Free chapter · Read without an account
31. ...nima na ba kaina mamaki...🖊️
Bayan na koma gida nayi duk abinda zanyi na fara biyawa sashen Khalil amma yau bai nan... wucewa nayi ɗakin Roman shima babu alamun yana ciki...na zagaye gidan duka..ƙila tare suka fita da Khalil koma meye banji daɗi ba...
Wurin yamma nida Diyaam muna zaune a ɗakinta aka aiko wai Hajiya Momma na kiran mu,kallon juna mukayi kafin muka tafi har third floor...iske ta mukayi ita da ya'yan ta sun ɓata parlor'n su kamar ƙananan yara...ga wani jan abu a ƙasa...wurin dai ba kyaun gani...ga biscuit da wani fari farin abu saman carpet ɗin
Gefe na kalla naga Hansa'u tsaye itama da alamu aikin aka kirata tayi...a ɗaɗɗage Badariyya tace '' kun wani ma mutane tsaye a ka..maza ku fara aiki...''
Hajiya Momma daga gefe tana cin gyaɗa tana hura hanci.... Allah matar nan mummuna ce sosai...
Badariyya''Ke zoki shafa min nail polish a ƙafa...'' kallon ƙafarta nayi da take kamar ta kutare...abu kamar anyi dyeing ɗinta tsabar bleaching
'' Oh...Khalil yace ba zamu sake aiki ba sai mun gama jarabawa!"
'' dan ubanki Khalil ke biyan kune? uwayen son banza...'' zagin ubana da tayi yayi min zafi amma bance komai ba...Diyaam ta ɗauki tsintsiyar dake ajiye a parlor'n ta fara shara... Hansa'u daga gefe ta rufe baki tana min dariya
'' ke...wuce bayen nan ki wanke shi!" Hajiya Momma ta nuna Hansa'u... Hansa'u na buɗe bayen wani irin wari ya gume parlorn
'' BABBAR BALA'I!!! ni zan wanke wannan abun?" Ta fito da gudu ta tsaya gaban Hajiya Momma tana yatsine fuska kamar zatayi amai...
'' toh ko ubanki zai wanke?" Mardiyya ta amsa a zafafe...naɗe hannu a ƙirji Hansa'u tayi tana cika tana batsewa '' kai da sake wallahi! Baxan iya cin kashin gardawa ba!"
'' waye gardin?"
'' wai Hajiya kin koga yanda wurin nan ya rine daga fari zuwa baƙi tsabar datti? Ko numfashi da ƙyar nake taya zan zauna cikin irin wannan wuri?" ganin Hajiya Momma ta miƙe ba shiri nayi ƙasa na fara shafawa Badariyya nail polish ɗin Diyaam tayi ƙasa kamar zata ɓoye ta cigaba da shara... Hansa'u taja baya
Damƙota Hajiya Momma tayi '' muje inga bayen..'' kamar wacce akayi arresting haka Hajiya Momma taja Hansa'u cikin bayen kuma fa da gaske yayi dattin saboda qarnin dake tashi...
'' au ashe ma babu omo...maxa sa hannu ki fara wanke wa...''
'' KAM BALA'I! Wai kamar ya?" Hansa'u tayi gardama tana ƙoƙarin ƙwace hannunta...Hajiya Momma taƙi saki..nikam harna gama shafawa Mardiyya Nail polis ɗin naja ruwa gefe ina share wurin daya ɓaci da wani jan abu idona akan su Hajiya Momma ina riƙe dariya ta
a fakaice muna kallon dramar dake faruwa...gani mukayi Hajiya Momma ta jefar da Hansa'u ta ɗane mata ruwan ciki.. Hansa'u sai ihu take tana neman ceto...ruwan dana goge wurin dasu na ɗauka nayi ma Diyaam alama da ido dan yanda take kallo Ido waje zaka san a tsorace take...su Badariyya sai dariya suke
nida Diyaam muka shiga ja baya '' ku riƙe min s...'' kafin ta gama mun kwasa da gudu su Badariyya biye damu...ni ban san meyake damuna ba ruwan mopping ɗin nan dasu na fito ina gudu suna zuba...
nida Diyaam kowa ya kama hanya daban daban...
