Free chapter · Read without an account
Chapter 11
by Salis M Reza · MIJIN AMAL
Chapter 11
Ta ƙarasa tambayar hawaye na cika mata idanu. "Please Amal ki saurari abun da zan..." "Kawai ka amsa min tambayata Yasir, an daura?" Ya ɗago da sauri jin sunansa ɓaro-ɓaro a bakinta. Ya ce "Amal suna na fa k..." da sauri ta sake tare shi cikin kuka tana sake tambayar sa. Ya ce "No ba'a ɗaura ba, na kasa jurewa, ba zan iya ba, gara mu zauna a haka". Sai kawai ta fashe da wani irin kuka wanda ta kasa gane na menene. Haushin taji ko farin ciki, ko kuma tsoron kar taje karya yake mata. Sai kawai ta rungume shi tana jin kamar tana kokarin daina yarda da maganar sa, anya ma wannan Yasir ɗin ta ne da har zai iya ɓoye mata wannan babban lamarin, kenan dama akwai abubuwan da yake ɓoye mata. Shima ya rungume ta, ya cigaba da faɗa mata yadda take a ransa da kuma tasirin soyayyar da yake mata. Ya daɗe yana maganar kafin itama ta fara faɗin "Abun da ka so yi haramun ne Yasir, koda ace ka shawarce ni ba zan baka goyan baya ba. Kuma ni nasan waye mijina ba zai iya aikata hakan ba. Kuma ba wai ina kuka akan auren bane, no ina kuka akan ta hanyar da za'ayi auran ne, da kuma yadda abun da nafi yarda da shi ya iya ɓoye min abu har haka ban iya ganowa ba. Ban isa na hana ka aure ba, kawai dai kaine bana so na rasa ka da soyayyar ka da kuma kulawa. Sannan ban san wacce zaka auro ba ko zata iya kula da kai rabin yanda nake maka, muddin da gaske na gaza maka ta wata fuskar to kaje kayi auranka ba zan hana ka ba, ka auro duk wacce kake so mai kyau da kuɗi fiye dani". Tana faɗa ta miƙe daga jikinsa tayi cikin daki tana jin kamar zuciyarta zata fashe, har wani irin sarawa kan yake yi abubuwan sun haɗe mata, ga na Mama ga na Nana ga wannan. Kawai wani irin yanayi take jin kanta Kamar mai ciwon as'ma zai tashi, sai taji Kamar kowa baya sonta a duniya gaba ɗaya, mai yake shirin faruwa da ita. Dama haka ake jin kishi, innalillahi wa innalillahi rajiun, ta gwammace ace ta mutu kawai maimakon wata ta auri mijinta. Idan ta hasaso kasantuwar hakan ma sai taji kamar tayi hauka tsabar tashin hankali. Haka taji gaba ɗaya haushin yan matan duniya take ji. Ta kwanta ta kifa cikinta tana cigaba da kuka ƙasa-ƙasa. Shima ßakinsa ya wuce wanda babu ko gado a ciki ya zauna domin ya bata sarari saboda yasan bata cikin natsuwarta, yasan idan ta huce zai shawo kanta, Amal ce, rayuwarsa, Mace ɗaya da yake kallo a matsayin mace. Sai ya fara tunanin abun da ya faru a gurin ɗaurin auran.
