Free chapter · Read without an account

WHAT THE HEART CONCEALS

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa 


AZZAM'S POV ...

Da wannan izzar da ya arowa kansa yake takawa cikin part din Ummi shi a dole yadda Fu'ad yake haka shima zaike yin abu. Ko sallama baiyi ba haka ya shiga cikin parlourn ya samu kan kujera ya hakimce ya zauna yana fito da wayarshi kirar 17 air ya fara dannawa hankali kwance. Bai damu sam da yaje ya dubo Ummin a sama ya gaisheta ba duba da yadda ya dade bayanan kuma sam babu wanda ya kira, ya kashe line dinsa ma gaba daya don haka ko an nemeshi ba samunshi za'ayi ba.

Ya jima sosai anan yana danna wayarsa da kamar ta dauke masa hankali da alama akwai abun da yake da ita wanda yake da matuqar muhimmanci a wajensa don daga yadda ya bada attention dinsa zaka gane hakan.

Sautin takalmi ne ya jawo hankalinsa ya dago wannan fuskar nasa ya sauke a side din daya jiyo sound din. It was Ummi sanye cikin shiga na alfarma as always. Sam bata lura da Azzam ba har sai data karaso cikin parlourn sosai sannan ta lura dashi. Wani kalar tsayawa tayi turus tana kallonsa yadda shima yake kallonta kamar wasu baqi da basu san juna ba.


Ummi kallon haushi da takaici take masa na yadda ya tafi ko neman mutane baya yi wato duk wannan haushin nasa da take ji tana sonsa duk kuwa da kalar halinsa da takaicin da yake kunsa mata a rayuwa. While Azzam gani yayi hankalin Ummi akwance yake da alamar bama tayi kewar dadewar da yayi a inda ba'a samunsa ba. Lokaci daya zuciyarsa ta raya masa da ace Fu'ad ne yayi wannan dadewar da ba'a samunsa ya tabbatar da har a asibiti Ummi sai ta kwanta amman yanzu look at her a tsaye kyam hankali kwance. 

Kawar da kansa yayi da sauri yana jin zuciyarsa tana sake yin tauri akan komai daya shafi Fu'ad his one and only brother. Karasowa cikin parlourn Ummi tayi ta samu waje ta zauna opposite to him ta daura kafarta daya akan daya tana karewa Azzam din kallo wanda ya dauke kansa daga kanta already.


"Mu'az this is you, idonka kenan Azzam?"

Kureta da kallo yayi ganin yadda take magana kamar ta damu dashi "Ummi kin damu dani ne?"

"Shut the hell up Mu'az... Where have you been? Nayi rashin lafiya Azzam ko dubani baka yi ba you're asking whether I care about you or not.. can't you be like Fu'ad for once?"

Anzo wajen! Anzo inda ya tsana. Anzo inda yake bata masa rai a rayuwarsa. Ya tsani a riqa hadashi da Fu'ad mutumin da yake ganin kamar bad luck ne a rayuwarsa.

"For goodness Ummi ya isa haka. Fu'ad is your forever favorite person so ko me zanyi ba zaki gani ba... Nayi nisa ne saboda aikin company dinmu and wajen is out of network babu wanda ake samu, it just turn out to me that Ummi baki damu dani ba. Of all dadewar da nayi Ummi wannan kawai shine abnda zaki ce dani, mu'az can't you be like Fu'ad... To hell with Fu'ad Ummi.... " Yana gama fadin haka ya miqe tsaye yana zura wayarsa aljihu yawa Ummi wani kallo kai ba zaka ce itace ta haifeshi ba ya juya ya fita zuciyarsa nayi masa zafi.

Shi daya kulla successful mission akan Fu'ad ammn ya fadi kamar kullum dai baida sa'a a rayuwarsa. Part dinsu ya shiga yana harar side din Fu'ad ya shige dakinsa yana banging kofar kamar itace tayi masa laifi. A tsakiyar dakinsa ya tsaya yana riqe kugu yana jin duniyar tayi masa zafi. Ya dauki wannan dogon hutun ne duk a tunaninsa aikinsa akan Fu'ad was successful just to find out bashi aka sawa acid din ba. 