Na ɗauka koma wacece ta Dena bina ashe wai tana biye dani...tsayawa nayi da ruwan a hannu na tana mayarda numfashi nima ina mayarda nawa nace '' wallahi idan kika matso ni sai na maki wanka dasu!"
'' shege ka fasa!" Ta faɗa tare da yowar cikina aiko na watsa mata ruwan...kaucewa tayi gefe suka sauka akan ROMAN!!! nida ita idon mu kamar zasu faɗi farar rigar shi ta sauya launi kamar yanda fuskar shi tayi duhu...ja baya na shiga yi.. kafin na juya da gudu nabar wurin batareda na juyo ba...
ban tsaya ko ina ba sai ɗakin Diyaam...idon muna haɗuwa muka saki dariya...kaya ta bani daga cikin nata na sauya muka zauna... TV ta kunna muna kallon fim..wurin ƙarfe takwas muka tafi sashen Khalil lokacin ya dawo daga ko ina ya tafi....
muka zauna muna hira tare yace ai gidan abokin shi ya tafi...'' wani abincin gargajiya aka kawo amma na kasa ci... however yanzu nayi nadamar rashin cin abincin...''yanda fuskar shi ta nuna alamun nadama yaban dariya '' meye sunan abincin?"
Sosa kanshi '' Uhmm...ɗan ke...''
'' ɗan ke?" Nida Diyaam muka tambaya a tare..'' ehm akwai wani abu kafin ke ɗin...''
'' oh ...ɗan wake?" Clapping hannun shi yayi '' ɗan wake...''
'' Na iya ..z..zan iya .. yi maka idan kana so...'' Diyaam ta faɗa a kunyace '' sure amma gobe...'' gyaɗa kanta tayi
ƙara jimawa mukayi kaɗan kafin muka tafi daga sashen shi, Diyaam ta wuce ɗakinsu na wuce sashen mu...
____
'' Abeedah meye ne?"buɗe idona na shiga yi suka sauka akan fuskar Mama Asabe '' meya faru?" Na tambaya ina murza ido
'' naga kin makara Sallah ina tada ke kina turo baki kina faɗin Romo...''. Gwalalo ido nayi kumatuna suka ɗau zafi kai.Na taune leɓe...mafalki nayi wai Romo yana kissing ɗina KAIII!!!....da sauri na rufe fuskata kunya ta dabaibaye ni Mama Asabe tayi tsaye daga gabana tana kallo da wani irin ido a gaggauce na sauka na shiga baye,
Allah ya taimake ni babu komai a kan pant ɗina babu ni ba wankan dole da sai munyi case dashi,amma duk da haka sai da nayi wanka da alwala nayi sallah na sauya kaya zuwa riga da wando baƙaƙe...nayi muraji'a..da ƙarfe shida na fita zuwa kitchen ina tunanin Mafalkina abun na ƙara sa ni a kunya ... lallai abun azimun ne,ni wallahi ban taɓa irin wannan mafarkin ba ko sau ɗaya sai yau Allah yasa ba'a sanin abinda ke zuciyar mutum dana shiga tara
Masu girki basu shigo kitchen ba a wannan lokacin...kuma har yanzu safiya bata iyarda waye ba,hakan yaba wajen wurin wani irin view mai kyau kamar kada safiya ta iyarda waye wa...amma hasken kitchen was dim...
na zuba ruwan zafi cikin cup na sirka...ina tsaka da shan ruwan sai gashi ya shigo da alamu daga gym yake...saye yake da baƙar singlet data kamashi sosai har take outlining six packs nashi...ƙirjin shi cike kamar na mace.. gashin shi ya rufe idonshi na hagu wasu kuma sun laƙe mashi a wuya...
Idona ya sauka akan jajayen laɓɓanshi, ruwan dake bakina na furzar suka wanke mashi fuska na shiga tari kamar xan mutu...tsaye yayi kamar an ɗasa shi a wurin..da alamu ji yake kamar na raina mashi wayo.. na mashi wanka da ruwan datti yanzu kuma da ruwan baki...
ruwan suka dalalo daga goshin shi zuwa lips zuwa ƙirji yake bina da wani matsiyacin kallo..if looks could kill Dana mutu
'' wallahi na wanke baki da daddare kafin in kwanta da kuma yau da safe!" na faɗa da sauri ganin yana tunkaro inda nake tsaye kafin ƙafafuna da kansu suka matsar dani gefe..idona na kaiwa akan ƙofa...
