Free chapter · Read without an account

Page 12

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU 

BY 

Khadijah Sulaiman 

Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1

Page 12

Cike da wani irin nutsuwa Sadauki ya koma makaranta,gabaɗaya ya nemi ɓacin ran abinda ya faru dashi ya rasa.
Sadiq dake zaune a ɗaki tare da wasu yaran ya ɗan bi shi da kallo ganin yadda yake murmushi,ya ajiye allon hannun shi da mamaki don abu ne da ba kasafai ya ke yi ba yace"ikon Allah,wai wani labarin ka samo ne haka ka shigo kana wannan murmushin?"
Da sauri ya juya suka haɗa ido,ya shafa kai ya nemi wuri ya zauna still yana murmushi yace"babu komai".
Sadiq yace"ban yarda ba gaskiya,haka kawai ba za ka dinga wannan murmushin ba Sadauki".
Ya miƙe ya bar ɗakin Sadiq ya bi shi da kallo.
Gabaɗaya yinin ranar cikin farin ciki Sadauki ya yi ta,shi kan shi ba zai ce ga ƙwaƙwaran dalilin da yasa yake wannan farin cikin ba.
Bayan an idar da sallar magrib ya kasa tafiya gidan kamar yadda ta umurce shi duk da yaso yin hakan,haka ya koma ya zauna yana kallon sauran dake cin tuwo.
Washegari kamar yadda aka saba bayan an gama karatu aka fara barin makarantar.
Bayan yayi wanka ya ciro riga daga jakarsa,duk da a koɗe rigar take amma bai da datti.
Har ya sa rigar maganar yarinyar jiya ya faɗo mishi,yayi murmushi yana tuna yadda take bin shi da kallo cike da mamakin koɗewar kayansa.
Tun da ya fita yake yawo ko Allah zai sa ya samu ɗan aikin da zai yi,tun ɓacewar Sani ya daina bara kuma gashi yanzu ya fara zama saurayi shi yasa yake kokarin neman aikin hannu da zai yi ya samu na cin abinci.
Sai da yayi sallar azahar a wani masallaci sannan ya taka har ƙofar gidan,ya kai kusan minti biyar a tsaye yana tunanin yadda zai shiga gidan.
Kamar haɗin baki sai ga motarta,suna isa dai dai inda yake ta sauke glass tana kallon shi tace"Sadauki ba ka shiga ba?"
Ya sunkuyar da kai cike da kunya yace"ina wuni".
Ba ta amsa ba tace"ka shigo ciki".
Driver ya ja motar suka shiga Sadauki ya bi bayan su bayan ya gaisa da mai gadi,ta fito sanye da hijab sai labcoat da ke riƙe a hannunta tace"jiya da daddare na jira shiru,me yasa baka dawo ba?"
Yayi shiru kanshi a ƙasa,Mami da ke lura dashi tace"ai ni nace ka dawo Umar,kar ka sake min haka,daga yau anan za ka dinga cin abinci daga na safe har na dare,idan dai ka zama mai gaskiya ba ka da matsala da ni,ka zauna zan aiko a kawo maka abinci".
Ya sunkuyar da kai yace"to Hajiya".
Sai kuma yayi saurin cewa "Mami".
Mami tayi murmushi tace"gara da ka gyara tun wuri".
Tana shiga parlour ta tarar da Zeenah riƙe da bulala sai Zarah kusa da ƙofa fuskar nan shaɓe shaɓe da hawaye.
Mami ta bisu da kallo tace"lafiya?"
Zarah ta rungume ta da sauri ta fashe da kuka,Zeenah ta taɓe baki don kukan da take ba cetonta zai yi a hannunta ba.
Mami tace"me ya faru,kin ishi mutane da kukan banza?"
Cikin kuka tace"Mami ! Aunty Zeenah want to flog me"
Mami tace"ai gara ta zane min ke tunda kin iya kukan banza,you're not more a kid Zarah amma kullum abin naki gaba yake ba baya ba,idan bata duke ki ba da kaina zan miki shegen duka a gidan nan".
Muryar Sudais suka ji daga bayansu yace"ki yi hakuri Mami kar a zaneta dan Allah".
Mami tace"dama kai ke ɗaure mata ƙugu ai,ku bani hanya ni kam banda lokacin wannan kukan nata,yarinya sai kukan tsiya kamar kin fi kowa ruwan hawaye,Zeenah ki wuce ki zuba abinci ki kaiwa Faruq a waje".
Zeenah tace"waye Faruq Mami?"
Tace"wanda ki ka kaiwa abinci jiya,me kika dafa?"
Zeenah tace"spaghetti".
