Free chapter · Read without an account
29. ...tayi mashi magana...🖊️
Da sauri Roman ya isa wurin allon bai bi takan painting ɗin ba ya ɗauki brush ɗin daya karye yana kallo like it's the most precious thing in the world...idon shi turned blood shot numfashin shina fita da zafi..taune leɓenshi yayi feeling sick to the pit of his tummy...
Wannan brush ɗin yana daga cikin memories ɗin da mahaifiyar shi tabar masa...shine farkon kyautar ta a gareshi bayan ya fara zane...she was the one who taught him painting..and now this clumsy girl...
Miƙewa yayi ya gyara komai da komai a studio ɗin ya kashe wutar ya fito..ɗakin shi
Ya shiga ya sauya kaya zuwa baƙaƙe daga sama har ƙasa ya tattare sumar shi into a bun ya fito... elevator ya shiga kafin ta rufe Farzan ya faɗo ciki... Roman bai kalle shiba...da wani smug face Farzan ya tsaya gefen Roman yana cin chewing gum yana ƙaras ƙaras... Wayar Farzan ce tayi ringing ya duba yaga Hajiya Hafsah ce.. ɗaukar wayar yayi yasa a speaker
'' Hello Farzan,ina kake ne?" Slowly yace '' zan fita ne MAMA'' ya kalli sashen Roman daga cikin wayar Hajiya tace '' okay,ina fatan kaci abinci ko?"
'' eh MAMA!"
'' ka dawo da wuri... Allah ya tsare min kai!"
Ya amsa da Ameen kafin ya katse kiran
'' Ah! It's such a wonderful feeling to have a mother...amma wasu Mutane ba zasu fahimci hakan ba ko kaɗan...'' ya jinginar da kanshi da elevator da murmushi a fuskar shi, however Roman bai nuna kamar yaji abinda Farzan ya faɗa ba if anything he was aloof
Hakan yaba Farzan haushi '' da yake yan wasu basu da ita ai baza su sani ba...'' dunƙule hannunshi Roman yayi zuciyar shina kaikawo... Farzan daya fahimci hakan ya tsaya da kyau
'' what's wrong? Na tado da tsohon ciwo?"
'' You are right it's a wonderful feeling having a mother...amma da irin uwar da kake da ita zama maraya is absolutely best...'' Roman ya amsa with a cold voice, batareda ya kalli Farzan ba
sai kuma ya matso kusa dashi face flat bakinshi saitin kunnen Farzan yace
'' come on,kayi saurin mantawa da baya do you need a recall?''
Dunƙule hannun shi yayi zai kaima Roman naushi.. Roman ya riƙe hannun ya juya sannan ya jefar da Farzan ta kafaɗar shi...
Yakai zuƙunne gaban shi '' you're embarrassing yourself... weakling!" Tsallake shi yayi ya fita daga elevator yabar Farzan kwance a ƙasa groaning in pain...
Parking lot ya isa bike ɗin shi ya hawo yau ko helmet ɗin bai saba ya fita da gudu...
Khalil na zaune saman gadonshi saye da farar riga mai V neck ƙirjinshi slightly out yana kallon gefe yayi nisa cikin tunani wayarshi ta fara ringing ganin mamar shice ke kira ya ɗauka murya sanyaye
'' ya kake Ibrahim?'' shiru yayi na lokaci kafin yace '' yaushe zaki zo?"
'' i can't come akwai abubuwa da yawa...''
'' that need your attention..what about me? Ni bana buƙatar kulawar kone?" Ya iyar mata,shiru akayi daga can ɓangaren
'' manta kawai...lafiya ta lau.. thanks for checking!" Ya katse kiran...tare da jinginar da kanshi...idonshi ya sauka akan ƙofar shi that was slightly ajar...gani yayi kamar akwai mutum a wurin....their eyes met...da sauri aka ja baya
'' zo nan!" Ya faɗa da muryar shi mai zurfi...ƙifta idonta Diyaam tayi several times kafin ta tura ƙofar ta shiga ciki zuciyarta na lugude...kanta ƙasa tayi tsaye daga bakin ƙofa...saye take da jar atamfa ta ɗaura farin hijabi sama.. average in height extremely fair in complexion..wasa take da hannun ta nervously
'' meyasa kike leƙe?" Taune jan leɓenta tayi murya na rawa da Fulani accent tace '' Uhmm..d..dama...ina neman...Ham..ma ne''
Khalil looking a bit disappointed yace '' forget it..na ɗauka kinzo ki duba ni ne...'' panicking Diyaam tace '' h..harda wannan..''
har lokacin bata ɗago kanta ba...'' hmm,are you sure gaskiya kike faɗa kuwa...You look suspicious...'' da sauri ta ɗago kanta ta waro manyan idanunta tace '' wallahi banyi komai ba...abinda ya kawo ni kenan...kayi haƙuri baxan sake ba...'' ta haɗa hannayenta alamun roƙo idonta na ƙyalli...this is the first time tunda tazo gidan nan cikin shekaru data taɓa magana da Khalil...