'' yet it smells like gutter!" ƙanƙantar da idona nayi na dena matsawa jin abinda ya faɗa '' kai fa kai kaɗai kake faɗa ma mutane baƙaƙen maganganu face flat!"
'' inyi murmushi ne idan ina faɗan?" farin towel ya ɗauka yana share ruwan dana mashi wanka dasu yana hararata...those hunter eyes are so sexyy...
🍁🍁: focus Abeedah 🤭
Abeedah: ehem ehem bana son sa ido🙄
Da sauri na girgiza kaina na Harare shi ..buɗe wani cupboard dashi kaɗai keda mukullin wurin ya ɗauko plates da blender cikin fridge ya ɗauko fruits da yawa daban daban ya ɗaura saman plates ɗin kafin ya juya ya kunna tap zai ɗauraye blender ɗin,wani purple fruit na ɗauka daga cikin wanda ya ajiye
kallon fruits ɗin yayi na tsawon lokaci sai kuma ya barsu wurin..na ɗauka zai dawo yayi amfani dasu ne sai naga ya ɗauko wani abu daban
'' wannan fa,bari in wanke ma...''
'' ai kin riga da kinyi contaminating ɗinsu I don't want it anymore!"
na saki baki...haka ranar dan na taɓa gashin shi yayi aski,na taɓa cup ya zubar da Lipton ɗin...is this person okay?
Fridge ya sake buɗewa ya ɗauko Greek yogurt,granola , honey ,peanuts,hazel nuts,da gyaɗa,almond nuts da wasu sauran gyaɗan da ban sani ba...
Ya haɗe su wuri ɗaya ya zuba yogurt da granola ya zuba zuma da yawa...sai ya kwasa zai mayar a fridge ya kalle ni ganin ina kallon abinda ya haɗa da ƙatuwar muryar shi ƙasa ƙasa yace '' don't touch it!" gyaɗa kaina nayi ya tafi ya ajiye ɗin abun ya biyo min a rai sosai ban san sanda na matsa kusa ba...yawuna suka tsinke suka faɗa ciki...
Ido buɗe nayi saurin goge bakina naja baya nake kallon bayan shi koda ya gani Allah ya taimake ni bai gani ba...'' phewww!" na share zufar da ba'a gani
'' kin taɓa?" girgiza kaina nayi ya gyaɗa kanshi'' ashe kina jin magana?"
'' oh..nima nayi mamaki! Kasan ni kurma ce...''
'' Uhmm..''
'' yanzu ba zaka sammun ba?"
'' kina sone?" ya tambaya yana kai cokali ɗaya a baki...it took everything in me kada in fashe da dariya...har na hango fuskarshi idan yasan cewa harda yawu na a ciki...
'' why are you smiling?" Ya ɗage gira yana jefa min kallon tuhuma...''
''.ba komai...'' na furta tare da jawo wani ƙaramin cup pink na miƙa mashi ya zuba min da yawa nasa cokali ciki...
'' na gode...'' juyawa yayi zai tafi...naji wani iri a raina..sai kawai nabi bayanshi daidai elevator zata rufe na faɗa ciki
Ɗaure fuska yayi '' why are you tailing me?" yayi maganar da serious face.. oh ...
'' ehmmm,da gaske ne akwai vampires a duniyar nan?" Na matsa kusa dashi..ido zare...'' eh..''
Ya taƙaita amsar shi.. curiously na ƙara matsawa kusa dashi '' da gaske? Ka taɓa gani kenan?"
'' eh..''
'' a ina?"
'' a gidan nan! ''
'' waye?" ya matsa zuwa ɗayan gefen ganin ina ƙara matso shi..ni kuwa idona babu abinda suke sai ƙyalli'' ke! You're the vampire!" ƙanƙantar da idona nayi tare da turo baki...'' wai ma...nida ban taɓa shan jinin kowa ba..''
'' but you drain my energy!" Ya bani amsa juya idona nayi nabi bayan shi sanda elevator ta buɗe...
ɗakin gym muka shiga...wurin kamar inda ake training mutane..akwai abubuwa da yawa...
