Free chapter · Read without an account

UNKNOWN TIES

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa


Lokaci daya hancinta ya shaqo mata wannan kamshin da awajen mutum daya ta taba jinsa, hakan yasa ta bude idanunta da sauri tana miqewa daga jikin kofar data jingina. Tana bude idanunta suka hada idanu da Fu'ad daya kafeta da idanu ko kiftawa ba yayi. Dan daburcewa tayi ganin yadda ya tsaya agabanta though there was still a little distance between them, amman sai taji kamshinsa ya cika mata wajen bama shi kadai ba, his presence filled the entire space around her.

Dan saita kansa yayi, still idanunsa akanta ba tare daya dauke ba, ya bude baki kamar mai rada ko wanda yake tsoron wani yaji muryarsa ya furta "Ina zaki je?"

Bata kalleshi ba saboda yadda yake cika mata ido sai ta nuna masa exit alamun fita zata yi. Kallon inda ta nuna masa yayi kamin ya dawo da kallonsa kan fuskarta dake kallon gefe "yanzu kika dawo.."

Shiru kamar ba zata bashi amsa ba sai can ta bude baki kamar mai ciwon baki tana cewa "aikena akayi..." Tsaiwarsa ya gyara yana zura hannayensa duka cikin aljihun baqin wandonsa yana kallonta "ya mai jiki?"

Instead of ta amsa mishi sai nuna masa dakin tayi tana kokarin barin wajen. Da sauri ya tare mata hanya yana cewa "wait, wait... Bara na dubata sai mu tafi tare..."

Da sauri ta kalleshi da mamaki tana cewa "mu tafi tare kuma?" Inda ta nuna masa shima ya nuna mata sai ta girgiza masa kai kamar wata yarinya tana barin wurin. Dakin da Mami take ya kalla kamin yabi bayanta da kallo yana tunanin abinyi sai kawai yabi bayanta da niyyar idan ta dawo sai ya shiga ya duba Mamin.

Yana fita ya tarar da ita bata wani yi nisa ba hakan yasa yabi bayanta da dan sassarfa a tafiyarsa. "NURIYYA!!!" ya kirata da wannan muryar nasa dake da amo kadan wanda ya saka Nuri saurin juyowa ta kalli fuskarsa. Shima kallonta yayi na sakanni kafin ya karasa inda take yana cewa "let me drop you inda zaki je"

Kai ta girgiza masa da sauri tana cewa "a'a ba nisa gida zan koma.."

"Eh muje.." dagowa tayi zata sake yin magana yayi saurin hade hannyensa waje daya da sigar roko afuskarsa yana lagwabar da kansa yace "please banda musu, kin sanni fa.."

Idanunta ta waro masa ba tare data kalleshi ba tace "a'a ban sanka ba.."

"Amman ni na sanki.." ya fada still hannyensa na hade waje daya idanunsa suna kanta. Kai ta girgiza masa tana dauke fuskarta daga kallon side din da yake zata sake magana yace "don't, please... Don Allah muje na kaiki..."

Wani kallo tayi masa daya sakashi dauke fuskarsa da sauri kamin ya dawo da ita yana sake kallonta yaji tace "ni ka bari zan hau napep.."

Zai sake magana itama ta hade hannyenta waje daya kamar dai yadda yayi tana cewa "Nima don Allah.." sai ta dago da kanta ta saci kallonsa suka hada idanu saboda yadda ya kafe idanunta akansa.

"Abinda kike so kenan?" Ya tambyeta yana sakin hannyensa da sauri ta daga masa kai ba tare data amsa ba. "Zan iya rakaki to idan kin yadda?"

Da wani kalar sauri ta sake dagowa ta kalleshi kai tsaye yanzu idanunta suka fada cikin nasa. Sai dai kamar dazu bata iya ta kalleshi ba ta dauke zata girgiza masa kai yayi saurin cewa "let's go... kar kice a'a kawai rakaki zanyi tunda kinqi yadda na kai ki..."

Dauke kanta tayi tana yin gaba zata tafi yayi saurin karasawa inda take suka jera tare. Ya kalli fuskarta da rana ta haske saboda yadda suke facing din ranar, dan kallon sama yayi yana kare fuskarsa shima da ranar ta haske kamin ya dawo da nasa kallon kanta. "Minti daya please, abu zan dauko don Allah karki tafi." Ya karashe da sigar roko afuskarsa. Bata kalleshi ba dukda taji yadda yayi mata maganar ta dai tsaya har ya bar wajen. Tana ganin ya tafi tayi gaba abinta tana mita aranta kuma abinka da jinin Inna. 

