Free chapter · Read without an account

11-12

by zahra muhammad · TSOHON ƊAN BARIKI...

A gigice Alhaji buba ya miƙe tsaye yana kallon aminin nasa.
Takawa daddy yayi ya shiga cikin office ɗin yana kallon ainin nasa yana tuno yadda ya sameshi da ƴarshi yana jin kamar yasa bindiga ya harbeshi.
"Alhaji buba kuma shikenan se kayi ɓatan dabo kowa nata nemanka amma babu kai babu alamarka,"cewar daddy bayan ya samu guri ya zauna 
Bakin alhaji buba rawa kawai yakeyi zufa na karyo masa yace"dan Allah d makama kayi haƙuri kasani wallahi wannan abu arashin sani ya faru,babu yadda zaayi inmaka haka alhanin nasan ƴarkace ka yafemin"cewar alhaji buba jikinshi na rawa.
Zare glass ɗin fuskarshi daddy yayi sannan ya bashi amsa da cewa"karka damu kanka buba,d makamane fa,ay halina ba baƙon ka bane,zan iya yafe komai aduniya amma bazan taɓa yafe maka laifin da kaminba,dan ina me tabbatar maka da sena rama,"
Da sauri alhaji buba ya zagayo yazo gaban daddyn ya zube agabanshi jikinshi na rawa yace agigice"dan Allah karka ɓatamin rayuwar ƴaƴana,ko ita fareeda ba nice na fara ɓatataba ahaka na ganta,kaimin rai d makama dan Allah"cewar Alhaji buba hankali atashe
"to zan haƙurane akan sharaɗi guda ɗaya"cewar daddyn.
"faɗeshi  sharaɗin wallahi zan bi dan Allah"cewar Alhaji buban.
"nan da wata biyu nakeso kafito ka auri fareeda shine kawai abinda zakayi in janye ƙudirina akan ƴaƴanka"cewar daddy ba tare da damuwar komaiba.
Da sauri Alhaji buba ya miƙe tsaye yace"me kace d makama in auri fareeda fa kace,wannan riƙaƙƙiyar karuwar kakeso in aura in kawo gidana ta ɓatamin tarbiyyar gida,to in bacci kake ka farka wannan taxi no garage ɗin bazan taɓa aurantaba,kuma koda kaga ina baka haƙuri ayba tsoro bane nayi hakanne kawai dan nasan nayi maka laifi dan nasan na riga na killace ƴaƴana ba abinda zaka iya yimusu"cewar Alhaji buba.
Sosai kalmar taxi no garage da Alhaji buba ya kira fareeda dashi ya sosa zuciyar daddy,dan haka miƙewa yayi yace afusace"Alhaji buba,ni riƙaƙƙen ɗan barikine,yawo da hijab cikin tinted glass kai kasan beyi tsaurin da ze iya hana  burata isa inda nakeso tajeba,dan haka inde kere na yawo zabo na yawo dole wataran zaa haɗu,tunda fareeda taxice no garage,zan maida naka ƴaƴan haka in yaso nidakai semu zauna mu samar musu da garage ɗin,na barka lafiya"daddy na gama faɗin haka ya miƙe ya fice a office ɗin yabar Alhaji buba cikin firgici da mamakin yadda akayi daddyn yasan cewa ƴaƴansa na yawone cikin hijab a mota me tinted.
Lalle akwai sake,ashe bonono yayi kenan  rufin ɗaki da ɓarawo,to tarkatasu  zeyi su  tafi saudiyya su zauna acan in yaso in suka gama hutunsu acan sesu wuce london ba tare da sun dawo nigeria ba.
Da wannan shawarar ya koma gida,inda yana komawa adaren ya amshi passport ɗinsu ya kira agents ɗinshi ya bashi ya shaida masa bayason tafiyar ta wuce nan da sati ɗaya 
Suko su jiddah sun cika da mamakin jin asu tafi umara kwatsam ba tare da sunyi requesting ba.
"abba wai ko lafiya kake,mufa mun kasa gane wannan sabon tsarin naka,wai meke faruwa,kanayin abu kamar me tsoon kar wani abu ya faru"cewar husna tana kallonshi.
"banason duk wata tambaya ahalin da ake ciki yanzu,in lokacin baku amsa yayi da kaina zan sanar daku."cewar Alhaji buban.
Haka sukai shuru suna juya maganar aransu,ita kuwa jidda godiya tayi sannan tai masa addu'a da fatan alkha'iri.
Ayko a satin suka ɗaga zuwa saudiyya,hankalin alhaji buba se yanzu ya kwanta tunda yasan sun bar ƙasar ma gaba ɗaya bare d makama ya cika ƙudirin daya ɗauka.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.