Free chapter · Read without an account
SO, THIS IS LOVE!
by Saddiqah M · NURI
NURI
By Saddiqa
Tunda Ummi take bata taba jin Fu'ad yayi mata magana da seriousness kamar yau ba. Kawai daga yadda yayi maganar zaka fahimci har zuciyarsa hakan yake nufi. Shi kansa baisan da wani irin full assurance yayi maganar ba kawai straight from his heart kalaman nan suka fito.
Shiru Ummi tayi na tsahon minti daya kawai zuciyarta tana luguden duka saboda abu daya data sani da Fu'ad shine da zuciya daya yake komai in ma so ko ki. Ko bai fito fili ya fada mata yana son yarinyar ba ta tabbatar yana masifar sonta!
Idan kuwa har yana sonta to komai kamar ya lalace mata tun daga nan kenan. Hakan na nufin karshenta yazo!! Haba da wani kalar sauri ta girgiza kanta tana miqewa tsaye ta kashe wayar tana zaman dirshan aqasa. Kanta ya kulle mata ta rasa kalar tunanin ma da za tayi.
"Fu'ad was in love!! While love was forbidden to him!! Babu shi babu kalmar so bare farawa bare ma aje ga last sharadin wato aure!"
Ji tayi kamar ta dora hannu akai ta fara ihu "wacce tsinanniyar yarinyar ce haka data sace masa zuciya? Duk da me yasa bai fara son ba sai da aka kafa wannan sharadin? Ashe dama Fu'ad zai iya bijirewa umarnina? Ashe ban isa Fu'ad yayi min biyayya ba? Karka zama silar baqin cikina Fu'ad!!!!!" Tana kaiwa karshe anan wani hawaye ya biyo fuskarta.
Ummi na mugun girmama duk wani abu da zai bata mata fame da dukiyarta. Idan babu su tayi imanin zata koma zero behind decimal point ne yadda take yiwa mutane kallon tara saura kwata. The worst part of the story ma shine ba iya rashin dukiya abin zai tsaya ba, asirinta zai tonu wa duniya! Za'a san kalar munanan abubuwan data aikata wanda ita kanta bata son tunawa dasu.
Me za tayi da zai hana Fu'ad son yarinyar nan? Me za tayi da zata raba Fu'ad da ita? She needs to separate them!! Fu'ad will never ever be with her, ba ita kawai ba babu wata 'ya mace aduniya da zai iya kasancewa da ita har karshen rayuwarsa saboda kungiya ta haramta masa wannan.
To amman there he's... Busy in love har yana fada mata he's feeling himself attached to her to the extent da yake jin kamar bazai iya jiran lokacin data dibar masa ba... "
Exactly yadda ya fada mata kalaman haka ta dawo dasu saboda ta mugun riqesu gam akanta kamar karatun Qur'ani.. yo ko Qur'ani ba tayi wa haka ba.
FU'AD'S POV..
Da kallo yabi wayar nasa jin Ummi ta kashe ya kura mata ido kamar Ummin zai gani ta ciki. Fin minti uku yana bin wayar da kallo kamin ya ajiye ya koma yana kallon kansa a mudubi. "Ba aiki ya kaika Kano ba daman mace ce ta kai ka? Soyayya ce ta kai ka Kano dama Fu'ad?" Tsaf kalaman suka dawo masa wannan karon har echo suke yi masa a kunne.
Yabi fuskarsa da wani kallo yana runtse idonsa da kyau zuciyarsa na bugawa da sauri. Nuri ta hau zuwar masa kai tun daga ranar daya fara ganinta. Their first encounter lokacin data fadi kasa tana wannan kukan. Never in his life zai manta da wannan ranar, never!
A ranar ne ya hadu da wadda komai yake tana nan tare dashi a zuciyarsa. Tun daga lokacin daya hadu da ita rayuwarsa ta sauya masa ya zama har so yake ya hadu da ita. Ya zama akwai abu wanda ya damu dashi bayan aiki da ahalinsa. Shi da komai nasa aiki.. as the workaholic he was an samu abinda ya rage masa wannan. Tunaninta kawai yana bashi wani kalar peace da babu wanda ya taba bashi kalarsa aduniya.. amman ita, tunaninta kawai ya bashi wannan.