Sai ya rasa takamaimai abinda zaiyi wanda zai saka yaji komai ya wuce masa akan Fu'ad. Acid plan wasn't successful then what again zaiyi to get rid of Fu'ad, his blood?

Wani huci yayi yana zama gefen gadonsa yana cukurkuda sumar kansa dake nan da yawa kamar na Fu'ad shi a dole duk abinda Fu'ad yake shima sai yayi. 

"I can't stand seeing you Fu'ad, kullum kaine kake nasara a arayuwa.. wallahi sai naga bayanka Fu'ad!!! Wannan alqawari ne nayiwa kaina.. Kuma I will go far ganin na cika wannan alqawarin..." Yana gama fadin haka ya miqe tsaye ya wuce bathroom dinsa ya sakarwa kansa shower yana fadawa tunanin ta yadda zai billowa lamarin yanzu. Duk sai yaji kwalwalwarsa ya toshe yama rasa abinda zaiyi to get rid of his blood.....


FU'AD'S POV...

Kamar kullum ahankali yake driving yadda ya saba. Sai dai zuciyarsa tana wani tunanin, tunanin da tunda ya shigo garin Kano zuciyarsa keyi. Abinda ba halinsa ba shi yake yi yanzu. Tunani akan mace, macen da ba Umminsa ko Ammi ba. Ko Adda Safa da Suhana dake 'yan uwansa yana dadewa basu zo masa rai ba. Amman wannan from the start ta maqale masa a zuciya. Komai nata yana nan zaune daram a ransa daga ranar farko. Muryarta, kammaninta yanayinta da komai nata suna nan stiff akansa. 


Yau ba iya su kadai ba hatta da sunanta yau yaji, sunan da yake unique bai taba ji ba kodan baya hulda da mutane ne bai sani ba, abinda ya sani kawai shine akanta ya farajin sunan. "NURIYYA" ya sake tuno yadda yaji Umminta ta fada. Iska mai sanyi ya fitar daga bakinsa yana son kawar da tunanin daga ransa dukda ya lura kamar zuciyarsa bata bashi hadin kai a wannan fannin. Tun yana jin haushin kansa akan hakan har ya dena. Bama wannan ba the fact that throughout yau din idonsa yana tare da ita shi yafi damunsa, me yake damun zuciyarsa ko dai baida lafiya? Shine tambyara da yayiwa kansa, hakan yasa da sauri ya dauki wayarsa yayi dialing number Pal dinsa hoping yana kusa.

Bai dade yana ringing ba Fa'iz from the other side ya amsa yana masa sallama. Da wannan muryar nasa dake da amo kadan ya amsa yana tambyarsa aiki. Gaisawa suka yi yadda suka saba Fa'iz yana tambyarsa yaushe zai dawo ya bashi amsa da yana so sai komai na site ya kammala sannan ya dawo.

Shiru for a while kamin Fa'iz yace "Pal are you ok?" Kai Fu'ad ya gyada masa kamar yana ganinsa yace "yeah Fa'izz"

"Muryarka sounds kamar kana son fadamin wani abu.." ba shiri Fu'ad yayi murmushin da bai shiryawa ba. Shi da Pal dinsa abotarsu is one unique bonded friendship da Allah ya hada bayan kasancewarsu 'yan uwa.

"There's this thing I wanna ask you Pal."
"Mene Fu'ad?"

Shiru kadan Fu'ad yayi yana daukar kwanar street din da zai kaishi bristol yace "wanne ciwo ke sawa mutum yayi ta tunani akan wani???"

"Ciwo? Tunani?" Fa'iz ya fada fuskarsa looking confused sosai. "Pal can you further explain wanne kalar tunani ne?"

Shiru Fu'ad yayi yana jin kawai daga tambyar zuciyarsa ya fara buga masa yadda yake yi idan yana tare da ita hakan yasa ya lumshe idonsa yana budewa ahankali still focusing akan driving din da yake yi.

"Pal kai nake saurare??"

"Tunani kawai pal, ka hadu da mutum sannan kayi ta tunaninsa daga baya manaaa..."

