Free chapter · Read without an account

A MOMENT LIKE THIS II

by Saddiqah M · NURI

NURI

By Saddiqa



Yasan nan is not the right place sam. Kawai yadda yake ji akanta ne kamar irin he can't control himself dinnan. He never imagined himself falling in love, not even for someone who would make him feel like he couldn't live without her. Ko da can idan suna hirar hakan shi dasu Fa'iz bai fiya saka baki ba ko zai tankasu ma sai dai yace shifa maybe wadda zai aura itace take son sa ba shi ba and now here he's madly in love.

Miqewa yayi daga inda yake yana maida wayarsa aljihu idonsa akanta ganin yadda ta kawar da kanta tana murmushi kadan-kadan yasa shi sake wani murmushi shima. Yadan duqar da fuskarsa saitinta da muryar rada ya furta "amman dai kinsan babu kyau rowa ko?"

Da sauri ta dago fuskarta jin muryarsa kusa da ita dab hakan ya mugun sauya mata abinda take ji azuciyarta. Dan ja baya tayi kadan shima ya miqe tsaye yana matsawa baya. Kamar ba zata kulashi ba sai can tace "rowar me nayi?"

Kanta ya nuna yana cewa "gashi nan..kin fini sani?" Da sauri ta girgiza masa kai za tayi magana Mami ta shigo dakin da sallama. Shi kadai ya amsa sallamar yana duqar da kansa qasa ya matsa daga wajen yana durqusawa har qasa ya gaida Mami.

Murmushi Mami tayi tana ajiye ledar dake hannunta ta amsa masa gaisuwar nasa tana qarawa da "ya aiki ya dawainiya damu kuma? Mungode Allah ya saka maka da alkhairi Allah ya biya maka buqatunka na alkhairi"

Kansa a qasa ya amsa mata da Aameen duk dama shi yanzu a yadda yake ji duk duniya kamar burinsa daya shine Allah ya mallaka masa yarinyarta dake gabansu.

"Mami zan dawo anjima idan an sallameku na mayar daku karku tafi da kanku"

"A'a ka barshi bamu da kaya kaga"

"zan dawo din dai In Sha Allah" Da kallo Mami ta bishi tana girgiza masa kai "wahalar zaiyi yawa Fu'ad" 

Ta gefen ido Nuri ta saci kallonsa ganin yadda ya durqusa kansa a qasa kamar wani wanda yake jin kunyar Mami ya sakata yin murmushi kamar ba shine yanzu ya gama takura mata da tsokana ba. Kallonta da Mami tayi yasa tayi saurin dauke kanta tana sakin fuskarta. Tunanin data tafi yasa bata san amsar daya bawa Mami ba kawai dai taga ya miqe ya fita haka kawai ta samu kanta da bin bayansa da kallo irin kallon daya sanya Mami kallonta itama tana cewa "ko zaki bishi ne?"

Firgigit ta dawo hayyacinta tana girgiza kanta cike da borin kunya "na bishi naje ina haba Mami" Itama Mamin bata sake cewa komai ba sai sauran kayansu da basu da yawa data hau tattarawa don suna saka ran bayan la'asar za'a sallamesu.

"Kinyi masa godiya kuwa Nuriyya?"

Kallon Mami tayi da wani irin kallo irin bata gane dinnan ba alhalin tasan tsaf da wa take "kinsan bansan rainin wayo ko? Kinsan da wa nake ai"

Kanta ta dauke tana turo baki gaba ta furta "ni ban san wa kike nufi ba fa Mami" 

"Ba zaki sani ba ai.." daga haka Mami ta bar zancen kamar yadda Nuri ta basar da maganar haka kawai tana jin indai za'a yi zancensa zuciyarta tana motsa mata. 

UMMI'S POV...

Idan tace hankalinta yana kwance tayi qarya, taya ma hankalinta zai kasance a kwance bayan taje an sake tabbatr mata da tabbas Fu'ad will marry in the future and wannan yarinyar dai da yace mata yana so ita zai aura. Dukan steering din motar tayi da hannunta tana jin kamar za tayi hauka tun yanzu.

Ta dawo ne daga wajen wani bokan daban wanda shima ta ajiye lamarinsa tunda ta shiga wannan kungiyar tasu. Sai dai shima kamar Baba na kan tudu ya bata tabbacin abinda Baba ya fada mata. Ya Kuma qara mata da "nan da shekara uku zuwa da rabi ta fara kirgar downfall dinta!!" Shi kam da ihu suka rabu ta fito tana zaginsa wai baisan kan aikin sa ba shisa yake mata wannan zancen banzan mara makama.

Wai kamar ita wani can mara sa'a zai yiwa magana irin haka, ita da tun tana yarinya komai ta saka agaba sai ta samu banda abu daya! Abu daya da shine ya jawo mata komai da take kai yanzu! Kuma har yanzu bata haqura ba duk kuwa da shudewar shekaru masu tarin yawa! Mutum daya dai kamar ko yaushe itace ta samu wannan abinda take qulafaci take so wato Boddo her twin sister!!!