Motarsa ya nufa kai tsaye yana zuwa ya bude ya shiga ya dauko p-cap dinsa baqa dake ajjiye gaban motar ya ajiyeta saboda idan zai shiga wajen da baiso aganeshi yake amfani da ita. Fitowa yayi yana rufe motar ya juyo sai dai bai ganta ba. Kai ya girgiza yana bin bayanta zuwa wajen asibitin lucky for him tana tsaye tana jiran napep tasa hannu ta tare hasken rana dake haske mata idanu.

Karasawa wajenta yayi da sauri yana dan sauke ajiyar zuciyar saurin da yayi. "Put this on.." ya fada yana miqa mata p-cap din dake hannunsa. Kallon hannunsa tayi kamin ta kawar da fuskarta ta girgiza masa kai. Bai sake cewa da ita komai ba ya saka mata  akanta yana tsayar da napep din da yazo wajen. Da kansa ya fada masa unguwarsu tunda yasan sunan wuri a dalilin site dinsa. Kallonta yayi yana cewa "ki shiga." Shiga tayi ba tare data kalleshi ba tana kallon gefen hanya ya dauki kudi ya biya mai napep din ya tsaya har suka tafi yana bin bayansu da kallo.

Ranar dake hakse mai fuska ne yasa ya juya ya koma cikin asibitin zai duba Mami kamin ya wuce shima. Yana zuwa yayi knocking bai shiga ba har sai da yaji an bashi izinin shiga sannan ya shiga kansa akasa.

Da kallo Mami tabi Fu'ad data gane shine wanda akace ya kawota asibitin jiya.

Ganin zai tsugunna kasa yasa Mami cewa "ka zauna mana.." tana nuna masa kujerar dake kusa dashi. Bai zauna din ba sai daya durqusa har kasa ya gaidata yana tambayarta ya jiki sannan ya miqe ya zauna kamar yadda ta buqata.

Kamar shi ake jira sai ga likitan daya dubata ya shigo dakin da sallama. A tare suka amsa masa sallamar suna kallonsa. Hannu ya miqawa Fu'ad suka yi musabaha yana tambyarsa ya mai jiki ya amsa da lafiya don shi a tunaninsa mamansa ce musamman da suka kasance dukkansu farare.

Wurin Mami yaje ya duba vitals dinta yana dubata da tambayarta yadda take ji duk ta bashi amsa. Kai ya gyada yana cewa "Masha Allah zuwa gobe ma In Sha Allah zamu sallameki idan jininki ya sake sauka kasa.." Kai ta gyada masa tana hadawa da godiya shi kuma ya juya suka sake musabaha da Fu'ad sannan ya fita. Miqewa shima Fu'ad yayi yana cewa " akwai abinda kike buqata?"

Kai ta girgiza masa tana cewa "a'a yaron kirki bana buqatar komai nagode sosai da taimako Allah yayiwa rayuwarka albarka..." Dan dagowa kadan yayi yana kallon Mami jin addu'ar da tayi masa wadda tunda yake da Ummi bata taba yi masa kalar addu'ar irin haka ba. Ammi ko yaushe itace wadda take saka masa albarka ko gaisheta yayi kuwa yana daya daga cikin dailin da ya saka yake son Ammi da son zuwa Inda take wannan thought din ya tuna masa da bai ma nemi Ammi din ba jiya ga yau ma.

"Allah ya qara sauqi yasa kaffara ne... Sai anjima..."

"Aameen ngd ka gaida gida.." Kai ya gyada mata yana fita daga dakin Mami tabi bayansa da kallo.

Kai tsaye ya wuce motarsa ya zauna yana kiran layin Ammi da bugu biyu kawai ta dauka. "Nayi fushi..." Shine abinda Ammi ta fara furtawa da ya saka Fu'ad girgiza mata kai da sauri yana cewa "I'm sorry Ammi don Allah.."

"Shikenan.. how's everything there, Fu'ad? "
"Alhamdulillah Ammi, komai lafiya ysu Abbie?"
"Lafiya qlw.."
"Yaushe zaka dawo?"
"Ammi ina so a gama komai dani.."
"Za'a dade ko?"
"A'a saura kadan, minor abubuwa suka rage..."
"Allah ya bada sa'a Fu'ad.. Allah ya shige maka gaba a dukkan al'amuranka.."

