Free chapter · Read without an account

THE WEIGHT OF A PROMISE

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa


Da kallo Abbie ya bita irin deep kallon nan mai dauke da wasu tarin ma'anoni. Hannu ya kai ya share mata hawayen dake bin fuskarta yana cewa "It's okay Fulani. Keep praying for him. Kinsan addu'arki akansa karbabbiya ce ko?"

Kai ta gyada masa da sauri tana cewa "ka kiramin shi to."

"Yanzu wai?"

"Eh."

Ganin yayi shiru kamar wanda yake tunanin ya kira ko kar ya kira yasa tace "rana ne acan kasan don Allah Yallabai.."

Kai ya gyada mata yana daukan wayarsa yayi dialing number din Fu'ad da yayi saving da Fu'ad Aliyyu sannan ya miqa mata.

Har kiran ya katse Fu'ad bai dauka ba ta miqa masa wayar da niyyar a ajiyeta sai gashi ya kira back. Da sauri Ammi ta karbe wayar daga hannun Abbie ta kai kunnenta bayan ta amsa.

Daga can Fu'ad ya amsa da "Assalamu alaikum Ammi."

Wani irin rufe idanu Ammi tayi hawaye yana bin fuskarta tana jin wani sanyin jiki ta amsa masa sallamar nasa "barka da..." Sai ya danyi shiru sanin basa qasar yasan ba rana bace kamar yadda yake a Nigeria su dare ne hakan yasa yace "barka da dare Ammi.." Bai jira ta amsa masa ba ya D
dora da "ba kiyi bacci ba Ammi lafiya is it late anan.."

Ahankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya tana jin duk wani damuwa nata yana yin nasa wajen daga kawai muryar Fu'ad din data ji "kwana biyu baka kira ba Fu'ad I'm worried about you kana lafiya?"

Shiru yayi yana son fahimtar yanayin da Ammi ke ciki wanda muryarta kawai ya nuna hakan. "Kiyi haquri Ammi.."

"Kayi busy da yawa ne Fu'ad?"

Da sauri ya girgiza kai kamar yana gabanta ya amsa da "a'a Ammi I'm sorry don Allah kinji.."

Murmushi tayi tana share sabuwar qwallar data cika mata ido ta furta "stop apologizing Fu'ad, you did nothing wrong besides nasan aiki kake.."

"Ammi meke damunki please?" Shiru tayi na dan lokaci kamin ta dago ta kalli Abbie dake jinsu yayi shiru kawai sai kallon Ammi yake yi "babu komai Fu'ad.. ka riqa yin addu'a don Allah banda wasa da azkar kaji.. make sure kana azkar dinka kullum don't ever dare skip it Fu'ad don Allah kaji.. Nima ina maka addu'a and I will continue doing it for you by Allah's Grace... "

Murmushi sosai yayi yana jin tarin qaunar Ammi kullum yana sake yawa aranshi to the extent da yake jin matsayinta sak like na Umminsa "I love you Ammi.. "

Ya Rabbi, his words melted Ammi's heart daya sake saka mata wani sabon hawayen "I love you more Fu'adi Allahumma Baarik fika.. Allah ya kularmin da kai wherever you're kaji take care of yourself Fi Amanillah... "

Yana murmushi ya amsa mata da "Aameen Yah Hayyul Qayyum Fi Amanillah Ammi. " Da haka suka yi sallama Fu'ad yabi wayar da kallo yana cigaba da murmushi abinsa while Ammi jefar da wayar gefenta tayi tana fadawa jikin Abbie ta rungumeshi tana fara kuka kadan kadan "I'm missing him Abbie, I feel like kamar na janye wannan alqawarin Abbie .."

NURI'S POV....

"Oya take malama kici karki batan lokaci na gaji da wannan halin kuma ace sai anyi dake kici abinci kamar yarinya..."

Bata kalli Mami ba ta miqa hannunta ta amshi bowl din da Mami ke miqa mata wanda yake dauke da wake da shinkafa da man gyada babu yaji saboda ulcer da take dashi. Da kallo tabi abincin tana danne zuciyarta kar tayi reaction din da Mami zata gane. Amman harga Allah bata qaunar wake da shinkafa tun bayan batan Abba.

"Ko a baki zan baki ne?" Da sauri ta girgiza mata kai tana daukar cokalin dake cikin bowl din ta fara cusa abincin bakinta ba dan tana so ba.

Shigowanda akayi yasa suka maida hankalinsu can gaba daya and it was Inna. Wani zaro idanu Nuri tayi kamar ba ita ke magana da kyar ba tace "batan hanya kika yi Inna?" Wani banzan kallo Mami ta mata hakan yasa ta hadiye sauran maganar nata tana dauke idonta daga kan Inna ta mayar da hankalinta kan abincinta.

