. Gyara dakin suka hauyi duk kuwa da ba karamin gyara yake da buqata ba amman haka nan suka gyara shi tsaf throughout har yamma sallar Asr kawai ya tsayar dasu. Sun maidashi ya koma tsaf daidai rayuwarsu ga katifar da Inna ta basu shimfide can karshen dakin da wani bedsheet mai kyau gefe sun jera akwatunansu da sauran kayansu na sawa sai daya side din Mami ta jera small kayan kitchen din data debo, dakin ya matse sosai amman akwai space din da mutum uku zasu iya zama ba tare da sun matsu ba.
Tagumi Nuri tayi tana kallon yadda Mami ke shirya kayan abincinsu da suka auno yau shima duk acan gefen dakin wani kusurwa ta maidashi kamar kitchen haka komai na amfanin girkin data debo anan ta ajiyeshi. Yadda suka gyara dakin sai yayi tsaf duk da yayi lacking kayan da kowanne daki ya dace ace yana dashi don ko lalube babu haka suka bar kofar da tagogin don ma lokacin zafi ne amman bazasu rasa sauro ba.
Dakin kawai Nuri take karewa kallo tana kallon yadda Inna ta maidasu babu shiri, akan kudi fa ita Inna mai yin komai ce. Burinta kudi, tana son kudi sosai da sosai. Kallonta Mami tayi tana zama agefe da ita without talking tasan dole yanzu za tayi tunani kala kala aranta. Ya kamata ace Inna ta barsu sun shirya a tsanake kamin su dawo nan din. Yanzu zata bata rabun kudin da tace zai zamar mata saura 15 thousand, aciki zata siyo musu wasu kayan amfanin. Tunanin Mami shine yadda zata yi da sana'arta, bata da hanyar samun kudi yanzu!!!
#like
#share
#comment