Free chapter 路 Read without an account

THE DEAL

by Saddiqah M 路 NURI

NURI


By Saddiqa


Da wani irin sauri ta dago kanta sai dai tana hada idanu da Bonefather ta sadda kanta kasa. Bata gane Fu'ad bazaiyi aure a rayuwarsa ba.

"Duk lokacin da yayi aure kuwa ina mai tabbatar miki ko mai zai fara lalace miki ne daga lokacin, zaki rasa komai, asirinki zai tonu. Kowa zai san asalin wace ke alokacin. Don haka kiyi duk mai yuyuwa ki hana shi aure. Babu Fu'ad babu aure Zuhra!!!!"

Gumi ne yake tsatssafo mata daga kowanne gaba na jikinta. Yadda take son Fu'ad bata son wani tawaya ko daya a tare dashi, rashin aure kam a wurinta tawaya ne. Ita da take son komai na Fu'ad ya zama na daban taya burinta zai cika idan baiyi aure ba. Ta riga da tayi masa tanadi idan yayi aure taya hakan zai faru?

A ajiye wannan aside, asirinta zai tonu, komai nata zai qare, kowa zai san asalinta yafi komai tsayawa aranta. Yadda take son ganinta a sama sam bazata so hakan ya faru ba. 

"Kin yarda Zuhra Mamman?" Wannan shine ake kira da tsaka mai wuya a wurin Ummi. Idan bata yarda ba tasan ita da kudi, suna, farinjini har abada amman idan ta yadda zata samu har fiye dasu. To amman taya zata hana shalelenta aure? Shine abinda yake ci mata zuciya.


Bakinta yana rawa ta furta "na...na..na yarda!!" And that is it, she agreed to the deal da bata san shine asalin abinda zai rusata ba har qarshen rayuwarta. Deal din da ba iya dukiya kawai zata rasa ba hatta wasu gaskiya da abubuwan da akayisu a sirri zasu bayyana kansu. Lokacin da zuciyoyi biyu suke shirin haduwa lokacin ne aka kulla deal din da ba zasu kasance tare ba. 

They we're forbidden to be together tun kamin su hadu!! (This is just the beginning of NURI, wannan duka sharar fage ne, the real story yana gaba just follow Saddiqa's pen to see how everything will reveal, I promise you a heart captivating love that will stick to your heart guys 馃挴 many mysteries, sacrifices and hardship are yet to begin)

NURI'S POV 

Sun gama sabawa da sabuwar rayuwar da suke ciki, cin mutuncin Inna ne kawai har yanzu Nuri take jinsa sabo a wurinta, duk sanda zata zagi Maminta sai taji kamar ranar ta fara. Sunyi nisa a makaranta, still Mami was struggling ta hada kudin registration dinta wanda sam yaqi haduwa, Inna taqi barin kudin ya taru, kullum cikin karba take da taji bata da kudi, ka rasa me takeyi da kudi. Idan Mami ta hanata kudin ta riqa yi mata barazanar korarta dole ta bata. Komai ya fara isar Mami kawai tana daurewa saboda Nuri da Afif dake Munich da har yanzu bai san halin da suke ciki ba.

Qarfe daya da rabi na rana Mami ta kammala komai na sana'arta na safe harta girkin rana ta gama don tana dan buqatar hutu shi yasa take kammala komai da wuri don haka ta samu ta kwanta ko zata samu bacci. Kwanciyarta ba dadewa aka shigo gidan ana sallama da wata qatuwar murya. Bata motsa ba sanin ba wurinta aka zo ba sai ma gyara kwanciyarta da tayi.

Rabe ne da suka sai gidansu Nuri yazo, wurin Inna yazo hakan yasa kai tsaye ya fada cikin gidan yana kiran "Laure... Laure kina nan kuwa." Daga ciki Inna dake cin soyayyen kawai ta turashi qasan gado tana goge maiqon bakinta da hannunta jikin kayan dake jikinta, don hajiya Inna fa akwai rowa jama'a. 

"Waye anan." Ta fada tana hararar kofar dakinta don ta tsani tana tsaka da cin dadinta tayi baqi. "Rabe ne." 

Miqewa tayi tana gyara daurin kallabinta ta leqa waje tana cewa "lafiya dai Rabe, ba mun gama abinda ya hadamu ba?"

Kai ya girgiza mata yana cewa "ai yanzu ne ma zamu fara abinda ya hadamu Laure, samuwa ce wadda tafi ta wancan karon." Tuni ta fito waje tana washe wannan haqoran da goro duk ya dafar dasu tana cewa "haba Rabe."

