Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 74
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCIATION
P74
Da la'asar Unaisa ta shiga ɓangaren Amirah,bayan shigarta ta tarar Amirah zaune cikin yara kasancewar Lahadi ce babu makaranta sallama dauke bakinta ta shiga parlour Amirah da yara suka amsa mata sallama,cike da girmamawa Amirah da Unaisa suka gaisa daga haka Unaisa ta zauna kan kujera one sitter tana shirin magana Amirah ta ce ''Abban Sudais ya tura mana ƙuɗin anko kin ga naki?" Unaisa ta ce ''eh na gani ya shiga ɗazu'' ok zan tura maki lamban Husnah wajenta ake siyan anko'' cewar Amirah da to Unaisa ta amsa ƴan danne danne Amirah ta yi cikin wayarta daga haka ta miƙawa Unaisa wayar tare da faɗin ''ga lambar ki dauka'' ƙarɓar wayar Unaisa ta yi ta kwashi lambar kafin ta mayar wa Amirah waya ba tare da ɓata lokaci ba ta kira layin sai dai har wayar ta ƙatse ba a ɗaga Unaisa bata hakura ba ta sake kira nan ma ba a ɗaga ba mayar da dubanta ta yi ga Amirah ta ce ''bata ɗaga ba'' Amirah ta ce ''fita harkarta ƙila bata kusa da wayar ne in ta ga miss call zata kira ki'' da dare misalin ƙarfe tara da ƴan mintina Unaisa na kwance kan gado ta rufa jiki da bargo hannunta riƙe da waya ta kunna American film a wayarta sosai flim ɗin ya dauke mata hankali,mayar da dubanta ta yi ga agogon wayarta ta ga karfe tara harda mintina ashirin tunawa ta yi har sannan Husnah bata kira ta ba,gashi da wuri take kwanciya yanzu saboda tana tashi cikin dare,tun sanda Mama ta yi mata nasiha ta ƙara dagewa wajen ibadah, daga ranar da Mama ta mata nasiha bata taɓa tsallake rana ba kusan kullum sai ta tashi cikin dare tana kaiwa Allah kukan ta,alhamdulillah sosai ta samu sauƙin damuwa yanzu wani sa'ilin har mantawa take da wani halitta wai Ɗalha,duk ranar girkinta da ta idar da sallar asuba zama take ta jira har sai ya dawo daga masallaci dake da wuri yake dawowa kafin gari ya waye,da ta ji motsinsa take zura hijab har ƙasa ta je ɗakinsa ta gaishi,in mutunci na kansa ya amsa in bai ga dama ba kuma ya ƙi amsa gaisuwar sau da yawa ko kallonta baya yi ko zai amsa gaisuwar baya ko kallon fuskarta,ita dai ta yi riƙo da nasihar Mama hakan yasa abinda yake mata bai cika damunta ba,sannan duk sanda yake ɓangarenta tana ajiye masa abinci,ta daina damuwa da ya ci abinci ko bai ci ba,ita dai tana dafa tana kuma sa masa,shiru ta yi tana tunani ko ta sake kira Husnah ko ta bari sai gobe bayan dogon nazari ta tsayar da flim daga haka ta kira layin Husnah bugu biyu Husnah ta amsa kiran,bayan Husnah ta amsa kiran ne suka gaisa sai dai Husnah bata gane wacce take magana ba hakan ya sa Unaisa faɗin ''Unaisa ce'' shiru Husnah ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''wace Unaisa?" Unaisa ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce ''matar Abban Sudais'' sai a sannan Husnah ta fahimta cikin wata iriyar murya ta ce ''ok na fahimta,ya ki ke ya kwana biyu?'' yadda ta yi magana jikin Unaisa ya yi sanyi cikin sanyin murya ta ce ''lafiya Alhamdullilah daman kan maganar anko ne Maman Sudais ta ce ke ake turawa kuɗi'' Husnah ta ce ''umhm okey'' ko kaɗan Unaisa bata ji dadin amsar da Husnah ta