Free chapter · Read without an account

WHEN CIRCUMSTANCES DECIDE

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa



NURI'S POV...

Washe gari tun bayan asuba Mami tace kar ta koma ta kwanta ta shirya ta tafi makaranta don tunda Mami ta kwanta ta dena zuwa. Itama dama tana da niyyar zuwan don tasan abubuwa da yawa sun wuceta don ma dai tana duba pdfs din da ake turo musu ta waya amman dai ba kamar tayi attending lectures ba. Miqewa tayi ta fita waje ta hau gyara gidan yadda ta saba sai dai an dawo abinda ta tsana wato diban ruwa. Haka dole ta fita da safen nan ta debo ruwa sai dai iya nasu drum din ta cika ta bar na Inna haka babu ruwan. Ta kunna wuta ta dora ruwa sannan taje ta wanke 'yan kwanukan da suka bata. Sannan ta dawo ta sauke ruwan ta dumama ragowar abincin da ya kwana sai da yayi ta sauke sannan ta shiga wanka. Bata gama shiryawa ba sai 7:40 tayi wa Mami sallama bayan ta bata kudin makaranta daga ragowar kudin daya rage awajenta.

Mami na zaune bayan azahar tana gyara waken suya zata kai markade don tana saka ran da yamma za tayi awara. Tana cikin wankewa Inna ta fito ta tsaya daga bakin kofarta tana kallon Mami tana tabe baki. Sai data jira ta gama tsaf sannan tayi mata magana "idan kin gama kizo ina son magana dake.." kallon Inna Mami tayi tana ajiye bokitin hannunta hadi da dauraye hannayenta da ruwa tana cewa "to Inna gani nan." Inuwa ta mayar dashi sannan ta miqe tabi bayan Inna zuwa dakinta.

Azaune gefen gadon karfenta ta tarar da ita ta sake mata sallama jin bata amsa na farkon da tayi mata ba. "Nafa jiki Bintu amsawa ce banyi niyyar yi ba yawwa."

Zama Mami tayi daf da kofa tana yin shiru jin abinda Innar tace "Ya maganarmu Bintu?"

Shiru Mami tayi na dan lokaci ko Inna ba tayi mata bayani ba tasan me take nufi. "Sun kirani awaya sun jaddadamin akan hadin da suke son yi Bintu kuma sunce shi mutumin yace babba yake so ba yarinya ba saboda shi ba yaro bane..."

Mami dai bata dago ta kalli Inna ba don already ta gama sanin abinda take nufi karshe kawai take jira ta kai "to shine nace zan fada miki yace tunda ba yara bane ku yana so nan da sati biyu ayi komai kawai agama!!!"

Sai yanzu Mami ta dago ta sauke idanunta kan Inna dake magana da baki washe kamar gonar auduga.

"Inna sati biyi? Inna bafa dole bane auren nan!"

"Eh na san ba dole bane amman Audu yafi shekara yanzu da bacewa don haka zaki iya aurenki karkiji komai... Kuma ni gaskiya na gaji da zamanku anan ne. Wasu sunce suna buqatar gida kuma biyansu yafi naku shisa nake so ki tafi ita mai idon mayu sai ta dawo zama dani anan dakin..."

Shiru Mami tayi ta rasa ma abin cewa wanne irin rayuwa ne wannan da bata da zabin kanta. "Inna kiyi haquri amman ban amince da wannan auren ba!!"

Baki Inna ta saki tana kallon Mami da mamaki saboda yadda Mami ta fito kai tsaye ta fada mata abinda ke zuciyarta.

"Baki yadda ba Bintu?" Shiru Mami tayi mata bata amsa ba haka kawai tana ganin kamar rashin yaddar shine yafi mata.

"To ki tattara ya naki ya naki kubarmin gida nagaji da ganinki Kuma."

"In Sha Allah yau zamu bar miki gidan kamar yadda kike so.."

A tunanin Inna zasu roqeta ne yadda suka saba hakan yasa amsar Mami ta sake bata mamaki. "Fitar min daga daki.." babu musu ta miqe ta fice mata daga daki hankalinta yana rabuwa gida biyu.

Dakinsu ta shiga ta samu wuri daga can gefe ta zauna tana yin tagumi. Ta rasa ma me za tayi tunani akai hakan yasa kawai taji hawaye yana bin fuskarta. Ta rasa wacce kalar mace ce Inna da take da mugun son zuciya. Ita indai ba zata amfana da abu ba kawai shikenan.

Mami tasan yanzu idan suka bar gidan nan to sai dai suyi gararamba agari don bata da kudi ko kadan duk ya kare dan zaman da tayi a asibitin ahakan ma wai don Fu'ad ya biya komai na bill din asibiti. 

Idan ta amincewa Inna kuma bata san wacce kalar rayuwa zasu yi ba. Bata son rabuwa da yarinyarta sam don ta tabbatar Inna ba kular mata za tayi da ita ba. Miqewa kawai tayi ta fara tattara musu kayansu tana hadewa a waje daya can kuma sai ta dakata ta tsugunna tana bin kayan da kallo.

Wani tunani ne yazo kanta lokaci daya, idan ta dauki Nuri basu da kudi ina zasu je bayan duniyar nan ba abin yadda bace sannan ba kowa ne zai taimaka musu ba. Kamar zama agidan Inna shi ne kadai mafitar da suke da ita. Mutumin nan yace zai dauki nauyin karatun Nuri wanda bata so ya ruguje kuma ita bata da yadda zata tayi da kudin makarantarta, yace zai kula mata da yarinya duk da zata kasance tare da Inna. Sannan tasan ita kanta Inna ba zata cutar da Nuri ba kasancewarta jininta. Kawai za tayi nesa da 'yarta ne amman ai zata rinqa zuwa inda take itama kuma zata rinqa zuwa dubata.