Fuskarta ta zamar masa abinda kullum yake so ya kalla, sai yaji duk duniya kawai an biyashi baya da sauran damuwar komai yaji ya manta da kowa da komai by merely looking at her face.
Duk wannan abubuwan yanayi ne ba tare da yasan mene ba, ba tare da yasan dalilin hakan ba.. har ya fara tunanin ko kwakwalwarsa ta samu wani problem dinne na yadda taqi barin zuciyarsa, yadda ya zama obsessed with her.
All of a sudden, yau Ummi ta fahimtar dashi komai ga wannan baqon lamarin da yake faruwa dashi. Farin shiga ne shi a wannan fannin, kuma abu ne da bai taba kawowa kansa shi kusa ba ko a mafarki kuwa.
But here he is, zuciyarsa falling deeply in love with a girl a ranar sa na farko a Kano! And he's falling deeper for her day by day to the extent that yake jin kamar he can't be without her!
Ya dago kansa yana sake kallon mudubi zuciyarsa na fada masa "So, This Is Love! all this while you're in love Fu'ad!" Miqewa yayi tsaye yana kallon sama ya cusa hannunsa cikin sumarsa da tuni ta bushe yana fitar da wata sanyayyar iska daga bakinsa kamin ya sauke kansa yana yin wani kalar murmushi dake daban da wanda ya saba yi, irin murmushin da duk wanda ya gani will fall for him over and over again.
"Idan har wannan shine son.. then I will keep falling for her till my last breath!!" Bathroom ya sake komawa ya daura alwala ganin lokacin sallah ya shiga ya fito ya wuce closet ya shirya kansa cikin wani black jeans da white long sleeve shirt na kamfamin Gucci ya zura flat takalmi na kamfamin givenchy ya fita zuwa masallaci.
Yau first in history na rayuwarsa, a addu'o'insa bayan ahalinsa da aikinsa yau ya saka da wata. Wani kalar doguwar addu'a da bai taba tunanin zai tsaya yayi irinta akan wata mace ba yau ita yayi. Still bayan ya idar ya sake roqar musu alkhairi both shi da ita.
Maimakon hankalinsa ya tashi da kalaman Ummi sam ko daya, daidai da sau daya hankalinsa bai tashi ba saima nutsuwa da yaji ya samu kawai na fahimtar ashe all this while soyayya ke dawainiya dashi bai sani ba. "Ashe you can love Fu'ad?" Zuciyarsa ya sake raya masa hakan da ya saka shi sakin murmushi shi kadai yana tafiya wajen guards dinsa da suka saki baki da hanci suna kallon yadda yake tafe yana murmushi shi kadai which is so unusual of him.
Bawai baida far'a ba, yana da far'a sosai amman a family dinsa kawai zaka sameshi relaxed yana far'a su din ma ba ko yaushe ba it depends on da wa yake tare. Yafi far'a idan yana tare da Pal dinsa fiye da kowa saboda yadda Fa'iz yake duk hade ranka ma zai saka ka dariya ne.
Hannu ya miqawa driver dinsa alamar ya basa key yabi hannun da kallo. "Afternoon sir."
Kai ya gyada musu yana cewa "afternoon, how're you all doing?" Tare suka amsa masa "na baku hutu duka yau bansan rakiyar kowa.." ya karashe yana amsar key dinsa ya wuce zuwa motarsa ya shiga.
Zama yayi yana karewa compound din hotel din kallo haka kawai yana jin wani nishadi na daban maimakon tashin hankali. Dama shi haka yake bai iya hiding feelings dinsa akan komai ba tun yana yaro. That's why Ummi tasha wahalar rabashi da Ammi wanda har yanzu ta kasa. Don shi idan yana yinka to kawai yana yinka.
