Free chapter · Read without an account

THE PROPHECY

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa

UMMI'S POV.....

Zane ya fara yi a kasa yana yi yana gogewa yana sake sabo na tsahon minti uku kafin ya dago ya kalleta da wannan jajayen idanun nasa masu sifar ban tsoro ya kureta da ido sannan ya sake duqawa yana cigaba da abinda yake shima na good three minutes.

"Ke wannan yaron naki bana ganinsa ma bare nayi aiki akansa. Kalla kiga yadda wani haske ya rufeshi gaba daya bama a iya ganinsa..."

Gaban Ummi ya fadi jin abinda yace "kinsan aiki akan irinsu da wahala dai ko kamar yadda muka yi dake waccan karon akan ALIYYU ARDO Ina tunanin wannan karon ma sai dai ki haqura fa."

Kai Ummi ta girgiza da sauri hankalinta yana mugun tashi "Baba don Allah ka...." Hannu ya daga mata yana cewa "dakata... Kinsan ba'a kiran sunan Allah anan wajen sarai ko?"

Kai ta gyada masa tana saurin cewa "kayi haquri bazan sake ba mantawa nayi."

"Na tuna miki yanzu."

"Ka duba kaga idan akwai wata hanya kaji Baba."

"Babu hanya ko daya akan yaron nan naki. Yana da addini shi akaran kansa amman kuma ba addininsa ne yasa baza'a iya aiki akansa ba da alama tun farkon sanda aka haifeshi akwai wani tsari da kuma wanda yake yi masa addu'a daga gefe..."

Wani baqin ciki yazo ya tsayawa Ummi arai... "Waye zai masa addu'o'in tsari bayan ni mahaifiyarsa?"

"Kin manta yadda kika sameshi ne???"

Gabanta yayi wani mugun faduwa lokaci daya tana kallon Baba na kan tudu. "Taya akayi yasan ta hanyar da aka samu Fu'ad? Bayan babu wanda yasan wannan sirrin da aka binne shekaru ashirin da tara da suka wuce" Ta tambayi kanta aranta amman sai ji tayi Baba yayi dariya yana cewa "kina tunanin bansan hanyar da aka samu yaron naki bane? Babu abinda bamu sani ba kamar yadda babu aikin da zamu iyayi akansa."

"Baba ka duba wata hanyar mana bana son alaqarsa da yarinyar kwata-kwata.. "

"Sai dai ko ta bangaren yarinyar zan gwada bi naga idan akwai yadda za'a yi"

Maida hankalinsa kan qasarsa yayi yana zane yana sake gogewa ba'a dau lokaci ba ya kalli Ummi yana cewa "ai ita yarinyar kinga bata sonshi shine wanda yake sonta kinga kuwa sai dai kiyi haquri sannan da zan baki shawara ki dauka da na baki"

Tana kallonsa tace "mene ne Baba? "

"Da zaki haqura da rabasu da kin kyautawa zuciyarki don tabbas akwai wani abu dana hanga a taurarinsu rabasu daidai yake da raba kanki da kwanciyar hankali... "

"Amman kace bata sonshi Baba?"

"Eh tabbas yanzu bata sonshi amma zata so shi nan gaba kuma kamar yadda na fada miki ne rabasu daidai yake da rabuwarki da kwanciyar hankali"

Da sauri ta dafe kirjinta hankalinta yana sake tashi fiye da dazu tace "kana nufin sai dai na zuba ido Fu'ad ya auri yarinyar nan bayan an haramta masa aure a duniya!!!"

Wata shewa Baba yayi yana tafa hannaye kana gani kaga dan duniya "to ki rubuta ki ajiye danki zai yi aure kuma wannan yarinyar da ba kyaso ita zai aura kuma aure ne za'a yi shi mutu karaba... "

Idan aka ce wannan zancen yafi komai dagawa Ummi hankali arayuwarta ba'a yi karya ba. Auren Fu'ad yana nufin rushewarta wadda ba zata taba so ko kauna ba.

"Baba babu wata mafita? "

"Babu gaskiya ta bangarena sannan ko wajen wa zakij je haka zai fada miki amman zaki iya gwadawa idan baki yadda ba. Sai dai zan fada miki wani abu guda daya kar ki kuskura kiyi tunanin cutar da daya acikinsu don duk abinda kika yi yunqurin yi kanki zai dawo. Na duba naga ita wannan yarinyar ma kamar akwai wani abu nata mai muhimmanci da kika rabata dashi!!!"

Wani kalar zaro idanu Ummi tayi tana cewa "ni kuma Baba? Yarinyar da ban taba gani ba hasalima ban santa ba!"

