Free chapter · Read without an account

THE DREAM

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa


FU'AD'S POV...

Hanging towel din dake hannunsa yayi kan hanger dake bakin bathroom ya karasa cikin dakin ya samu waje nan kan sofa ya zauna yana miqe kafarsa kan center table dake wajen. Relaxing sosai yayi shi ba akwance ba shi ba'a zaune ba yana lumshe idonsa. For some moments haka ya zauna yana barin brain dinsa ta huta ba tare da tunanin komai ba sai dai inaa.. Fu'ad din da ne yake iya yin hakan yanzu an samu wata wadda komai yake tana tare dashi a tunaninsa.

Hakan kawai daya raya yasa shi sakin murmushin gefen baki yana bude idonsa ya miqa hannu ya dauki wayarsa yayi dialing number din Fa'iz. After several ringings yayi picking daga can yana masa sallama.

Komawa yayi ya kwanta yadda yake da yana sake rufe idanunsa ya amsa sallamar nasa yana adding da "ina ka shiga kwana biyu ko nemana ba kyayi Fa'iz.."

"Ina Houston fa!"

"Houston?"

"Eh jiya nazo ma.."

"Ban gane kana Houston ba? Me kake acan and why didn't you inform me about it?"

"Abbu ne baya da lafiya?"

Idanunsa ya bude yana kallon sama yace "subhanallah mene ya samu Abbun?"

"Ciwonsa ne ya tashi akace za'a yi masa aiki Alhamdulillah kaga ma anyi aikin day before yesterday and it was successful.."

Idanunsa ya sake rufewa ya gyara kwanciyarsa ya kwanta daidai unlike yadda yake dazu "ammn baka fadamin ba Pal.."

"I'm sorry Pal, amman na kira wayarka jiya duk baya shiga nasan network ne sannan nayi dropping maka message baka duba ba seems like you're busy tunda kaje Kano dinnan ka rage replying messages din mutane in fact ka dena neman mutane ma.."

Tsaki kadan Fu'ad yayi yana cewa "I didn't really get what you're saying here Fa'iz, just admit it I'm ignoring you ba na dena reply wa mutane ba."

"As you said Pal, tell me aikin was it that though daya dauke maka hankali kake mantawa da amininka."

Shiru Fu'ad yayi lokaci daya yana tunawa da Nuri da yasan babu tantama she's the one da tayi diverting hankalinsa daga kan komai.

"Fa'iz Aliyyu. "

"Yes Fu'ad Aliyyu."

Murmushi sosai Fu'ad yayi har Fa'iz yana jiyo sound dinsa daga can side din hakan yasa Fa'iz saurin gyara kwanciyarsa yana cewa "seems like da akwai magana abakinka Pal fadamin what is it that will make you smile like this Fu'ad?"

"Finally, I've fallen for someone Fa'iz!!!"

Wani irin ihu Fa'iz yayi yana miqewa daga kwancen da yake yace "repeat what you've just said Fu'ad don Allah.."

Murmushi Fu'ad ya sake yi kamin ya sake furta "Fu'ad Aliyyu Jimeta has fallen for someone kaji ko na maimaita.." Kai Fa'iz ya girgiza da sauri yana cewa "ah naji wallahi wannan ma ya isa."

If kunga yadda bakin Fa'iz yaqi rufewa you can swear shine wanda ya fadama wani ba Fu'ad ba, kawai he was overwhelmed and shocked at the same time irin like no one da zai taba kawowa ransa Fu'ad will fall for someone in years ahead talkless of ace this year "kai nifa I really can't believe you Fu'ad.. wai kaine kake cewa you're in love are you for real man?"

Miqewa zaune Fu'ad shima yayi fuskarsa amugun sake da kana gani zaka san yana cikin farin ciki yace "as you heard Pal, dagaske nake maka.. "

At that moment Fa'iz ji yayi dama suna tare da Fu'ad kawai saboda yaga fuskarsa hakan yasa yayi saurin cewa "look Pal let's switch to video call I wanna see your face"

"Saboda kamin isakanci ba to anqi " ko saurarasa Fa'iz baiyi ba ya katse kiran yana kiransa video call. 

