Free chapter · Read without an account
Chapter 12
by Salis M Reza · MIJIN AMAL
Chapter 12
Ta ce "To yanzu da cikin ne danin fa"? Ta faɗa tana kallonsa. "Da zubar wa za'ayi saboda bana so". Shima ya bata amsa yana tashi domin sallamar asibitin. Transfer yayi musu ya juyo ya kama hannunta domin su tafi gida, farin ciki fall fuskarsa. Sai yaji ta tsaya ƙiƙam bata taho ba. Ya joyo ya kalleta yaga ya kafe shi da ido. Ya ce "Ko na ɗauke ki ne?" Ya faɗa da gaske yana murmushi. Zata yi magana ya fara ƙoƙarin ɗaukar ta. Amma taƙi yarda, tana ture shi. Ya ce "Lafiya dai ko?" Ta ce "Cewa fa kayi da ciki ne zubarwa za'ayi, kasan hakan mai yake nufi?" Yasir ya riƙe kai yana dariya ya ce "To yanzu anan kike so muyi maganar kenan ko yaya?" Sai ta kalli gefe da gefen su. Sain kawai tayi gaba da sauri. Yayi sauri ya riƙe mata hannu yana faɗin "Ba fa a haka muka zo ba Madam". Yana faɗa yana riƙe mata hannu har gurin mashin ɗin. Bayan ta hau ya ce "Da nace ba zan sake fita dake ba sai a mota, amma wannan banzar likitan ta sa na karya alƙawari, dole ne na samo wata, saboda ita bata da hankali". Yana cikin maganar shi ɗaya yaji an sake kiran waayarsa. Yasan su waye shi yasa ya ƙara gudu yana faɗin "Bana so naga matata tana fushi da ni, sai na ji na tsani kaina. Dan Allah ku ce mata tayi hakuri ta min uzuri akan abun da na faɗa, ina da dalili na". Tana jinsa dai bata ce komai ba domin ita abun ya bata mamaki. Ya yaya wanda yake sonka ba zai so ya aihu tare da kai ba, ta yaya hakan zata faru. Gaba ɗaya ya sata a dogon nazari da tunanin wani irin so yake mata ne". Ya ce "Wai kayan murnar cikar shekara biyun nan ina aka kai su ne, naga ban gansu ba?" "Na saka su a freza". Ta faɗa a hankali. Ya ce "To idan na dawo zan taya ki mu ƙarasa sai muci kayan mu ko?" Ta ce "Umm"
Ya ce "Kiyi hakuri dan Allah bana jin daɗin hakan sam". Ta ce "Ni baka min laifi bafa, kuma ka ɗaga kiran ka da ake tayi kar wacce take kira tayi fushi". Ta faɗa jin ana sake kiran nasa. Yasir ya ce "Ko na baki ki ɗaga ne kiji wacce?" Ya faɗa yana ciro wayar ya mika mata. Sai kawai ta faɗa tunanin lokacin da idan an kira shi take ɗaga massa waya, shima haka. Sai ta ƙi amsar wayar. Daidai lokacin suna shawo kwananr gidan su.