Rufe idanunsa yayi yana murmushi ya amsa mata da "Aameen Ammi." da haka suka yi sallama fuskarsa har sannan dauke da murmushin. Zai ajiye wayar saiga kiran Ummi ya shigo masa.

Bin wayar yayi da kallo yana tuna yadda suka yi sallama dazu ya amsa "Hayaty"
"Na'am."
"Na manta dazu ban fada maka ba, dafatan baka hadu da kowacce yarinya ba?" Shiru yayi yana son gane mai take nufi "ban gane ba Ummi?"

"Ina nufin dafatan babu yarinyar daka hadu da ita anan har kayiwa magana..."

Nuriyya maganarta ta tuna masa.. yarinyar da tunda yazo Kano ta hargitsa masa lissafinsa da tunaninsa... Ta maidashi bashi da aikin yi sai na tunaninta akomai masa da yake yi har yake tunanin ko bashi da lafiya..

Samun kansa da amsa mata da "a'a" yayi wanda yasa Ummi sauke wata nannauyar ajiyar zuciya dashi kansa sai da yaji. Mamaki ya dan kamashi na hakan amman yayi shiru har sai da Ummi ta sake cewa "kar ka manta da maganarmu Hayaty... Babu kai babu kula ko wacce yarinya akwai wadda na zaba maka idan lokaci yayi zaka gani..." Kamar yana gabanta ya daga mata kai tana fadawa tunanin son sanin abinda Ummi ke magana akai. Yana kula wata? A'a ba yayi ya sani kuma babu wata aransa.. da kenan, amman yanzu wannan data maqale masa a komai nasa fa?

Da sauri ya girgiza kansa jin zuciyarsa zata masa fassarar daya dace wanda ba haka yake son ji ba "Hayaty, take care." Kamin ya amsa mata ma ta kashe wayar.

Ajiye wayar yayi ya kunna motarsa yayi warming dinta kadan sannan yayi reverse ya fita daga asibitin sai dai maganar Ummi ta sake dilmiya shi cikin tunanin da sam yasan bama zaiyu ace haka bane. Ummi na nufin bashi ba kula ko wacce diya mace har so ya shiga while shi kuma tun ranar daya shigo Kano zuciyarsa ta hadu da wadda ta dabaibayesa ta ko'ina..

He just sighed yana ture tunanin agefe ya dauki hanyar komawa site kamar yadda yayi da farko.....

AMMI'S POV...

Murmushi tayi kadan bayan sunyi sallama da Fu'ad idonta yana tara kwallar da bata san dalili ba. Kamshin turaren Abbie data ji ya sakata dago fuskarta da sauri sanin ya tafi mene kuma ya dawo dashi. Sai dai yanayin yadda ya shigo din ne ya sanyata miqewa tsaye da sauri tana nufarsa "yallabi lafiya?" Hannunsa ya miqa mata ragowar ta kama suka nufi inda ta tashi suka zauna yana dafe kansa da daya hannunsa.

"Yallabai..." Shiru yanzun ma Abbie ya sake wanda hakan yake dagawa Ammi hankali.

"Ranka ya dade ka kulani don Allah.."

"Fulani na kasa.. na kasa cikawa Abbu burinsa... I failed again Fulani..sun kawomin report din da nake tunanin shine zau hadani da ita amman ba shine ba wata ce daban...." Shiru tayi jikinta yana sake yin sanyi sanin yadda ya dauki burin Abbu da muhimmanci.

"Bansan ya zanyi ba kuma yanzu... An kirani ance jikinsa ya tashi nasan kuma damuwar da ya jawo hakan.... Fulani ni kaina ina buqatar haduwa da ita.. Abbu ya kasa a matsayinsa na uba nima kuma kamar na kasa a matsayina na Yaya..."

Hannunsa dake cikin mata ta damqe in a comforting way tana cewa "Baku kasa ba Yallabai.. In Sha Allah zaku hadu da Fadimatu.. zaku ganta.. Abbu zaiga jininsa da yardar Allah..."

"I have to go to Jimeta yau dinnan ina son ganin jikin nasa..."

"Zan bika Yallabai.."

"Kiyi zamanki kinji akwai aiki."

"A'a zan bika..." Kai ya jinjina mata sanin ba yadda za tayi ba tunda ta riga da tayi niyya. In less than 15 minutes sun shirya sai dai basu samu jirgin da zaije Adamawa ba a lokacin dole suka bari bayan azahar sannna suka tafi. Zuciyar Abbie cike fall da tunanin ta inda zai bi ya cikawa Abbu burinsa na haduwa da gudan jininsa!!!!!

To be continued....

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.