'' Okay...zan yi haƙuri idan kin zauna tare dani,Kinga banda lafiya kuma kowa yabarni nikaɗai...'' ya faɗi hakan da wasa but he was deeply lonely...
'' eh zan zauna...''
Murmushi yayi ya nuna mata gefen gadon shi '' zoki zauna anan...'' hesitantly taje ta zauna a ƙarshen gadon a maimakon inda ya nuna mata...
'' meye sunan ki?'' ya tambaya suddenly finding the girl interesting'' D.. Diyaam!"
ya ɗage gira '' kaɗai?" ta girgiza kanta '' Safiyyah Diyaam..''
'' oh DIYAAM na nufin ruwa ko?" Jinjina kanta tayi '' ranar da aka haife ki kenan ruwa ake yi a garin ku?" daji abinda ya faɗa tayi yar ƙaramar dariya mai daɗin sauti sai kuma fuskarta tayi ja sanda tagane kallonta yake
'' eh... haka ne...baban mu yace, ranar da aka haife ni anyi ruwa sosai kuma dama ƙauyen mu,babu ruwa lokacin sai anyi tafiya mai nisa zuwa birni kafin a samu ruwa shine ranar da aka haifeni ana ta ruwa shine yan ƙauyen mu ke kirana DIYAAM...'' tayi mashi bayani a kunyace tana wasa da hannun ta '' I like the sound of it...amma xan kira ki Sofia..can I?"
gyaɗa kanta Diyaam tayi feeling so happy at last tayi magana dashi,zuciyarta kamar baloon tsabar yanda take farin ciki
***"
Bayan Roman ya Kore ni daga ɗakin zanen shi kasa komawa sashen mu ko ɗakin Diyaam nayi... lambu na tafi na zauna zuciya ta tayi nauyi kamar inyi kuka amma me zai sa inyi kuka? Laifina ne dana shigar masa wuri Batareda ya gayyace niba babu abinda yafi min ciwo irin fushin dana gani a fuskar sa...na daɗe zaune a wurin kafin na tafi kitchen...abincin ranar da aka dafa na karɓa na wuce dashi sashen Khalil sai dana ƙwanƙwasa ya bani izinin shigowa sannan na shigo..nayi mamakin ganin Diyaam a ciki suna hira ita da Khalil kamar ƙawaye...da yake ta daɗe gidan ƙila ƙawaye ne
'' Oh kitten...'' Khalil ya kira murmushin shina ƙara faɗaɗa...nima murmushi nayi mashi na ƙaraso kusa dashi '' ya jikin ka?"
'' naji sauƙi baki zo kin dubani ba...''
na zauna kusa da Diyaam '' nazo jiya kaine dai baka ganni ba...''
'' oh I must have missed...'' ya nuna min Diyaam '' kinga sabuwar ƙawata yar fullo..'' sadda kanta Diyaam tayi blush ya mamaye fuskar ta...ajiye mashi abincin nayi '' kyakkyawar ƙawa kake da ita!"
Dariya yayi data fito daga ƙasan ƙirjinshi '' Are you jealous?" tsuke fuska nayi shi koda yaushe idan anyi magana sai yace jealous
'' a'a...ga abinci nan kaci...'' gyaɗa kanshi yayi ya fara cin abincin..Diyaam ta tashi zata tafi nima zan bita yace mu zauna mu taya shi hira...zaman mukayi...nan ne yasan gobe zamu fara jarabawa..yace zai sa a ɗauke mana aiki har sai mun kai ƙarshen jarabawa...dan muyi karatu da kyau ya ƙara da faɗin '' plus..I want to spend lots of time with you!" Ya kashe min ido...
Ɗauke kaina nayi gefe ina murmushi wannan Khalil ɗin...