Bayan sun shiga ya faka ta sauƙa da sauri tayi cikin gidan. Shi kuma ya sake juyawa da sauri ya fita domin ana ta jiran sa, har yaron shagon nasa ma yana ta kiran sa. Ta na shiga cikin gidan ta shige ɗaki ta zauna a bakin gadon tana jiran sa. Shiru bai shigo ba yasa ta miƙe ta dawo falon. Ganin baya nan sai ta leƙa waje taga ba mashin ɗin sa. Ta tsaya a gurin ta kasa juyowa. Ta daɗe a haka kafin ta juyo tana jin ba daɗi a ranta. Kichin ta shiga domin yin girki, sai dai ba komai a ciki. A lokacin ne wani tunani ya fado mata, anya ba zata fara sana'a ba kuwa, tabbas zata shawarce ne domin zata iya taimaka musu ta wannan hanyar. A cikin abincin da ya kawo wancen lokacin ta ɗobo ta ɗora sanwa, da yake dama ɓoyewa tayi. Har lokacin jikinta ba ƙwari sosai. Ta fito falo ta tarar ashe kafin su tafi asibiti ya gyara ko ina. Sai ta ɗauko wayarta wacce ta faffashe ɗin. Tana son ta kira shi amma ta fasa akan sai ya dawo. Kallon ma da yake ɗebe mata kewa sai taji gaba ɗaya bata son yi. Haka kawai komai ya fita mata a rai. Kamar daga ƙasa taji sallmar Mama. Hakan yasa ta tashi da sauri ta shiga kichin ta ɓoye wannan abincin da Yasir ya kawo buhu dayan nan. Ta zo ta buɗe gidan tana mata maraba. Mama ta ce "Marabiyo nace, wato yanzu dole dai muddin zan zo gidan ki sai kowa ya sani a maƙwafta ko, wai meye a cikin gidan da ake garƙamewa ne har haka"?. Ta faɗa tana shiga daga ciki. Amal tayi shiru. Sai Mama ta samu guri ta zauna a karo na biyu tunda take zuwa gidan. Hakan ya tabbatar mata da cewar akwai wani abun. Hakan yasa itama ta zauna tana addu'a a ranta. Mama ta kalleta ganin kamar ta ɗan rame ta ce "Lafiya kike kuwa Amal?" Ta faɗa kamar dai kulawa kamar kuma bugar ciki. Hakan yasa Amal faɗin "Zazzaɓi ne ya rufe ni tun jiya, yanzu ma muka dawo daga asibiti, amma dai da sauki". "Duk saboda auran Nana ɗin ne hakan?" Ta ɗago da sauri. Ta ce "Mama..." "Tambayar ki kawai nayi". Kafin Amal tayi magana Mama ta fara faɗin abun da ya kawota cikin kwantar da murya. "Kinga duk bama wannan ba, aure dai an riga an ɗaura, masu so da marasa so kowa yayi haƙuri. Kaman yadda na faɗa miki jiya cewar shine yayi mata komai na kayan gida to haka ne. Amma ai kin san a matsayin mu na iyaye dole ne mu ɗan mata wasu abubuwan kamar dai wasu daga kayan kichin. Saboda dai muma mu san munyi wani abu. Gashi dai nice mai yi, sai kuma ke da Allah ya haɗa ki da jarabawar auran matsiyaci. Dan haka shima Nana ai ta zama ƙanwarsa, ki faɗa masa da ke da shi ku san abun da zaku haɗo domin a fita kunya. Nasan ko zuwa bayan auran ne kema zaki mori wannan auran, ko ɗan sauran abincin nan nasu na masu kuɗi take tattaro miki ai kin gode". Amal ta ce "Gaskiya Mama bamu da kuɗi daga ni har shi. Kuma tunda kince yayi komai meye sai kin wahalar da kanki, Allah ya basu zaman lafiya kawai?". Ta faɗa hankalinta