Free chapter · Read without an account

025

by Kansa'u Bello · MEERAH

*MEERAH*

    *025*


   Nawaz na ƙoƙarin yin magana kira ya shigo cikin wayarsa, don haka ya dakata da maganar ya kai kallonsa kan wayar. JB ne mai kiran don haka ya miƙa hannu ya ɗauki wayar ya ɗaga kiran ya saka ta a kunne.

   Sallama ya yi JB ya amsa masa daga can ɓangaren, gaisawa suka yi irin tasu ta abokai JB ya tambayi su Umma da jikin Abba.

   "Duk suna lafiya Alhamdulillah, Abba kuma sai dai muce Alhamdulillah." Nawaz ya faɗa cikin sanyin murya.

  "Allah ya bashi lafiya." JB ya faɗa sannan ya ɗora da sanar masa dalilin da ya saka ya yi kiran nasa.

   "Dama na kira na faɗa maka aikin nan ya kammala, na fitar da kiɗan zaka iya shigo wa kawai a ɗora aikin." Cewar JB. Ajiyar zuciya Nawaz ya sauke sannan yace.

   "JB aikin nan ba zai yiwu gobe ba, don gobe ne zamu kai Abba asibiti ayi masa gashi. Ina ga mu bari zuwa jibi in sha Allah."

   "Okay ba matsala, Allah ya bashi lafiya. Sai na gan ka ɗin kawai."

   "To shike nan na gode JB."

        "No kar ka damu." JB ya faɗa daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar. Hira suka ci gaba da yi da ƴan'uwansa da Umma, sai ƙarfe 10 na dare sannan suka kama Abba dake kwance a can gefe ɗaya suka mayar da shi ɗakinsa.

  Shima sallama ya yi wa Umma kafin ya shige nasa ɗakin, wanka ya yi ya yi shirin bacci sannan ya kira masoyiyarsa a waya. 

  
 ******* A nan A. M. G Mansion kuwa sai ƙarfe 10 saura drip ɗin da aka saka wa Ajmal ya ƙare, Yaya Sultan ne ya cire masa sannan ya saka ni na haɗo masa tea mai zafi na kawo masa. 

   Kaɗan ya sha ya ajiye don haka Ya Sultan ya saka ni haɗo masa abinci, tashi na yi ina ƙoƙarin tafiya ya dakatar da ni ta hanyar cewa na bar shi baya buƙata.

   Koma wa na yi na zauna ina taɓe baki, a zuciyata nake gulmar sa cewar. 'Mutum bashi da lafiyar ma ba zai sauya hali ba.'

  Saukowar Momy ce tasa na mayar da hankalina kansu ganin tana rarrashin Ya Ajmal a kan ya daure ya ci wani abu. Tagumi na saka da hannu biyu ina kallon yanda ta saka ƙaton saurayi a gaba da rarrashi tamkar wani ɗan ƙaramin yaro.

  Ajmal kuwa ganin Momy ta damu a kan yaci wani abu ya saka shi cewa.

   "Meerah ta dafa min Noddles ta kawo min, bari naje na watsa ruwa kafin ta kammala."

   "Okay Sultan raka shi ɗaki ya samu ya watsa ruwan. Auta je ki dafa wa Yayanku Noodles yanzun nan ki kawo masa." Momy ta ƙare maganar tana kallona.

   "Okay Momy." Na faɗa ina miƙe wa na nufi Kitchen ina ƙun-ƙuni a zuciyata, don gani nake yi da gayya yaƙi cin abinda aka dafa don kawai ya saka ni aiki.

   Sultan kuwa taimaka masa ya yi ya miƙe tsaye saboda jirin da yake gani.

   ɓangarensu ya kai shi ya taimaka masa ya zauna saman gado sannan ya shiga bayi ya haɗa masa ruwan wankan ya fito.

    "Ka tashi kaje kayi wanka." Sultan ya faɗa yana kallon sa. Tashi ya yi zaune ya cire Cannula dake hannunsa sannan ya shiga bayin. Wanka ya samu ya yi da ruwa mai zafi ya yi alwala da brush ya fito.

  Samu ya yi Sultan ya fito masa da kayan bacci ya ajiye masa a saman gado, baya ɗakin don ya tafi nasa ɗakin shima don ya yi shirin baccin. Cikin juriya ya daure ya saka kayan ya zauna saman gadon yana jingina bayansa da filon da ya saka ya lumshe idanu, dai-dai lokacin aka yi masa knocking a bakin ƙofa.

   Umarnin shigo wa ya bayar  ba tare da ya buɗe idonsa ba.