Ba site ya nufa ba kawai haka ya samu kansa da zaga area din da suke yana wannan tuqin nasa kusan yau rashin saurin yafi na ko yaushe ma.
UMMI'S POV..
Kamar an tsikareta haka ta miqe tsaye a zabure tana figo mayafinta da mukullin motarta ta fita. Kallo daya zaka yi mata kasan hankalinta a mugun tashe yake duk gumi ya bata mata wannan fuskar nata da take mugun ji da ita.
Motarta ta shiga ta fita @360 tana nufar hanyar barin Abuja. Rabonta da zuwa wajen tun sanda ta haifi Fu'ad bata sake komawa ba. Ta ma manta da babinsa sai yau Allah ya tuna mata. Tasan ko karen hauka ya cijeta ba zata je wajen bonefather da wannan batun ba saboda komai sake lalacewa zaiyi bayan ita kuma mafita take nema hakan yasa ta yanke shawarar zuwa wajen Baba na kan tudu!
Tsohon bokanta da yake mata aiki ada kamin ta shiga kungiya ne. Aikinsa kamar yankan wuqa haka yake indai yayi maka aiki to zaka samu komai ya tafi maka daidai koma fiye da yadda kake so.
Awa daya tayi cif kamin ta dauki asalin hanyar da zata sadata da garin da yake. Wani irin kauye ne garin dake can kan kwari hakan yasa ake ce masa Baba na kan tudu. Gaba daya kauyen baiyi kama da gwamnati tasan da zamansa ba duk kuwa da cewa yana wajen da suke. Irin kauyen nan ne dake karkashin wani kauyen hakan yasa ko wuta ma basu da ita.
Haka ta rinqa sharara gudu akan kwazazzabai don ko titi basu dashi. Awa biyu da rabi tayi cif kamin tazo inda yake tayi parking din motarta da duk ta baci da kura tayi jajawur gata fara tass. Fitowa tayi tana saka face mask saboda kurar garin irin mai saka murar nan ce ta wuce wajen wata bukka dake nan ita kadai awajen.
Daman babu sallama atsarinsa sannan ita kanta sallamar ba tsarinta bace Fu'ad ne mai yawan sakata yin hakan. Kai tsaye ta yaye buhun da aka rufe kofar dashi a zuwan labule ta shiga.
As usual yadda ta sanshi tsahon shekaru haka yake sai tsufa da furfura da suka tarar masa. Bai dago ya kalleta ba har bayan data zauna ita kuma tayi shiru tana jiransa.
Ba tare daya kalleta ba yana ta bugunsa akasa yaja ya goge ya sake har fin minti biyar bai kulata ba yana ta zanensa aqasa. Yadda yayi ma zaka rantse bai san da wanzuwar wani mahaluki awajen ba bayanshi. Gashi dokarsa ce hakan don haka duk garajen Ummi haka ta haqura har zuwa sanda ya gaji ba tare daya dago kansa ba yace "kwana da yawa Zuhra.."
Shiru tayi bata ce komai ba sanin bai kammala magana ba "kin tuna damu kenan yau."
Ya sake dakatawa kamar yadda yake dabi'arsa idan yana magana "dama nasan ko ba dade ko ba jima zaki dawo... Barkanki da dawowa wajen tabewa!!" Ya karashe yana dago kansa ya sauke idonsa akan fuskarta.
"Kin sake dawowa dai akan wannan dan naki.. dan da kika saka akayi miki aiki akansa yau ma kin sake dawowa a sake yi masa aiki.... " Kasa ta duqar da kanta tana bashi tabbaci da kai "dafatan kin fahimci mu kadai ne za mu iya yaye miki damuwar duk wani abu daya shafesa hhhhhhhhhhh" ya qarashe da wata mahaukaciyar dariya da gaba daya tsukukin dakin nasa ya amsa.
"Me ke tafe dake?"
Babu bata lokaci ta bude baki tana cewa "Ina so kayi masa farraqu da yarinyar da yake so!!!! "
To be continued......
#like
#comment
#share