Free chapter · Read without an account
WHY DOES IT MATTER?
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
Ba Uncle Farouk kawai ba hatta da Aunty Mimi kallon fuskar Afif kawai take da mamaki written all over her face. Shi baima lura da kalar kallon da suke masa ba saboda kansa yana kasa. Jin shiru yasashi dago kansa yana nuna musu dakin yace "She's inside... I will take my leave..."
Da kai Uncle Farouk ya amsa masa yama kasa magana sai Aunty Mimi ce tayi karfin halin cewa "mungode Jazakallahu Khairan.." Kai kawai Afif ya gyada musu yana barin wajen. Har ya bar wurin Uncle Farouk bai daina kallonsa ba.
"Azeez mu shiga ciki." Kai ya jinjina mata yana kallonta "Darling baki ga abinda na gani bane?"
"Is not the time for that Azeez.. we will talk about it later... Yarinyar mu is waiting for us."
"Hakane muje." A tare suka shiga dakin da suka tarar da Suhan tana bacci ga drip sanye a hannunta. Karasawa wajenta suka yi suna kallon yadda fuskarta ya fada na yini daya kawai.
"Daman tacemin she's having a headache dazu amman ban dauka it's severe har haka ba."
Kallonta Uncle Farouk yayi yana cewa "Is not like it's your fault naji kinsa muryar tausayi kuma" wani kallo tayi masa kamin ta mayar da kallonta kan Suhana tana daura hannunta akan nata "Wish you a quick recovery autan Ammi."
Anan suka zauna har dare yayi sosai sannan Aunty Mimi tace dashi ya kawo musu abnda zasu buqata zata zauna da ita haka ya koma gida adaren ya dauko musu kayan da zasu buqata plus ya tsaya a supermarket ya sai musu wasu abubuwan ya dawo. By the time he came back, ya tarar da Suhan ta farka ammn ko magana bata iyayi kamar har sannan zazzabin bai saketa ba, bashi ya koma gida ba sai around 12.
Daya koma gidan ma kasa bacci yayi ga dai shi yayi shirin baccin amman ya samu waje kawai ya zauna. Har sannan fuskar Afif na yawo a idanunsa. Kawai ya kasa yadda da abinda yake gani a fuskar nasa. Wayarsa ya zaro da sauri ya lalubo hoton mahaifinsu GIDADO ARDO ya saka agaba yana kallo. So yake yayi comparing kamannin Afif dashi and it's obvious kana kalla za kaga muguwar kamar da sukeyi vividly.
"Yah Allah what's this nake gani yau kuma... The resemblance is obvious kamar Abbu ne ya haifeshi.. in fact duk cikinmu babu wanda yayi kama da Abbu kamar shi sai ko Hamma...." shiru ya sake yi na wasu mintina zuciyarsa na raya masa kawai kama ne daga Allah.
Da sauri ya girgiza kansa yana cewa "This can't be.. kamar yayi yawa ace kawai kama ne bana jini ba. Wannan yaron probably jininmu ne.. dan Abbu ne... But wait taya nake da assurance... Kawai kama ne... Kama ne..." Gaba daya ya gama rudar da tunaninsa akan kamar da Afif yake yi da Abbunsu. Shi kawai zuciyarsa ta kasa yadda kama ne bana jini ba.
"Idan kuma zato na gaskiya ne fa? Waye mahaifinsa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana ture tunanin daga ransa bayan ya tabbatarwa da kansa kama ce bata jini ba wadda Allah yake sawa a tsakanin bayinsa. Ya tabbatar yaran Abbunsu guda biyar ne biyu sun mutu su uku kawai suka rage daga Hammansu Abbi dinsu Suhan sai Uncle Sadiq plus shi dan auta.. Can it be Abbu nada wani dan?
"Kai damn it... We're five nine auta Hamma Isma'il da Hamma Yusuf sun rasu... That's it.. Allah ya jiqansu da Rahama."
Yana kaiwa nan ya miqe tsaye da sauri ya shiga bedroom dinsa yayi shirin bacci baya son ya takurawa kwalwalarsa da tunani akan abinda yake zato kawai ba gaskiya ba.
Ilai kuwa tsabar saka abin aransa har mafarkin hakan sai da yayi amman a mafarkin it turns out that Afif dan uwansa ne na gaskiya. Bai wani bawa kansa space din saka abin arai ba haka ya tashi ranar shi ya shirya yaran ya taimaka musu da breakfast sannan yayi dropping dinsu a makaranta shi kuma ya wuce asibiti.....
FU'AD'S POV...
"Kamar jiya, I'm the one that will drive na hutar daku yau ma.. everyone should take his leave..." Da kallo suka bishi suna jin kamar basu cika aikinsu ba tunda abinda aka daukesu suyi kenan. Ganin basu tafi ba yasa Fu'ad daure fuska sosai yana cewa "What are you guys waiting for? I said you should leave.." da sauri suka daga masa kai suka juya kowa yayi nasa various hanyar.
