Free chapter · Read without an account

SOMETHING IS COMING.....

by Saddiqah M · NURI

NURI


By Saddiqa


Jin shirun Ummi yasa Fu'ad dagowa yana kallonta ganin shi take kallo sai ya komar da kansa kasa yana jiran abinda za tace "Hayaty nikam shekarunka nawa ne ma?"  

Yasan ba mantawa tayi ba akwai dalilin da yasa tayi masa wannan tambayar don haka ya bude baki ya bata amsa da wannan muryar nasa da yake nan da amo kadan ba mai zurfi ba yace "29."

Kai Ummi ta gyada tana kallonsa still tace "you're almost 30 Hayaty but you’re so quiet.." tana so ta bugi cikinsa ne taji ko akwai wata aransa duk kuwa da tasan sarai babu.  

Kansa bai kawo masa abinda take nufi ba don haka ya girgiza mata kai saying "i didn't really get what you're saying Ummi."  

"I mean Hayaty when are you going to settle down? shekarunka sun fara ja, banji kana zancen wata ba let alone thinking about marriage..." Sadda kansa kasa yayi sosai yana dan sosa keyarsa yace "ummm Ummi ai..ai babu ko wacce da nake kulawa ne.."  

Ta gyada kai ahankali tana cewa "kamar ma baka shirin hakan ko?" Shiru yayi bai bata amsa ba, shirun nasa shine amsar don haka Ummi tace "it's okay, take your time. ni zan zaba maka wacce zata dace da kai when the time comes. just focus on your future Hayaty, Ka kula da kanka nasan mata basa gabanka don haka babu ruwanka da ko wacce mace. akwai tanadin da nayi maka kaji ko?" Da kai ya amsa mata yana cewa "zanje na gaida Ammi Ummi..." Da ace yana kallon fuskarta yayi maganar babu abinda zai hanashi ganin yadda annurin fuskar Ummi ya dauke nan take daga ambatar Ammi da yayi.  

"Me zaka yi acan kuma?" Dagowa yayi ya kalli Ummi yana jin tambayar nata wani iri. Me zaiyi a wurin Ammi? Qanwar Umminsa dake sonsa. Matar da yakejin wani strong affection idan yana tare da ita fiye da wanda yakeji idan yana tare da Umminsa.  

"Zanje nayi mata sallama ne tunda gobe zan tafi idan Allah ya kaimu" banza tayi da shi tana dauke kanta daga side din da yake tayi kamar ba taji abinda yace ba har sai daya maimaita "sai ka dawo..." Shine kawai abinda tace masa wanda ya sakashi yin shiru. Ba haka Ummi ta saba amsa masa ba, bama haka ta saba yi masa addu'a ba, then what's the reason behind this? Bai sani ba.  

Miqewa yayi bayan ya sake yi mata sallama ta amsa masa kamar yadda tayi yanzu ya fita. Bai wani sa zuciyarsa cikin tunani ba ya wuce direct zuwa wata arniyar motarsa kirar Tesla wadda take fara mai tint glass. Shi zaiyi driving don dama ya saba hakan hardai fita na radin kansa ne yafi so yaga shine yake tuqi da kansa.  

Ahankali yayi tukin har zuwa gidan Ammi dake guzape. Da kallo yabi parking lot din gidan ya tabbatar Pal dinsa yana gidan, ajiyar zuciya ya sauke yana kashe motar ya fita. Hasken rana dake shirin faduwa ya haske masa fuskarsa dake glowing haka kaman wata mace, wannan baqin sajen nasa da yake kara masa kyau ya kwanta luf a fuskarsa. Dan rage girman manyan idanunsa dake da mugun haske yayi yana takawa zuwa cikin gidan.  

Da sallama a bakinsa ya shiga parlourn Ammi. Safa da Fa'iz suna zaune dab da juna suna kallon abu a iPad din Safa din hankalinsu gaba daya yana kai har basuji sallamar da Fu'ad din yayi ba. Zama yayi shima yana kallonsu ba tare da ya katse musu abinda suke yi ba ya zaro wayarshi ya fara dannawa hankali kwance.  

Ammi ce ta fito daga kitchen bayan ta kammalawa Abbie girkinsa na dare don haka take duk rintsi ita keyi masa girki. Da kallo tabi Fu'ad wanda ta dauka Fa'iz ne da farko. Tsaf ta kare masa kallo tun daga shigar jikinsa na wani plain blue black exclusive yard da akayiwa dinkin half jumper daya bala'in yiwa masa kyau, shigar native attires yana mugun yi masa kyau ammn bai fiya yi ba. Ko yayi ma is hard ka ganshi da hula don bai fiya sonta ba ya fiso ya bar sumarshi mai uban yawa hka nan.  