Tsaki Fa'iz yayi ganin kamar wasa da hankali Fu'ad din yake son yi masa yasashi cewa "look Pal ina da abinyi seriously, can you just tell me what exactly kake nufi? "

"Forget it Pal.. " wani hararar wayar Fa'iz yayi kamar suna tare yace "ka isa ma Fu'ad, kana ina? Da waye ka hadu a Kano din? Wait ko dai..... "


Da sauri Fu'ad yace "ba kowa Pal I'm driving idan na qarasa za muyi magana.. "

"Baka da gaskiya pal?" Fa'iz ya fada yana ajiye pen din dake hannunsa.

"Za muyi magana anjima pal bye.. " yana fadin haka ya kashe wayar daidai yana parking ya kashe motar yana bin guards dinsa dake tsaye a premises din wajen alamun suna jiransa. Kai kawai ya girgiza yana jin shifa baison yaga komai zaiyi akwai masu kula dashi yana son privacy. Dama wannan bodyguards idea din sam ba nashi bane na Ummi da Abi ne shi kuma bashi da yadda zaiyi da ya wuce yabi umarnin iyayensa hardai akan daidai ne.

Kamin ya bude motar tuni sun zagayeshi sun bude masa suna jiran fitowarsa. Kallonsu yayi one by one bayan fitowarsa yana cewa "what are you guys waiting for a daren nan?"

Head acikinsu ya sunkuyar da kansa yana cewa "sir we're waiting for you..." Dauke kansa Fu'ad yayi yana cewa "better idan kunji ni shiru ku daina damuwa I'm okay and will be okay In Sha Allah..." Yana fadin haka yayi gaba suka take masa baya abinda yake sake bashi takaici kenan hakan yasa ya juyo duka ya sallamesu yace kowa yaje nasa makwancin ya kwanta tunda sun ga ya dawo. Dole suka juya suka koma nasu suit din banda kalilan da suke anan.

Bai wani dauki lokaci ba shima ya shiga nasa wajen da kai tsaye bathroom ya fada yana sakarwa kansa ruwan dumi saboda gajiyar daya kwaso duk kuwa da ba aiki yayi ba....


20mins ya bata a bathroom din kamin ya fito sanye cikin bathrobe baqa daya mugun haska wannan farar fatar nashi dake mugun kyalli kamar na mace. Closet ya wuce ya sake bata wani sabon 20mins din yana shafe-shafe kamin ya sanya white pyjamas yazo ya zauna kan sofa yana saka order din abinci...


NURI'S POV....


Sanyin asuba ne ya tasheta daga baccin da tayi akasa kan darduma. Ta miqe zaune ahankali tana kallon Mami dake bacci hankali kwance. Ajiyar zuciya ta sauke tana miqewa tsaye ta nufi inda Mami take ta kureta da idanu kamar wadda ke duba ko canza mata Mami akayi kamin ta juya ta fada bathroom tayi alwala ta fito ta tayar da sallar asuba da already masallatai wasu har sun idar. Bayan ta idar tayi zamanta anan tana cigaba da addu'a wanda duka akan Mami ne sai Afif. 

Tana nan zaune har gari ya fara wayewa sannan Mami ta farka daga baccin da magani ya sakata. Da sauri Nuri ta miqe ta nufi inda take tana mata sannu. Da kai Mami ta amsa mata tana miqewa zaune Nuri ta taimaka mata zuwa bandaki ta dauro alwala tazo tayi nata sallar a zaune saboda jirin da takeji idan tana tsaye. Nuri duk sai kallonta take hankalinta akan duk wani motsi da Mami keyi. 

Mami na lura da yadda Nuri ke kallonta wanda lokaci daya ya karya mata zuciya bayan tuna asalin abinda ya jawo mata ciwon da tayi. Ta tuna kalaman Inna sune suka jawo mata wannan rashin lafiyar. Ta tuna kalmar aure da Inna ta ambatowa dukkansu. Ta tuna zabin da Inna ta bata akan rayuwarsu ita da 'yarta!!!!

Bata kalli Nuri ba amman hankalinta yana kanta.. sam ba zata bari Inna tayiwa Nuri aure da wani wanda bata sani ba! Never! Kamar yadda take uwa! Zata sadaukar da nata farincikin wa 'yarta! Ta yadda ita za tayi auren da wanda bata san waye ba! Sai dai ba wannan ne yake daga mata hankali ba. Wanne kalar rayuwa Nuri za tayi agidan Inna bayan tayi auren ta tafi ta barta?????

To be continued....  

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.