Free chapter · Read without an account

9-10

by zahra muhammad · TSOHON ƊAN BARIKI...

Koda ta fito falo bata tsayaba ɗakinta ta wuce ta kulle kanta ta haye gado ta rushe da kuka,yama zaayi ta iya rayuwa kulle acikin gidansu,kuma wai ba waya wannan ay cutarwace agareta.
Da sauri ta zaro wayarta ta turawa laila sms ta shaida mata hukuncin da mahaifinta ya yanke,sannan ta kashe wayar dan kar lailar ta
Kirata daddyn ta yaji.Ranar ko abinci ba ta nemaba,haka ta kwana da yunwa tana kuka.
Koda gari ya waye ta fito taje ta gaida mamynta sannan ta bata wayar,tace daddyntane ya ƙwace.
"kuna ɓoyemin abinda ya faru kea daddynki amma tabbas akwai wani abu da kikayi fareeda wanda har ya fusata abbanki haka inba haka ba mezesa ya miki wannan hukuncin"cewar mamy cikin damuwa.
Shuru fareeda tayi dan batasan me zataceba,hakade mamy tasata agaba tana ta mata faɗa kan sanin daraja da mutuncin kai amatsayinta na ƴa mace.

********
A nashi ɓangaren Alhaji buba tun ranar da daddy ya kamashi da fareeda hankalinsa ba akwance yakeba,dan yafi uban kowa sanin waye daddy,
Ga yaranshi guda uku ƴan mata dake gidansa,sun dawo hutun makaranta daga london,yasan tunda har ya ci masa ƴa shima dole ze maida biki shiyasa hankalinsa yatashi matuƙa.Musamman yanzu daya samu labarin an sallameshi a asibiti.
Rashin natsuwarsace tasa yaje ya,siyowa yaran nashi hijabai da niƙabi da safa,ya kawo musu gida inda yasa ummansu ta kirawo masa su.
Jidda,rahama,da husna,haka rahama da husna suka shigo cikin falon suna taunar cingam,yayinda jiddace kawai ta shigo cikin natsuwarta.
Kan carpet jiddah ta zauna yayinda su husna kuma suka haye kan kujerar suka harɗe husna tace"abba gamu ance kana kira hope de komai normal?"ta faɗi tana tsureshi da ido.
Gyara zama yayi ya dubesu fuskarsa ɗauke da damuwa yace"yau an mana waazi a masallaci kuma waazin ya shigeni sosai kan tarbiyyar ƴaƴanmu mata"
"akace me a waazin?"cewar rahma.
"ance mu hanasu fitar da kwalliyarsu waje sabida kariya daga zinace zinace dan haka daga yau har hutunku ya ƙare wainnan kayan zaku dinga sawa in zaku fita"ya faɗi yana miƙawa kowaccensu nata.
Amsa sukai da sauri suka buɗe,ayko agigice su rahama da husna suka dubeshi suka haɗa baki wajan faɗin"abba mune zamu dinga saka wannan ƙaton abun?Haba abba in bamuyi adonba angani waye zece yana sonmu nide wallahi bazan iya sawaba"cewar rahma wacce ita ta ƙarasa bayanin.
"ba raayinku na nemaba wannan umarnine kuma duk wacce nasamu ta karya wannan umarnin zata gane kurenta"cewar Alhaji buan afusace.
Ayko haka rahama da husna suka miƙe riƙe da hijaban suka bar alon suna diddira ƙafa aƙasa,alamun ransu bayaso.
Itako jidda duƙawa tayi har ƙasa tai godiya sannan ta ɗauki nata ta wuce nata ɗakin abban nasu yabi bayanta da kallo yana me alfahari da godiya ga Allah daya bashi ita a mazaunin ƴarsa dannkaf cikin ƴaƴansa itace ta daban wacce Allah ya bashi me tsananin  kunya tarbiyya da kuma biyayya.
**********
Haka rayuwar taci gaba da garawa yanzu hankalin alhaji buba ya kwanta tunda yasan yanzu ya adana yaran nasa,duk motocinsu yasa musu tinted ga hijabi da niƙabi,duk yasa musu agida kawai suke zama babu 
Duk da ya adana nashi ƴaƴan kullum yana adduar sake haɗuwa da fareeda dan ya sake cinta koda so ɗayane dan aduniya be taɓa cin durin da yay masa daɗi irin nata ba,ga numbobinta duka basa shiga,yaje makarantarsu ance masa ta dena zuwa,sosai yake jin damuwa da kewarta aranshi .
Yau daddy ya kimtsa ya nufi office ɗin Alhaji buba dan tun bayan faruwar abun be bari sun haɗuba ko majalisar da suke zama ya dena zuwa shiyasa yau ya shirya yaje ya sameshi.
Tura ƙofar office ɗin yayi ya shiga kamar yadda ya saba.
Ƙamshin turarenshine ya sanar da alhaji buba ko waye ya shigo tun kan ya ɗago kansa.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.