  ***** A hankali na murɗa ƙofar na shigo da sallama ƙasa-ƙasa, a kansa na sauke idanuna yana zaune a saman gado sanye cikin fararen kayan bacci wando da riga mai dogon hannu. 

   Fuskarsa da naga ta ɗan faɗa na zuba wa ido ina kallo, a bazata naji saukar muryarsa yana cewa.

   "Malama ki kawo min idan kin gama kallon nawa." Baki na tura gaba jin abinda yace ɗin.

   "Toni me ma zan kalla a jikin naka, da zaka ce wani ina kallon ka?." Na furta ƙasa-ƙasa sosai lokacin da nake ƙaraso wa na ajiye masa abincin saman ƙaramjn table ɗin da ke gaban gadon.

   Ajmal kuwa sarai ya ji abinda tace, don haka ya buɗe idanunsa ya sauke mata su cike da mamakinta. Shigowar Sultan ce ta saka ya haɗiye maganar da ya yi niyyar faɗa mata ya mayar da idonsa ya lumshe.

   "Har ka fito, yaya jikin?." Sultan ya tambaya da kulawa.

   "Alhamdulillah." Ya bashi amsa ba tare da ya buɗe idon ba. Ganin haka ya sa na lallaɓa na fice abina.

   Bayan fitar Meerah Sultan ya zauna a kusa da shi tare da buɗe plate ɗin da ta sako masa Noodles ɗin yace.

   "Ka daure ka ci ko kaɗan ne sai ka sha magani gashi an kawo." Ya ƙare maganar yana nuna masa laidar wani Pharmacy da aka siyo maganin a can.

   Da ƙyar ya daure ya ci spoon ɗin da bai fi uku ba ya ajiye, tashi Sultan ya yi ya ɗauko ruwa yazo ya ɓalla maganin ya bashi ya sha. Yana cikin shan maganin ne kiran Dady ya shigo masa, sai da ya kammala sannan ya ɗaga kiran ya gaishe da Dady.

   Amsa masa Dady ya yi da kulawa haɗi da tambayar sa jikinsa, don Momy ce ta kira take sanar masa Ajmal ɗin ba ya jin daɗi kasancewar baya nan yana Abuja.

   "Alhamdulillah naji sauƙi Dady." Ajmal ya faɗa da muryarsa wacce ta ɗan risina. Addu'a sosai Dady ya yi masa sannan suka yi sallama ya ajiye wayar.

   Tamkar jira ake yana ajiye wa wani kiran na shigo wa, Abby ɗinsa ne ya kira don haka ya ɗauka da sallama sannan ya ɗora da gaisuwa.

   "Kana lafiya kuwa Ajmal?." Dady ya jefo masa tambayar ba tare da ya amsa gaisuwar da ya masa ba, lumshe ido ya yi sannan ya ba shi amsa da cewa.

   "Kaina ke ɗan min ciwo Abby, Doctor ya zo ya bani magani naji sauƙi." 

   "Subuhanallah! Tun yaushe ne?." Abby ya tambaya. Mamy dake zaune a gabansa tana zuba masa shayi tace.

   "Me ya samu Ajmal ɗin ne?." Ta yi masa tambayar cikin damuwa. Da ido Abby ya yi mata nuni da yana zuwa, kafin ya mayar da hankalinsa kan bayanin da Ajmal ɗin ke masa.

   A ɓangaren Ajmal kuwa cewa ya yi.

   "Tun a hanya nake jin ciwon Abby, bayan mun sauka ne ya matsa min. Amma naji sauƙi yanzu, in sha Allah gobe zan taho Mamy na son gani na."

   "Ka tabbatar dai babu wata matsala ko?." Abby ya tambaye shi da kulawa.

  "Yes Abby I'm recovering." Ajmal ya faɗa.

   "Okay to ka huta sosai idan kaji ba zaka iya taho wa gobe ba kar ma matsa wa kan ka, ga Mamy ɗin ku zata yi magana da kai." Abby ya faɗa yana miƙa wa Mamy wayar. 

   Tamkar jira take dama yana miƙo mata ta amshe da sauri, don tunda taji an ambaci Ajmal ɗin ba lafiya gabanta ke faɗuwa da tunanin ba dai wani abu ne ya same shi ba.

   Sallama ta yi masa ya amsa haɗi da gaishe ta, da kulawa ta amsa masa sannan ta tambaye shi abinda ya same shi. Bayani ya yi mata kamar yanda ya yi wa Dady, jin cewar ya ji sauƙi ya sa ta sauke ajiyar zuciya da yi masa fatan samun lafiya ta ɗora da ce masa.

   "Ko dai in zo in taho da kai ne goben?." Tayi masa maganar tamkar wani ɗan ƙaramin yaro, murmushi ya ƙwace masa jin abinda Mamy tace. 