"To ki yi sauri ki kai masa dan Allah".
Zeenah tace"to Mami".
Zarah dake tsaye riƙe da hannun Ya Sudais tayi saurin fincike hannunta ta bi bayan Zeenah zuwa kitchen,Mami ta taɓe baki ta haura sama.
Surutu ta dinga zubawa Zeenah harta gama zuba abincin suka fito,yana tsaye inda Mami ta bar shi Zeenah ta ƙaraso.
Sai yau ta samu damar ganin fuskar shi da kyau,ya nada ɗan haske don ba za'a kira shi baƙi kai tsaye ba.
Zai girmeta sosai don da gani zai kai shekarun ya Sudais.
Ba tare da kowannen su yace komai ba ta miƙa mishi abincin,ta juya ta karɓi ruwa a hannun Zarah ta ajiye kusa dashi.
A hankali yace"nagode".
Zarah ta matsa kusa dashi tana kallon fuskar shi tace"yau ma ka sa old clothes?"
Ya ɗan ɗago ya kalleta ya ɗauke kai, Zeenah za ta buge mata baki taji muryar Sudais yana cewa"a yi haƙuri Aunty Zeenah kar a taɓa mu".
Zeenah ta taɓe baki tace"wannan kanwar taka sai a hankali Ya Sudais,wallahi ta cika surutu".
Ya ɗan kalli Sadauki suka haɗa ido ya ɗauke kai ya dubi Zeenah yace"amma kin san surutun namu ba na banza bane ko,tunda were brilliant".
Zeenah tace"kullum dai maganar ka kenan Ya Sudais,Allah yasa kowa da nasa ƙoƙarin dai dai gwargwado".
Yayi dariya ya shafa kan Zarah da gabaɗaya hankalinta ke kan Sadauki yace"little sis an daina kukan?"
Nan da nan ta ɓata rai tace"ban gama ba ya Sudais".
Zeenah da Sudais suka fashe da dariya,shi kanshi Sadauki sai da ya ɗago ya kalleta jin abinda tace, Sudais yace"ashe chu chu bata gama ba,to feel free to continue Zarah".
Ta fashe da kuka tace"ni dai bana so,stop laughing at me".
Ya gimtse dariyar da yake yace"babu wanda yayi dariya autan Mami,yi hakuri".
Sadauki kam da mamaki kawai yake kallonta,ta juya da gudu ta shiga ciki.
Sudais ya dinga dariya kamar an aiko sa Zeenah na taya shi.
Da kyar yace"to ya isa haka tunda kin sa ta kuka".
Zeenah tace"babu ruwana Ya Sudais kai ma ka sani,abun kuka baya wuya a wurin Zarah."
Hango Mama da ƴan matanta yasa yayi saurin haɗiye sauran maganar da ke bakin shi.
Jamila tace"Mama ga Yaya can harda dariya da Zeenah".
Ta tsaya tana watsa mishi wani mugun kallo tace"Jidda wuce ki kira min shi".
Da sauri tace"toh".
Tun da ya hango tahowarta ya san abinda ya kawo ta, Zeenah ta taɓe baki tace"Ya Sudais bari in shiga ciki,sai ka shigo anjima".
Kai kawai ya iya gyaɗa mata don yana iya hango irin mugun kallon da Mama ke watsa masa daga tsayen da take.
"Yaya Mama tace ka je tana jiran ka".
Bai ce mata komai ba ya wuce ya nufi inda take,tun kafin ya ƙaraso tace"wallahi Sudais idan ka yi wasa sai na tsine maka idan yaso sai ka koma wurin Hafsah tunda itace uwarka,ban hana ka shiga wurinta ba?"
Kanshi a ƙasa yace"kin hana".
A fusace tace"to uban me kake a wurin,ko ban isa ba?"
Sudais yayi shiru don bai san amsar da zai bata ba,ta nuna shi da yatsa tace"wannan shine gargaɗi na ƙarshe,idan ka sake saka ƙafarka a wurinta sai nayi mugun saɓa maka wallahi".
A hankali yace"ki yi haƙuri".
Bata kula shi ba ta wuce wurin motarta ta buɗe ta shiga driver seat Jamila ta zauna kusa da ita sai Jidda da ta buɗe baya ta shiga.
Ya matsa baya yana kallonsu har ta tada motar ta bar wurin.
Tana isa inda Sadauki yake ta sauke glass ta kalle shi daga sama har ƙasa,shima kallonta yake don duk maganganun da take ya jita sarai.
Ta watsa mishi wani mugun kallo cike da tsana,a rayuwarta ko dabba ce idan ta kasance mallakin Hafsat ta tsane ta kenan balle kuma mutum.
Bayan sun fita Jamila ta ɗauke kai daga kallon Sadauki tace"waye wannan?"
Jidda ta taɓe baki tace"kamar fa almajiri ne".