kwance, domin ta lura idan tace zata dinga sa maganganun Mama a rai, tsaf zata iya sawa kanta ciwon damuwa. Mama ta ce "Ai dama nasan kalmar da zan samu kenan ta bubu idan nazo gidan ki. Wallahi Amal har abada ina nadamar wannan auarn naki da babu komai a cikinsa. Dan cikin nan ma da ake yi a shekarar farko ke babu shi, gashi har shekara biyu. Allah dai ya tsinewa aure irin wannan". Ta miƙe tsaye tayi waje tana ta kwashwa auran albarka har ta fita. Bayan ta fita tayi shiru tana nazartar wasu malamai daga maganganun Mama. Tabbas tasan farkon auransu ta yarda sunyi tsarin iyali, amma a lokacin bata san cewa aihuwar ce gaba ɗaya baya so ba. Gaba ɗaya sai take ganin kamar wannan yawan tsinewa auran da Mama ke yi ne ma zai haifar musu da matsala. Idan ba haka ba mai ya kawo ƙin son aihuwa ga Yasir mutumin da bai da kowa a duniya sai Yaya, ai zai so ya samu zuri'a. A fili ta ce "Bari yazo naji dalilin sa na faɗin haka kafin na yanke masa hukunci, na san halin mijina". Daga nan ta cigaba da girki har ta gama ta juye. Sannan ta tashi tayi Sallah. Ta ɗaga hannu kaman yadda ta saba akan Allah ya kawar da sheɗanun da suke ƙoƙarin shiga lamarin auransu, Allah ya basu zaman lafiya, ya kawo fahimtar juna a tsakaninsu. Tana cikin nade abar sallar taji yana buga kofar. Ta tashi da sauri ta buɗe ta rungume shi tana baiyanar da fara'a a ranta duk ganin sun dawo yadda suke. Sai dai ganin fuskarsa yasa itama hankalinta ya tashi. Bata ma lura da babu mashin ɗin ba. Hannunsa na hagu ta kalla taga laptop babbar tasu, ga wata leda a gefen hannun. Ta amshi laptop ɗin tana kallon sa, tana sake masa sannu. Ta je ta juno a chaji ta dawo kusa da shi inda ya zauna tana masa sannu. Ya amsa yana faɗin ya jikin nata. Itama ta amsa da sauƙi tana tashi ta kawo masa ruwa ya amsa ya sha. Ta ce "Wanka ko abinci?" Ya kalleta yana jin daɗin yadda bata da riƙo a ranta, ga kuma uzuri da take masa akan komai. Ya ce "Wadda kika zaɓa min". Ya faɗa shima yana kokarin kawar da nasa damuwar. Tayi murmushi ta ce "Zaɓina shine wanka naga ka gaji da yawa". Ya ce "Zaɓin ki shine daidai a koda yaushe". Ta kama hannunsa wai zata ɗaga shi. Shi kuma ya sakar mata nauyinsa. Sai gashi ta biyo shi kan kujerar suna dariya a tare. Ya ce "Har yaushe kikayi karfi haka?" Ta ce "Kana ganin ba zan iya bane?" "Ai ga fili ga mai doki". Sai ta tashi. Ta cire hijabin jikinta. Ta juya masa baya ta ɓalle maɓallin rigar jikinta, ya zama ta bar ƙirjinta a waje. Sai ta sunkuya ta kama hannunsa tana murmushi. Tana ja sai gashi ya biyo ta. Ta fashe da dariya tana yin ciki da gudu. Ya biyota shima yana dariya. Tana shiga ɗaki ya shigo yana faɗin "Kut! Wannan ai siddabaru ne". Ta ce "Idan mu mata bamu da karfi amma muna da dabaru iri-iri ko?" "Tabbas yau na tabbatar, dan haka yanzu ma cigaba za'ayi da wannan dabarar".