bata ba,shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni Unaisa ta ji kamar ta kashe wayarta amma sai ta daure ta ce ''in babu damuwa ko za ki tura min account number sai na sa maki'' gaba ki ɗaya Husnah ta ji ta gaji da zancen,ko kaɗan bata kaunar Unaisa hasalima haushi take bata cike da ƙaguwa da zancen ta taɓe baki kamar tana gaban Unaisa ta yi magana cikin ɗan jin haushi ta ce ''ok zan tura maki'' daga haka ta katse wayar ba tare da ta yi sallama da Unaisa ba,a hankali Unaisa ta cire wayar daga kunnenta cike da mamakin abinda Husnah ta mata,ta kafe wayar da ido tana jin babu daɗi cikin zuciyarta wani irin tsana ne haka?tun kafin ta aure Ɗalha bata taɓa tsanar ƴan uwansa ba,Ammi ce dai bata cika burgi ta ba saboda ta samu labarin yadda Ammi ke son Amirah wanna dalilin yasa bata wani son Ammi,sai dai bayan ta aure Ɗalha ya fahimci Ammi mutumiyar kirki ce ta kuma fahimci kyawawan halaiyar Amirah yasa Ammi ke son ta,ba iya Ammi ba duk wanda ya zauna da Amirah dole ya ƙaunace ta saboda kyawawan ɗabi'unta,bata taɓa jin tsanar Husnah ba,tana da tabbacin babu abinda ya taɓa haɗata da Husnah,tun kafin aurenta da Ɗalha Ɗalha ke nuna mata hutunan Husnah da yaranta,amma bata taɓa jin tsanar Husnah ba,to me yasa Husnah bata kaunarta?"sai bayan aurensu ta fara ganin Husnah ido da ido ranar da Ɗalha ya korata da mota a ranar ta fara ganin Husnah,ta dauki sama da sakanni goma riƙe da waya ta ƙure fuskar wayar da ido,nan take idanunta sun ciciko da ƙwallah bata anƙare ba sai jin saukar hawaye a hankali ta kai hannu ta goge hawaye tana jan hanci jiki babu kwari ta ajiye wayar gefe,ta takure kanta cikin bargo nan ta shiga rera kuka a hankali tana tuna abubuwa da dama a haka bacci ya dauke ta,washe gari karfe sha ɗaya da wasu mintina na safe Unaisa na ɗaki tana shirya gogaggun kaya cikin saif tun jiya Aina'u ta goge mata su amma jikinta ya mata nauyi bata iya gyara ba sai yau,wayarta ce ta yi ƙara alamar shigar saƙo bata bi ta kan wayar ba sai da ta gama shirya kayan gaba ɗaya kafin ta zauna ta dauki wayar,bayan ta cire wayar a key ta ga Husnah ce ta tura mata account number,taɓe baki Unaisa ta yi nan take ta turawa Husnah kuɗin,bayan ta tura mata ƙudin ta kunna data ta tura mata reciept a whatsapp bayan ta tura mata reciept taga Husnah online hakan yasa Unaisa yi mata sallama ga mamakin Unaisa Husnah ta buɗe duka saƙonni biyun amma bata amsa ba ta buɗe hoton reciept sanan ta karanta sallamar da Unaisa ta mata amma bata amsa,Unaisa ta yi ƙwafa kawai daga haka ta cigaba da sabgoginta
Bayan sati ɗaya Husnah ta aika masu da zannuwansu kowacce ta ba da ɗinki,duk sun saya abinda za su bukata na biki,a haka ciki Unaisa ya shiga wata shidda,kamar yadda Anty Aisha ta fada duk bayan sati biyu tana zuwa gidan Unaisa su yi ta hira ko bata samu zuwa ba tana kiranta a waya su yi hira,sosai hakan ke taimakawa Unaisa wajen rage tunanuka da wasu damuwowi na yau da kullum,tun bayan sallar asuba Unaisa bata kwanta ba ta shiga shirin zuwa asibiti,karfe takwas da wasu ƴan mintina ta fita daga ɗaki zuwa ɗakin Ɗalha,sallama dauke a bakinta ta shigo ɗakin Ɗalha dake tsaye gaban madubi cikin shirin zuwa ofis