Free chapter · Read without an account
FIRE AND ACID
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
UMMI'S POV
Abinda take gudun shine ya faru don washegarin ranar da Suhana ta tafi aka kirata daga cult group dinsu. Jikinta yana bari haka ta shirya ta tafi zuciyarta cike da tsoron me za'a ce mata kuma. Har ta isa bata da wani nutsuwar zuciya don hankalinta a mugun tashe yake.
Tafiyar 1hr tayi kamin ta isa wani katon wuri more like a company that manufactures things, sun bude companyn ne saboda gudun saka musu ido wanda a zahiri sai mutum ya dauka yawan wa'anda suke shiga wurin ma'aikata ne sai dai abin ba haka yake ba.
Red kimono ta daura akan atamphar jikinta tayi rolling da red metallic veil sannan ta fito ta nufi katon flat din dake wurin like a storey building. Jiki yana bari haka ta shiga tasan akwai mutane da yawa sosai don ta fahimci kamar akwai wani shima da bai cika Bonefather's will ba hakan yana nufin su biyu ne zasu fuskanci hukunci sai dai natan yafi nashi coz she's always not fulfilling what she was asked to do, to abu ne bana Allah da manzonsa ba.
Ba sallama a rule din shiga katon dakin da suke taruwa don haka kai tsaye shiga tayi. Dan tsayawa tayi tana binsu da kallo ganin sun zagaye wannan black idol din da aka shafe da red paint. Kasa tayi da kanta ta samu wuri acan karshen dakin ta zauna ba tare data dago kanta ba. Babu wanda ya kulata don dukansu were making some enchantations known to them. For more than 15mins suna abu daya sannan suka kammala.
Lokaci daya hall din ya dauki wani irin shiru kamar ba shine yake cike da hayaniyar enchantations dinsu ba. Hatta motsin kirki babu wanda yayi kowa yana a position din daya zauna tun zuwansa duk kuwa dacewa da yawa sun gaji suna son canza zama amman hakan bai cikin rules dinsu. Bonefather ya dago wannan mummunar baqar fuskar nasa yana bin kowa da kallo daya bayan daya har zuwa kan Ummi da wani Labaran dake gefenta. Su biyun yake kallo, idan ya kalli wannan sai ya koma ya kalli wannan. Da alama su biyun basu cika will din kingiya ba.
"Labaran.." wanda aka kira da labaran ya sake dukar da kai qasa without answering don babu hali "hukuncinka shine kaje ka samo matar data taba yin aure ka aura wadda take da yara kuma, wannan shine last favour din da zamu iya yi maka, idan kayi hakan dukiyarka zai dawo" Sai ya koma kallon Ummi yana yamutse wannan fuskar nasa da kallonta kawai tashin hankali ne.
"Zuhra Mamman..." Bata dago kanta ba saima rusunar dashi data sakeyi cikin zallar ladabi wa shugaban kungiyar. "Wannan shine karo na uku da kika saba umarnin kungiya...." Gumi ne ya fara tsatssafowa Ummi gashi bata da halin gogewa duk kuwa dacewa akwai Aircons a kowanne kusurwa na hall din, kawai she is afraid of the kind of punishment they will give her "zaki ga sakamakon kin bamu jinin da muka buqata..." Baki yana rawa ta bude za tayi magana ya daka mata tsawa yana cewa "don't talk, keep mute, whatever you will say will not be accepted or tolerated. You can leave..." Ya karashe yana nuna mata hanya.
Babu yadda ta iya haka ta miqe a dole ta fita tana share zufar daya bata mata fuska. Tana fita waje ta sauke katuwar ajiyar zuciya mai cike da damuwa. Damuwarta shine wanne kalar hukunci zasuyi mata, sun mugun iya hukunta mutum hardai ya saba umarnin kungiya. Fatanta kawai kada su taba mata dukiyarta don tana bala'in ji da kudinta. Motarta ta shiga ta fara driving a hankali tana tunanin me zai faru yanzu ahaka ta karasa gida. Tana yin horn kira yana shigowa wayarta, picking kiran tayi ganing manager din boutique dinta ne yake kira. Da wannan banzan shan qamshin ita a dole ga CEO ta amsa wayar. Cikin tashin hankali manager yake sanar da ita "madam there was a fire a boutique diu and it was serious, mun kira fire service sunzo amman har yanzu taqi mutuwa almost half of the mall was burnt....."