Sai da aka gama sigan aure gaba ɗaya sai kawai ya miƙe tsaye. Ya ce "Dan Allah a dakata, ina da magana". Ya faɗa yana daga hannu kamar ɗalibi a cikin aji. Kowa ya kallo shi ana jira aji mai zai ce. Ya ce "Alhaji ina son yin magana da kai kafin a ɗaura". Ya nuna baban Suhailait. Da mamaki ya nuna kansa. Ali kuwa sai jansa yake yana dukan ƙafarsa da hannu amma ina. Haka dole suka koma gefe ɗaya. Ya ce "Jiya da naje gurinka akwai wasu maganganu da ka min wanda sun tsaya min a rai, hakan yasa naga ba zan iya cin amanar ka ba. Zan faɗa maka gaskiyar magana. Ni da yarinyar ka ba soyayya mukeyi ba, hasali ma ban santa ba. Sun haɗa baki da tsohon mijinta ne domin suyi auran kisan wuta dan ta koma masa. Abun da zasu bani shine miliyan shida, zan aureta na sati ɗaya sai na saketa. Farko ban yarda ba, amma haka wata zuciyata ta rinjaye ni, ina da mata guda ɗaya, ko ita bata san da maganar ba, haka wannan iyayen nawa ma na karya ne bani da wata alaƙa da su. Dan Allah kayi hakuri, ba zan iya aikata hakan ba". Yana gamawa ya ce "Innalillahi wa innalillahi rajiun, yanzu Suhailait ɗin ce ta iya shirya wannan abun?. To yanzu yaro yaya za'ayi kenan, mai zan fadawa wannan mutanen da muka tara fisablilillahi?" Yasir ya juya zai tafi sai yaji alhajin ya ce "Zo mana yaro". Yasir ya dawo yana sauraron sa. "Kace kana da mata daya ko?" Ya ɗaga kai. Ya ce "To dan Allah ka rufa min asiri ka aureta ɗin, kuma ka amshi kuɗin da zasu baka, sai dai bana so ka sake ta, zan kara maka miliyan goma akai. Idan suka naimi saki ka sanar dani. Dan Allah ka ceto min yarinya daga hannun wancen ɗan iskan mijin nata, wallahi itace take sonsa shi ba sonsa take ba". Yasir ya kalle shi da sauri yana girgiza kai. "Dan Allah ka taimaka min, idan ma kana son fiye da haka ne zan ƙara maka". "Alhaji kayi hakuri, ba zan iya yin auren kuɗi ba". Yana faɗa ya barshi a gurin ko ta kan Ali da iyayen nasa bai biba ya kama hanya.
Ali ya biyo shi da gudu yana kiran sunansa. Yana zuwa ya ce "Wai Yasir meye kake yi haka ne kamar wani yaro ko mara hankali, yanzu fa ɗaurawa kawai ya rage amma kana so ka bamu matsala, dan Allah mai kace masa?" Ya juyo a fusace ya ce "Na faɗa masa gaskiyar abun da muka shirya ne, ba zan iya wannan auran ba". Ali yayi mutuwar tsaye yana kallon sa ya kasa magana. Ya ce "Anya kana da hankali kuwa, kasan irin asarar da kayi kuwa Yasir? Miliyan shida ba tare da ka kasa komai ba, alhali ko dubu ɗari ɗaya baka da ita taka, ka gwammace ka mutu a haka kenan da bakin talauci?" "Eh na gwammace na mutu a haka muddin ta wannan hanyar zan bi nayi arziki". Daga haka ya koma shago ya saka wayarsa a chaji ya shige cen ciki ya kwanta kawai ya fara hawaye shi ɗaya. Bayan ya dawo daga tunanin ya tashi ya nufo ɗakin nasu. Yana buɗewa ya sameta tana ta rawar sanyi. Ya ƙaraso da sauri yana kiran sunanta. Cikin muryar zazzaɓi ta ce "Kaina zai fita, ciwo yake min, ɗauko min magani". Ya tashi ya fita da sauri ya ɗauko mata magani ya bata tasha. Yana tai mata sannu yana mata alkawarin wallahi ba zai iya rayuwa da wata mata ba, kuma duk abun da take tunani ba haka bane. Sosai ya dage mata har shima yana kuka ganin yadda yake yi. Haka suka kwana yana mata alkawari da kuma tabbatar mata da cewar ba aure zai ƙara ba, kuma ya ma fita daga wannan sabgar. Washegari da safe ma dai jikin ya tsananta. Hakan yasa ya kira likitar su tazo ta duba ta. Wannan karan da tazo ita da kanta tai mata gwajin ciki. Yana zaune a palo yana kallo shi ɗaya sai gata ta fito. Bayan an gama saka mata ruwa da allurar barci ne likitan tazo ta same shi. Ta ce "Daga kai har matarka ban san waye zan bawa laifi ba". Ta faɗa tana murmushi. Ya ce "Laifi akan ciwon?" "Eh akan ciwon fa, ciwon da ya kai kusan wata guda a jikin ta, daga ita har kai baku gane ba". Ya sake kallonta da Kyu. Ya ce "Ban fahimta ba?" "Amal na ɗauke da ciki, duk da ban san ko wata nawa bane, amma ina tunanin ba zai fi ɗaya ba". Ta faɗa tana sake murmushi. Yayi shiru yana kallonta ya kasa magana. Ta ce "Awa ɗaya zata iya farkawa, kuma idan da hali zaku iya zuwa asibiti domin a tabbatar. Idan an tabbatar a tura min da tukuicin ta opay". Tana faɗa ta bar gidan ganin bai ce komai ba.