hannusa riƙe da kwalbar turare yana feshi jikinsa mayar da dubansa ya yi ga kofa ba tare da ya amsa sallamar ba ya kafeta da ido,a hankali ta tako har inda yake cike da girmamawa ta durkusa ta gaishi shi,har sannan idonsa kansa,sanin kansa ne da yawa yawan mata mune suke duk sanda suke da ciki amma banda Unaisa wani irin musulmin kyau da cikar halitta take ƙarawa kullum,har ta miƙe daga rusuni bai amsa gaisuwar da ta yi masa ba,waje ta samu ta zauna kafin ta mayar da dubanta garesa ta ce ''ina son zan tafi asibiti kwanakin da suka ɗiba min ya cika'' daga haka ta yi shiru ta shiga wasa hannun ƙaramar jaka dake hannunta,kamar daga sama ta ji muryarsa ya ce ''kina lafiya?" cike da mamaki ta ɗago ta kallesa ta ga ita yake kallo ƙasa magana ta yi kawai ta gyaɗa masa kai alamar eh,tana nan zaune ta ga ya tako har inda take zaune yazo daf da ita,jakar da take riƙe da shi ta ajiye gefe da niyya masa magana kawai sai hannusa ta ji a haɓarta yana daga tsaye ya kafe fuskarta da ido kamar yadda ita ma take kallonsa gaba ki ɗaya ya shagaltu da kallon kyakkyawar fuskarta bai san sanda ya fara yawo da hannusa fuskarta ba kamar wanda a ka yiwa dole ya buɗe baki da kyar ya ce ''ya suke?" cikin rashin fahimtar inda tambayar sa ta nufa Unaisa ta ce ''su wa?" bai amsa ta ba ya kai duka hannayensa biyu ya ɗagota tsaye yana ƙara binta da wata shu'umar kallo a hankali ya haɗata da jikinsa ya rungumeta a hankali tare da rintsa idanunsa,ta cikin dreassing mirror Unaisa ta kalle fuskarsa ganin yadda ya wani rintsa idanu ta taɓe baki bata ce komai ba,sun dauki a ƙallah sakanni biyar a haka kafin ya kai bakinsa daidai kunnenta ya yi magana da ƙyar yana jan numfashi ya ce ''my babies inside you'' ƙwafa kawai Unaisa ta yi ta masa banza bata ce komai ba a yanzu babu wata soyayya a gabanta burinta Allah ya sauke ta lafiya,in ya so ya yafe mata ko kar ya yafe mata tana nan tana addu'ar Allah ya zaɓar mata abinda yafi zama alkairi rayuwarta,kamar baza ta amsa sa ba sai kuma ta daure ta ce ''suna lafiya'' raba ta ya yi da jikinsa tare da manna mata kiss kunci sai kuma ya ce ''oky'' Unaisa kamar jira take ta koma ta zauna tare da ɗaukar jakarta,tana satar kallonsa ta ga ya dauki wasu file daga bed site drower yana dubawa,bayan wasu ƴan sakanni ta mayar da dubanta garesa kafin ta yi magana cikin sanyin murya wannan rungumar da mata ya sa ta shiga wani irin yanayi amma yanzu ba shi ba ne gabanta a hankali ta ce ''kuɗin mota da kuɗin awo za ka bani'' ya bata amsa a takaice ya ce ''nawa?" shiru ta yi tana nazari nawa zai ishita can ta ce ''20k'' ba tare da kallon inda take zaune ba ya ce ''ok zan tura maki'' kamar jira take ta tashi da sauri tare da yi masa godiya daga haka ta bar ɗakin,da ido kawai Ɗalha bi bayanta bayan fitarta ya sake murmushi shi kadai,a gajiye Unaisa ta dawo gida wannan ranar harda ta fita da wuri amma ta samu kusan mutum goma gabanta harda asibitin kuɗi ne amma suna samun jama'a sosai musamman masu ciki,bayan dawowarta gida farar taliya ta dafa babu mai babu yaji haka ta ci,tuwon shinkafa miyar taushe da Aina'u ta dafa bata iya ci ba duk yadda Aina'u ta yi da ita ta ci tuwon ko kaɗan ne Unaisa