Free chapter · Read without an account
AHAD
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
Bai buqatar kowa ya tuqashi hakan yasa ya amsa mukullin mota a wurin driver dinsa ya shiga da sauri ya tada motar ya fita daga clinic din. Hankalinsa gaba daya yayi wurin Ahad da halin da aka ce yana ciki. Tafiyar 30mins yayi ta in 15mins saboda tsabar gudun da yake yi na wuce sa'a. Ko daya je asibitin ma wrong parking yayi ya fito da sassarfa ya wuce ciki ta wurin A&E yana zuwa ya tarar da minister da muqarrabansa daman shi suke jira zasu tafi. Kamin ya qarasa wajensu suka karaso inda yake.
"How is he sir?" Ya tambayi minister hankalinsa akansa.
"His condition was critical Fu'ad, he was moved back to ICU he wasn't responding to treatment...."
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un..." Gaba kawai yayi yana tambayar nurses din da ya gani a wurin suma duk a tsaitsaye. Sallama yayi musu suka bishi da kallo irin na kurillar nan kafin suka amsa masa. Likitan dake kula da Ahad ya tambaya suka nuna masa office dinsa without waste of time ya wuce office dinsa.
Da sallama ya shiga ya tarar da likitan a zaune yayi shiru yana kallon papers hankalinsa sam baya wurin, shine head a wurin and case din Ahad ya mugun kashe masa jiki. Har yanzu ya kasa yadda akwai marasa imanin da zasu iya using concentrated acid ajikin mutum.
"Sir." Fu'ad yayi calling attention dinsa ganin he was taken away.
Da sauri ya kalli Fu'ad sai ya miqe tsaye in respect for the great NoveBuild Ltd CEO. Hannu Fu'ad ya miqa masa yana cewa "I'm his family, I mean the acid victim.."
Tashi tsaye likitan yayi da sauri ya zagayo yana cewa "alhamdulillah you're here, and before I proceed, don Allah you have power and the money, Ka kwato masa haqqinsa don Allah."
His words broke Fu'ad's heart, Kai kawai ya gyada masa yana cewa "can I see him?"
"Actually no sir, I don't know if you can withstand what you will see, even though his faced was bandaged, but I'm sorry to say, he can't see at all, his eyes were damaged completely together with his face."
Zama Fu'ad kawai yayi a kujerar dake kusa dashi yana salati a fili. His heart was full of questions "waye yayi wa Ahad haka?" He was like me yasa ma ya turashi shi kadai.
"Do me a favour please doctor, I want to see him?" Ya shaqu da Ahad sosai to the extent that yake daukansa dan uwa fiye da yadda yake jin Azzam aranshi.
Shiru likitan yayi shi baya so aganshi ne saboda duk mai tausayi zai shiga wani hali, idan mutum mai saurin kuka ne ma da wuri zai fara kuka. Kallon Fu'ad da yake kallonsa yayi ya fahimci jarumi ne to amman bai san yadda zaiyi ba idan yaga Ahad duk kuwa da cewa fuskarsa was sealed with bandage.
"Ok sir, let's go." Miqewa Fu'ad yayi yana zaro wayarshi yayi dialing number din maman Ahad. Har ya fara ringing yayi saurin katsewa aranshi yana jin he can't be the first person to inform her this bad news, her one and only son, dan da shi kadai ya rage mata don Ahad tun kamin a haifeshi Abbansa ya rasu. Mamansa ce tayi fadi tashin rayuwa don kula dashi duk da akwai masu taimaka mata daga dangi but she suffered alone for her son, yayi government boarding school har zuwa candy kamin ya samu scholarship a Harvard uni USA. Da yaje can bai zauna ba ya hada karatu da aiki yake turowa mamansa kudi don ta dena wahala amman bata dena ba. Tayi wankau, tayi aikin girki duk saboda Ahad.
Allah ya taimakeshi ya fito da good result he then applied for work a NoveBuild da aka bude a shekarar, his dedication yasa har Fu'ad ya zabeshi as his PA. And gradually suka fara shaquwa ya zama bayan Fa'iz babu wani wanda yake tare da Fu'ad yasan sirrinsa like Ahad, har ya kaisu ga kulla zumunci da gidansu. Don Fu'ad yakan ziyarci Maman Ahad time to time and itama tana mugun son Fu'ad don yana taimaka mata duk kuwa da danta was no more poor, Ahad was rich though not like Fu'ad but he was on his own way.
