Free chapter · Read without an account
HER PAIN, HIS ACHE
by Saddiqah M · NURI
NURI
BY Saddiqa
Da dare ciwon cikin Nuri ya tsananta sosai da ya saka Mami noticing don ba bacci take ba tana kan sallaya tana sallah. Kallon yadda ta riqe ciki tana juyi Mami tayi kamin tayi saurin miqewa ta nufi inda take "Nuriyya." Hankalin Mami tashi yayi ganin yadda ta hada zufa. Tabata tayi tana kiranta "Nuriyya... Nuriyya... Ke kalleni Nuri.."
Sam bata jin abinda take fada saboda kamar hankalinta ya fara gushewa muryarta ma daga nesa sosai take ji. Ahankali bakinta ya fara motsawa amman muryarta bai fita hakan yasa Mami ta durqusa kusa da ita tana cewa "gani nan mene ne fadamin..."
"Mami cikina zan mutu..." Hankalin Mami idan yayi dubu ya gama tashi ta tabbatar ulcer dinta ne ya tashi don kalar haka yayi mata time din da aka tabbatar tana dashi. Wayarta Mami ta kunna ta kalli lokaci hudu saura na dare. Nuri ta sake kalla ganin yadda take juyi kana gani kasan tana mugun jin jiki.
Miqewa tayi da sauri ta dauki kofi ta tsiyaya pure water ta fara mata addu'a aciki ko zai lafa mata kamin safe yayi ta kaita asibiti. Hannunta yana damqe da nata haka tayi mata tofin sannan ta dagota jikinta ta bata. Mayar da ita tayi ta kwantar da ita ta cigaba dayi mata addu'ar daga haka. Har hudu da rabi suna nan cikin nata bai dena ba kamar ma daduwa ciwon yake don numfashinta yanzu har kamar yana daukewa idan ya fara murda mata. Sai dab da za'a yi kiran asuba ya lafa mata har baccin wahala ya dauketa Mami ta buga tagumi tana kallonta cike da tausayi. Sai bayan minti biyar da taga baccin nata ya danyi nauyi sannan ta miqe ta fita waje ta dauro alwala tazo ta tayar da sallah. Ganin ta samu bacci yasa Mami bata tasheta ba sai dab da karfe shida sannan ta tasheta.
Kallo daya zaka yi mata kasan bata da lafiya dare daya kawai gaba daya ta zabge. Miqewa Mami tayi ganin tana tafiya da kyar ta kamata suka fita waje ta zuba mata ruwan alwala ta kaita bandaki ta jira har ta gama ta fito sannan ta kara mata ruwa a butar ta tsugunna ta taimaka mata tayi alwalar suka koma daki ta saka mata hijab a zaune tayi sallahr tana idarwa ta kwanta anan wajen.
Mami ta dawo kusa da ita ta shafa fuskarta taji kamar zafi hakan yasa ta taba wuyanta taji jikinta ya dauki zafi kamar zazzabi haka.
"Ina keyi miki ciwo Nuri?"
Cikinta ta nuna mata hawaye yana bin fuskarta da kyar ta furta "Mami ki kaini asibiti don Allah..." Da kuka ta karashe saboda wani murda mata da cikin yayi. Miqewa da sauri Mami tayi ta saka hijab dinta ta fita waje garin fayau babu kowa saboda farar safiya ce. Bakin titi taje ta tsaya ko zata samo napep amman shiru ranar kamar an daukesu babu ko daya. Sai can ta tuna asabar ce kuma ranar sanitation ne sai karfe goma suke fitowa.
Jiki a sanyaye ta juya ta koma gida. Wani baccin wahalar ta tarar ya sake dauke Nuri hakan yasa ta gyara mata kwanciya ta zauna ta buga tagumi tana kallonta. Shiru har bayan karfe tara bata farka ba hakan yasa Mami matsawa kusa da ita tana tabata taji tana numfashi ahankali ahankali. Miqewa tayi ta fita waje ta fara gyara gidan ga Inna ta fito sai mitar rashin ruwa take hakan yasa dole Mami ta dauki botikan ta fitar dasu ta hau layi zata debo ruwa. Minti ashirin tayi anan kamin layi yazo kanta ta matsar dasu zata kunna famfo taga wani farin hannu ya kunna mata yana cewa "Mami kije zan debo miki..."
Ahankali ta dago fuskarta ta sauke kan Fu'ad dake sanye cikin wandon track suit baqi da black T-shirt. Kallonsa Mami tayi na wasu sakanni kamin tayi murmushi tana cewa "a'a yaron kirki zanyi ...."
Murmushi kadan yayi kansa a kasa yace "kije kawai Mami ki huta zanyi...." Murmushi Mami tayi masa tana cewa "Allah yayi maka albarka nagode sosai dan albarka..."
Aransa ya amsa afili sai murmushi kawai yayi ya tara mata botikin ita kuma ta wuce ta koma cikin gida. Sai daya cika mata botikan data kawo tsaf sannan ya dauka da biyu biyu ya kai kofar gidan yayi knocking. Yana knocking ya juya ya koma cikin site while Mami na budewa ta hau shigar dasu daya bayan daya ta ajiye a inda suka saba ajiyewa.
Wuta ta kunna ta dora musu ragowar abincin jiya da basu wani ci ba ta dumama. Karfe sha daya dot wani azababben ciwon cikin ya sake tada Nuri wannan karon kuka ta fashe dashi sosai mai sauti wanda kana ji zaka san ba lafiya ba. Kukanta ne ya jawo hankalin Mami ta dauraye hannunta daga kumfar wanke wanken da take ta rugo dakin nasu. Ganinta tayi tana rolling adakin hannunta dafe da cikinta tana yarfewa ga gumi duk ya jiqata.