Har ta fita bai sani ba sai da yaji ta rufe kofar gidan. Da sauri ya shiga cikin ɗakin yana kallonta, a ransa yana ta maimaita kalmar cikin. Ya kalli fuskarta sai yanzu ya kula da ta ɗan faɗa ta fuska. Ga wani irin fayau da tayi duk ta bashi tausayi. Yasa hannu ya ɗaga rigar jikinta yasa hannu akan cikin nata yana shafawa. Sai yaji ta sauke ajiyar zuciya. A fili ya ce "No, ba yanzu ba, no ban shirya ba. Ciki!" Ya faɗa yana yin waje da sauri. Ya fita daga gidan ya hau mashim ya tada shi kenan yaji ana kiran number sa. Ya ɗauka ganin number masu amsar kayan nan ne. Yana cikin yin magana da su, sai ga motar Ali ya faka a ƙofar gidan. Kafin ya gama sallama da su yaga sun fito tare da tsohon mijin Suhailait ɗin gaba ɗaya fuskarsu a haɗe. Ya sauke wayar yana kallon yadda suke binsa da kallo kamar sun zo faɗa. Ganin haka shima ya haɗe rai yana saka wayar a aljihu.
"Kai dama ashe baƙauye ne ban sani ba? Idan kasan ba zaka yi ba mai yasa baka faɗa mana ba sai ka fadawa babanta, kasan hakan mai ya haifar mana?". Mutumin ya faɗa yana zare masa ido. Ali ya ɗora da faɗin "Bama iya ƙauyancin ba, harda rashin hankali da nuna cewar shi na Allah ne, idan ba haka ba, kai da akayi abu da kai a sirri mai ya kaika fadawa mahaifinta". Yasir ya ce "Mai ya kawo ku gida na?" "Ubanka ne ya kawo mu gidan naka, ɗan iska kawai mara mutunci wawa dan ƙauye". Mutumin ya faɗa a fusace, daga ji kasan ya gula. Ali ya ce "Har tambaya ma kake Yasir, to wannan kuɗin da ya baka zaka dawo masa da shi tunda baka san mutunci ba". Yasir juya ya shiga gida ya dauko kuɗin ya fito ya mika musu. Mutumin ya karɓa ya na faɗin "Saura ɓata mana lokaci da kayi, da kuma ɓata mana shiri?" Sosai Yasir yake kokarin tausar kansa kar ya biye musu. Jin yayi shiru yasa mutumin ya juya baya yayi alama da hannu. Sai ga wasu samari biyu sun fito daga cikin motar. Suna zuwa ɗaya ya kai wa Yasir naushi ya sameshi a fuska. Ganin haka Ali ya shiga tsakiya yana faɗin "No ba haka mukayi da ku ba, iya kuɗin ku kuka ce zaku amsa. Dan Allah ku bari". "Kana nufin sai mu barshi haka kenan duk da abun da yayi". Daga haka faɗa ya kace me a gurin. Suna dukansa yana ramawa.