"Hauka ma kenan manager you're fired..." At 360 ta juya motar nata ta fara zuba uban gudu har ta isa surutai take na zallar rashin hankali kamar sabo ma. Tana shiga street din mall din ta fara hango yadda wuta take ci ganga-ganga gaba daya wurin ya turnuqe da hayaqi yayi baqiqqirin. Parking tayi daga can nesa ta fito mayafin kanta yana zamewa amman bata damu ba ta karasa ahakan, ashe daga nesa ba taga komai ba don shagon nata ya gama konewa kurmus harda wasu mutum biyu da suke da karan kwana. Her heart and brain hadn't finished assimilating abinda ya faru ta yanke jiki ta fadi, da sauri akayi kanta ana kiran "hajiya, hajiya hajiya..." Ammn ina Ummi tayi nisa haka aka kinkimeta gata ba ta wasa ba aka sakata a motarta aka nufi Novecare Clinic da ita, don shine a kusa....
FU'ADS POV
He was rounding off all his schedules at the Abuja branch don he wants to visit the site in Kano, yana so yaga yadda construction din yake tafiya duk da yasan workers dinsa are almost the best team, sun mugun sanin kan aikinsu.
Yana so yaje yayi handing over project din wurinsa wa minister of environment don haka ya dauki briefcase dinsa suka fita tare da Ahad, suna tafiya Ahad yana sake briefing dinsa kan construction din bridge din da akeyi a Cameroon wnda kamfaninsu ne yake yi and the bridge was 100% going to be the best a Cameroon. Har suka fita waje abinda Ahad yake fada masa kenan, a mota daya zasuje don haka suka nufi motar Fu'ad din, guards dinshi sun taso ya dakatar dasu yace suyi zamansu tunda ga Ahad.
Ahad da kansa ya bude masa back seat wai ya zauna Fu'ad ya banka masa harara yana bude front seat zai shiga wayarsa ya fara ringing. Zaro wayar yayi daga aljihunsa ganin Fa'iz yasa bai wani jira ba yayi picking "pal can't live without hearing from me..."
"Pal Ummi aka kawo asibiti, she was at the emergency!!"
"What!!! asibiti? Wanne asibitin? Meya sameta?"
"Novecare pal, I really don't know what has happened exactly, she was unconscious..."
"I will be there right away.." ya katse wayar yana kallon Ahad dake kallonsa yace "you take the car, ka kai masa project din Ahad Ummina ce aka kai asibiti I have to be there." Kai Ahad ya gyada masa yana cewa "Allah ya bata lafiya sir.."
Kai kawai Fu'ad ya gyada masa yana nufar site din da motocinsa ne kawai awurin without waste of time guards dinsa suka rufa masa baya this time around babu wanda yayiwa musu ya shiga back seat suka fice daga NoveBuild.
Ahad ya rufa musu baya sai dai kowa yayi taking separate way dinsa. Ministry of environment Ahad ya wuce kai tsaye kasancewar ansan da zuwansa bai sha wahala ba ya damqa saqon wa minista sannan ya fito. Kansa a qasa ya nufi motar Fu'ad kirar mercedes maybach ya bude zai shiga yaji anyi masa sallama, bai gama dago fuskarsa ba yaji an watsa masa wani abu a fuska daya sakashi sakin ihu yana durqushewa kamin security su qaraso waren culprit din ya tsere a mugun guje, this was already planned. Wurin Ahad suka nufa da yake kusan a kwance akasa yana surutai marasa kan gado numfashinsa kaman yana shirin daukewa, he was just saying "ya shiga uku fuskarsa, idonsa, hancinsa..." Ataqaice dai komai na fuskarsa.