ta ce bata jin cin tuwon ita farar taliya take son ci karshe a firiji Aina'u ta sa abinci,karfe biyar da wasu mintina yammacin wannan rana Unaisa na zaune ɗaki fitar ta kenan daga wanka tun bayan dawowarta daga asibiti take son yi wanka amma nauyin jiki ya hanata,tun bayan ta ci farar taliyarta ta ƙasa taɓuka komai sai kwanciya,zaune take saman karamar kujera dake gaba madubi tana shafe jikinta da body lotion bata ɗauki lokaci ba ta gama shafe shafenta ta gyara sumarta inda ya shafa masa mayuka masu kyau da ƙhamshi,wata doguwar riga pakistan marar nauyi ta dauko ta zura da kadan rigar ta wuce mata gwiwa,zama ta yi bakin gado hannunta riƙe da waya Ammi take son kira, tun sanda Amirah ta bata lamba take son kiran Ammi su gaisa sai dai ta ƙasa bayan dogon nazari ta daure ta dannawa layin kira har kiran ta ƙatse ba a ɗaga ba,sake kiran layin ta yi wayar tana daf da katsewa Ammi ta ɗaga tare da sallama daga ɗaya ɓangaren Unaisa ta amsa sallamar daga haka suka gaisa,ga mamakin Unaisa sai ta ji Ammi na tambayarta karfin jiki hakan ya nuna Ammi ta gane muryarta cike da kunya Unaisa ta amsa ta ce ''da sauƙi sosai'' Ammi ta ce ''masha Allah rabbi ya inganta ya raba lafiya'' ƙasa amsawa Unaisa ta yi sai a zuciyarta ta ce ameen a zahiri kuma ta yi magana cike da girmamawa ta ce ''daman na ga an kwana biyu ne na ce bara na kira na yi gaisuwa'' Ammi ta ce ''masha Allah kin kyauta Allah ya yi albarka nagode'' sosai Unaisa ta je dadin amsar da Ammi ta bata ta ce ''ameen'' Unaisa na shirin magana ta ji Ammi na magana a gefe inda take faɗin ''Salame ki duba miyar dake wuta ko ta nuna ga tumatir ba ki dauka ba har ta fara tsayayi cikin leda'' jin haka haka yasa Unaisa tunanin Ammi tana aiki ne hakan yasa ta shiga faɗin ''hello Ammi sai anjimuma'' ta faɗa hakan ya fi a ƙirga sai dai Ammi bata amsa ta ba karshe ta je Ammi ta kama hira da wata ƙawarta,jiki babu ƙwari Unaisa ta kashe wayarta,bayan ta kashe wayar ta shiga tunani ganin tunani zai mata yawa yasa ta kunna flim cikin wayarta haka ta kasance har lokacin da aka fara kiran sallah magrib a masallatan unguwa da kyar ta samu ta yi sallar magrib da isha saboda yadda jikinta ya mata nauyi sosai ga kumburi da fararen ƙafafunta suka yi har wani daukan ido suke,misalin ƙarfe takwas na dare Unaisa na kwance tana kallo a TikTok ta ga an tura saƙo a group ɗin matan gida cewar akwai taro da za a yi gidan ɗaya daga cikin ƴan kungiyar karshen sati,shiru Unaisa ta yi tana nazari har cikin zuciyarta bata son zuwa taron amma tunawa da irin kalaman da ƴan kungiya suka riƙa fada mata watan da ya gabata yasa ta yanke hukunci zuwa taron a wannan karon,hakan kuwa ta yi sati ya zagayo Unaisa ta cewa Ɗalha zata je gidan Mama ba tare da jan rai ba ya ce ta shirya ya ajiye ta gidan Mama,tsabar rashin tsoro irin na Unaisa har kofar gidan Mama Ɗalha ya ajiyeta ta shiga ta gaida Mama amma bayan ta tabbar Ɗalha ya tafi ta cewa Mama za ta je kasuwa ta siya wani bau zata dawo,a gurguje ta tafi gidan taro ta bada ƙudin taro daga can ta wuce kasuwa ta yi siyayyar kayan jarirai da bata yi niyya ba,daga kasuwar ta wuce gidan Mama sai yamma Ɗalha ya dawo ya dauke ta
SHUUKRAN