Ali na shiga tsakani amma bai hana suyi masa shegen duka ba saboda harda mutumin suka haɗe masa. Sosai suka ci galaba a kansa sannan suka tafi. Ali ya fara kokarin ɗaga shi su shiga cikin gida ya kutuntuma masa wani zagin da yasa ya ja da baya yana kallon sa.
"Ni kake zagi haka Yasir?"
"Eh na zagege Ali, kuma kar ka kuskura ka sake taɓa ni na faɗa maka". Ya faɗa yana mikewa tsaye yana ɗaukar makullin mashin ɗin nasa da ya fadi.
"To Mai kake so na maka Yasir". Na kawo maka harka ka watsa min ƙasa a ido. Har ga Allah ka ɓata min rai wanda ba'a taɓa min ba. Kuma ina da kuɗin da zan iya bashi amma saboda na nuna maka banji dad'i bane yasa na zo da shi". "Ba dai na baku kuɗin ba. To fita min daga gida, kuma daga yau Ali karka ƙara shiga sabgata, babu ni babu kai har abada, banza mutumin banza kawai". Yana faɗa yayi cikin gida. Ali ya tsaya yana kallon sa har ya shige.
Toilet ya shiga ya kunna ruwan fanfo ya cika bokita ya ɗaga ya juye a kansa. Sai da yayi haka sau uku kafin ya sake yin wanka. Bayan ya fito ya sauya kaya ya fita. Ya hau mashim yayi tafiya mai nisa yana tunanin ina zai samo kuɗin bayain allanan na masu kaya. Bai iya tambayar kowa bashi ba, sai kawai ya yanke shawarar sayar da mashin ɗin sa. Hakan yasa ya nufi gurin da ake sayar da mashin. Har an fara ciniki sai kuma ya tuna da zai kai Amal asibiti. Hakan yasa ya hau mashin ɗin ya nufo gida. Yana shiga ya samu ta tashi har tayi wanka ta sa doguwar riga. Yana shiga ta fitowa daga kicin riƙe da cofi. Ta ce "Babu komai a gidan nan, kuma yunwa nake ji". Ta faɗa tana hamma tana kuma sha shayin da ta haɗa babu madara. Ya ƙaraso ya riƙe ta yana tambayar ta jiki. Ta ce "Da sauki, kawai dai kaina ne yayi min girma". Zaiyi magana ta ce "Lafiya kake kuwa". Ya kama hannunta ya ce "Asibiti zamu je". "Yin me kuma a asibiti?" Bai bata damar magana ba, ya ɗauko mata hijjabi ta saka ya ɗauki Niƙaf ya bata tasaka suka nufi waje. Ta ce "Wai lafiya dai ko?" "Lafiya lau!" Ya faɗa daidai ta hau mashin ɗin. Lokacin da suka isa ya samu a kwai layi. Sai ya tafi babban asbiti. Duk da bai da kuɗi ya gwammace ya biya ko nawa ne domin yasan meye gaskiyar magana. Ko kafin su isa masu kayan nan suna ta kiran sa, wannan dalilin yasa yake ta sauri domin ya dawo da ita yaje ya sayo masu kayan su. Koda aka gwada likitar ta tabbatar musu da cewar babu ciki a jikinta, kawai zazzaɓi ne. Ai kuwa take Yasir ya sunkuya har ƙasa yana godiya ga Allah cike da farin ciki. Hakan ya bawa Amal mamaki sosai. Ta ce "Wai saboda babu cikin ne kake godiya? To dama waye yace maka ciki ne? ka manta ban fi kwana biyu da yin piriod ba?" "Eh na manta ne, kuma wannan likitan ce ta faɗa min, dan haka dole mu sauya ta, bata san aikinta ba". "To yanzu da ciki ne fa?"...📝
Kuyi hakuri ba yawa. Zamu cigaba in sha Allah..