Mama na jinsu ta cigaba da tuƙin da take don ba wannan ba ne damuwarta.
Sadauki ya cigaba da cin abincin sa a nutse,kamar daga sama ya hango Zarah rike da ƙaton teddy bear.
Sai da ta iso inda yake sannan ta ja kujerar kusa dashi ta zauna tana kallon shi.
Ya ɗan kalleta ya ɗauke kai,ta gyara zama tace"what is your name?"
Yayi shiru kamar bai san abinda tace ba,jin bai kula ta ba yasa ta sake cewa"ba ka jin turanci?"
Ya ɗago ya kalleta,haskenta har wani ɗaukan ido yake.
Ta sake cewa"nace mene ne sunanka".
Ya buɗe baki da ƙyar yace"Sadauki".
Ta waro ido da mamaki tace"Sadauki,Mami tace sunanka Faruq,why are you lying?"
Ƙasa ƙasa yace"ashe kin sani".
Tace"me ka ce,banji ba".
Ya share ta don ya fara gajiya da surutunta.
Ta sake cewa "why are your clothes old,ba ka da new clothes?"
Firdausi wacce Zarah ke bi ta fito ta na dube dube,ta na hango Zarah ta nufo wurin a fusace.
Zarah na ganinta ta miƙe da sauri ta shiga ciki da gudu,rai ɓace Firdausi ta bi bayanta don kallo take aka ce ta fita ta nemo Zarah.
Mami dake fitowa daga kitchen tace"daga ina kike?"
Tayi shiru tana zare ido,Firdausi ta zauna kan kujera tace"Mami tana can zaune kusa da wannan almajirin sai surutu take zuba mishi".
Mami tace"zo nan Zarah".
A tsorace tace"ki yi hakuri Mami,ba zan sake ba".
Mami tace"ki zo kar ki ɓata min lokaci Zarah".
Kuka sosai Zarah take don ta tsani a taɓa lafiyar jikinta,tayi yinƙurin barin wurin Mami ta cafko ta.
Ta fasa wani ihu jiki na rawa tace"Please Mami ba zan sake ba".
Mami ta riƙe mata kunne tace "za ki sake fita waje ki zauna?"
Da sauri tace"a'a Mami".
"Idan kika sake me zan miki?"
Tace"flog me Mami,ba zan sake ba".
Mami ta sake mata kunnen tace"ki daina zuwa wurin maza babu kyau,idan kin sake duka za ki sha".
Kai kawai take gyaɗawa a tsorace, Na'ima dake gefe ta taɓe baki don ta san ba karamin aikin Zarah bane ta koma anjima.
A hankali Zeenah tace"ki yi hakuri Mami ba zata sake ba".
Mami ta ɗauki hijab ta fita compound inda Sadauki ke zaune,yana ganinta ya miƙe da sauri ya sunkuyar da kai.
Tace"Faruq ka gama?"
A nutse yace"eh na gama,akwai aikin da za'a miki ne?"
Mami ta girgiza kai tace"babu wani aiki amma ina da saƙon kasuwa,za ka iya zuwa kuwa?"
Sadauki yace"zan iya".
Mami tace"yawwa,bari in rubuto maka abubuwan da nake buƙata,amma ka iya karatu?"
Sadauki yace"eh na iya".
Tace"to shikenan,ina zuwa".
Ta juya ta koma ciki ta haura har sama ta buɗe handbag dinta ta ƙirga dubu shida sai paper da biro ta zauna ta rubutu abinda zai siyo ta fito waje.
Ta miƙa mishi takardar tace"ga abubuwan da zaka siyo min,karanto min inji".
Ya karbi takardar ya karanta abinda ke rubuce,Mami ta gyada kai tace"ashe kayi School?"
Kanshi na ƙasa yace"ina Jss 3".
Mami tace"Masha Allah,to yi maza ka dawo dan Allah,ga kuɗin,ka dauki dubu daya ka hau abin hawa sauran kudin su zaka min cefane dasu."
Ya amsa da toh ya juya ya bar gidan.
Bai wani jima ba ya dawo,Mami ta ƙarbi sakon ta buɗe taga ya siyo komai yadda tace,tayi murmushi tace"nagode Faruq,za ka iya tafiya sai ka dawo anjima da yamma ka karɓi abinci".
Sudais ya fito daga ƙaramin apartment dake can ƙarshe yana tafiya a hankali,yana hango Mami yayi saurin canza hanya.
Mami tayi murmushi ta ɗauke kai tamkar bata ganshi ba.
Sadauki dake kallon shi ta gefen ido ya ɗauke kai ya yiwa Mami sallama ya bar gidan.
Da yamma ya dawo kamar yadda ta umurce shi,bayan yayi sallama Zeenah ta buɗe kofa,tana ganin shine ta ɗan yi still,sai kuma tace "ina zuwa".