Kallon doctor din yayi yana cewa "can you inform his mother please, I can't tell her." Kai doctor din ya gyada masa yana amsar wayar Fu'ad da yake miqo masa ya kira Maman Ahad. Bugu biyu ganin Fu'ad ne yasa tayi picking da far'arta kana ji "dana Fu'ad."
"Ina yini Mama, ba Fu'ad bane, daga national hospital nake kira, idan babu damuwa kizo please...." Miqewa Mama tayi da sauri tana cewa "me ya samu Fu'ad din? Kar kace wani abun ya sameshi."
Zamewa Fu'ad yayi ya sake zama akan kujera, irin kara da kirkin Mama is different, she was not like his Ummi ya dade da fahimta. Just look at yadda hankalinta ya tashi daga kawai an kirata da number din Fu'ad ta zata wani abun ne ya samu Fu'ad, to idan tasan danta ne ya gamu da his lifetime injury ya zata yi kenan? Kallon Fu'ad likita yayi yana cewa "kuyi haquri, addu'a zaku riqa yi masa, Allah ya bashi ikon cinye jarabawarsa."
Kai kawai Fu'ad ya gyada yana sake miqewa suka fita. ICU suka nufa bayan an bashi sterilised clothes na shiga ICU ya saka sannan ya shiga shi kadai.
Idonsa ya sauka kan Ahad dake lying flat his face facing upward, ya kalli e-line dinsa dake running slowly tabbacin bugun zuciyarsa ma ahankali yake tafiya, ya sake kallon ruwan da ake kara masa kafin finally ya dubi fuskarsa.
Kasa cigaba da tafiya yayi yana maimata Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un aransa kawai. If you guys zaku ga Ahad at that condition you can cry for him idan kana da saurin kuka. Duk da ba'a ganin fuskar nasa daya tashi daga aiki, kawai yadda aka nade fuskarsa da bandeji ma wani sabon tashin hankali ne ga spot din jini yayi staining some parts of the bandage duk da anyi treating dinsa amman he was a little bit bleeding ahankali.
Kamar mai ciwon kafa haka ya taka zuwa inda yake yana sauke idonsa akan tafin hannunsa da shima yake daure da bandage din duka biyun. Zuciyarsa alokacin ta gama karyewa ya rinqa jin kamar duk laifinsa ne daya tura Ahad wurin. He was feeling the guilt concise as if he was the one that do it or behind it.
Just 3mins akace yayi hakan yasa time din nayi ya fito yana zare kayan daya dorawa kayansa jikinsa duk yayi sanyi. Ahad ya tashi daga Ahad din daya sani. Bayan yayi disposing kayan ya fito daga ward din ya samu wuri kawai ya zauna yana zaro wayarsa.
Kasancewarsa mai kudi yana da mugun connection da mutane masu mulki da muqami a kasar hakan yasa kai tsaye ya kira IG wanda yasanshi adalilin Abiensa.
Bai sameshi a kiran farko ba sai na biyu. He was glad daya dauka hakan yasa yayi masa sallama a nuste yana gaisheshi don abokin Abie ne duk da shima nasa matsayin ya jawo masa connection mai karfi da manyan masu fada aji na kasar baki daya.
"Fu'ad."
"Yes sir, barka da yamma."
"Barka Fu'ad, ya aiki?"
"Alhamdulillah sir, i want to file a case to you sir."
"Which case Fu'ad..."
"Someone used an acid on my PA, he was in a critical condition now, please sir do me a favour, just assigned one of your units let them traced down whoever was behind it please sir."
"Stop begging Fu'ad, the case has already went viral, I have seen it on social media. We will In Sha Allah find the real culprit.
"Thank you sir, thank you so much sir."
"Thank me not Fu'ad, is my duty that's just it."
"Ok sir."
"Take care Fu'ad sai anjima."
Sauke ajiyar zuciya Fu'ad yayi yanajin idan ba'a kama wanda yake da alhakin cutar da Ahad ba kamar hankalinsa ba zai taba kwanciya ba. Zallar rashin Imani kawai ya gani anyi using wa Ahad.
Yana nan zaune ya hango Mama da sauri ya miqe yana jin kamar ya fice daga ward din he can't face Mama bayan shine ya tura danta inda aka cutar dashi to amman shi kadai yake da alhakin sanar da ita abinda ya faru.
