Free chapter · Read without an account

THE WAY HE SAID HER NAME

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa

Suna landing a Jimeta Ammi ta kira Fai'z a waya ta sanar dashi Abbu baya da lafiya. Yana asibiti a time din yana duba vitals din wasu patients da yayi wa surgery yace da ita zai duba yaga idan yana da time zai zo Jimeta din shima amman ba ranar ba da haka suka yi sallama. Ammi ta kalli Abbie da duk jikinsa yayi sanyi sanin abu daya kawai yake tadawa da Abbu ciwonsa which was about her always. Hannunsa ta riqe in a comforting way tana kallon fuskarsa.

Kallonta yayi shima ganin kalar kallon data sawa fuskarta duk don ya saki nasa jikinsa yasashi dan yi murmushi kadan yana cewa "After all I have Fulani beside me..."

Murmushi tayi masa tana gyada masa kai "Yes Yallabai I will always be on your side through thick and thin ranka ya dade..." Murmushi yayi mata mai soothing zuciya yana sake damqe hannunsu dake tare waje daya daidai driver nayin parking bakin gate waiting for the gateman to open the gate for him.

Anan harabar katon compound din gidan da yake nan babban gida duk da ginin gidan na masu kudi ne amman irin nada dinnan Abbu yaqi yadda ayi renovating gidan acewarsa tafiyar tazo karshe lokaci kawai ake jira. Gaisawa suka yi da ma'aikatan gidan in a formal way kamin suka nufi cikin asalin main building din bayansu wani dan aiki yana dauke da luggage dinsu.

A babban parlourn dake gidan suka zauna lokaci daya gidan har ya cika da 'yan uwa na kusa suna kawo musu gaisuwa tare da kayan ciye ciye. Duk anan suka zauna tare dasu suka gaisa for some time kamin wata gwaggonsu Abbie dake zaune agidan tayi musu iso zuwa dakin da Abbu yake.

Da sallama duk suka shiga dakin sai dai halin da suka tarar da Abbu ciki ya sake daga musu hankali fiye da da. Da sauri ya kalli gwaggo yana cewa "Abbu's condition is worse this time... Asibiti take buqata wannan karan."

Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke saying "hmmmmm kasan halin mahaifin naku sarai.... sam baya kaunar zuwa asibtin nan.. sai daya jaddadamin koda kunzo ma ku barsa nan agida likita yazo yana dubashi kullum haka yake... Ya kuma roqi alfarmar na sanar daku wannan..."

Kallon Abbu suka yi tare kamin suka dawo da kallonsu kan gwaggo a tare suka furta "Gwaggo amman yana buqatar akaishi asibiti..."

"Kunsan Gidado da kafiya kun fini sanin halin baban naku yanzu ma na tabbata ciwon nan nasa yana lafa masa sai ya sake fada muku hakan.."

Kai Abbie ya girgiza saying "No way... Babu yadda za'a yi na bar mahaifina agida suffering with heartache kuma ace ba zan kaishi asibiti ba. I think we should take him abroad for the surgery he said he didn't want...."

Kallonsa Ammi tayi da sauri "amman yallabai...." Kai ya girgiza mata yana cewa "Fulani wannan kawai shine solution kamar yadda likitansa yake fadamin akoda yaushe... Bazanso wani abun ya faru da Abbu baiga Fadimatunsa ba!!!!"

Maganar Abbie ya mugun kashe musu jiki da lokaci daya yasa suka yadda da aikin da ake fargabar yi masa tun tsahon lokaci.

"Idan muka cire tsoron aikin... Babu komai In Sha Allah.... Ba akan Abbu za'a fara ba... And it will get rid of the illness for good... Let's just pray for him.. za muyi magana da likitansa da kuma Fa'iz, let's schedule everything ayi a wuce wajen kawai... "

Kai duk suka gyada masa suna yadda da zancensa har suna jin hankalinsu ya kwanta da dan wannan maganar da yayi musu kawai.....

NURI'S POV....

Da murna take tattaro dan shirgin da suka tara a asibitin kasancewar an sallamesu yau da safe. Alhamdulillah jikin Mami yayi sauqi sosai babu wani alamun ciwo na bayyane a tare da ita sai dai a badini zuciyar Mami na dankare da tarin damuwowin data binnewa ranta kawai. Duk da tasan komawarta gida komai zai fito fili abinda take hiding wa yarinyarta will be open Nuri zata san komai amman not soon.