'' fita daga nan!" Ya tsaya hakan yasa naci karo dashi...ɗan abinda ke riƙe a hannu na ya zubar mashi a riga...taune leɓenshi yayi dan yaji sanyi a fatar shi... he's eyes shooting blazers at me '' ai ban san zaka tsaya ba shine yasa...'' nasa hijabina ina goge wa... kaucewa yayi yana hararata sai kuma ya fita daga gym ɗin a fusace kamar zai ɓalle ƙofar bayan shi nabi ina jin daɗin yanda nake bashi haushi
cikin lambu ya tafi nima na bishi...ya zauna gaban allon zanen shi yana kallon abinda ya fara zanawa amma bai gama ba...zama nayi saman kujerar dake kusa da tashi
'' My painting is in danger...matsa baya!" Bakina cike da yoghurt na zaro ido ina kallonshi jin abinda ya faɗa...ya haɗe fuska..sauke ƙafafuna nayi ina jan kujerar baya...cokali ya faɗi daga cikin cup ɗina da yoghurt da yawa cikin shi ya fallatsar ma painting ɗin
'' OH MY GOODNESSS!!!!!"ya faɗa da ƙarfi tare da cusa hannun shi cikin sumar shi yana ja kamar hakan zai sassauta mashi haushina a ranshi...
Nayi tsaye da alamun rashin gaskiya...ya juyo ya kalleni kamar zai dake ni sai kuma ya sauke ajiyar zuciya '' manta kawai! You always bring disasters to my painting!"
zama yayi yana kallon yoghurt ɗin daya zama kamar ƙasa saman painting ɗin completely smearing it...
Ɗage kafaɗa nayi na sake zama...har rana ta fito ta haska gefen fuskarshi..ƙwayar idonshi kamar zuma..bakin shi ya ƙara ja...ɗauke idona nayi ina jin wani iri... kai gaskiya mutumin nan ya koya min abinda ba shi ba
'' i can feel you staring at my lips,I ain't gonna kiss you idan ma abinda kike tunani kenan!"yayi maganar casually kamar yana magana akan weather
naji kunya ta lulluɓe ni,idona kamar zasu zube..to make it worse sai ya wani juyo yana kallona blankly shi ɗan abunda ban ce ba
'' hasbunallahu wani'imal wakeel...a'udhubillahi minash shaiɗanir rajim!!! nifa ba..uhm...a..abin..da nak!!!!"
ɗauke idonshi yayi daga kallona jin yanda nake ta ina ina,na kasa ɗago kaina zuciyata na tsananta bugu a ƙirjina
'' ai baka ma iya kiss ɗin ba,salan kaje ka cinye min laɓɓa kabarni da cizon yatsa!!!"
na tattaro duk jarumtar data rage min na faɗi hakan ina kallon cikin idonshi ƙafafuna na rawa haka ma hannu na, numfashi namin wahalar ja.
Sai kawai ya ɗage kafaɗun shi ba tare da ya sake cewa komai ba,duk da naso maganar ta cigaba
🍁🍁: Innalillahi wa inna ilaihi raji'una..ke Abeedah ashe haka kike
Abeedah: aunty no full my ears abeg...
🍁🍁: 😂😂
bayan lokaci ya shafa sumar shi ..nima na kai hannu na taɓa ƙarshe ƙarshen kafin na bubbuga kanshi kamar yanda ake ma yara...bai kalle niba ya cigaba da shan abunshi irin magana dake ɓata lokaci ne.. nayi murmushi '' ehmm,yanzu ƙara aske gashin ka zakayi dan na taɓa?"
'' Yes!" Ya ban amsa
Miƙewa tsaye nayi batareda nayi tunani ba na rungume shi ta gefe har yoghurt ɗina ya zuba akan cinyar shi... ya zaro ido dan baiyi tsammanin hakan ba...ya shiga shock matsawa baya nayi da murmushin nasara nace '' ka haɗa da fatarka duk ka canja...bye!"
Da gudu nabar wurin ina cigaba da dariya ban ko kalli gabana ba naci karo da Farzan shima dai ya karɓi nashi rabo dan fuskar shi ta wanku da yoghurt
'' MEYE HAKA!!!?" Ya faɗa kamar mahaukaci yayo kaina..cikin rashin Sa'a yayi taku ɗaya cikin yoghurt ɗin daya zuba ƙasa ji kake RAGAJAB!!! Yayi muguwar faɗuwa
Ƙasa haƙura nayi na fashe da dariyar da duka hallway ɗin sai da ya ɗauka...'' YOU!!!!" Ya fara ƙoƙarin miƙewa da gudu nabar wurin ina faɗin '' sowwy!!!"