Kamar Fu'ad ya rabu dashi yaqi dauka sai kawai ya girgiza kansa ya amsa yana dan hade fuska irin karma Fa'iz ya kawo masa rainin nan shi ga Boss 

Yana picking Fa'iz daga can ya qarema fuskarsa kallo tsaf kamin ya fara dariya sosai yana kallon Fu'ad. Baki Fu'ad ya saki da farko yana kallon Fa'iz sai daga baya da yaga abin nasa bana qarewa bane sai ya hade fuska yana binsa da kallo "I'll end the call man."

Da sauri Fa'iz ya dan dakata yana toshe bakinsa ya furta "ah no wait I'm sorry.." ya dan nutsu yana shiga hankalinsa amman kana ganinsa kasan dariya yake son yi Fu'ad yayi saurin rigashi furta "me abin dariya anan?"

"I'm thinking of wacce yarinyar ce wannan that will make you fall for her? Kai dinnan da kallo daya kawai kake wa mace, kace finally an samu wadda ka tsaya ka karewa kallo kenan."

Shiru Fu'ad yayi shi dama yasan ba abin arziqi zai ce masa ba "during our early twenties time din you always said kai kanajin sai dai fa kawai ayi maka auren hadi don baka da time din zabar wadda zaka so and now with all due respect Mr CEO yaushe ka samu time din zabar wadda ta dace da kai?"

Shiru Fu'ad yayi masa yana jiran ya gama duka surutan nasa "wait Man.. fadamin ya komai ya tafi ehnn wai ni yama akayi hakan ta faru.. Kai can't really believe, Fu'ad in love ai dole nima na bazama na fara soyayyar nan.. now fadamin me akeji aciki?"

"Masu hankali ne kawai suke yi ka dakata sai kayi hankali don naga kamar baka dashi." Wani banzan kallo Fa'iz yayiwa Fu'ad yana cewa "bamu dashi za kace." 

Shiru Fu'ad yayi na sakan kadan kamin ya koma serious yace "seriously Fa'iz, I met her my first day being here and believe me she steals the man in me..."

Kai Fa'iz ya jinjina kamar gaske ya furta "ah ko baka fada ba na gani. Alhamdulillah Pal, may Allah make it khair for you, In Sha Allah she's your woman.."

"Bata sani ba Fa'iz.."

Wani kallo Fa'iz yayi masa yana cewa "ohhh ashe ma kai kadai kake kidanka kake rawarka I thought kun gama tsaida magana daka dawo Abuja musha biki.."

Harararsa Fu'ad yayi yana cewa "when will you be serious Fa'iz?" 

"Time din daka fadawa yarinyar da kake so cewar kana sonta... Ya sunanta??"

Ya bude baki zai amsa masa sai ga normal call daga Abie hakan yasa yayi saurin cewa da Fa'iz "pal Abie is calling me we'll talk later."

Da haka suka yi sallama yana jin Fa'iz yana cewa "bye farin shiga.. "

Murmushi kawai yayi yana girgiza kansa ya amsa wayar Abie yana rusunar da kansa qasa "barka da rana Abie." 

"Barka Fu'ad how's everything there?"

"Alhamdulillah Abie ya Lagos din, Ummi tace kaje can."

"Eh maybe ma gobe in Allah ya kaimu zan dawo kai fa yaushe zaka dawo ne ko sai an gama duka zaka dawo?"

Sumar kansa ya shafa yana cewa "uhmmmm.. eh Abie" 

"Ok sai ka dawo so nake ka dawo dama ina da magana daku kai da Azzam ban fahimci abinda ke faruwa tsakaninku ba."

"very soon zan dawo Abie ina kammala abinda nake In Sha Allah."

"Ok Allah ya taimaka ya bada sa'a."

"Aameen Yah Rabbi ngd Abie."

"Allah yayi maku albarka"

"Aameen Abie mungode."

"Take care."

HOUSTON, USA.

Dirowa yayi daga kan gadon bayan sun kammala waya da Fu'ad ya fita parlour inda ya tarar da Ammi zaune tana duba wayarta. Kusa da ita ya qarasa yana zama ya kwantar da kansa akafadarta yana cewa "Ammieeeee."

"Mesa wai kai ka girma baka san ka girma ba?"

