Free chapter · Read without an account

NEW BEGINNINGS 2

by Saddiqah M · NURI

NURI


By Saddiqa 


NURI'S POV 

Rayuwa agidan Inna sam babu dadi, komai suke idonta akansa. Bata taimaka musu da komai amman kullum cikin roqonsu take. Dan abincin nasu duka idan suka dafa sai tace su zuba mata. Hatta ruwa wannan sai dai su nemo nasu basu isa suyi mata amfani da nata ba. Ga yawan zagin Mami da takeyi akan asalinta. 

Kullum Nuri kuka take akan hakan, she keeps on saying su bar gidan Inna kawai su tafi wani wurin ita. While Mami tana ganin zama gidan Inna shine mafitar da suke da ita. Bata da kudin da zata iya kama musu wurin zama. 'Yar sana'arta ma yanzu babu sai kame kame da take. Ta samu da sauran 10k din wurinta ta siyo waken suya ta fara saida awara agidan da safe da dare, cikin ikon Allah sai gashi ana siya don dama akusa dai babu mai saida irinsu awarar.

Ga ma'aikata suma duk suna aikowa siya, 'yan makaranta da sauran 'yan unguwa. In no time Allah ya buda mata ta samu ninkin kudin data saka. Nuri tun tana mita har ta dena ganin Allah ya budawa Mamin sosai. Wannan kudi da Inna taga tana samu yasa ta kara matsa musu kullum cikin bani-bani take.

Yau Nuri zata koma mkrnta hakan yasa ta shirya da wuri ta taya Mami dan abinda zata iya ta debo mata ruwan a wani borehole da masu ginin wannan companyn suka bude don mutane da yawa da basa samun ruwan anan suke diba. 


Bayan ta gama diba ta shige wanka already ta gyara gidan gaba dayansa don yanzu hatta dakin Inna ita ke gyarawa. Marabarta da 'yar aiki kadan ne agidan nan. Aunty Zakiyya bata nan tayiwa Inna qaryar ta samu aiki a wurin kwana which is a total lie. Hakan yasa suke dan samun sauqi don Zakiyya kamar tafi Inna takura da masifa.

Cikin wani plain material cream colour ta shirya tayi rolling da black chantilly veil ta rataya jakar makarantarta a kafada jikinta yana tashin qamshin humra mai dadi. Sallama taje tayiwa Mami da mutane masu siyan awara suka zagayeta. Daga bakin soro take saidawa don tace ita bazata iya fita waje tanayi ba. Qulla mata awaran Mami tayi ta bata tana mata addu'a tare da jaddada mata kula da kanta.

Fita tayi tana dan rage girman wannan manyan idanun nata saboda rana data haske mata su. Ahankali ta fara tafiya har ta qaraso bakin titi da yake basu da nisa dashi. Wannan qaton ginin da akeyi a farkon layin tabi da kallo. Qaton gini mai mugun girma iya ganinka, although har yanzu da saura kamin agama amman she doesn't know why tun ayanzu kamin a kammala ya mugun haduwa har takejin ko na waye wannan ya iya zaben yadda za'a iya masa gini.

Dauke kanta tayi tana tsaida napep ta fada masa inda zai kaita tana tunanin for the first time za taje mkrnta without Zara her best. She's in 300lvl now, don haka sun koma AKTH acan zasu ke yin lectures sun gama da preclinical yanzu. Sun dade sosai kamin su isa don akwai mugun nisa sosai.


Idan tace bata ji dadin mkrnta ba yau ba tayi qarya ba. Wuni kusan guda a makaranta gashi babu wani interval da zasu huta. Sannan babu Zara wadda ita kadai ce kawarta, she's doing her school life ita kadai yanzu. Allah ya taimeketa yanzu sun rabu da Khaleel.

Sai after 4 ta dawo gida ahakan ma akwai lecture guda daya da basuyi ba. Agajiye ta shiga gidan ta tarar da Mami tana yanka awara mai uban yawa. Kallo ta bi Mami dashi, sati daya kawai amman taga Mami ta sauya, farin fatar Mami duk ya ragu, ta fara yin baqi ga wahala sosai ya fara bayyana a tare da ita. 