Kai ya jinjina yana cewa "tabbas gashi na gani kinci bashinta bazan miki karya ba."

Wani kalar gumi ne yake bin Ummi tun daga fuskarta har zuwa kafarta yana diga "zaka iya fadamin bashin  mene Baba?" 

"bazan fada miki ba don kin fini sani ma. Kije kiyi tunanin kalar abubuwan da kika aikata a duniya aciki akwai wanda yabi ta kanta!!! "

Kallonsa kawai Ummi take yi shi kuma ko ajikinsa sai sake cewa yayi "na gani Zuhra, bashin nan zai biki kuma yana daya daga cikin abinda zai rusaki nan gaba... "

Da kusan ihu tace "dakata Baba banzo wajenka don ka fadamin wannan maganganun ba.. tunda ba zaka iya biyamin buqatata ba shi kenan zanje inda za'a iya biyamin.. "

"Qofa abude take Zuhra kuma ina mai tabbatar miki da duk inda za kije abu daya za'a fada miki. Bara na kara miki da abu guda daya ta silar yarinyar nan qarshenki zai zo."

Afujajan Ummi ta miqe tana masa wani mugun kallo ta fita tana sakin huci. Bata zo nan don ya fada mata kalar abubuwan nan ba. Tazo ne don a shiga tsakanin Fu'ad da yarinyar da yace mata yana so.

Kasa tuqa motarta tayi bayan ta shiga kawai ta zauna tana tuna maganganun Baba na kan tudu. Ta sanshi ta san aikinsa kamar yankan wuqa yake kuma bai taba fadar abu ba daidai ba. To amman yanzu sam zuciyarta ta kasa yadda da abinda ya fada.

Da kyar ta samu courage din tayar da motarta ta bar wajen sai dai hankalinta idan ya kai dubu to ya gama tashi. Tunaninta ya rabu zuwa waje daban daban.

Ta tafi son ta tuna ko tasan yarinyar ammn ko sunanta bata sani ba bata san komai akanta ba to taya zaice ta taba cutar da yarinyar a baya me tayi mata? Kusan wannan yafi komai tsaya mata arai. Har ta shiga cikin Abuja bata hayyacinta gaba daya ta takura kwakwalwarta da son tuna ta inda ta cutar da wadda bata sani ba. Ahaka taje gida da wannan tunanin da ta kasa samo ko abu daya da zai tuna mata ta inda tasan yarinyar.

Tsabar kanta ya kulle wrong parking tayi sannan ko cire mukullin motar ba tayi ba ta fita ta wuce part dinta kai tsaye zuwa dakinta. Tana shiga ta zare dankwalin kanta tana zama gefen gadon ta dulmiya duniyar tunani.

Taje don samun mafita an bata mata komai! Tuno da zancensa na yadda ta samu Fu'ad ya sakata miqewa zumbur tana share gumi. Taya sirrin da mutum hudu ne kawai suka sani zai zama wani can ya sani. Taya akayi ma Baba yasan wannan sirrin bayan a iya saninta bata taba fadawa kowa ba?

Ita kanta mantawa take yi da yadda ta samu Fu'ad kuma bata son tunawa kwata-kwata. Akwai abubuwa da yawa da suke lullube da duniyar Fu'ad da shi kansa bai sani ba. Wata iriyar rayuwa yake da duk duniya babu wanda ya sani sai ita ciki har dashi Fu'ad din da kansa. Fu'ad kusan shine mukullin dukkan wasu kulluka data aikata a doron duniya. Ta hanyarsa ne kawai asirinta zai tonu shi yasa bonefather ya fada mata idan yayi aure komai nata zai ruguje saboda asalin komai nata ya samu ne daga haihuwar Fu'ad, silar kudinta da komai na rayuwarta Fu'ad ne! Komai nata Fu'ad ne! That's why Fu'ad was a treasure a wajen Ummi!!! Fu'ad was everything to Ummi. Wannan yana daya dag cikin babban dalilin da yasa take bala'in ji da Fu'ad aduniyarta!!

Ba zai yu ta zauna ta zuba ido Fu'ad yayi aure ba! Dole ta samo mafita zama ba nata bane, bai ma ganta ba! Hakan yasa ta dauki mayafinta ta sake shirin fita ta fara neman mukullin mota ta tuna kamar bata cire ba hakan yasa ta fice babu bata lokaci ta sake daukar sabuwar hanya daban. Ga sam bata da kawa wadda take abu da ita don one thing data yadda da shi shine no matter yadda kake da kawarka indai ba abin arziqi ne zai hadaku ba to one will go after the other.

