Free chapter · Read without an account

HIS UNSPOKEN CONCERN

by Saddiqah M · NURI

NURI


By Saddiqa


Da sauri ta shiga gidan nasu tana mantawa da yin sallama is like faduwar Mami da haduwa da Fu'ad ya rikitata.  A yadda ta barsu haka ta dawo ta tarar dasu Inna tsaye akan Mami tana binta da kallo. Mami ta nufa kai tsaye ta tsugunna tana riqo hannunta da niyyar dagota sai dai sam ba zata iya ba. Kallon Inna tayi da kalar tausayi kamar za tayi kuka tace "Inna ki kamamin ita mu fita da ita don Allah.."

Kai Inna ta girgiza mata da sauri tana cewa "Ina ni ina kama bintu? Ai ki maza kije waje wataqila ki hadu da kakkarfan namijin da zai iya kama miki ita don bintu dai tafi karfin mata sai maza.." 

Kuka Nuri ta fara irin silent one dinnan tana miqewa da kanta trying taga ko zata iya dagata daga tsaye amman sam ta kasa, ba wai Mami nada kiba bane a'a, kawai tana nan daidai. Miqewa tsaye tayi kawai tana kallon Mami tana hawaye ta rasa yadda zata yi.


Waje ta nufa da niyyar ta shiga ko maqota ne ko za'a taimaka mata.


Tana fita Fu'ad dake tsaye jikin rilar gidan ya dago kansa idanunsa suka fada cikin nata. Gyara tsaiwarsa yayi yana maida wayarsa aljihi ya nufo inda take ganin fuskarta duk hawaye. 

"Where's the patient?" Gidan ta nuna masa tana cewa "tana ciki.." idonsa stiff akan fuskarta yace "to why are you alone?"

Da wannan muryar nata mai cike da sanyi a kowanne lokaci tace dashi "ni ba zan iya daukanta ba kuma babu mai taimaka min na dauketa...." Da kuka ta karashe masa tana share hawayen fuskarta da hannunta. Dauke idonsa daga kallonta yayi yana jin ba dadi ganin yadda take kuka.


"Baku da maqota?" Ya tambyaeta yana dawo da kallonsa kan fuskarta da haka kawai yake jin baison dauke idanunsa akanta. Kai ta girgiza masa yace "then kiyi sauri kije wurinsu kinji..." Wucewa tayi da sauri kaman yadda yace ta shiga gidan dake kusa dasu Allah ya taimaketa matar gidan na zaune kan tabarma tana kallo a wayarta. Gaisawa suka yi take tambayar Nuri lafiya ganin fuskarta duk hawaye. 

Goge hawayen fuskar nata tayi saying "don Allah maman Hanif kizo ki taimakamin mu kai Mamina asibiti ta suma.."

"Subhanallahi." Ta fada tana miqewa tsaye da sauri tace "Me ya sameta?"


"Ban sani ba Nima, kawai ta fadi ne..." Ta bata amsa tana sake share wani hawayen da yake zuwar mata. Tare suka fito da maman Hanif suka shige gidan Fu'ad yana bin Nuri da kallo ganin har sannan idonta da hawaye shi kuma bai taba haduwa da wanda yaji kukansa ya tsaya masa a rai ba kamar ita. Basu dade ba sai gasu sun fito tare da Mami sun kamata ta both sides miqewa daga jinginar da yayi a bango ya nufi motar ya bude musu back seat suka shigar da ita suma suka shiga sannan ya rufe ya zagaya side din driver ya shiga ya tada motar yana gyara mudubin motar idonsa akanta. He wants to be seeing her face ko zata daina kukan yana jin idan ba denawa tayi ba zuciyarsa bazai ji sauqin abnd yake ji ba.

Bai tambayesu wnne asibiti suke zuwa ba yayi amfni da wayarsa yayi searching asibitin da yake da kyau ammn na kusa a wayarsa ya samu wani private clinic da baya da nisa dasu sosai. Bayan yayi parking ya fita kamin su fito yayi magana da wata nurse daya gani zata wuce yace suna tare da patient. Ba'a wani dauki lokaci ba abinka da harka ta kudi da masu kudi in no time akayi admitting Mami aka hau dubata. Nuri tana tsaye bakin kofar dakin kamar ta shiga haka take ji idonta akan glass din dake dakin da bata iya ganin komai tana share hawaye akai akai. Fu'ad na can gefe ammn hankalinsa yana kanta. Ya rasa gane dalilinsa na rashin son kukanta bama wannan ba yadda yaji zuciyarsa ta damu da nata damuwar ya tsaye masa arai. He just calm himself down  yana raya kawai saboda baya son ganin damuwa a tare da mutane ne that's why. 

After almost 20-30mins likitocin dake tare da Mami suka fito suna discarding mask da gloves dinsu. Da sauri Nuri ta matsa kusa dasu tana cewa "likita ya take?" Basu amsa mata ba ganin Fu'ad daya nufo inda suke sai suka karasa wajensa suna cewa "thank God an kawota akan lokaci da hakan zai iya jawo mata wani matsalar amman alhamdulillah she's conscious bacci take yi yanzu.."