Sallama tayi tana shiga ta ajiye jakarta agefe da Mami tana amsar wuqar hannun Mami tace "kawo Mami je ki huta kinji."

Kai Mami ta girgiza mata tana cewa "je ga ruwa can da yayi saura ki hada kiyi wanka, kinyi sallah?" 

Kai ta gyadawa Mami tana cewa "Mami nasan baki huta ba ki kawo."

Kai Mami ta sake girgiza mata tana cewa "a'a Nuriyya, akwai aikin debo ruwan dake jiranki gidan sam babu ruwa..."

Idan akwai abinda Nuri tafi tsana shine debo ruwan nan, yafi ci mata rai fiye da aikin gidan. Mami ta samo almajiri da zai riqa diban ruwan amman basu da mutunci hakan yasa ta rabu dasu dole Nuri ke debowa.

Ciki ta shiga ta ajiye jakarta tana ware mayafinta ta zuro hijab kawai ta fita ta dauki bokiti. Kallonta Mami tayi tana cewa "ba zakiyi wankan ba?"

"Bara na fara debo ruwan." Kallonta Mami tayi har zuwa sanda ta fita. Aduk kalar rayuwar da suke yi yanzu tafi tausayin Nuri. Yarinyar data taso cikin gata da kulawar jajirtaccen uba, rayuwa ya juya musu baya yanzu. Mami kullum cikin addu'ar Allah ya sauqaqa musu qaddararsu take yi. 


Kullum suna waya da Afif amman ko da wasa basu taba fada masa halin da suke ciki ba, suna saka ran kamin ya dawo da yaddar Allah komai ya zama labari.

Nuri na fita ta nufi can wajen famfon da ake dibar ruwan wanda baya da nisa da wannan sabon ginin da akeyi, gashi akwai layi haka ta ajiye nata bokitin akan layi sannan ta koma ta sake dauko wasu ta sakasu suma a layi. Bayan wani lokaci layin yazo kanta sai data tara duk kayan ruwan data dauko sannan ta fara diba daya bayan daya ahankali tana kaiwa gida don Mami ta hanata cikowa da yawa tace take diba ahankali ita mace ce. Sai da tayi sahu hudu sannan ta cika komai na gidan agajiye ta zauna agefen Mami dake hura wutar gawayi. Kallonta Mami tayi tana cewa sannu. 


"Ina Inna Mami?"

"Kinsanta da fita, bansan ina tayi ba tun safe." Kai kawai Nuri ta gyada tana tashi ta daukowa Mami duk abubuwan da take amfani dasu kafin taje tayi alwala don yanzu za'a yi kiran sallahr kamin ta idar da alwalar ma anyo kira. Tare da Mami suka yi sallar Magariba. Suna idarwa Mami ta fita ta fara suya don mutane da yawa sun taru suna jira. 


Bata dade ba Nuri ta fita ta amsheta dole ta bata ita kuma ta dora musu girkin dare. Suna haka Inna ta dawo, da wani kalar kallo tabisu ba tare da tace komai ba. Don tasan dai tana qaruwa sosai da wannan sana'ar and ita kanta Mami wannan tafi kawo mata kudi akan waccan da takeyi. Sai dai wannan tafi wahala sosai nesa ba kusa ba. 

Around 10 suka gama and gaba daya babu wadda yayi saura duk an siye suka gyara gidan a wannan daren sukayi wanka sannan sukayi sallahr Isha. Nuri ta dauki abincin Inna ta kai mata don yanzu dai Inna ta dena girki sai wanda suka bata kuma idan baiyi mata ba hakan bazai hana ta zagesu tas ba. Kawai dai ita ba'a iya mata.

Wannan stage din shine another phase of their life da basu taba kawowa ransu ba ko a mafarki ba. Mami sam bata hutawa kullum cikin aiki takeyi ga zama gaban wuta duk ya kodar da ita. Jikinta har ya fara canzawa daga yadda yake duk gayunta ya tashi babu shi. She's overworking duk saboda ta samu ta tara kudin mkrntr Nuri but still bai kai mata yadda take so ba. Ga kudin hayan da Inna ke binsu kusan kullum sai ta tuna musu kudin nan. Ga siyan kayan abinci da sauran abubuwan amfani na yau da kullum. Ko yaushe cikin lissafi take, is like karfinta yana shirin fara karewa. Wahala duk ta sauya ta. Ko yaushe cikin tunani take yi abubuwan duk sunyi mata yawa.