Fa'iz Ammi ta kalla ta sake tabbatar da lallai suna mugun kama, the only difference is Fu'ad yafi Fa'iz haske shine kawai amman komai nasu sak iri daya. Kai ta jinjina tana sake girmama ikon Allah aranta.  

"Fu'ad yaushe kazo.?" Da sauri Fu'ad ya dago kansa daga danna wayar da yake ya kalli Ammi dake daga dan nesa dasu kadan sanye cikin wata super wax da akyima dinkin T-bubu. Safa da Fa'iz suka dago suma suna kallon Fu'ad da sai yanzu suka lura dashi.  

Kamin ya amsa Safa ta riga da cewa "Laaa yaushe ka shigo wai?" Ammi ya bawa amsa da "just now Ammi, suna ta danna waya ko kallona ma basuyi ba..." Ya kare maganarsa da sigar shagwaba zalla yana kallonsu. Murmushi Ammi tayi tana karasowa ta zauna a kujerar dake opposite to Fu'ad "rabu dasu kaji son, yayyen kwabo ne ai." Murmushi yayi yana zamewa kasa ya gaida Ammi cike da girmamawa mai tarin yawa irin wadda yake mata don yadda yake jin Ammi aransa is like yadda yake jin Umminsa ne arai, yana ganin ko don su biyun twins ne kamar shi yasa yake mugun son Ammi.  

"Pal we're sorry plz.." Fa'iz ya fada yana hade hannayensa biyu waje daya. Harar wasa kawai Fu'ad yayi masa yana gaida Safa data girmesu da kusan shekara uku. "Pal manaa..ni zakayu ignoring ina maka magana?"  

"You didn't even notice my arrival too pal." Murmushi Safa tayi tana damqawa Fa'iz din iPad din nata tace "kunfi kusa kukam bara na hau sama." Amsa yayi yana cewa "ok, pal how far?"  

Dawowa kusa dashi Fu'ad yayi yana zama yace "alhamdulillah pal sai stress kadan.."  

Ammi ce ta amsa masa da "the way you're overworking Fu'ad ai dole, ka riqa sassautawa please." Kai ya gyada yana cewa "Ammi yanzu dole sai na qara maida hankali a kamfani, da akwai Ahad amman yanzu babu shi.." duk sai sukayi shiru kowa yasan kalar muhimmancin da Ahad yake dashi awurin Fu'ad especially bayan daya rasu.  

"Allah ya jiqansa da Rahma." Ammi tayi masa addu'a tana cewa "me zan kawo maka son?" Kai ya girgiza yana cewa "daga gida nake ai, bana jin yunwa."  

Ya jima sosai a zaune anan suna hira da Fa'iz har Safa ta sauko kasa ta dawo cikinsu akayi hirar da ita while Ammi na gefe tana saka baki kadan kadan.  

"Ammi I'm leaving to Kano Tomorrow In Sha Allah." Dagowa tayi tana kallon Fu'ad dake kallonta. Murmushi tayi masa wanda yake nan sak irin nasa. "Allah ya kaimu Fu'ad, Allah ya bada sa'a ya kiyaye hanya."  

Har cikin jikinsa haka yaji addu'ar, gadai addu'ar very short amman tayi masa 100%. Umminsa ba tayi masa ba sai ma wani zance na daban da tayi masa. Ture tunanin daga ransa yayi yana kallon Fa'iz da yake tambayarsa me zaije yi Kano kuma. "Zanje new site din can ne, ban taba zuwa ba tunda aka fara gininsa har gashi an kusa kammalawa and ina son naje na gaida Maman Ahad." Don Maman Ahad tuni ta koma Kano tunda wanda take Abuja donshi baya nan.  

"Allah ya sanya alkhairi Fu'ad." Adda Safa tayi masa addu'a tana daga kwance tana danna waya. Da Aameen ya amsa yana cewa Fa'iz "ko zaka rakani?"  

Kai ya girgiza masa da sauri yana cewa "ah adawo lafiya yallabai Allah ya tsare hanya." Harararsa yayi, Fa'iz sam baya son yake nesa da gida, idan ka cire karatun da yaje yayi a india da ya rabashi da gida for almost 10yrs babu inda yake son zuwa har dai ba umarah haka ko hajji ba.  

"Kasan dai inada patients da yawa anan ko?"  