Wurin Fu'ad da tun kamin ta karaso ya sadda kansa kasa Mama tazo. Wani ajiyar zuciya yaji ta sauke tana cewa "hankalina ya tashi Fu'ad da akace nazo asibiti... Lafiya amman?"
Kai ya girgiza mata yana cewa "ki zauna mama."
"Ka fara sanar dani abinda yake faruwa tukunna sai na zauna, ina abokinka?" She asked at the right time...
Sai daya yayi ta maza sosai kamin yace "shine baida lafiya." He can vividly saw yadda hankalin Mama ya tashi, tana son Ahad dinta.
"Me ya sameshi Fu'ad."
"Sit down Mama please"
"Mene ya samu Ahad don Allah Fu'ad?"
Bai iya amsa mata ba sai dauke kansa da yayi "Fu'ad kodai Ahad ya mutu ne?"
Da sauri ya girgiza mata kai yana cewa "no Mama, Ahad was alive..."
"Alhamdulillah" ta fara fada kamin ta sake cewa "duk halin da yake ciki bayan mutuwa ne Fu'ad, ka fadan ko mene kuwa zan iya dauka, ni musulma ce wadda tayi imani da qaddara mai kyau ko mara kyau, zan jure komai Fu'ad."
Wallahi Mama ta sake karya Fu'ad, like ta gama yadda koma mene tun kamin ta san mene.
"Mama wani ne ya zuba masa acid a fuska."
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un" kawai ta riqa maimatawa tana zama at same time gumi yana tsatssafo mata har sannan bata daina maimaita Inna Ilaihi Wa Inna Ilaihi Raje'un ba.
Tsugunnawa Fu'ad yayi agabanta yana riqo hannunta tare da ita suka cigaba da maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raje'un just to let her back from the shock she was in. Sai data dawo daidai sosai ta fara jin wata nutsuwa from nowhere tana jin dauriya sosai ta kalli Fu'ad "zan iya ganinsa?"
Ganin Ahad will completely let her down, she will not take it yasan don haka ya girgiza mata kai yana cewa "no Mama, yana ICU."
Kai ta gyada masa tana cewa "Allah ya bashi lafiya."
Kallonta ya sakeyin ahankali yace "Mama Ahad bazai sake gani ba!!!!"
"Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni Khairan Minha..." Ta riqa maimatawa this time around.
"Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawar" ta sake fada Fu'ad yana amsa mata. Bai barta ba throughout har akayi Maghrib duk kuwa da yana so yaje wurin Ummi amman case din Ummi mai sauqi ne compared to case din Ahad.
"Kije kiyi sallah mama, zanyi magana idan akwai abinda za'a iya yi masa ko a canza masa asibiti kawai akwai wanda yafi wannan sosai.
Kai kawai Mama ta gyadawa Fu'ad tana kiran wasu daga cikin 'yan uwanta dana mahaifin Ahad ta sanar dasu duk kuwa da basa kusa suna Kano ne, Ahad ya dawo da ita nan tare da 'yar qanwarta Zannira.
Sai daya rakata har inda za tayi sallah sannan shima ya wuce yayi alwala yabi jam'i. Bayan sun idar baija doguwar addu'a ba ya fito ya sake komawa yayi magana da likita yana so suyi kokarinsu koya canzawa Ahad asibiti kawai. Sun bashi assurance zasuyi duk mai kokarinsu akansa sannan ya dawo wurin Mama. Anan ya tarar da Zannira ta qaraso fuskarta yayi ja alamar tayi kuka don ba kowa ne zaiyi withstanding din jin halin da Ahad yake ba sai mai taurin zuciya irin na Mama da Fu'ad.
He was there with them har bayan Isha sannan yace wa Mama suzo ya maidasu ya gida ya biya akula da Ahad din sosai tunda ba ganinsa za'a iya yi ba.
Da kyar ya shawo kansu suka yadda da kansa ya kaisu gida bayan ya sake kwantar musu da hankali.
Lokacin da yake driving back zuwa gida don ya samu info an mayar da Ummi gida zuciyarsa yana gaya masa cewa duk wanda yake da hannu acikin abinda akayiwa Ahad for sure zaisa ayi masa hukunci sak irin wanda akayiwa Ahad!!!!!
#like
#share
#comment