Nuri ma yanzu bata da lokacin kanta sam, tun kamin asuba take tashi ta fara gyara dakinsu tsaf sanda zata gama anyi kiran sallah sai tayi sallah. Tana idarwa zata fita tayi wanke wanke ta gama tayi sharar gidan kaf dinsa ta wanke bandaki. Sai kuma ta tafi diban ruwa wanda shine yake cinye mata lokaci zata gama dab da bakwai tayi wanka ta shirya sama sama taci abinci Mami ta kulla mata awara ta tafi da ita makaranta. Idan taje makarantar ma sam babu hutu ga rana duk akansu take karewa, sam basa hutawa. Gradually Nuri ta fara canzawa, wannan kyan nata rana ta fara gusar dashi, baqinta ya sake qaruwa don ita dama ba fara ce ba. Rashin samun isasshen lokacin da zata ci abinci yasa lokaci daya tayi wata rama dama ita ba jiki ba duk ta zabge sai idanu kawai. 


Rayuwar ya mugun sauya musu fiye da yadda suke tunani, ta yadda basu zata ba. Kansu kawai suke dashi sai Allah. Inna banda kara musu pressure kan wanda suke dashi babu abinda take yi. Zuwa yanzu sun fara sabawa da yadda rayuwar ta sauya musu ko nace ma sun saba gabaki daya. Basu da lokacin hutu sam, basa gama abinda suke arana kullum sai wajen sha daya da rabi na dare, a wannan lokacin Nuri zata dauko wayarta ta fara karatu, tana farawa sai bacci karatun sam baya yuyuwa don haka ta dena. It has started to affect her academical studies, don hatta a makaranta yanzu ba komai take kashewa ba. Abubuwa sunyi wa kwakwalwarta da jikinta yawa sosai at her age tana yin abinda maza masu qarfi ya dace suyi especially wannan diban ruwan da takeyi duk ya fara taba mata kashinta. Hannunta ko yaushe cikin ciwo da kafarta amman bata taba fadawa Mami ba, haka kirjinta da takejin yana budewa shima ko yaushe ciwo yake mata. And she started developing ulcer as a result of bata wani nustuwa taci ta koshi saboda makaranta. 


Ulcer bai fara nunawa ba sai wata rana ta dawo daga makaranta. Tun a makaranta dama takejin wani azababben ciwon ciki haka dai ta daure har ta karaso gida. Tana zuwa ta zube agaban Mami tana riqe cikinta. Hankalin Mami a tashe tayo kanta tana tambayarta lafiya sai dai sam ta kasa magana cikinta kawai take nunawa Mami. Taimaka mata Mami tayi suka shiga daki ta canza mata kaya zuwa masu sauqi sannan ta fita ta samo mai napep yazo ya dauketa suka nufi wani karamin pharmacy dake dan gaba dasu. Suna zuwa ya fara duba Nuri ya tabbatarwa Mami yunwa ce ta kamata. Bata cin isasshen abinci hakan ya jawo mata ulcer.


Mami tried hard kar tayi kuka zuciyarta kamar zai fashe da tausayin Nuri. Ya basu magunguna yana sake jaddadawa Mami akula da abincinta sannan ya hanata cin wasu abubuwan.

Suna dawowa gida Mami ta hada mata ruwa tayi wanka ta zauna ta sata agaba sai data ci abinci. Ranar Mami ba tayi awara ba ta zauna kula da Nuri, ita tayi duk aikin da Nuri take yi hatta da diban ruwa kuwa ranar ita ce ta debo. Washegari Nuri bata je makaranta ba sannan Mami ta hanata aikk sam sai itace tayi komai ranar plus awararta na siyarwa. Inna sam bata nuna ta fahimci Nuri babu lafiya ba banda ma kudi data zo ta ara masu dan yawa awurin Mami wai zata dawo mata dasu. 


Mami tasan ba zata dawo dasu ba don haka bata saka rai ba, dama ta ware ragowar kudin hayarta idan ta dawo zata bata don haka ta zare dubu goman da innar ta ara acikin kudinta.....

To be continued....

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.