Tsaki ya danja yana bin wajen da kallo saying "I can't even be on my own bayan na girman ma, da Ummi and now wa'ennan.." wani tsakin ya sake ja yana bude motar nasa kirar Tesla 2025 model ya shiga ya kunna yana yin addu'a. Ahankali kamar yadda ya saba haka ya fara driving din har ya fita ya dauki hanyar site duk da yasan yayi safiya wajen karfe tara ne amman yau yana son ayi aikin dashi ne shisa zaije da wuri.
Fresh ya tashi yau babu wani tunani duk kuwa da cewa shine yake ture tunanin ta karfi da yaji hakan yasa ma zaije ayi aikin site dashi duk saboda ya zama occupied kar ya samu space din tunani. Sai dai kamar bai da sa'a akan tunanin nasa yana parking acikin layin inda yaga driver dinsa yana yi idonsa ya sauka akanta.
Sai dai ba ita kadai ce ba yau ma tare da wani ya ganta hakan yasa bai san sanda ya kware ba ya fara tari kadan kadan idonsa akansu. Shi daya tashi yau babu wani damuwa ko bacin rai lokaci daya yaji wani bacin rai from nowhere daga kallonsu kawai. Yaso ya basar ya fita ya wuce ciki amman ina baima san sanda ya fita daga motar ba ko mukullin bai cire ba.
Yana fita kuma ya tsaya cak kamar an dakatar dashi yayi kasa da hannunsa saying "Meye naka aciki Fu'ad? What is your problem with her being with someone else Fu'ad?"
Sai kuma yasa hannunsa yana sosa sumar kansa mai tarin yawa dake nan very curly ya busar da iska yana gyada kansa ya dauke idonsa akansu yana cewa "Yeah bani da hadi dasu..." Juyawa zaiyi ya tuna da keyn motar yana jiki hakan yasa ya koma ya cire yana zurawa aljihu ya dago zai wuce site idonsa ya sake sauka akanta.
Wannan karon anyi sa'a ta dago fuskarta zata bawa Bilyaminu haquri akan ya kyaleta ta tafi idonsu ya hadu waje daya. Da sauri ta kawar da fuskarta gefe tana kara saurinta duk don tayi sauri ta bar layin nasu.
"Kayi haquri haka nan mana Bilya ka barni asibiti fa zanje wajen Mamina..." Iska ta kwasowa Fu'ad maganarta data sakashi tunawa da Maminta dake asibiti. Still bai bar wajen ba bai kuma je inda suke ba har dai daga karshe ta samu napep ta hau ta bar wajen.
Yabi Bilyaminu da wani kallo shi ba harara ba shi ba kallon arziqi ba wanda shi kansa bai ma san sanda yayi masa ba. Minti biyar ya kara a tsaye awajen kamin ya sake komawa cikin motar nasa ya kunna ya bar unguwar zuwa asibitin da akayi admitting Mami. By the time he parked in the hospital compound, yaga shigewarta ciki. Dan zama yayi a motar yana tambayarsa kansa me kuma ya kawoshi asibitin?
Ringing din wayarsa ne ya katse masa tunanin hakan yasa shi dagowa yana daukar wayar. Ummi ke kira hakan yasa babu wani delay yayi picking yana mata sallama.
"Wa'alaikumus Salam Hayaty, how was your night?"
"Barka da safiya Ummi."
"Barka ykk.. ya Kano?"
"Lafiya Ummi ygd sai ke kadai ko?"
Kai ta girgiza masa saying "a'a biyayyenka ya dawo jiya ai mantawa nayi ban fada maka tun jiya da dare da muka yi waya ba."
Zamansa ya gyara yana cewa "Azzam ya dawo Ummi?"
"Eh ya dawo.."
"Yaron nan.. ya fada miki ina yaje yayi wannan dadewar? Kullum fa sai na kirashi amman layinsa baima tafiya. "
"Yace wai business trip yayi sannan inda suke je was out of network.. "
"Karya yake Ummi... Wanne business trip zaije yayi fin wata daya? Shi da ba head a company dinsu ba, ba mataimaki ba ba wani ba acan... "
"Ya isa FU'AD!!"
Da sauri ya ciro wayar daga kunnesa yana sake karanta sunan Ummi da yayi saving da Hayaty kamin ya mayar yana maimaita sunansa da Ummi ta furta "Fu'ad" da mamaki a fuskarsa.
Itama Ummin shiru tayi tana jin wani irin yadda ta kira Hayatyn nata yau amman kamar he's taking Azzam so low yadda yake magana. Dukkansu yaranta ne, aciki ma tafi son Fu'ad da bata boyewa agaban kowa amman yau kawai sai taji wani iri daya fadi haka akan Azzam.