"Kalla Mami... Wannan zaman da kika yi ma a asibitin nan sai matga kamar fa kinyi haske, ya karbeki..."

"Akwai wanda rashin lafiya yake karba dama Nuri?"

"Yes yes Mami kamar dai ke... You look kaman..." Sai ta nuna kanta da sauri saying "kamar ni Mami..."

Murmushi Mami tayi tana kallon fuskarta dake kama da ita sosai just that Nuri was dark.

"Muna kama ne??"

"Sosai ma Mami... Kowa daya sanni ya sanki haka suke cewa Mami.. kamar ke haka.. Mami da kina 'yan mata kema haka kike??"

"Kenan wai 'yanmata ce?"

"Eh mana."

"Crying baby dai ko..."

"Ohhhh, come on Mami.."

Knocking kofar da aka yi musu yasa suka juya da sauri suna bada izinin shigowa a tare.

Fu'ad ne! Likitan dake kula da Mami ya fada masa musamman saboda shi har ynzu kallon maman Fu'ad yake mata. Shisa ma ya dauki number dinsa daga documents din Mami ya kira ya fada masa, out of concern and respect for the great CEO that he was.

Wani dakatawa da aiki zuciyar Nuri tayi na wucen gadi... She was like, why did he come here today? Bata da mai amsa mata wannan hakan yasa ta kalli Mami dake tattara sauran kayan dake kusa da ita.

"Yaron kirki...."

Murmushi Fu'ad yayi jin yadda Mami ta kirashi dukda kamar ya fahimci sunan data saka masa kenan. Tsugunnawa yayi har kasa yana gaida Mami da girmamawar data sakata nustuwa tana kare masa kallo tsaf. Yana da ladabi da biyayya sosai.. daga ganinsa ya fito ne daga babban gida mai tarbiya... Abinda yazo kan Mami kenan sanin a wannan zamanin ba kowa ne zaiyi kalar abinda yayi ba.

"Tashi tashi tashi don Allah.... Ka dena tsugunnawa zaka bata fararen kayanka.. ga waje ka zauna sai mu gaisa a zaunen..."

Kallon Mami Nuri tayi jin yadda take amsa masa kamin ta juyo zata kalleshi sai ta fasa tayi saurin dauke kallonta daga kansa ta juya ta kwashe sauran kayan. 

"Baki iya gaisuwa ba?"

Rudewa ta kusan yi kamin ta dake ta dan risina kadan tana cewa "barka da safiya.." 

Yaso ba'a gaban Mami tayi wannan gaisuwar ba amman tunda Mami na nan yasa shi amsawa brief da "barka."

"Mami zanje na samo napep sai mu wuce.."  

"Okay... then take care.."

"Mami ba sai ta sami napep din ba.... Nazo maidaku gida ne.."

Kai Mami ta girgiza masa da sauri tana cewa "kayi haquri amman mun gode.. haka ma ya isa... Dawainiyar sai yayi yawa ai... "

Da sauri ya amsa mata da "It won't be a problem Mami... Don Allah karkice a'a ki bari na karasa ladana... "

Mami can't deny it halayen yaran nan daga nan kawai sun kara tabbatar mata da tabbas ya samu horo daga uwa tagari. Kawai a yadda tasan society dinmu yanzu especially matasa dake jin suna da kudi sunfi kowa raina mutane musamman na gaba dasu...

"Allah yayi maka albarka ya baka masu yi maka fiye da haka..."

Addu'an Mami yayi masa.. kalar addu'ar da yake so ya riqaji daga mahaifiyarshi sai dai koda wasa da wayonsa bazai iya tuna ko Ummi ta taba saka masa albarka ba sai dai kulawa da tattali akoda yaushe. Kawar da tunanin yayi yana miqewa yaje ya dauki wani pack daya na kayan da suka tattara yayi gaba yana cewa "bara na kai kayan...."

"Nuriyya ki amsa daga hannunsa ki hada da na wajenki ki kai... "

Kai ta gyadawa Mami kamar wata kurma ta karasa zata karba ya fice hakan yasa kawia tabi bayansa tana tafiya kamar mai tsoron taka kasa.

Yana fita ya tsaya daga gefen kofar kamar yana jiranta wanda a zahiri ita ya tsaya jira. Tana fitowa tayi kamar bata gansa ba tayi gaba abinta. Murmushi Fu'ad yayi aransa yana cewa "She's always avoiding me..." Can kuma sai ya girgiza kai kawai yana karasawa wajen da take suka jera tare.

