Free chapter 路 Read without an account

WHEN HEARTS STALLED

by Saddiqah M 路 NURI

NURI 


By Saddiqa 
Da sauri Nuri ta miqe tsaye tana salati tayi wajen Mami hankali tashe. "Mami... Mami... Mami...." Ta riqa maimaita sunan Mami da already tayi passing out. Dago kan Mamin tayi ta dora kan cinyarta tana cigaba da kiran sunanta.

Hayaniyar yadda take kiran sunan Mami ne ya jawo hankalin Inna dake daki. Ta leqo da niyyar daka mata tsawa sai dai ganin halin da Mami ke ciki ya dan sakata dakatawa tana binsu da kallo.  Fitowa tayi wajen da suke ta tsaya akan Nuri saying "lafiya dai Nuriyya?"
Nuri data fara kuka already ta girgiza kai tana miqewa tsaye tace "she passed out.."

"Ke kika san wannan kuma ni ina zan san me kike cewa da wannan yaren yahudu da nasaran ...." Nuri bata kulata ba taje ta samo ruwa a kofi tazo ta shafa a fuskar Mami da har sannan take akwance. Bata motsa ba sam hakan ya sake tadawa Nuri hankali ta wuce wajen kayanta ta zaro mayafi ta yafawa kanta da yake nan babu dankwali ta fito da sauri zata fita Inna tace "ina kuma zaki je Nuriyya waye zai kular miki da ita?" Ko kulata ba tayi ba tasa kai ta fita waje da sauri da niyyar samo napep ya kaisu asibiti.

FU'AD'S POV

Bai sha wahalar neman gidan Maman Ahad ba don yasan gidan ya taba zuwa sau biyu kuma ba wani wahala ne da unguwar ba. Time din da yaje Mama tana zaune kan kujera a tsakar gida tana daka yajin da zasu ci danwaken da Zannira keyi musu. Sallamar da Mama taji daga waje ya sakata tsayawa da dakan tana amsa sallamar tare da dorawa da "shigo." Hijab dinta dake tsakale kan taga ta jawo ta zurawa jikinta tana bin kofar gidan da kallo. 

Ganin Fu'ad ya sata miqewa tsaye tana sakin fuskarta sosai "lale lale, maraba da Fu'ad..." Murmushi yayi ganin yadda ganinsa kawai yasa Mama far'a zai tsugunna kasa ya gaisheta tayi saurin dakatar dashi tana cewa "a'a karka tsugunna ka bata kayanka mu shiga parlour sai muyi gaisuwar acan. " Still wannan kiler smile din nasa har yanzu yake yi suka shiga parlourn gidan dake madaidaici daidai su hudu dake zama agidan, bayan Mama da Zannira akwai wasu yaran qannen Maman namiji daya Jabir sai mace daya Ikram.

A kan carpet din dake dakin Fu'ad ya tsugunna duk kuwa da yadda Mama ke cewa ya zauna kan kujera.

"Barka da rana Mama an yini lafiya?" Da far'a sosai Mama ta amsa masa tana binsa da kallo . Ta tuna Ahad dinta da ko yaushe yake nan maqale cikin ranta. Zuciyarta ya raya mata da tuni yanzu har dashi sai hakan yayi breaking din Mama har muryarta yana yin rawa wajen amsa masa gaisuwar nasa .

Muryar Maman da yadda ta amsa gaisuwar nasa ya tabbatarwa da Fu'ad ta tuna Ahad ne don haka ya danyi shiru yana bata space kadan tayi calming kanta da kanta. Jin shirun yayi yawa ya sakashi dago kansa just to see Mama in tears.

"Subhanallah, Mama.... Ahad need our prayers... Nasan kina yi masa Mama... Kukan nan is of no use to him Mama please stop crying kinji..."

Hannu tasa tayi wiping tears din off but still wasu suna bin fuskarta. Da muryar kuka tace "Fu'ad kawai na tuna abokinka ne... Yadda kazo dinnan na tuna last zuwanku Kano tare.."

"Allah ya jiqansa da Rahama.."

"Aameen Yah Rabbi. Bara na kawo maka ruwa kamin a kammala abincin..."

"Ki barshi Mama ba sai kin tashi ba.."

"Haba a'a." Tana fadin haka ta miqe ta fita tana kiran Zannira "Zannira kizo ki gaida yayanki Fu'ad.." da to ta amsawa Mama daga kitchen kamin ta fito tana goge zufar dake goshinta ta shiga dakinta da yake gidan mai falle -falle ne. Hijab ta zunbula har qasa sannan ta fito ta nufi hanyar shiga parlourn. Sai da ta dan dakata ta saita kanta sosai sannan ta shiga dakin bakinta dauke da sallama.