   "No Mamy zan iya zuwa da kai na kiyi zaman ki." Ajmal ya faɗa.

   "Okay Allah ya sauwaƙa, sai ka zo ɗin." Mamy ta faɗa daga haka suka yi sallama ya jiye wayar.

   "Akwai abinda kake buƙata ne.?" Sultan ya tambaye sa.

   "No babu abinda nake buƙata, kaje ka kwanta sai da safe." Ajmal ya faɗa ya bashi amsa yana zame wa ya kwanta.

   "Okay good night, and take care of your self. If you need something give me a call." Sultan ya faɗa sannan ya fice a ɗakin.

 ***** Bayan fitar Sultan tunani mai zurfi Ajmal ya shiga a kan yanda zai ɓullo wa al'amarin nan. Yana buƙatar saka mata ido sosai ya fahimci inda ta dosa kafin ya ɗauki mataki. 

   Sai dai yanzu abubuwa ne da yawa a gabansa, gashi gobe zai wuce Abuja kuma ba zai dawo ba daga can zai wuce Turkish a kan maganar kayan da Company ɗin sa zai fara shigo wa da su.

   Dole zai ajiye komai yanzu sai abubuwa sun masa sauƙi kafin ya juyo kan al'amarin ya fuskance sa, ya daɗe a haka kafin bacci ya ɗauke sa cike da saƙe-saƙe a zuciyarsa.


★★★

   Washe gari ya tashi jikinsa da sauƙi Alhamdulillah, don haka ya yi shirin wuce wa Abuja. Karfe 8 na safiya dai-dai lokacin duk suna zaune a saman dining suna breakfast.

   Bayan sun kammala ne yake sanar da Momy wucewar tasa. Kallon sa ta yi da kulawa tace.

   "Amma Son kana ganin zaka iya tafiya a haka babu matsala?." 

   "Babu matsala Momy na warke ai." Ya bata amsa da girmamawa.

   "To shike nan Allah ya ƙara sauwaƙa wa." Momy ta faɗa.

   "Ameen duk muka amsa da ita.

   Bayan mun kammala breakfast Ya Sultan ne ya kai sa airport ya hau jirgin da zai tashi zuwa Abuja.


*Meerah....*

    Tun da Ya Ajmal ya wuce nake jina a sake sosai, don haka tuni na manta da shi na ci gaba da gudanar da al'amurana yanda na saba, don Allah ya sani bana jin sake wa ko kaɗan idan yana nan.

   Musamman yanda yake saka ni a gaba da takura min, duk abinda zan yi idonsa a kai na kuma sai ya ji dalili.

  Zaune nake a ɗaki ni kaɗai ina chatting a group ɗin mu na School ɗin da muka kammala, na jima a cikin group ɗin muna shan hira kafin na sauka a online ɗin na yi kira Nawaz don ya ce min yau za su je asibiti kai Abba gashi da ake yi masa duk bayan sati biyu.

   Bai ɗaga kiran nawa ba sai da ya katse sannan ya kira ni back, ɗaga wa na yi da sallama na ɗora da gaishe sa. 

   "Lafiya lau masoyiya, ya kike." Nawaz ya faɗa daga can ɓangaren.

   "Ina lafiya, yaya jikin Abba?." Na bashi amsa hadi da tambayar sa.

   "Alhamdulillah, yana ciki ma ana yi masa aikin." Ya bani amsa.

  "Allah ya bashi lafiya." Na faɗa.

     "Ameen ya Allah." Ya amsa min daga haka muka bar zancen, hira muka ɗan taɓa ina tambayarsa yaushe zai zo gidanmu na yi missing nasa, don ya daɗe bai zo ba.

   "Zan zo in sha Allah." Ya bani amsa daga haka muka ajiye wayar.


  *Abuja B. M. G Mansion....*

       Yau Mamy cike da farin cikin dawowar yaronta ta tashi, don haka tun da safe ta shiga Kitchen da taimakon masu aiki don shirya wa Ajmal abinci, duk abinda ta san yana so sai da ta aka girka masa shi aka jere a dinin.

  Karfe 11 Flight ɗin da ya biyo zai sauka, don haka kafin 10 an kammala komai na tarbar sa. 

   Jauhar dake gidan tafi kowa murna da ɗokin zuwan nasa, don haka tun 10 ɗin ta kammala shiri. Gayu taci sosai ta ɗame cikin riga da wando ta yana wani ɗan yalolon mayafi a kanta.

   Ƙarfe 10 da rabi Mamy, Jauhar da Fatima suka wuce airport don ɗauko Ajmal da jirjinsa ke gab da sauka......

   *Oum Fatima*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.