"I'm sorry Ummi.."
"Is okay Hayaty, I will call you later." Tana fadin haka ta kashe yabi wayar da kallo yana ajiyewa. Cikin asibitin ya kalla kamin ya cire seat belt dinsa ya fito ya fara takawa cike da wannan charisma din nasa ya shiga ciki.
NURI'S POV...
A darare haka ta miqawa Mami plate din abincin ta samu waje ta zauna akan kujera bayan ta jata baya. Kallonta Mami tayi ganin yadda take abu kamar wadda tayi laifi. "Are you okay Nuri?"
Da sauri ta gyadawa Mami kai tana cewa "eh.. Mami kici abincinki kinji." Kai Mami ta gyada mata tana daukar fork din dake ciki tayi Bismillah zata kai abincin baki Nuri tayi saurin cewa "Mami ba'a komai ake magana ba ko? Don Allah kiyi shiru kawai kici...ba'a magana idan ana cin abinci..."
"Kona abincin kikayi Nuriyya?"
Wani irin zaro idanu tayi tana kallon Mami da mamaki sai tayi saurin girgiza kai tana cewa "Kona abinci kuma? Ni? A'a ba ko daya.."
Mami na kallonta tace "amman haka kike yi duk lokacin da kika barmin abinci ya kama..."
"Wayyo Mami.. abinci bai kama ba...kici kawai keda baki da lafiya ina ke ina magana?"
Murmushi kadan Mami tayi tana barin kallonta sanin ko ta sake magana wani sabon shirmen zata mata amman ta tabbatar abincin ya kama ne yana kauri shisa take behaving haka.
Banza tayi da ita ta fara cin abincin da tun kamin ta kai baki taji kaurin amman tayi kamar ba taji ba taci rabin abincin ta ajiye Nuri tayi saurin miqa mata ruwa a kofi ta amsa ta sha tare da magungunanta sannan ta miqa mata ragowar.
"Kinci abincin ne ke?"
Kai ta girgizawa Mami "sai ance kici zaki ci.?" Nan ma ta sake girgiza mata kai tana miqa hannu ta dauki ragowar na Mami "dan wannan zaki ci?"
"Zai isheni Mami." Kai Mami ta gyada mata kawai tana yin shiru idonta akanta. Spoon daya Nuri tayi taji kamar ta dawo da abincin don har wani daci taji kamar yana yi ta dago a sace ta kalli Mami taga idonta akanta. Runtse idonta tayi ahankali aranta tana furta "ahaka Mami taci abincin?"
Ta kai wani spoon din baki Mami tace "abincin yayi dadi sosai..." Kwarewa tayi ta fara tari tana kallon Mami da ta tabbatar magana kawai ta fada mata zata yi magana Mami ta sake cewa "Ina ke ina magana ke da kike cin abinci.."
Ajiye abincin tayi tana girgiza kai ta kama kunnenta saying "kiyi haquri Mami."
"Da kika yi me?"
"Maganarki ce banji ba na biyewa Inna shisa komai ya lalace.."
"Ohh I see. Bani da lafiya kinzo kina sani magana.. by the way Ina wayana..."
Runtse idonta tayi da sauri tana cewa "Innalillahi... Mami na.. manta.." wani kallo Mami tayi mata tana cewa "koma ki daukon.."
"Mamiiiiii... Yanzu fa na dawo ki bari anjima.."
"Biyayyenki zan kira nasan yana can mun daga masa hankali..."
"Ko hutawa banyi ba Mami.." shiru Mami tayi mata bata kulata ba hakan yasa ta miqe da sauri "Zanje na dauko. "
"Saura ki biyewa Inna ni dake ne.. "
"Banza ma zanyi mata.. "
"Me kika ce? "
"Sai na dawo Mami. "
"Allah ya tsare hanya.. "
"Aameen. "
Da sauri ta fita daga dakin nasu tana rufe kofar ta jingina da jikin kofar tana rufe idanunta da karfi tana tunanin idan ta koma kuma dawa zata hadu..
_________
Da sauri yaja baya ganin yadda aka bude kofar da sauri idonsa akan kofar yana son ganin waye zai fito. And it was her.. the girl that keeps on making his heart flutter. Bama ta lura sam da mutum ba ta jingina da kofar tana rufe idanunta folding her arms.
Kawar da nasa fuskar yayi da sauri sai dai amar wanda ake sarrafawa haka ya dawo da kallonsa kanta. Fuskarta ya kafe da kallo kamar shine abinda ya kawo shi asibitin yana jin yadda zuciyarsa take skipping like it was about to leap out of his chest.....
To be continued...
#like
#comment
#share