"Kinsan bana miki wasa ko?" Kai ta gyada masa tana cewa "hakane kuma, shigo daga ciki."

Dakinta suka shiga ya zauna akan wannan matacciyar tabarmar dake dakin nata yadda kasan bata amsar kudin jama'a.

"Yawwa Rabe ina jinka me ya faru?"

Ya gyara zamansa yana cewa "me yake shirin faruwa dai..."

Kai ta gyada da sauri tana cewa "fadamin dOn Allah Rabe wallahi har zumudi nake nason tabbas zan qaru fiye da da."

"Kwarai kuwa Laure...kinsan Alhaji Labaran?"

Shiru tayi tana tunani kamin can tace "yo ina zan sani Rabe."

"To wani attajirin mai kudi ne daya ke da mahaukatan kudi ina fada miki." Mutuniyarku taji kudi, don haka tuni ta sauko daga kan gadonta ta dawo kusa dashi tana yaqe haqora "don Allah Rabe, aiki za'a yi masa?"

Kai ya girgiza yana cewa b"a'a kina daga zaune zaki zama hajiya ina fada miki. Zaki tashi daga laure ki koma hajiya Laure." Zo kuga yadda take washe baki kamar gonar auduga taji kudi tun kamin tasan me za'a yi tace "wallahi na yadda Rabe." Daman ya sani ita ce wadda yafi sanin zatayi komai akan kudi.

Zamansa ya gyara yana cewa "matar aure yake nema.." tsaki Inna tayi tana cewa "aure kuma, ban gane ba."

"Matar aure yake nema wadda ta taba aure take da yara zai aura. Ya saka kudi naira miliyan dari duk wanda ya kawo masa matar zai bashi tare da kyautar gida da mota." Baya Inna tayi tana dafe kirji, miliyan dari. Kudin da ko a mafarki bata taba hasasowa kanta su ba. 
A rikice tace "ni ina zan samo masa irin wannan matar?" 

"Kaji Laure da rashin lissafi...ke da kike da kadara agidanki.."

Kudin ya gama ruda Inna da kanta ya kasa hasko mata abinda yake nufi "kadara Rabe?"
"Eh kwarai kuwa kadara Laure.."

"Kana sakani acikin duhu fa...Ka budemin komai a fili.."

"Ga matar danki nan, wannan farar balarabiyar mai kyau. Ai ina ganin faduwa tazo daidai da zama Laure?"

Shiru tayi tana tafiya tunani sam kanta bai kawo mata Mami yake nufi ba. Ta duba ta hasaso ta ko'ina fa ba zata bar damar miliyan dari ta wuceta ba, miliyan dari, gida da mota malam. Har ta hango yadda zata fantama, yadda zata tashi daga laure ta koma hajiya Laure. Haba tuni zuciyar Inna tayi amanna da wannan zancen babu wani tunani ta amincewa Rabe. Tanajin kamar lokacin talaucinta fa ya qare samuwarta tazo duk ta silar mara asali, yau rashin asali zaiyi mata rana. 

Ai dole mata yanzu ta fara lallaba Mami kodan ta samu ta shawo kanta. Shi Alhaji Labaran yace kawai a samo matar bai buqatar ganinta a fada masa zai bada komai da ake buqata na biki kawai akai masa matar baya buqatar komai. 


Kanta har wani rawa yake tana jin dole fa zata fantama anan gaba kawai she's imagining gata a katon gida tana juya kowa yadda take so. Banda murmushi babu abinda take zubawa. Da haka ta raka Rabe har kofar gida wanda yake sake zugata don tuni ya dena kiranta da Laure zalla, hajiya Laure yake kiranta. Har kofar gida ta rakashi suna taya junansu murna kawai sun hango kudi ya samu malam.


Da kallo tabi dakinsu Mami tana wani murmushi, sai takejin ba'a taba kawo mata labarin daya mugun yi mata dadi sama da wannan ba. Dakinta ta shige tana fito da farantin kwan da ta zira qasan gado ta cigaba da ci. Loma daya tayi taji ba dadi kamar dazu sai ta ture gefe tana cewa "babu dadi ma, inaga na dena ci gaskiya idan nayi kudi ai sai nama wannan bai fiya dadi ba." 


Sai can yamma Nuri ta dawo duk agajiye ga wata azababbiyar yunwar da takeji. Da kallo tabi gidan ganin yau Mami kamar bata aikin awararta. Shiga tayi da sallama tana ajiye jakarta. Dagowa Mami tayi daga kwanciyar da tayi tana kallon Nuri.