FU'AD'S POV...

Yana tsaye bakin kofar dakin da aka kwantar da Nuri. Yana so ya shiga ciki amman Mami tana ciki shi kuma nauyinta yake ji irin sosai dinnan. Sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa yake mugun jin kunyar Mami ashe ya samo asali daga zuciyarsa ne. Ajiyar zuciya ya sauke yana jinsa wani iri kamar baya da lafiya haka duka saboda wacce yake ji da ita
bata da lafiya. Bude dakin aka yi yayi saurin dagowa yaga Mami ce sai yayi kasa da kansa yana matsa mata hanya don akan hanya yake atsaye.

"Ka shiga ciki kaji ta farka bara naje na fadawa likita." Kai ya gyada yana sake matsa mata hanya ta wuce shi kuma ya saka hannu ya bude dakin da take ya shiga ciki da sallama abakinsa.

Tana kwance idanunta suna kallon sama fuskar nan nata kamar ba nata ba duk ta fada na dare daya da safiya kawai. Tsayawa yayi daga bakin kofa yana karewa fuskarta kallo ganin yadda ta sauya a idonsa sosai kana gani kasan bata da lafiya.

Ahankali ya daga kafarsa ya fara takawa zuwa inda take ya tsaya daga gefenta yana kallonta. Jin inuwar mutum akanta yasa ta juya kanta idonta ya fada cikin nasa. Sai dai sabanin yadda ta saba da sun hada ido ta dauke yau yaqi bata wannan damar ya kafeta da idanu yana aika mata da wani kalar kallo tun daga zuciyarsa.

Da kyar ta janye idanunta daga kansa tana jin dakin yayi mata kadan saboda kasancewarsa. "Ya kike so nayi idan kina wasa da cin abinci?"

Bata gane abinda yake nufi ba hakan yasa ta dago fuska zata sake kallonsa ta tuna abinda ta gani a idonsa da bata taba gani a idon wani da namiji ba. Don haka sai ta fasa kallonsa ta dake tana kallon waje daya a sama amman zuciyarta yana tare dashi.

"Kina son wani abun ya sameni ko?" Bata motsa ba sam kawai banda bugawa babu abinda zuciyarta take yi. Kujerar dake wajen ya jawo ya zauna yana matsowa kusa da ita dab yayi qasa da muryarsa yadda babu wanda zaiji abinda zaice bayan ita da yake da ita "ki dinga kula da kanki ko ba don kowa ba sai don wanda suka damu dake don Allah!!"

Kusancinsu ya sake sanya mata bugun zuciya fiye da wanda take yi abaya "ki daina wasa da abinci please kina son wani abun ya sameki ko NABDI"

"Ya Ilahil Aalameen" shine abinda Nuri ta furta aranta tana runtse idonta da qarfi. Da ace Fu'ad yasan kalar yadda yake tarwatsa mata zuciya da wannan ordinary kalaman nasa da yayi shiru. Common words ne da kowa zai iya fada mata amman ta rasa mesa komai idan ya shafesa take jinsa daban. Common magana idan yayi mata sai taji ta daban aranta.

"kalleni." Ya fada in a low tone, shi kansa daban din yake ji aransa daga lokacin daya fahimci so ne yake dawainiya dashi. Kai ta girgiza masa da sauri don ta tabbatar ba zata iya kallonsa ayanda take jin zuciyarta daban akansa ba.

"Shi kenan tunda ba zaki kalleni ba.." yadda yayi maganar kamar wani yaro da bai samu abinda yake so ba. Miqewa tsaye yayi daga kan kujerar da yake ya dan duqo da fuskarsa dab da nata da wannan muryar nasa mai tsayawa arai ya furta "ki kularmin da kanki har naje na dawo... Amana na baki." Miqewa ya sakeyi yana kallon fuskarta da duk duniya itace abu na farko da yaji baya taba gajiya da kallo ya zura hannayensa aljihun wandonsa yana yin taku baya kadan yace "take care." Bata kalleshi ba shima kuma bai saka ran zata kalleshi ba ya juya da niyyar zuwa pharmacy ya basu takardar da likita ya bashi Mami da doctor suka shigo.

Qasa yayi da kansa yana basu hanya suka wuce "tafiya zaka yi?" Mami ta tambayeshi ganin ya nufi hanyar fita "eh Mami zanje pharmacy na karbo mata magani.." kallonsa Mami tayi, da akwai wani intense care da yake fita akalamansa dashi kansa bai sani ba... It looks like duk wani abu indai ya shafeta muhimmancinsa daban yake awajensa da har baya iya boyewa.......

To be continued...

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.