Security din farko daya samu ya cire hannun Ahad din daya danne fuskarsa dashi baya ya koma da sauri yana cewa "Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakeel..." Don fuskar Ahad dai ya tashi daga aiki, komai ya zagwanye, hatta idonsa ya tabu sosai ga fatar duk ya salube ba kyan gani dai. Daukarsa suka yi suka wuce dashi mota bayan anyi informing din minister. Tare da minister aka nufi national hospital da Ahad da kamin su karasa ya sume musu kamar ba rai a tare dashi.
Minister sai kiran wayar Fu'ad yake amman sam baya dauka shi kansa condition din da yaga Ahad aciki ya mugun tsoratashi it was something da bai taba gani ba. Kai tsaye emergency aka wuce da Ahad, likitoci kusan biyar suka tsaya a tare dashi, nurses are just roaming in and out duk don a ceto bawan Allah Ahad. After good three hours suka fito a time din minister yana zaune ya kasa tafiya kawai abin ya mugun tsoratashi musamman daya kasance a ministry dinsa komai ya faru da Ahad din.
Ministan likita guda daya ya nufa yana cewa "sir are you his family?" Kai kawai ya girgiza masa yana cewa "we need them here sir.."
"What is it doctor, just tell me I can do the needful, what has happened to him?"
"Someone used concentrated hydrosulphuric acid on his face. His face and his hands were damaged especially his face. He will never see again sir because it seems ya shigar masa idonsa..."
Miqewa tsaye minister yayi yana salati "Ya Rabbil Aalameen, yanzu meye abinyi babu yadda za'ayi."
"Actually no sir, sai dai ko plastic surgery wanda ba'a yi anan. Munyi dressing fuskar da hannun nasa kawai, shima hannun taba fuskar nasa da yayi ne acid din ya shafa that's why, amman sir ya kamata akama whoever was behind this scene. Wallahi abin was very critical, he was unconscious ma mun kaishi can ICU don he was not responding..."
Kai kawai minister ya jinjina masa yana kallon PA dinsa yace ya sake trying number din Fu'ad don shi baisan yadda za'a samu family din Ahad ba.
FU'ADS POV
Kamin su karasa sai daya ji kamar yayi tsunstuwa haka ya tashi don kamar wurin ya danyi nesa dasu haka. Already he was informed about the fire daya tashi a shagon Ummi yasan wannan shine dalilin daya saka tayi passing out. Ana parking bai jira abude masa ba ya fita da dan sauri amman cike da nustuwa ya karasa cikin asibitin.
A reception ya hadu da Fa'iz daya sauko ya bawa receptionist din saqo. Kallon Fu'ad yayi yana cewa "pal, alhamdulillah Ummi has gained consciousness, she's awake."
Ajiyar zuciya a fili Fu'ad ya sauke yana cewa "Alhamdulillah, Shukran Yah Rabbi. Muje na ganta." Riqeshi Fa'iz yayi yana cewa "she was crying tunda ta tashi pal, gobaran ya tabata da yawa...." Kai kawai Fu'ad ya gyada suna nufar can amenity ward, tun kamin su shiga dakin da Ummi take ya jiyo muryarta tana ihu tana surutai "na shiga uku, shagona, wayyo Allah na, me yasa ya qone duka. Me yasa sai akaina hakan zata faru bayan ga mutane masu shaguna da yawa...." Cak Fu'ad ya tsaya jin kalar surutan da Ummi takeyi wanda suke sabo da rashin tawakkali. Yana shiga Ummi ta miqo masa hannu, ya miqa hannunsa aka kirashi.
Kamar zai share kiran haka kawai yaji zuciyarsa yana dan bugawa da sauri don haka ya damqe hannun Ummi yana daga kiran minister.
Without any formalities aka sanar dashi someone used an acid on Ahad's face. Sakin hannun Ummi yayi lokaci daya yana cewa "acid? On Ahad's face? Kun kaishi asibiti ne?" Aka bashi amsa daga can side din.
Cire wayar yayi daga kunnensa yana kallon Fa'iz yace "Fa'iz, Ahad, wani ya zuba mishi acid a fuska, wai fuskarsa yayi dameji gaba daya..."
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un..."
"Take care of Ummi Fa'iz, I have to be there, inaso na gansa and I will sue whoever is behind this!!!!"
To be continued.....
#like
#share
#comment