"Kin dawo Nuriyya..."

"Mami baki da lafiya ne?" Kai Mami ta girgiza mata tana cewa "lafiyata qlw, zo ki cire kayan kici abinci..." Ita dai bata yadda da Mami tana lafiya ba. Yanayinta ya gama nuna bata da lafiya, dole ta ajiye jakarta kawai ta cire kayan jikinta ganin magariba yasa ba za tayi wanka a lokacin ba sai bayan magaribar. Abinci ta zubo taci ba mai yawa ba tana sake lura da Mami dake mugun nuna dauriya ta ko'ina.

Miqewa tayi ta fita waje ta duba kayan ruwansu ganin suna da ruwa ba qaramin dadi taji ba don sam ta tsani diban ruwan nan da take yi. Gyara gidan ta sake yi tsaf tana gamawa tayi alwala ta shige dakinsu ko ta kan Inna ba tabi ba.

Tana shiga akayi kiran sallah, miqewa Mami tayi ta fita waje tayo nata alawalar.......



FU'ADS POV 


Yana zaune gaban system dinsa yana sake qarewa ginin da suke yi a kano kallo. Ya gama tsaruwa sosai kusan yafi sauran branch din duka kyau. Ba kowa ne ya tsara masa shi haka ba kuwa face Ahad. Kai kawai ya girgiza yana cewa "ashe ba zai ga what he designed ba..." Har yau zuciyarsa ya kasa mantawa da Ahad din. Indai yana aiki shi kawai yake tunawa don yawanci suna tare a office suna tsara wani abun.


Miqewa yayi yana jin he have to leave zuwa Kano. Is high time yaje can site din yaga komai in reality. Fita yayi zuwa flat din Ummi da yake nan shiru. Da kallo yabi yadda yake nan a gyare sai tashin kamshi mai dadi kawai yake, murmushi kadan ya subuce masa. Yana son kamshi irin sosai dinnan don zaka iya yaudararsa da kamshi da tsafta. Abinda yake kara masa son Umminsa kuwa harda kamshi.


Sama zuwa dakinta ya wuce. A zaune ya tarar da ita kan gado ta rafka uban tagumi. Tun lokacin da ta amince da buqatar Bonefather take cikin zullumi. Sai take ganin kamar ta tauyewa Fu'ad haqqinsa. Kamar ta rageshi ta wani wurin. Kalmar rashin auren nan ta mugun tsaya mata a rai. Abu daya kawai ta sani ta amince bazai yi aure ba har abada a rayuwarsa there's no going back.


"Ummina..." Da sauri ta dago tana kallonsa, ta karewa kyakkyawar fuskarsa kallo tsaf, ta tabbatar akwai matan da suke sonsa a yanzu, ko baya kulasu yanzu there's possibility of nan gaba zai fara kulawa har ma yaji urge din yana son yayi aure don haka zata fara masa addu'a kar ya hadu da wata ya sota.


"Hayaty.." a kasa ya zauna yana cewa "me kike tunani Ummi? Ba dai boutique dinki ba? Nasa an fara gina miki sabo fa..."

Kai ta girgiza masa tana cewa "a'a kawai rayuwar nake tunawa Hayaty, yadda abokinka ya rasu, yana tafe ashe kwana ya qare.."

Dan kallonta yayi yana jin me ya fara nutsar da ita don a yadda yasan Ummi bata kaunar mutuwa yasan ba zata taba dawowa daidai kan wannan tsanar ba kuwa.

Kai ya jinjina yana cewa "kowa ma dan can ne Ummi, duk ita muke jira...."


"Dan dakata da zancen nan Fu'ad...." Murmushi yayi kawai yana girgiza kansa.


"Ummi ina Azzam ya shige kwana biyu ko na kirashi fa baya dauka."

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin Azzam kam anyi asarar haihuwa. Har tayi rashin lafiya ta warke bai zo ya dubata ba sam in fact babu wanda yasan ma baya Abuja ya wuce Ibadan wajen wata karuwarsa.

"Ban sani ba Hayaty nima wayarsa baya shiga." Shiru kawai yayi yana jin ido zai fara saka masa kawai shi da yake so ya nustu ya dawo hanya yaga kamar sake baci abin nasa take.


"Ummi zanje Kano gobe in Allah y kaimu!!!"

Da sauri ta kalleshi tana jin wani iri, bawai bai saba tafiya ba, a'a ita yanzu tun bayan deal din nan tafi so ya kasance tare da ita kar taje yayi wata tafiyar yaje ya hadu da wata wadda zai ji yana so!!!!!!!!


To be continued....

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.