Yana zaune ya tankwashe kafarsa bayansa jingine da kujerar da Mama ta tashi yana danna wayarsa. Ko da Zannira tayi sallamar bai dago kansa ba yana danna wayar ya amsa mata sallamar. Samun kanta da kare masa kallo tsaf tayi kamar ko yaushe idan dai zata ganshi tana yawan satar kallonsa. Shigarsa jikinsa ta mugun yi masa kyau sosai fiye da tunani. The way kansa yake kasa yasa sumar kansa dake da yawa da laushi rufe masa goshinsa har zuwa idonsa wanda hakan ya mugun sake kara mishi kyau.

Dauke kanta tayi da sauri gudun kada ya dago wannan idanun nasa da suke mugun kara masa kwarjini. Tsugunnawa tayi har kasa tana cewa "ina yini Yah Fu'ad, ya hanya.." 

Kallo daya tak ya dago kansa yayi mata wanda shima kusan inda take kawai ya kalla ya maida kansa kan wayarsa yana amsa mata tare da dorawa da "makaranta fa?" Ahankali yayi maganar da kai tsaye ta fahimci me yake nufi. 

"Nayi candy saura Jami'a."

"Allah ya bada sa'a.."
"Aameen."

Miqewa tayi ta juya ta fita da sauri. Tana fita ta sauke wata katuwar ajiyar zuciya tana shaqar iska da kyau aranta tana raya "ban taba ganin mutumin da yake da kwarjini irin nasa ba..." Kitchen ta karasa daidai Mama na shigowa tace da ita "Mama ina kika je? "

"Ashe ruwan firinjin ya kare shine na fito na siyo masa wani pure water din mai sanyi... Kiyi sauri ki karasa abincin ki zubo masa don Allah.. "

" To. " 

Mama na shiga ta ajiye masa ruwan tana cewa "yi haquri na barka kai kadai ko? "

Murmushi yayi yana ajiye wayarsa yace "babu komai ai... "

"Ga ruwan nan ka Sha. "

Dauka yayi yana yin Bismillah ya fasa ya fara sha ahankali cike da wannan tarin nutsuwar nasa dake mugun yi masa kyau. Bai wani sha da yawa ba ya ajiye kan farantin da aka doro masa ruwan yana duba agogon wayarsa daya nuna masa 3:15. Miqewa zaiyi Mama ta dakatar dashi tana cewa "tsaya fa, yanzu za'a kawo maka abincin nasan baka ci komai ba." Bai iya musu ko ja da mutane ba musamman manya don haka ya koma ya zauna. Yana zama Zannira ta shigo kanta akasa ta ajiye tray din data hado masa abincj ta juya ta fita.

Mama da kanta ta zuba masa danwaken da yaji kayan hadi ta tura masa gabansa tana cewa "Bismillah ko.." kallon abincin yayi a zuciyarsa yana tunanin yadda zai iya ci don sam baya sonshi. Dama Ummi ba gwanar yinsa bace Ammi ce keso to ko tayi shi da pal dinsa basa ci.

Fork din da aka ajiye masa ya dauka yayi bismillah ya juya kadan ya fara ci don bai son dorawa Mama wata wahalar yasan tana gane baya ci zata tashi nemo sabon abinci wanda shi kuma bata masa lokaci hakan zaiyi.

Gudu biyu kawai yaci yaji kamar zai dawo don haka ya ajiye fork din yana duba wayarsa yace "Mama jirana akeyi karna makara..."


"Aiho, ai baka fadamin ba Fu'ad. Amman dai zaka dawo kamin ka tafi ko mu rinqa zumunci ko bayan abokinka..."

Kai ya gyada mata yana cewa "In Sha Allah Mama..." Sannan ya miqe yana ajiye mata kudin da bai san adadinsu ba yayi mata sallama.

"Haba Fu'ad dawo ka dauke kudin nan, abin yayi yawa ai bayan dawainiyar mu daka dauka gaba daya." Bai juyo ba sam yasa kai ya fice hakan yasa Mama miqewa tabi bayansa sai dai kamar wanda yake saurin dagaske har ya fice daga gidan.

Yana fita driver dinsa ya bude masa back seat ya zauna. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin danwaken daya ci guda biyun nan kamar sun tsaya masa hakan yasa ya dauki bottle water dake gefensa ya bude ya sha da yawa har sai da yaji daidai sannan ajiye. 

Ganin driver ya dauki hanyar mayar dashi masaukinsa yasa shi saurin cewa "where going back to the site Siddiq.." "ok sir."

Sai bayan da suka dauki hanyar site din kuma zuciyarsa ta fara tambayrsa me zaiyi a site din bayan ya kammala komai na yau din. Shiru yayi yana nutsuwa jin yadda wannan tunanin kawai ya sauya masa rate din heartbeat dinsa daga asalin yadda yake. Shi kansa bai san me zai koma yi ba, ya daiji kamar akwai wani abu da yake son yaje ya gani ko yayi.