"Sannu Inna ga wuri ki zauna." Sai data gama qarewa dakin kallo tsaf sannan ta kalli Mami tana cewa "Bintu a ina kika samu kudin kawo yarinyar nan wannan asibitin kinsan nawa ake biya kuwa na kwana daya bare ku da yau kuke na biyu?"

Mami ba tace komai ba sai kujera data miqawa Inna da nufin ta zauna ta daga mata hannu tana cewa "dakata ba zama nazo yi ba magana za muyi dan fito waje"

Bin Inna data juya ta fita Mami tayi tana son hasaso abinda zasuyi maganar akai.

"Ba sai kinje ba Mami don ba alkhairi bane wallahi.." Mami ba taji ta ba ma saboda hankalinta baya kanta.

"Mamiiiiiiiiii." Da sauri Mami ta kalli Nuri tana cewa "mene ne Nuriyya? Akwai abnd kike so ne?"

Kai ta girgiza mata ba tace komai ba Mami ta kama hanya ta fita ta samu Inna a tsaye ita da Rabe da bazata taba mantashi ba don shine wanda suka rabasu da gidansu.

"Yww gata nan ta fito Laure"  juyawa Inna tayi ta kalli Mami tana tabe baki tace "na zata ban isa dake ba ai ni matso nan kiji abinda ke tafe damu ba zama muka zo yi ba.."

Qarasawa kusa dasu Mami tayi ta tsaya daga dan nesa dasu kadan ta sadda kanta qasa hakan yasa Inna da Rabe suka sake matsawa kusa da ita.

"Zancen aurenki ne dama ya taso saura kwana sha biyu!!!"

Da wani irin sauri ta dago ta kalli Inna da mugun mamaki. Tasan ta amince da auren to amman ai a daga mata qafa yarinyarta taji sauqi sai ayi duk abinda za'a yi. Dama da ace babu Nuri babu abinda zaisa ta amince da auren, ta amince ne saboda goben yarinyarta.

"Inna kuma a asibiti za'a yi wannan zancen sannan Nuriyya bata da lafiya ajira ta warke idan muka dawo sai ayi duk abinda za'a yi ko."

Kai Rabe ya girgiza yana cewa "Kinga shi yallabai ne a matse yake da auren shi yasa dama cewa yayi atambyeki abubuwan da kike so na bikin kiyi list akawo miki ga kudin saka rana nan karbi." Wallahi Mami bata san sanda ta aikawa da Rabe da kudin hannunsa harara mai zafi ba kamin ta dago ta sauke idonta akansa ta furta "idan zai iya jiran yarinyarta taji sauqi to idan ba zai iya jira ba to ya haqura kawai babu dole.."

Tana kaiwa qarshe a zancenta ta juya ta tafi ta barsu da baki sake suna binta da kallon mamaki musamman Inna da sam bata san Mami da haka ba. Mugun sanyi tasan Mamin dashi shisa take takata yadda taga dama

"Ke Laure ya haka? Bata amince ba dama kika ce ta yarda?" "wallahi da bakinta tace ta yarda kasan mayyar kudi ce yanzu ma burga ce kawai take yi, za kuma kace na fada maka zata dawo ta amince da bikin da bakinta ma kuwa."

Kai ya jinjina yana cewa "ba wannan ba Ina sauran kudaden wajenki suke?"

"Kai anan zamuyi wannan zancen muje gidana tukunna. " Juyawa suka yi suka bar asibitin don daman abinda ya kawo su kenan sunga kudi bazasu iya jiran har Mami ta koma gida ba saboda zalama.

Ba karamin dakewa Mami tayi ba ta shanye damuwarta aranta saboda kada Nuriyya ta fahimta. Samunta tayi a tsaye tana jera plates din dake wajen acikin leda.

"Kin cinye abincin ne?"

Juyowa tayi ta kalli Mami irin kallon qurillar nan taga ko zata ga sauyin yanayi a tare da ita sai dai bata ga komai ba hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tana zama gefen gadon tace "Mami kicewa likita ya sallamen naji sauqi an fara test fa a makaranta.."

Zama akusa da ita Mami tayi tana kwantar da ita ajikinta tace "bara ya shigo zan fada masa ."

"Me Inna tace miki Mami?"

"Ban hanaki irin haka ba."

"I'm sorry Mami.." duk shiru suka yi na lokaci Nuri tana son ture abinda ke ranta ta qarfi da yaji amman kamar zuciyarta ta rinjayeta haka.

"Mami yau bai zo ba?"

To be continued...

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.