Bayan ya fito daga wanka ta zuba musu abinci. Ita kaɗan ma ta iya ci, duk da hakan ma ya taƙura mata. Bayan sun gama ya lura a kwai maganganu a bakinta. Sai ya takaita mata saboda yasan duk abun da take son faɗa. ya ce "Amal na sayar da mashin dina ne. Na sayo wannan kayan da nace miki na amshi kuɗin su na kashe. To sune suke ta kira na tun ɗazu. Kowanne na basu nasu. Kuma na sayo laptop da sauran kuɗin. Sannan na sake miki waya, zaki ajiye wannan wacce ta fashe ɗin ni zan cigaba da amfani da taki har zuwa lokacin da Allah ya yi. Sai kuma ga wannan dubu ashirin ne ki kaiwa Mama gudun mawar bikin Nana, kinga bamu san da shi ba, yazo lokaci ɗaya. Da naso na sayi wani abu ne, amma na rasa mai zan saya ne, shine nace kawai ki bata kice naki ne fa". Ya faɗa yana ɗorawa da ki bata hakuri dan Allah". Amal tayi shiru tana ta kallonsa ta kasa magana. Ya jawota jikinsa yana faɗin "Kema an jima zan zo miki da ɗaya daga cikin kayan da matan suka saya, haka kawai naga zasu miki kyau a jiki, na kai ɗinki". Ta ce "Bab da gaske ka sayar da mashin ɗin naka?" Yayi murmushi yana faɗin "Eh na sayar, dama Allah ne ya bani, kuma ya sake bani damar sayar da shi domin nayi wata buƙatar". "Mai yasa baka shawarce ni ba?" "Saboda na san ba zaki bari ba ne. Kuma bani da kuɗi. Wannan dubu dari biyu na mayarwa da Ali kayarsa saboda abun da ya faru kar ya main wulakanci". Kawai ki cigaba da mana addu'ar Allah ya hore mana".
Ta tashi da sauri ta rungume shi tana addu'ar Allah ya saka masa da alkairi. Ta godo ta gode. Ya ce "Kin san mai yasa nake tsoron aihuwa?" Ta ɗogo da sauri domin dama maganar da ta ke son suyi kenan.
Ƙarar kiran da ya shigo wayarta ne ya zaburar da ita. Har ta saki tsaƙi ganin an katse mata karatu, sai kuma taga number Hafiz ne. Hakan yasa ta kalli agogon wayar sai kuwa ta saki salati a hankali tana ɗaga wayar. "Wai Hafiza mai kike yi ne kwana biyu ayi ta buga miki gida amma shiru?" Tana jin haka tayi waje, sai ku ta dawo ta shiga kichin. Ta samu komia a kashe. Ta godewa Allah. Ta zo da sauri. Daidai tana buɗe masa ƙofar maganar Hadiza na faɗo mata a rai. Hakan yasa bata san lokacin da ta haɗe rai ba. Suna haɗa ido taga nasa fuskar ma a haɗe. Bai ce mata komai ba ya wuce ciki da sauri. Ta biyo bayansa har cikin ɗakin nasa. Tana kokarin sanyaya nata ran. Ta tuno da yadda Amal ta kawar da nata damuwar har kuma suka samu fahimtar juna. Sai tayi ƙarfin halin faɗin "Barka da dawo?" "Mai kike yi a waya kwana biyu Hafiza, na miki magana kince min nayi hakuri zaki daina, amma steel kin ci cigaba, Hafiza kina so ki sauya ne daga yadda na sanki?" Ya faɗa yana kallonta. Ta ce "I'm sorry again, nayi maka alƙawarin zan daina, yanzu dai mai zaka fara yi. Wanka ko abinci?" Tana faɗa tana tuno yadda Amal ta yi a nata gidan. Ya ce "Magana nake miki kan abun da kike yi ba wannan ba, faɗa min mai yake ɗauke miki hankali a waya? Ko kina so na karɓe wayar taki ne?" Ta zaro ido cike da mamaki. Kamar ta fusata amma ta sake kokarin jarraba wata dabarar. Ta kama hannunsa da nufin ta ja shi toilet ɗin ko zai huce. Sai kuwa ya fusge hannu yana sake faɗin "Kina ce wasa nake yi ko Hafiza, kullum sai dai kice I'm sorry I'm sorry, Kuma ba zai hana ki ƙara ba ko? To bani wayar taki?" Ya faɗa da gaske yana miƙa mata hannu alamar ta bashi. Ta ce "Ar You serious?"...📝
Ina barar addu'o'in ku yan uwa. Na gode sosai, masu kira da masu turo sako jaje. Jiki da sauki zamu ce. Kun samu wannan rubutun ne ta hanyar yi muku editing kawai dama yana nan a ajeyi, shine na bayr aka kawo muku shi.