Ta maida kofar ta rufe ta sanar da Mami dake sanye da hijab don so take ta shiga part ɗin mai gidan nasu da dawowarsa kenan daga tafiya.
Mami tace"ki wuce ki zubo mishi tuwo,akwai wani ceramic bowl da na ajiye a gefe shi zaku dinga zuba masa abinci".
Zeenah ta wuce kitchen ta zuba mishi tuwon shinkafa miyar egusi,ta buɗe ƙofa ta karasa har inda yake tsaye ta miƙa mishi.
Ya sa hannu ya karɓa yace"nagode".
Bata ce komai ba ta koma ciki.
Mami na ganin ta dawo ta buɗe ƙofa ta fita, Sadauki ya tsugunna ya gaisheta cike da girmamawa.
Da fara'a tace"sannu Faruq,ka dawo?"
A hankali yace"eh".
Tace"ka ci abinci ina zuwa".
Sai da ta bar wurin ya buɗe kwanon abincin,yana ganin tuwo ya rintse ido,ga miyar sai kamshi yake da manyan nama kusan guda huɗu.
Yana ɗaga ido ya hango Zarah kamar wata aljana sai sanɗa take sanye da kayan bacci pink and white,kanta sanye da black turban.
Ta ƙaraso kusa dashi tana dariya tace"ai wayo na yiwa Aunty Zeenah".
Ya zuba mata ido yana kallonta,ta zauna kusa dashi kamar mai raɗa tace"ce mata nayi zan sha ruwa shine na zo nan".
A hankali yace"ki tashi ki koma ciki".
Ta maƙe kafaɗa tace"ba zan koma ba ni ina son zama da kai".
Ya zare mata ido yace"tashi ki shiga ciki".
Ta miƙe da sauri don sosai ya bata tsoro,ya ɗauke kai daga kallonta.
Ya ɗauki bowl ɗin tuwon ya miƙa mata ba tare da ya kalle ta ba yace"ki tafi dashi".
Da sauri tace"ba za ka ci ba?"
Yayi shiru kamar mai tunanin yadda zai sanar da ita,a hankali yace"bana cin tuwo".
Ta waro ido da mamaki tace"ba ka cin tuwo?"
A gajiye yace"eh,ki shiga dashi sai da da safe".
Ta ɗauki bowl ɗin ta wuce ya bita da kallo,yana ganin ta shige ya mike yayi sallama da mai gadi ya fita.
Yana barin wurin Mama ta fito sai baza kamshi take ta nufi part ɗin mai gidan nasu.
Mami na zaune kusa dashi a parlour tana zuba mishi shayi cikin wani golden tea cup,sai da ta zuba kusan rabin cup sannan ta miƙa mishi.
Yasa hannu ya karɓa yayi ɗan murmushin ƙarfin hali yace"thank you".
Mami dai sai kallon shi take,ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace"my General,anya lafiya kuwa?".
Ya ɗan kurɓi shayin kaɗan ya maida kofin ya ajiye,ya kafe tangamemen hoton shi dake parlourn sanye da Uniform din sojoji mai ɗauke da star biyu.
Mama ta shigo parlourn fuska ɗaure hango Mami zaune kusa dashi.
Ta zauna a kujerar da ke kusa dashi yace"Barka da dawowa".
Ya ɗan kalleta yace"thank you".
Mami ta miƙe zata bar musu parlourn ya kalleta yace"ina za ki je?"
Tayi murmushi tace"babu inda zan tafi,zan duba abu ne ina zuwa".
Yace"koma ki zauna ina son magana daku".
Mama ta watsa mata harara ƙasa ƙasa tace"munafuka".
Ta koma ta zauna tana kallon shi,duk da shi ɗin ba mai yawan fara'a bane amma da ganin shi ka san akwai abinda ke samun shi.
A nutse yace"na ajiye takardar barin aiki".
Da sauri duk suka yi saurin kallon shi.
Mami tace"innalillahi wainna ilahiri raju'un,abin har ya kai haka?"
Ya sauke numfashi yace"ya wuce yadda kike tunani,ya wuce yadda ni kaina nake tunani".
Mama tace"kai innalillahi wainna ilahiri raju'un,me yasa za ka yanke wannan ɗanyen hukuncin yallaɓai?"
Cikin kaushin murya yace"saboda barin shine mafi alkhairi".
Mami tace"gaskiya ƙasa tayi rashi,tayi rashin mutum mai kishin ƙasarsa".
Yayi murmushin takaici yace"na barsu su yi abinda suka ga dama,Allah ya gani nayi iya nawa ƙoƙarin".
Mami tace "amma barin babu abinda zai haifar sai sake dagula komai".
Ya mike tsaye ya shige ciki duk suka bishi da kallo.





Oum Rijalain 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.