Miƙewe Farzan yayi ya ɗan kalli ko ina yaga babu wanda yaga abinda ya faru...ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya saki murmushi shima abun ya bashi dariya...
Da ƙarfe ɗaya na koma sashen mu, tunda bani da aikin yi kawai na zaɓi yin bacci...da ƙarfe huɗu wayata tayi ringing..Jay d ce na ɗauka tun kafin inyi sallama
'' ya dai? Kinyi abinda na faɗa maki ɗin?" Ta tambaya da rashin haƙuri
Kwantawa nayi da murmushi a Fuskata na shiga zayyana mata abinda ya faru...tayi dariya tace '' ƙilama shima sonki yake...!" zaro ido nayi..'' wannan iƙirari yayi girma ke Jay d''
'' Hmph zamu gani ai!" daga nan muka cigaba da hirar exam...
Da ƙarfe biyar na tafi sashen Khalil yana saye da glasses yana karanta wani littafi..yana gani na ya saki murmushi '' Oh... kitten ''
'' na'am Abraham...'' dariya yayi har sai da haƙwaranshi suka fito...na zauna daga can gefen shi...idona ya sauka akan abincin dake gaban shi '' it's pizza... Rome ya haɗa..''
'' ya iya abinci ne?"
'' yep.. he's a top chef...''
'' hmm..akwai daɗi?"
Tura min plate ɗin yayi '' ciki ji..'' nikam abun ƙyama yake bani..yake kallona da murmushi ganin yanda nake nuna ƙyanƙyami...'' ka tabbata wannan abun na sama ba majina bane? ƙila kaki yayi ya tofa ciki!"
Dariya Khalil yayi '' come on...Rome yana daga cikin mutane masu tsafta sosai..ko kaɗan abu yayi datti sai ya wanke!"
'' oh key...'' jan abun nayi na kafe da ido amma na kasa ci,daga ƙarshe ajiyewa nayi '' wallahi baxan iya ba..''
'' wannan abun fa Cheese ne...'' girgiza kaina nayi...ina
'' it's Italian food shine yasa...''
''.uhm..ko cizo ne'' na taɓe baki..bai matsa min ba muka cigaba da kallon fim ɗin da ake nunawa... tashi nayi xan fita sai ga Diyaam ta shigo itama '' Sofia.. zoki tayani zama Kitten guduwa zatayi...''
zama tayi a ɗayan kujerar bayan ta gaishe da Khalil ta gaishe dani...
'' bari inje zan dawo!" Na faɗa kafin na fita...
Diyaam tabi bayan Abeedah da kallo kamar tabi ta, she's not comfortable zama ita kaɗai da Khalil.. kunyarsa take ji sosai
'' ga pizza!" Ya tura mata plate ɗin...a kunyace ta ɗauka tareda faɗin '' na gode...'' amma ta kasa ci.. zuciyarta sai bugu take da ƙarfi..duk da Khalil ya mayar da hankalinshi akan littafin da yake karantawa... can ya ɗago ganin bata taɓa pizza'r ba...'' idan bakya jin daɗin zama a nan You can leave...'' cije bakinta tayi...taya zata ƙi zama dashi? Duk da dai kunya ke hanata magana dashi ba kamar Abeedah ba .. at this point taji ina ma ace itace Abeedah..she could speak to him freely..
Ɗaukar Pizza ɗin tayi ta fara ci kaɗan kaɗan can ta ɗago kanta da niyar satar kallon shi their eyes met..sarƙewa tayi... Khalil ya baro inda yake hannun shi riƙe da gorar ruwa ya buɗe ya miƙa mata yana mata sannu...karɓa Diyaam tayi tana sha ido jajir...'' na gode!" Ta faɗa...gyaɗa kanshi yayi...