Da kyar Nuri ta gado courage ta bude baki da kyar ta furta "da baka zo ba.. zamu iya tafiya da kanmu fa.."

Kallonta yayi har ta kammala zancenta sannan ya dauke kansa yana dan lumshe idonsa ya bude yana cewa "Uhhmmm, I didn't come to pick you up... I came to pick up Mami."

Yadda yayi magana ne yasa ta dago kanta da sauri ta kalleshi suka hada idanu. Da sauri ta dauke idanunta daga kallonsa tana juyawa.

"Me yasa kike haka??"

Dakatawa da tafiya tayi tana son sanin abinda yake nufi. Shima tsayawa yayi yana kallon fuskarta da indai tana waje baya iya dauke idonsa akanta.

"Why pleaseeeeeeee?"

Yadda ya karashe please dinnan kamar wani karamin yaro dake roqon ayi masa wani abu haka. Zuciyar Nuri ta fara bugawa da gudu tana jin wani kalar uneasiness.

"Duk muka hadu sai kinyi min haka..." Ya dan dakata yana yawo da kwayar idonsa a gaba daya fuskarta.

"You're always avoiding meeee..." Muryarsa yadan yi kasa  yana matsawa kusa da ita kadan yana rage katuwar tazarar dake tsakaninsu.

"I'm not a monster da indai kika kalleni zaki yi saurin dauke fuskarki..." Ya kalli sama ganin yau babu rana kamar hadari ne ma yake shirin tasowa don garin har ya fara wannnan iskar na ruwan sama.

"ki dena...kina hanani kallon..." Ya dawo da kallonsa kanta ganin yadda ta tsaya cak kamar an kafata awajen..

"NURI!!" At that moment, Nuri tasan da za'a gwada rate at which zuciyarta take bugawa tasan ta gama wuce kima. Bata sani ba ko kunnenta ne baiji daidai ba, but she believed no one has ever called her name in a way that made her heart stop like this man. Kawai accent na yadda ya kira sunanta was different.. babu wanda ya taba kiranta in a way daya sa taji sunanta yana da dadi sai shi. Bama ta tabbatar sunanta yana da dadi ba sai yau da taji bawan Allahn nan ya fada. 

"Don Allah...." Ya hade hannyensa waje daya da sigar roqo a fuskarsa yana saka silly look kamar yaro "ki denamin haka... Ki dena dauke idonki kinjiiiiiii."

Gumi taji yana bin gefen fuskarta duk kuwa da cewa garin sanyin tasowar hadari yake yi. Taji kawai tana so tayi gaba ta barshi don yana shirin tarwatsa mata zuciya ne kawai da wannan ordinary kalaman nasa.

Handkerchief dinsa dake aljihu ya zaro ya miqa mata "take.."

Bata kalleshi ba sai farin hannunsa dake miqo mata handkerchief din tabi da kallo wanda yake sanye da agogon patek Philips and co kalar baqi da yayi masa kyau.

Hannunta yana rawa ta karba ta goge gumin dake fuskarta ta miqo zata bashi sai ta dakata da sauri tana kallon farin handkerchief din data ga kamar tadan bata masashi kadan da gumin.

Zata dauke hannunta yayi saurin karbewa yana cewa "ara miki nayi..." Shiru tayi ba kuma ta kalleshi kamar yadda yayi insisting.

"Muje Mami na jiran mu.." ya fada yana yin gaba ganin hadari yana tasowa dagaske har kamar an fara yayyafi kadan kadan. Bin bayansa tayi da sauri itama ganin ruwan zai sauko suka je suka saka a booth sannan suka juyo tare suka sake jerawa har zuwa cikin asibitin sai dai wannan karon babu wanda yayi magana acikinsu har suka shiga dakin da Mami ke tsaye tana jiransu.

"Mami kije zan biyoku idan na dauko wancan..." Kai Mami ta gyada mata suna fita tare ita da Fu'ad suka kai har bakin motarsa ya bude mata back seat ta shiga tana cewa ta gode.

Juyawa baya yayi ganin ruwan ya sauko kuma bata fito ba har sannan. Ya juya zai bi bayanta ya tuna maybe kamin su dawo ruwan ya sauko da karfi hakan yasa ya koma ya dauko lema dake motar nasa yabi bayanta dashi.

Daidai entrance din asibitin suka hadu wanda yayi daidai da tsugewar da ruwa yayi kamar da bakin kwarya.......

To be continued....

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.