Tun farkon layinsu take zabga horn saboda karma taje gateman ya bata mata rai Allah ya taimaketa ma gate din abude yake saboda fitar Azzam. Da wani irin gudu haka ta shiga gidan tayi wani parking marar kan gado ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya. Can kuma sai ta fita a fusace kowa ya hadu da ita a hanya shiga hankalinsa yake don sun san one mistake game over.

Afujajan haka ta shiga dakinta ta fara zagayeshi daga farko zuwa karshe kamar mai yin safa da marwa taje ta dawo har wani gumin tashin hankali take hadawa. The thought of ta fara kirga downfall dinta nan da three years is the worst bombshell of her life. Wannan wani abu ne da bazata taba bari ya faru ba no matter what. She will never let this happen. Za tayi duk abinda zata yi don ganin ta daqile faruwar hakan. Bata damu da takan wanda zata bi ba kawai abu daya ta sani shine asirinta bazai taba tonuwa aduniya ba.

Wayarta ta Ciro daga jakarta tana dialing number din Fu'ad hoping ya dauka har wani bugawa zuciyarta yake akan haka. Don an tabbatar mata Fu'ad shine nasararta aurensa da wannan yarinyar kuma faduwarta to taya zata bar wannan al'amarin ya kasance?? Matsalar shine bata san yadda zata rabasu ba!! Wani tunani da yazo mata kai yasa ta sake dialing number din Fu'ad bayan ya kai karshe bai dauka ba.

FU'AD'S POV...

He tried hard ya kammala abinda zai kammala kamin la'asar don yana so ya maidasu gida gani yake kamar shi kadai ya dace yayi hakan besides bugun zuciyarsa ce wadda zai maida gida. Yana parking a asibitin ana kiran La'asar hakan yasa yana fitowa yaje ya daura alwala ya shiga masallacin dake asibitin yabi jam'i. Koda aka idar bai yi saurin fita ba sai daya zauna ya kammala addu'o'insa da azkar dinsa sanin shima likitan da zai sallamesu yana masallacin so babu zancen tafiya ba tare daya sallamesu ba. Bai dade sosai ba ya miqe ya fita yana tafiya yanda ya saba irin wanda yake jawo hankalin mutane kansa ba tare daya shirya ba.

Knocking dakin nasu ya fara yi kamin aka bashi izinin shiga ya shiga kansa a qasa yana yin sallama. Da kallo Mami ta bishi kamin ta amsa masa sallamar ta fara cewa "ba ka ji ko Fu'ad? Sai daka dawo ko?"

Wajenta ya qarasa ya durqusa yana girgiza mata kai yace "kiyi haquri Mami bani da abinyi shisa" Kai kawai ta girgiza masa tana miqa masa kujera tace "kaima dai kamar wannan da in tayi niyyar abu sai tayi kake ungo zauna karka bata kayanka"

Sai data idar da addu'ar da takeyi sannan ta juyo tana sauke idonta akansa fuskarsa na kallon qasa yana wasa da mukullin motar dake hannunsa. Ajikinta taji ba zai amsa kujerar da Mami ke miqa masa ba hakan yasa ta miqe tsaye ta dauki abin sallar da take kai ta miqa masa ba tare da tace komai ba.

Dagowa yayi yayi mata kallo daya yana amsar abin sallar ya furta kalmar nagode yana shimfidawa nan inda yake ya zauna. Basu dade ahaka ba likitan dake duba Nuri ya shigo yana cewa "kiyi haquri Mama na barku kuna jira."

Murmushi Mami tayi tana cewa "babu komai" sai da ya sake dubata tare da vitals dinta ya tabbatar taji sauqi sannan ya sake jaddada mata banda wasa da abinci kamin ya sallamesu ya fita ya barsu.

Miqewa Mami tayi tana cewa "sauko Haskena!!"

The word Haskena hit Fu'ad so deeply that it made him smile softly as he got to his feet. Ya amsa ledar dake wajen Mami ya juya ya fita ba tare daya ce dasu komai ba.

Kallonsa Mami tayi kawai tana girgiza kai ita kawai hankalinsa yana mugun burgeta. Miqewa Nuriyya tayi itama tana sake gyara rolling din kanta suka fito tare ita da Mami some of the staffs da suka dan saba dasu suna musu sallama ahaka suka fita harabar asibitin inda suka tarar yana jiransu. Qarasawa suka yi Mami ta bude back seat ta shiga Nuri tabi bayanta itama tana zama. Kallon Nuri Mami tayi tana cewa "driver dinki ne shi da zaki zauna anan? oya koma can" baki ta turo gaba zata bude motar ta fita ya tada motar ya fara tuqi abinsa without saying anything to them.