jin sound na tashi daga TV'n yasa su biyun at the same time sun mayarda kallonsu akai...of course ..Idanun Diyaam kamar zasu faɗo a cikin shekaru sha biyar na rayuwarta bata taɓa ganin abu irin haka..na mijin da macen suna kissing juna hannun namijin a ƙarƙashin rigar macen,ita kuma tana jan belt ɗin shi it was explicit
Zaram!! Diyaam ta miƙe a ruɗe zuciyar ta na bugu da ƙarfi...har ta manta da cewa Khalil na zaune a gefenta ta juya da niyar barin wurin, tuntuɓe taci da ƙafarshi.. completely ta faɗa saman shi...their eyes met...fuskar Diyaam tayi jawur kamar tumatur... idon su biyun a waje da sauri ta miƙe baki na rawa...sai kuma ta juya ta fita daga sashen tana cin karo da abubuwa along the way...Khalil ya daskare a wurin utterly stunned
wurin swimming Pool Diyaam ta isa ta dinga zuba ma fuskar ta ruwa...har Saida zafi da jan ya ragu ta sauke ajiyar zuciya,sai kuma ta tuna yanda take zaune a jikin Khalil,wani sabon blush ya fara spreading daga fuskarta har zuwa ƙirjinta
****
Koda na koma sashen mu babu kowa duka yan aikin suna duty wasu kuma sun tafi gida waya'nda ke zama anan garin kenan... nikam sai wani sati,waya na ɗauko na kira su Mama muka gaisa nidasu Asma'u mun daɗe muna magana kafin mukayi sallama da juna
Washegari asabar da rana muna kitchen nida Diyaam muna haɗa ɗan wake sai ga Khalil ya shigo saye da baƙin jeans da farar riga wai yazo yaga yanda ake haɗa ɗan wake...na kalli Diyaam dake jefa ɗan waken cikin tukunya naga fuskar ta tayi ja ko meyasa? Oho...
'' Are You sure wannan abun haka ake haɗa shi?" Ya tambaya yana tsoma cokali cikin tukunyar kuma yanzu tasa ɗan wake
'' laha ila! Ka ɓata ɗan waken..'' ya zaro ido sai kuma ya kalli Diyaam data kasa haɗa ido dashi ya riƙe kunnuwan shi '' oh sorry Sofia..'' gyaɗa kanta kawai tayi
Ya dinga rounding ɗin mu yana tambayar meye wannan da wancan...daga ƙarshe an gama ɗan wake ..harda clapping hannunshi '' yauwa! Wannan shine abinda aka bani a gida abokina... can i have some now?" Yanda yake yi kamar ƙaramin yaron da aka ba candy
Plate ta ɗauko ta zuba mashi...tasa yaji dasu cabbage da ƙwai ɗaya ta miƙa mashi..
'' thanks Sofie...'' ya faɗa tare da karɓa... saman dining ɗin dake kitchen ɗin ya zauna yana murza hannu kafin ya ɗauki cokali zai fara ci... Diyaam tana wanke wanke ina daga gefe ina lasar yaji mukaji Khalil na kokuwa da ɗan wake a kwano..ta kalleni na kalleta
Can muka ga ɗan wanke yayi sama kafin ya sake komawa cikin kwanon..mai yayi baltsi cikin idonshi...da ƙarfi yaja kujerar baya ya miƙe yana murza ido
'' Ahh...!!!" Da sauri nida Diyaam muka isa wurin...kujera ta hau ta kama fuskar shi a hannunta tana hura mashi idon tunda ita bata sha yaji ba
Ni kuma na isa fridge na ɗauko ruwan sanyi na kwarara mashi a babban yatsan ƙafarshi dake saye cikin slippers...na sake kawo gishiri
'' buɗe bakin ka...'' buɗewa yayi na zuba mashi a ciki Diyaam ta cigaba da hura mashi ido,muka rufa kanshi kamar wasu likitoci...
ajiyar zuciya ya sauke bayan yaji ya ragu Diyaam taja baya saman kujerar...ya ƙifƙifta ido kafin ya buɗe... fuskarshi tayi haja hakama idon...
'' waih,mun ci sa'a da yau mun rasa aikin mu...'' na riƙe baki '' ashe baka iya cin ɗan wake ba..kake sama abun ƙarfi kamar Kana dambe!"
yayi murmushi bai ce komai ba...Diyaam ta sauka daga sama kujerar tsayuwar ta kusa da khalil ya ƙara guntar da ita...sosai...