Ahankali taji zuciyarta na nutsuwa da batun auren da Inna keso. To amman taya za tayi wa Nuri bayanin aure za tayi?

NURI'S POV

Agajiye suka fito qarfe shida lokacin kana ganinta kasan ta mugun gajiya. Gashi ba wani abin kirki taci ba saboda ba wani isasshen kudi ne tare da ita ba. Suna tare da qawarta Fauzah da tunda suka fito take ta zuba don Fauzah akwai surutu kamar tafi Zara ma.

Bakin titi suka fito zasu tsallaka Fauzah tace tayi mantuwa awajen mai cafe dake makarantar. Da kallo Nuri ta bita tana cewa "ni dai na tafi tunda hanyar mu daban dama..." Kai Fauzah ta daga mata tana cewa "shikenan sai gobe ki gaida Mami da jiki.."

"Za taji In Sha Allah" da haka suka rabu Nuri ta tsallaka titi ta tsayar da abun hawa da kyar suka daidaita ya kaita gida lokacin magariba tayi. Haka ta karasa gida jikinta kamar anyi mata duka saboda gajiya ta tarar da Mami tana alwala. Kallon kayan awara tayi da mamaki tana cewa "Mami sai da kika yi awarar nan?"

"A ina zan samu kudi Nuriyya idan banyi ba bamu da ko sisi agidan.."

Shiru Nuri tayi idonta yana tara hawaye tace "amman kika turani makaranta keda baki da lafiya Mami..."

Kallonta Mami tayi da kyau tana cewa "ni wuce ciki don Allah... Zaki hada ki saukemin rigimar gajiyar da kika kwaso da wannan..." Shiru tayi tana hadiye maganarta ta fada dakinsu tana share hawayenta ta ajiye jakarta sannan ta fito ta daura alwala ta koma ta tada sallah.

Bayan sun idar Mami ta kalleta tana cewa "kije ki debo abinci kici idan kin gama ki debo mana ruwa Nuriyya sannan don Allah ki debo da Inna kinji.."

Shiru tayi ba tace komai ba sai can tace "awarar zan soya miki fa.."

"Na hutar dake ki fara cin abincin tukunna sai ki debo ruwan..."

Miqewa kawai tayi ta fita tana cewa "banajin yunwa ni..."

"Zo nan Nuri.."

Juyowa tayi tana kallon Mami idonta har ya tara hawaye tace "dare zai yi idan na tsaya cin abincin Mami..."

"Abincin da zaki ci kawai.."

Haka dole ta haqura ta koma ta debo abincin taci sannan ta fita diban ruwan lokacin har an fara layin awara Nuri fuskar nan ahade haka ta gama jidon ruwan ta cika ko'ina sannan ta dibi ruwa ta shiga tayi wanka ta fito ta daura alwala ta koma daki ta tayar da sallah.

Kasa tashi tayi daga wajen jin cikinta ya kulle ya fara mata ciwo saboda dadewar da tayi bata ci abinci ba. Tana nan Mami ta shigo dakin bayan tayi wanka itama saboda kaurin suyar da take yi ta tayar da nata sallar.

"Lafiya Nuriyya?" Mami ta fada bayan ta idar da addu'ar da take yi ganin tunda ta shigo tana position daya. Kai kawai ta daga mata ba tare data dago kanta ba saboda yadda take ji kamar ana tsinka mata kayan cikinta.

Kusa da ita Mami ta karasa tana dago fuskarta tace "fadamin mene yake damunki..." Kai ta girgiza mata tana cewa "babu Mami gajiya ce.."

"Kin tabbata ba wani abun bane?" Kai ta daga mata Mami ta sake cewa "ki fadamin gaskiya Nuri bana son irin haka.."

Kuka ta fashewa Mami dashi tana cewa "Mami don Allah...." Sai ta saka kuka sosai harda shessheqa. Rungumeta Mami tayi tsam ajikinta tana shafa bayanta da sigar rarrashi ta kasa magana. Ita dake shirin fada mata abinda ke shirin faruwa amman ganin haka sai ta hadiye maganarta aranta tana rarrashinta "kiyi haquri kinji tashi muje ki kwanta idan kika yi barci zaki dena jin komai kinji... Tashi muje taso ki kwanta kinji yarinyar kirki taso..." Mami da kanta ta dagota taje ta kwantar da ita kan 'yar katifarsu tana dora kanta akan cinyarta tana shafa gefen fuskarta "It's okay, kinji... ya isa kukan haka nan. Ko kina son wani abun ya faru dani ne haskena?"

Kai ta girgiza mata Mami ta sake cewa "yawwa haskena 'yar albarka kiyi bacci kinji zan miki addu'a.."

Saboda Mami ta dena kukan tana qanqameta kamar za'a kwance mata ita. Da haka baccin azaba ya dauketa don har sannan cikin nata bai dena ciwo ba ita kuma tace ba zata sanar da Mami ba.

Da kallo Mami ta bita jin yadda numfashinta yake sauka alamar tayi bacci hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tana shafa gefen gashinta daya bayyana tana jin wani mugun tausayinta. Har bata son tunawa da cewar ta amince da kudurin Inna. Yaya Nuri za tayi idan Mami ta sanar da ita batun auren? Batun rabuwar da zasu yi?

To be continued...

#like
#comment
#share 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.