"Nuriyya... Nuriyya.. haskena.." dagota tayi jikinta tana shafa gefen fuskarta "sannu bara mu tafi asibiti kawai sannu kinji..." Hijab ta zura mata taje ta dauko kudin awarar da tayi jiya wanda baifi 6500 ba gaba daya ta dawo ta kamata suka fita Nuri tana tafiya da kyar da kyar ahaka har suka isa bakin titi ta samu inuwa ta zaunar da Nuri tana tsare musu abun hawa.
Daga bakin site yana sallama da maginan da suka karaso idonsa ya sauka akansu. Kallo daya yayi musu yasan ba lafiya ba wanda hakan ya saka hankalinsa tashi lokaci guda ganin Mami tare da ita and by mere looking itace babu lafiya. Sallamarsu yayi ya nufo wurinsu Mami da sauri sauri.
Daidai Mami ta tsare napep Fu'ad ya karaso yana cewa "Mami lafiya??"
Kai Mami ta girgiza masa tana kallonsa tace "Nuriyya ce babu lafiya tun daren jiya..."
"Subhanallahi bara na dauko mota Mami sai muje asibitin.."
"A'a dan albarka ka bari ga napep na tare sai mu wuce aciki."
"A'a Mami." Ya fada yana sallamar mai napep din ya juya da sauri ya dauko motarsa zuwa inda suke. Idonsa akan Nuri yana jin kamar ya dawo da ciwon nata jikinsa ganin yadda Mami take taimaka mata yasan she's in serious pain. Budewa Mami back seat yayi suka shiga sannan ya koma shima ya shiga driver seat ya kunna motar suka bar wurin.
Asibitin da Mami ta kwanta ya nufa dasu sai dai wani kalar gudu da bai saba yi ba yau shi yayi hankalinsa gaba daya yana tare da ita ganin yadda take juye-juye acikin motar.
Yana parking ya fita ya kirawo nurse suka zo suka dauki Nuri aka wuce da ita emergency da sauri suna bin bayansu. Abakin kofa Mami ta tsaya tana karfafawa kanta gwiwa kar tayi kuka with the hope yarinyar ta zata samu lafiya.
While Fu'ad yana can gefe ya samu waje ya zauna azahiri zaka rantse baida wani damuwa sai dai deep down kamar yafi kowa damuwa. He was just praying for her, yana mata fatan samun lafiya. Ganin yadda Mami ta tayar da hankalinta yasa ya tabbatar abinda ke damunta was serious hakan ne yake sake daga masa hankali. Ga wayarsa yana ta vibration alamar kira amman yayi ignoring hankalinsa da komai nasa yana can tare da ita.
Thirty minutes kawai likitocin suka yi suka fito suna zare mask dinsu. Miqewa Fu'ad yayi ya qarasa inda suke kamar yadda Mami tayi. Yana zuwa yaji Mami na cewa "likita tana lafiya?" Kai daya ya daga musu while dayan barin wajen yayi yana excusing kansa.
"Alhamdulillah tana lafiya ta samu bacci amman hajiya ya akayi ulcer dinta ya zama chronic har haka..abin was serious da har zai fara gusar mata da hankali. Binciken mu ya nuna bata cin abinci yadda ya kamata gaskiya, a yadda muka duba har da malnutrition ma.."
Kasa Mami tayi da kanta hawaye yana taruwa a fuskarta. Yau wai ita ake fadawa yarinyar Abdullahi akwai malnutrition atare da ita, ciwon yunwa yake damunta. Wani kalar kewar Abba ya rufeta ta tabbatar da yana nan kaddara ne kawai zai sa hakan ya faru though yanzun ma kaddara ne. Kai kawai ta daga masa ta kasa magana "ga magunguna nan a siyo mata sannan don Allah akula da ita sosai idan irin haka ya sake faruwa da ita gaskiya bazai zo da sauki ba sam.."
Fu'ad ne ya amsa takardar da yake miqawa Mami yana kalla duk da ba fahimtar komai zai yi ba. Ya kalli yadda Mami ke share hawaye da gefen hijab dinta. Wani kalar tausayinsu gaba daya yazo ya rufeshi at that time ji yayi dama yana da halin da zai yaye musu wannan damuwar.
"Ki shiga ciki Mami.." da kyar ta fara takawa har ta shiga ciki ta nufi wajen da Nuri ke kwance da drip ajikinta. Kwantar da kanta Mami tayi agefen fuskarta tana hana kanta kukan rashin Abba data mugun hadiye aranta.
Hakan ya mugun karya zuciyar Fu'ad da yasashi fita da sauri. He can't stand yaga kukan Mami, yana mata kallon Ummi ne domin ta haifi wadda yake jin ta zamar masa tsoka da jini.
Takardar hannunsa ya karewa kallo na wani lokaci zuciyarsa na tuno masa abinda akace yake damun Mami wancan karon wanda hypertension ne sannan likita yace masa damuwa ne ya jawo mata and now Nuri was suffering from a chronic ulcer. Hadasu yayi tare ya tabbatar dalilin ciwukan nasu zai iya zama daya.
Dakin da take ya kalla yana jin dama yana da yadda zaiyi ya yaye mata ciwon or maybe ciwon ya dawo kansa ita ta huta....
To be continued....
#like
#comment
#share