Da haka suka isa daidai ana kiran sallahr Asr hakan yasa yana fita ya wuce wurin famfo dake cikin site din ya daura alwala suka tafi masallaci tare da sauran masu aikin ginin. Bayan an idar yayi addu'a da azkar kadan ya miqe ya fito suna rufa masa baya....

___________

Da sauri-sauri gudu-gudu ta nufi bakin titi tana addu'ar Allah yasa ta samu napep da wuri. Bata dade da tsayawa ba Allah ya kawo wani sai dai basu daidaita ba. Kusan duk wanda zata tsayar basa wani daidaitawa, wasu kuma ciki ne ba zasu shiga ba. Tsayawa kawai tayi ganin na karshen ma ya tafi ya sakata fara hawaye tana sharewa. Har tayi niyyar juyawa sai ga wani mai napep din yazo ya tsaya agabanta. Da muryar kuka tayi masa bayani ya amsa da zai kaisu amman sai dai ta fito da Mami shi bazai shiga ba saboda ruwan dake kwance akan hanya na sama.

Babu yadda ta iya haka ta juya gida da niyyar fito da Mami duk da tana tunanin yadda zata dauko Mamin. Tana juyawa Fu'ad yana karasowa wajen ya dawo daga masallaci. Ba ita kadai ba, hatta shi sai da zuciyarsa ta sauya bugu da sauri wanda yasashi tsayawa yana kallonta. He noticed that itace ke sauya masa bugun zuciyarsa daga jiya zuwa yau. Ya ganeta tsaf in fact baya jin zai iya mantawa da yarinyar nan. Yarinyar da daga jiya zuwa yau kawai ta kasa barin zuciyarsa da kwakwalwarsa su huta daga tunaninta. Har ya fara tunanin anya ba mayya ce ba if not babu yadda za'a yi daga haduwa da mutum ya maqale maka azuciya idan ba maye bane馃槄

Dauke fuskarta tayi tana jin yadda zuciyarta take bugawa da karfi daga kallonsa kawai wanda shima bata kalli cikin idonsa ba. Ta gane shine na jiya, kuma tun ajiyan ta fahimci yana daga cikin sahun mazan dake da mugun kwarjini har ba zaka iya jurar kallon cikin idonsa ba kai tsaye.

Yauma kamar jiya hawaye ya gani afuskarta, it looks like hawayenta basu da wahalar zuwar mata ko kuma kukan ne baya yi mata wahala. Takawa ta cigaba dayi har tazo wucewa ta gefensa taji muryar mai napep ya kwalo mata kira yana cewa "baiwar Allah zan tafi fa, jirana ake nima ki dauko mara lafiyar mu tafi idan kuma na tafi ne to..?"


Kallonsa Fu'ad yayi, irin niggas dinnan masu shaye-shaye ne.  Kamar dai dazu, haka ya sake jin wani abun ya tsaye masa a wuya. Bai san kuma mene yake damunsa ba sannan ba tare da yayi shawara da zuciyarsa ba yace "ka tafi zan kaita asibitin.." wani kalar daga masa kafada yayi irin na 'yan zamanin nan yana cewa "tasan da kai ta batamin lokaci... " Kallonsu duka Nuri tayi za tayi magana Fu'ad ya rigata cewa "kayi haquri.." wucewa yayi jin an bashi haquri ita kuma ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya. 

Taya zaice zai kaisu asibitin bayan bata san wayeshi ba, shima bai san wace ita ba. "Where's the patient?" Taso yi masa musu tace ya tafi amman wannan kwarjinin nasa ya hanata musamman daya zuba mata wannan idanun nasa dake nan tubarkallah dasu. Sai kawai samun kanta tayi da nuna masa gidansu "jeki ku taho tare.." ba tare data kalleshi ba da wannan muryar nata da ko yaushe yake da sanyi mai dauke da shagwaba tace "she passed out, bazan iya daukanta ba.." 

Already idanunsa suna kan fuskarta tun dazu yana yi mata kallon da bai san dalilinsa ba, yadda tayi masa maganar yasashi dan dakatawa kadan before saying "let's go..." Tare suka jera sai dai suna tafiya da dan sauri har suka je gidan. "wani ya taimaka miki acikin gidan ku fito da ita lemme pick my car..." yana fadin haka ya dauko wayarsa ya kira driver dinsa a waya yana binta da kallo har ta shige cikin gidan. Tambayar kansa yayi "why is my heart stalled to her daga jiya zuwa yau, who is she?" 


To be continued.....


#like 
#comment
#share


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.