Murmushi yayi yana dagowa daga jikinta ta bishi da kallo tana girgiza kai budar bakinta sai cewa tayi "mutumin da yaci ace yana da da ko 'ya shine kemin wannan abun better kai da Pal dinka ku shiga taitayinku wallahi or maybe sadakarku zan bada a masallaci.."

Dariya yayi yana cewa "sadaka kuma ai sai dai ni kadai dan danki yana can Kano wata tayi wuff dashi I swear addu'arki ne ya amsu Ammi.. "

Dan dakatawa da danna waya Ammi tayi kamin ta dago ta kalli Fa'iz har za tayi magana sai tayi shiru kawai ba tace komai ba "Ammi zan tafi na dauko Abbie."

"Adawo lafiya ka kula da kyau."

"In Sha Allah..."

"Ya fada maka zaka dauko Farouk a airport ne?"

Juyowa yayi yana kallon Ammi ya girgiza kai yana cewa "zuwa zaiyi? Me zai zo yi to?"

Dakuwa Ammi ta masa tana cewa "me kake yi anan kai.. Ina Abbu babansa ne.."

"Ooooo na tuna Ammi"

Kai kawai Ammi ta girgiza tana cewa "ni tafi please let me be" 

"Sai na dawo."

"Allah ya tsare."

Da haka ya tafi ya bar Ammi zaune tana cigaba da danna wayar da take haka kawai tana murmushi ita kadai aranta. Sai wajen goma suka dawo gidan duka Abbu akwai mai kula dashi a asibitin so su sai dai suje da safe da rana da dare kuma su dawo. Ko uncle Farouk sai da safe zaije.

Abinci Ammi tayi serving dinsu bayan sun gaisa da Uncle Farouk sannan ta tashi ta basu waje ta koma dakinsu tayi shirin bacci ta kwanta. Bata dade da kwanciya ba Abbie ya shigo da sallama, binta yayi da kallo yana cewa "Fulani har kinyi bacci yau da wuri haka."

Miqewa zaune tayi tana girgiza masa kai tace "barka da shigowa Yallabai."

Murmushi ya mata back yana amsawa tace "na hada maka ruwan wanka."

"Allah yayi miki albarka"

Murmushi kawai tayi tana binsa da kallo har ya shige bathroom din ita kuma ta koma ta kwanta tana jiran fitowarsa sai dai kamin ya fito bacci ya dauketa kuma mai nauyi da har Abbie ya fito ya gama shirinsa bata sani ba.

Ganin tayi bacci shima sai ya zauna kan sofa ya bude system dinsa da nufin yayi sauri ya qarasa abinda aka turo masa shima ya kwanta don agajiye yake.

Minti ashirin kawai yayi ya kammala ya ajiye ya miqe ya kashe hasken dakin ya zagaya shima da nufin kwanciya Ammi ta miqe zaune a zabure tana furta "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajee'un." Da sauri ya kunna fitilar daya kashe yana haurowa gadon ya riqota jikinsa yana cewa "lafiya Fulani?" Ganin wani kalar gumi da take hadawa.

Banda haki babu abinda take tana bin dakin da kallo sai maimaita kalmar Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajee'un take. Barinta Abbie yayi har ta dawo hayyacinta sannan ya sake tambyarta lafiya?

Instead of Ammi ta amsa masa sai hawaye kawai ta fara tana girgiza masa kai "It's okay kiyi addu'a kinji" 

"Ka miqomin wayata."

"Me zakiyi da ita?"

Tana kallon cikin idonsa tace "Fu'ad zan kira.. ina so naji idan yana lafiya"

Kureta da kallo Abbie yayi kamin ahankali yace "kinyi mafarkinsa ne?"

Kai ta gyada masa da sauri tana cewa "nayi mafarkinsa yana cikin mawuyacin hali.. yana daure da sarqa wata mata agefe tana yankar jikinsa tana shan jininsa abin ba kyan kyan gani Abbie"

"Mafarki ne ba gske ba Fulani"

Kai ta gyada masa da sauri tana cewa "na sani Abbie but I need to know idan yana lafiya"

"Yana lafiya Fulani"

"Haqqina ne na tabbatar idan yana lafiya ranka ya dade!!! "

To be continued....

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.