Da ƙarfe ɗaya muka bar ɗakin shi zuwa na Diyaam mukayi sallah kwantawa nayi saman gadonta ina kallon sama duk na damu da Roman
'' meya faru ne duk kin damu?" naso in ɓoye mata amma sai kawai na faɗa mata abinda ya faru tsakanina da Roman...'' kada ki damu... eventually zai sauko...'' gyaɗa kaina nayi
'' kin shirya ma gobe kuwa?" Ta tambaya tare da kwantawa kusa dani itama tana kallon ceiling '' gabana faɗuwa yake..duk da nayi karatu!"
'' nima!"ta faɗa...littafan literature guda biyu ta ɗauko drama da prose ta bani prose ɗin ...muka shiga karatu... Har bacci ya ɗauke mu...
Wurin ƙarfe uku na farko daga baccin nayi kwance ban motsa ba..can dai na sauka daga saman gadon na tsaya gaban full length madubin ta ina kallon kaina...abinda na daɗe banyi ba...ƙurajen fuskata sun rage sosai...gashin girata dayake kamar an aske ya taru yayi baƙi da kauri duk da ba sosai ba...gashin idona ma sun ƙara tsawo kaɗan...sai ƙirjina daya fara tasowa shima kaɗan...
Cikina da yake ƙato yanzu ko ganin shi banayi ta cikin rigata dayake banci abinci ba...taune leɓena nayi ina danne murmushin dake ƙoƙarin wanzuwa a Fuskata...da gaske nice?
Yar ƙaramar dariya nayi kafin na koma gaban madubi na ɗauko mashaci da tsinke ina kunce kaina a nan tsaye har na gama..na shace gashin..gani nayi ya ƙara tsawo da cika amma har yanzu bai da laushi sai taurin tsiya...
'' tunda kin kunce ki shiga Baye ki wanke mana...'' ta cikin madubi na hangeta zaune daga bakin gado...
'' kina da shampoo ne?"
'' eh mana..''
Ajiye tsinke da mashacin nayi na shiga bayenta da yake a tsabtace nayi wanka na wanke kaina na tsane shi sannan na fito sai lokacin na gane ashe banda kaya a nan...
wasu riga da wando palazo ta bani daga cikin kayanta harda singlet baƙa nasa na dawo gaban madubi ina goge gashina sosai reflection ɗina ya daɗaɗa min rai...ƙirjina ba kamar daba...ya ƙara girma nake ji kamar in rungume wani...da ace ina gida dana nuna masu Mama...dariya nayi da wannan tunanin sai kace wata marar kunya
Bayan na gama busar da gashin Diyaam ta ɗauki wasu hair cream da oil ta zaunar dani akan kujerar dake gaban madubi ta shafa min su Sannan ta fara yimin kalaba '' tana sa gashi yayi tsawo!" Gyaɗa kaina nayi cike da godiya
'' shekarunki nawa?''
'' shabiyar..''
'' ya kamata ki dinga kirana aunty Abeedah...''
'' Hahaha..to aunty Abeedah da shakaru nawa kika girme ni...''
'' biyu...'' na bata amsa
''a she ke tsohuwa ce?" Zaro ido nayi hakan ya bata dariya...wani ƙaramin littafi na gani na miƙa hannu na ɗauka..daga sama an rubuta abinda ke raina...kenan diary ne..har xan buɗe in karanta ta warce abinta '' ba'a karantawa mutum diary aunty Abeedah!" ta turo baki..she looked cute!
'' oh ban sani ba...yi haƙuri aunty Safiyya Diyaam..inji Anaaam!" Muka yi dariya...
Da daddare da muka tafi dining Khalil ma yazo da alamu ya gaji da zama ɗakin shi
Munyi mamaki daya faɗa masu cewa ba zamu sake aiki ba saboda jarabawar da zamu rubuta har sai mun gama..hakan ya jawo cecekuce da kuma harara cike da tsana...