Wanke wanke na cigaba dayi ita kuma tana nuna mashi yanda ake cin ɗan wanke shikam sai caccakar abun yake da cokali hakan yasa yaji ya shigar mashi ido
Kaɗan na ɗiba nasa cikin plate na kaiwa Roman amma gayen nan a Fuskata yace baici kuma fa naga yanda yake kallo da alamu yana so yaci amma ya hana kanshi...hmp!
Bayan wannan ma na kai mashi abubuwa da yawa kullum amsar itace '' bana so!" Kuma babu wani bayani daga wannan...
Wani sati ranar laraba na shiga toilet ɗin Khalil xan wanke da wayata riƙe da hannu ina karanta text ɗin Jay d akan abinda ya kamata inyi gaba tsakanina da Roman
Na kawo wurin bathtub naji an buɗe ƙofar a firgice na juyo hakan yasa wayar faɗawa cikin ruwa ..na saki baki
'' don't jump out of your skin,we don't have an extra!" Khalil ya faɗa da murmushi,duƙawa nayi ina kallon wayar data gama jiƙewa da ruwa sai bubbugawa nake amma taƙi kawo wa
'' meya faru?" Ya shigo bayan..nuna mashi wayar nayi..yace '' no worries,bari mu saya maki sabo!"
Zaro ido nayi..fitar dani daga bayen yayi
'' jeki shirya...''
Da gudu na koma sashen mu na sauya kaya zuwa doguwar rigar atamfa na fesa turare nasa hijabi fari daya tsaya min a guiwa na shafa kwalli da man baki.. Hansa'u zaune akan kujera tana kallona a fakaice '' ina zaki haka Abeedahtu?" Mama Asabe ta kasa haƙura sai da ta tambaya
'' Khalil yace inzo mu tafi wani waje..'' na bata amsa..tsuki Hansa'u taja nikam ko a slippers ɗina
Hangoshi nayi a parking lot jingine da baƙar mota..saye da baƙar t shirt da baƙin jeans ina matsowa ƙamshin shina daɗa shiga hancina ... Sai naga ya ƙara kyau musamman daya juyo ya sakar min Murmushi...nima na mayar mashi
'' You look stunning!" Ya faɗa min....dariya nayi dajin shi...'' kai dai..bani ba...kada fa yan mata su tare mana hanyar shiga...'' na faɗa tare da zagayawa na zauna a gefenshi
yasa seat belt yana murmushi yace '' ko insa face mask ne?"
'' dana ji daɗi...''
'' ban san kina kishina har haka ba...''
dafe kumatuna nayi ina blushing..wannan Khalil ɗin...hararar shi nayi ya kashe min ido kafin ya ja motar muka fita daga gidan
Wani ƙaton mall ya kawo mu yayi parking muka shiga daga ciki...sanyin wurin na dukan fuskokin mu... elevator muka shiga zuwa top floor..na ɗauka nan ake sayarda wayar naga mun zo sashen kaya... na kalle shi amma ya nuna min yace '' ki ɗauki kome kike so..as much as you want!"
'' duka mall ɗin nake so!" Na naɗe hannu na a ƙirji '' oh..okay... Mutafi reception..'' yayi gaba ina biye dashi dan na ɗauka wasa yake sai da naga da gaske fa abinda yake shirin yi kenan
'' wasa fa nake!" Na zaro ido tare da riƙe hannunshi da yake shirin miƙawa receptionist kati yana faɗin ta kira mai wurin...kam bala'i
Ƙifta idonshi yayi '' wasa? Ni da gaske nake...'' ya bani amsa... receptionist ɗin take bina da mugun kallo
Haƙuri na bata na jaye Khalil daga wurin hannuna maƙale da nashi...i was shocked muka sake shiga elevator..na juyo ina ta mashi faɗa shikam sai murmushi yake...can yaja kumatuna '' kina ƙara kyau idan kinyi fushi...''
Wannan sentence ɗin ya rufe min baki. na ɗaura hannayena saman kumatuna kada yaga sunyi ja
Muna fitowa muka haɗu da wasu mata turawa...suna ganin Khalil suka yo kanmu suna murmushi '' Hi Abraham!!" Doguwar ciki ta faɗa tare da matsowa zata rungume shi... tsalle nayi na shiga tsakanin su ta rungume ni...ɗayar ta rufe baki Khalil ya zaro ido...nima naba kaina mamaki....