Idonsa ya sauke kan Nuri dake kallonsu da wannan idanun nata da suke rikita masa lissafi yana furta Alhamdulillah daidai itama tana fada coz she can hear them. "za'a iya ganinta yanzu?" Kai ya girgiza masa yana cewa "she needs some rest a barta ta huta plz...jininta yayi mugun hawan da bata son hayaniya around her.." "Ok" kawai Fu'ad ya amsa masa da suna yin musabaha likitan ya tafi ya barsu anan. Agogon rolex dake hannunsa ya kalla kamin ya dawo da idanunsa kan Nuri dake nan tsaye har sannan tana kallon maqociyarsu dake mata magana. 

Ganin time din magariba ya taho yasashi juyawa ya nufi masallacin dake cikin asibitin anan yayi Maghrib da Isha sai bayan da ya kammala addu'o'insa sannan ya fito ya koma cikin ward din da suke. Bai tarar dasu anan ba tabbacin suna ciki knn.


Da kallo Nuri ke bin Mami kamar irin an canza mata ita haka. Komai kankantar motsi za tace "sannu" da kai kawai Mami ke amsa mata saboda wani irin ciwon kai na bari daya da take ji. Maman Hanif har sannan tana tare dasu tayiwa mai gidanta waya ta sanar dashi yace ta bari zaizo ya dauketa hakan ne ya zaunar da ita.

Knocking din kofa da suka ji yasa duk suka kalli kofar a tare har Mami dake zaune jingine da gadon. Sau uku yana yin knocking kamin Maman Hanif ta tashi ta bude masa ganin ance ashigo ba'a shigo ba.

Da sallama a bakinsa ya shigo wannan turaren nasa mai sanyi da mugun qarfi ya cika dakin tun kamin ya karasa shigowa. Idonsa bai sauka ako'ina ba sai akan wadda zuciyarsa take bugawa indai tana wuri wato Nuri wadda itama nata idon ya fada cikin nasa for the first time knn data taba kallon cikin idonsa sai dai na sakan daya kawai ta iya jurewa ta janye saboda kwarjininsa da yake cikita tuni taji dakin yayi mata kadan.

Da wani kalar kallo Mami ke binsa har zuwa sanda ya karaso cikin dakin daga tsakiya ya tsugunna har qasa yana gaida ita. Ta amsa masa politely yadda ta saba yiwa mutane ya tambyeta jiki yana ajiye ledar hannunsa ya juya zai fita Mami ta kalli Nuri tana cewa "wayeshi NURIYYA???"

"NURIYYA!!!" haka sunanta ya amsa akansa da wani kalar echo yana ta maimaita kansa. Yaso ya juya ya kalli wadda aka ambata da sunan amman haka ya saka kai ya fita yana iya juyo sanda ta bawa Mami amsa da wannan muryar nata da yake tsayawa aransa "ban sanshi ba nima..." As always da wannan sigar nata na sanyi da shagwaba ta amsa wanda ya saka Mami gyada mata kai tana cewa "waye ya biya kudin asibitin nan?" 

Shiru Nuri tayi ta rasa abin cewa sai Maman Hanif ce tace "shine Maman Afif..." Da sauri ta kalli Nuri tana cewa "amman shine baki fadamin ba nayi masa godiya Nuriyya?" 

Baki ta turo gaba tana cewa "nima fa bansan ko shine ya biya ba..."

"Oya maza jeki ki kirawomin shi kamin ya tafi ina ake haka..."

Ba'a son ranta ta miqe ba sam. Ta rasa dalilin da yasa taji kawai bata son kasancewa dashi saboda yadda zuciyarta take yi mata wanda yake so unusual. Haka ta fita tana wannan tafiyar nata har zuwa harabar asibitin just to find out ya tafi hakan ya mugun yi mata dadi ta koma ta sanar da Mami ya tafi. Kai kawai Mami ta gyada mata tana tunanin ya zata hadu dashi ta gode masa taimakon da yayi mata. Ba jimawa mijin Maman Hanif yazo ya dubata harda kayan dubiyarsa sannan ya kwashi matarsa suka tafi. 

Sai a sannan Nuri ta kalli Mami tana cewa "Mami to ban dauko mki abubuwan da zaki buqata ba..." Nuna mata pack din da Fu'ad ya ajiye Mami tayi tana cewa "akwai komai aciki Nuriyya." Dauke kallonta tayi tana gyara zamanta gaban Mami tayi shiru bata sake cewa komai ba har bacci ya dauke Mami don akwai maganin bacci a magunanta. 


Nuri ta jima ba tayi bacci ba ranar tana ta kallon Mami kamar wadda ke gadinta kawai zuciyarta na raya mata da wani abun ya samu Mami ya zata yi rayuwa babu ita? Da sauri ta kawar da tunanin daga ranta tana miqewa taje ta dauro alwala tazo ta tayar da shafa'i da wutiri da ba tayi ba bayan Isha. Anan kasa bacci ya dauketa bayan ta idar ba tare data shiryawa hakan ba.


To be continued......

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.