Mukhtar ne yazo wurin shima..har lokacin bai warke ba .sai tambayar shi ake mai ya faru dashi
'' wannan mahaukaciyar ce ta kusa kasheni!" Ya nuna ni kafin ya ƙirƙiro ƙarairayin sharri ya sauke akaina wai na kawo mashi kaina ɗakin shi dan yaƙi yarda shine na buga mashi bedside lamp akai..na tsere...dukansu harda ni kaina na shiga shock...
miƙewa Hajiya Wareesha tayi ta juyo dani ta ware tafin hannun ta zata sauke min a fuska.. kamar iska Khalil ya tsaya gabana ya kare ni da jikinshi hakan yasa marin ya sauka akan bayanshi... Diyaam ta rufe baki idonta suka ciko da hawaye kamar yanda nawa ke tsiyaya
Sauran ma'aikatan suka zaro ido...su Seraphina suma sun shiga shock da abinda Khalil yayi... ajiyar zuciya ya sauke ya sake ni yana kallon cikin idona yace
'' are you okay Kitten?" naji kamar lokaci ya tsaya kamar babu kowa sai mu...my heart broke
'' wallahi ƙarya yake min..''
'' shhh...na yarda dake!" Ya katseni ya juyo ga sauran '' Abeedah bazata taɓa yin hakan ba!''
Hajiya Wareesha ta kama da wuta '' yanzu Ibrahim ka gwammace ka goyi bayan yar waje sama da ɗan uwanka?"
Fuska ba annuri Khalil ya kalleta '' I'm just supporting the truth aunty!"
'' Kai wannan yarinya anyi annoba! daga zuwanta gidan nan an samu matsala yafi a ƙirga shegiya mayya!" Inji hajiya Ruƙayyah...
'' ya kamata a koreta daga gidan nan kawai wannan shine maslaha!" Sharply Khalil ya juya ya kalli Hajiya Momma datayi maganar kafin yayi magana daga baki baki Muryar shi mai amo ta karaɗe wurin
''No body is firing her!" Maganar ta fito da wani irin absolute finality babu batun musu... juyawa mukayi...it was Roman! Fuskarshi tayi duhu ya ƙaraso wurin
'' Toh marasa ta ido nuna mana cewa ka kai girma!" Hajiya Zeenatu ta miƙe tana nuna shi da cokalinta mai yatsu
'' ai na faɗa yarinyar nan annoba ce..ji yanda ta haɗa faɗa bayan bata daɗe da kasancewa a gidan ba!" Hajiya Momma ta sake faɗa ...
Nikam babu abinda nake sai kuka...abinda Mukhtar ya faɗa yayi min ciwo fiye da tunanin mai karatu...
'' dan kaga Hajjo bata nan shine zaka faɗi hakan...mu muka haife Romano bakai ka haife muba! Yanzu xan kira securities su fitar da yarinyar nan!" tana faɗar haka ta ɗaga waya ta kira wasu mutane
Few minutes later sai gasu sun shigo cikin baƙaƙen kaya...nuna masu ni tayi tace su fita dani...
Khalil ya ƙara riƙe ni a jikinshi..nima ina ƙara ɓoyewa bayanshi...dining ɗin yayi duhu da da nauyi da tension ɗin dake maƙale da iska..yan mata da samari suna jira suga yanda zata kaya.. mafiyawanci idan da za'a yi ƙuri'a da zasu sa in bar gidan..Nima da badan Khalil da kuma Roman ba,da nayi tafiya ta..
''.me kuke jira? Ku fita da ita!" Hajiya Momma ta faɗa... mutanen saye da baƙaƙen kaya sukayo kaina...mutum na farko daya miƙa hannu don fincikoni ganinshi mukayi kwance a ƙarshen bango..muka kalli Roman da yake tsaye kamar Boss na cikin TV
.ya kalli su Hajiya Momma yace
'' I said No one FIRES HER!" Da wani irin calmness yayi maganar emphasizing each word... Mutanen wurin were shocked nida kaina abun yaban mamaki...aka shiga kallon kallo
Sauran securities suka ja baya... Hajiya Momma ta sallame su da baƙin ciki ganin babu abinda zasu iya aiwatarwa..suka ɗauki ɗan uwansu daya kasa tashi suka tafi dashi
'' mu muka haife ka bakai ka haife...''
'' KE DA WA?" Ya katse Hajiya Momma dake repeating sentence ɗinta, tayi shiru kunya na ɗiga daga jikinta,sai zarar ƙananan idonta take
'' dake ki kasance uwata...Gara na mutu tun ina ciki!" Maganar ta sauka kamar bomb sauran matan suka zaro ido amma babu wanda ya isa yace komai...yan aikin sukayi ƙasa da kansu
Fuskokin duka waya'nda ke wurin sukayi duhu... Seraphina take kallon mu cike da tsana ba ita kaɗai ba harda yan uwanta...da gudu tabar wurin tana kuka...
Diyaam yadai?? 👀👀
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️