Har qofar gidansu ya kaisu kamar yadda yayi wancan karon. Kalar godiyar da Mami ta rinqa yi masa sai da yasa ya fara jin kunya kamar wanda ya bata duniya haka har sai da ya gaji da kansa yace "Mami don Allah ki dena ya isa haka"

Kai ta girgiza masa tana cewa "a'a Fu'ad godiya bata kadan and it will never be, Allah ya rabaka da iyayenka lafiya Allah ya baka masu yi maka"

Ahankali ya amsa mata da Aameen sannan suka fita tare har shi ya dauko musu kayansu ya miqawa Nuri da kebin Mami a baya. Dagowa tayi ta kalleshi sau daya kamin ta sauke kanta tana miqa hannunta ta amsa sai ta kasa cigaba da tafiya ta tsaya awajen kamar yadda shima yake a tsaye a wajen yana kallonta.

"uhmmmmmmm... " Sai ta rasa abinda za tace ma gaba daya.

"ba zaki yi min sallama ba?"

Kai ta girgiza masa da sauri tana dagowa ta kalli cikin idonsa wanda gradually dan sabawar da suka fara yi yasa takan iya kallan cikin idon nasa duk da ba zata iya kura masa ido ba.

"Mungode....." Da sauri ya daga mata hannu yana girgiza mata kai yace "kul babu godiya atsakaninmu kinji."

Kai ta gyada masa tana yin qasa da kanta ya dan durqusa ya maida tsayinsa daidai nata yana cewa "kinji abinda likita yace miki ko?" Girgiza masa kai tayi ahankali ba tare data dago ta kalleshi ba.

Miqewa yayi tsaye sosai yana kallon tsakiyar kanta don tubarkallah ya fita tsayi "ohh haba baki ji ba?"

Bata amsa masa ba this time around sai daga masa kai da tayi. Wayarsa ya zaro daga aljihunsa ya bude yana miqa mata yace "put your number here. I will call anjima na fada miki abinda yace yanzu duk kin qararmin da energy dina"

Da sauri ta dago ta masa wani kallo ganin yana kallonta sai tayi saurin kawar da kanta gefe yayinda shi kuma ya bita da kallo yana waro idanunsa yace "hararata fa kika yi."

Baki ta turo gaba da wannan muryar nata ta bashi amsa da "nidai na barka da Allah kawai sai sharri kake min kuma kasan babu kyau.."

Hannunsa ya hade waje daya yana cewa "I'm sorry ranki ya dade Nabdi na tuba"

Kallonsa ta sake yi kamar dazu amman ahankali tace "Nuriyya ne fa sunana.." dan tabe bakinsa yayi kadan yana cewa "yayimin tsayi ne shisa."

"To NURI kawai yafi sauqi"

Kai ya girgiza yana cewa "babu dadi shi kuma... I'm waiting for you madam oya saka min number din." Wayar tabi da kallo kamar mai tunanin amsa ko karta amsa daga qarshe dai ta amsa ta rubuta masa number sannan ta miqa masa ya amsa yayi saving da Nabdi in caps sai emoji din heart agaba yana murmushi ya dago ya kalleta yana cewa "I will call you anjima In Sha Allah and don't forget we will discuss something very important kinji.." Kai ta gyada masa tana kallon cikin idonsa tace "na tafi?"

Kai ya girgiza mata da sauri yana cewa "kin gama kallona ne ko harkin gaji?"  she doesn't even know lokacin data masa hararar wasa tana yin gaba tace "wai kallonka, nace na kalli me to?" Da kallo ya bita har ta shige cikin gida yana tsaye haka kawai yana murmushi shi kadai at that point he felt like the happiest man in the world. Ya dade atsaye awajen kawai yana kallon gidansu kamin ya juya ya shiga motarsa ya tada ita ya bar wajen. Driving back to Bristol was superb to him saboda nishadin da yake jin yana ciki. By the time ya shiga suit dinsa is past 5pm don haka yamma yayi bazai yi wanka ba sai kawai ya samu waje ya zauna yana kunna system dinsa ya fara duba email dinsa.

Wayarsa daya ajiye kan center table ya fara ringing. Dagowa yayi yana bin wayar da kallo daga nan inda yake ya hango sunan Ummi yana yawo akan screen din wayar.

Hannu ya miqa ya dauki wayar yana amsawa da sallama. Kamar yadda ta saba masa ba ko yaushe take amsa masa sallama idan yayi ba shi kuma bai taba gajiya ko jin zai daina ba.

"Kana ina?" Dagowa yayi yabi dakin da yake da kallo kamin ya amsa da "I'm in my suite"

"Ka bude kunneka da kyau kaji abinda zan fada maka."

"Ummi bamu gaisa ba."

"Bana buqata Fu'ad.." shiru yayi yana son ya fahimci wani abu daga muryarta sai dai kamin ya fahimci komai Ummi ta katse masa numfashi da "Fu'ad idan har nice mahaifiyarka kuma na isa da kai to ina mai baka umarni da ka tattara komai naka ka bar Kano ka dawo!! As from today henceforth babu kai babu yarinyar nan ko kulata ka sake yi ban yafe ba! Safiyar gobe kawai na baka ka bar kano kwana daya ka qara akan haka Allah ya isa tsakanina da kai!! Kuma duk ranar daka qara taka garin consider yourself motherless Fu'ad!!!! "

To be continued...

#like
#comment
#share

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.