"Ko baka da patients ma ba rakani zakayi ba nasani." Kai ya gyada masa yana cewa "Thank God you know kake tambayata, nifa kawai na ganni gani ga Ammi shine kawai."  

Safa ta kalleshi tana cewa "kuma dole ka bar wa Ammi gida ba."  

"Naje ina?" Zaune Safa ta miqe tana cewa "Ammi wannan yaran fa sai kinyi musu fada naga ma fa kamar babu wadda suke kulawa dukansu bare ma mu saka ran biki nan kusa." 

 
Waya Fu'ad ya fara dannawa don karma aja zancen da nisa dashi. "Komai ai lokacine Safa, zaki gani hala ma tare za'a yi bikin nasu."  

Fa'iz yayi murmushi yana cewa "Ammi amsar nakin nan yayi daidai, da take zancen biki nan kusa indai ba Fu'ad ne zai zama macen ba ayi bikin ya za...."  

Wani kallo Fu'ad yayi masa ba tare da yace dashi komai ba hakan yasa yayi shiru yana gimtse dariyar dake ransa, Ammi da Safa suka dara abinsu ganin yadda yayi shiru kamar yana jin tsoron Fu'ad haka.  


Har dare Fu'ad yana gidan, har Abbie ya dawo sukayi dinner tare sannan yayi musu sallama Abbie da Ammi suka sake yi masa addu'a. Tare da Safa da mijinta yazo ɗaukanta suka fito. Fu'ad yana cewa "nikam dama gidan nan yazo ya gina muku gida, ke kullum kina gida.."  

"Sai ka bashi shawara ai..." Ta fada tana yin gaba ta sake cewa "wataqila kaima hakan zakayi idan naka lokacin yazo ko yaushe tana gidansu..."  

"Ashe ma ba aurenta nayi ba.." ya bata amsa daidai suna karasowa wajen mijinta mai suna Ansar suka gaisa. Ba wani dadewa da sukayi kowa ya kama nasa hanyar tafiyar.  

NURI'S POV  

Tana zaune ta saka wayarta agaba ita bata yadda ba karatu take za suyi zazzafar test gobe. Sai dai as usual wannan gajiyar tana shirin rinjayarta kamar kullum tasa mata bacci.  

Miqewa tayi ta fita tsakar gida duk da cewa dare yayi wajen sha daya haka ta shimfida darduma ta zauna awajen duk don kar tayi bacci ta cigaba da karatun daga inda ta tsaya. Allah ya taimaketa ta kai har sha biyu tana karatun sauro yaqi barin barci ya dauketa. Duhun dare ya sakata miqewa ta koma ciki ta dora daga inda ta tsaya sai dai bata dade ba barci barawo ya saceta.  

WASHEGARI  

Hakanan ta tashi bata da wani kuzari, jikinta kamar wadda akayiwa dukan tsiya duk ciwo yake mata. Haka dole ita tayi aikin gidan kaf yadda ta saba ta kuma debo ruwan da bata kauna. Mami tana hada-hadar abincin safe da awararta. Wanka tayi ta shirya cikin wani plain material ta saka hijabi onion colour daya mugun yi mata kyau ta fito tsaf tana tashin kamshin khumrar Mami data saka. Abinci Mami ta zuba mata ta amsa ta koma dakinsu ta zauna taci don masu siyan awara already har sun fara zuwa. Tana kammalawa ta miqe ta fitar da kwanon ta goge bakinta ta sake gyara fuskarta ta dauki jakarta tayiwa Mami sallama ta fita tana addu'a.  

Garin yau babu rana sosai ko da yake safiya ce around 7:30 haka. Miqar hanya tayi har zuwa bakin titi. Kamar kullum yauma ta sake samin kanta da karewa wannan ginin kallo. She don't know why kawai ginin yana mugun burgeta tun kamin a kammala shi. An mugun baje basira wajen tsara ginin da ko waye ya kalli ginin sai yaji ya tafi dashi tun yana incomplete .

Napep ta tare sukayi ciniki ta hau. Ta sake maida kallonta kan ginin da masu ginashi tuni sun fara zuwa.  

Ahankali bugun zuciyarta ya fara sauyawa wanda ya sakata nutsuwa tana saurarar yadda take bugawa har tana iya ji. Ta rufe idonta tana addu'a aranta don bata tabajin kalar wannan bugun daga zuciyarta ba. Har suka karasa makaranta kuma bata daina ba hakan yasa ta fara jin ko akwai wani abin da yake shirin faruwa ne da ita..... 
 

To be continued.... 

 
#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.