Free chapter · Read without an account
Chapter 13
by Salis M Reza · MIJIN AMAL
Chapter 13
Hafiz ya ce "Ki bani wayar nace ko?" Ya faɗa da tsawar da ya tsorata ta. Har ta ɗaga zata bashi sai ta tuno da cewar tana bashi fa shikenan babu ita ba cigaba da karatun ta, har sai lokacin da ya bata. Sai kawai ta fashe da kuka mai amon gaske ta faɗa jikinsa ta na faɗin "Dan Allah kayi hakuri, wallahi tana ɗebe min kewa idan baka nan, kuma daga yau ba zata sake yarda ta ɗauke min tunani ba in sha Allah. I'm sorry my husband abun alfahari na. Muje nai maka wanka ko zaka huce". Ta ƙarasa tana jawo shi hanyar toilet, kuma tana ta ɓoye fuskarta. Hafiz yayi saroro yana kallon ikon Allah, ya sake kallon fuskarta yaga ba hawaye, sai abun ya so bashi dariya, tabbas Hafiza ta fara sauyawa daga yadda ya santa. Dole ya kawar da maganar amsar wayar ya bita da kallo. Suna shiga ta haɗa musu ruwan wankan. Dama itama batayi ba, haka suka sha wanka tare, a nan ma ta sake shayar da shi zubar mamakin da bai taɓa shan irinta ba. Nan tayi iya ƙokarinta ta kawar da wannan maganar, duk da itama a kwai maganganu a bakinta. Bayan sun fito ya ce "Mai kika dafa mana ne yau?" Ya faɗa yana kokarin fita daga ɗakin zuwa Palo saboda ya riga ta gama shiryawa. Gabanta ya faɗi. A ranta ta ce "Oni Ni Hafiza na shiga tara, daga wannan sai wannan". Ta ce "Yau fa indomi zamu ci". "Saboda baki yi kirki ba ko?" "A'a kawai ita nake marmari ne". "To kawo mana muci". Ya sake faɗa yana fita daga ɗakin. Ta baro abun da take yi ta biyo shi harda gudun ta. Yana zama ta shige kichin ta ɗora ruwan. Faka-faka ta hau girki. Tana yi tana tauna maganar da zata masa. Sannan tana tunanin kenan suma masu karatun novels haka suke sangarcewa basa yin aikik gida ko dai ita ɗaya ce. Gashi dai tana ƙaruwa a cikin labarin, amma kuma lamarin gidan ta na son kufcewa, dole ne ta natsu ta bawa karatun iya lokacinsa, duk daɗin da zai mata lokacin na cika kawai zata ajiye shi in sha Allah. Kuma ba zata sake yi ba sai wani lokacin yayi. Tabbas haka za'ayi. Bayan ta gama ta juye a fleet biyu. Ta haɗo da ruwa ta nufo palo. Tana zuwa taga baya nan. Ta ajiye abincin tana kiran sunansa. Ta shiga ɗaki baya nan. Ta duba har toilet baya nan. Sai ta nufi waje da sauri. Tana buɗe wa sai gashi yana mayar da waya aljihu yana ƙokarin shigowa. Suka haɗa ido. Ya ce "Kin gama ne?" Ta bashi hanya ya wuce ba tare da amsa ba. Kishi ne ya mamaye mata ƙirji, ta bishi da kallo kamar ba shi ba. Kenan da gaske Hadiza take. Ya ce "Lafiya kuwa kika tsaya a nan kamar mai gadi?". Ta ce "Ai gara na fara koyan gadin tun yanzu kafin na zama". Ta faɗa tana ƙarasowa ta zauna ranta a ɓace. Ya kalleta yana son fahimtar maganar tata.
"Mai kike nufi?"
"Mai nace?" Sai ya kawar da maganar
Ya ce "Na samu aiki, zan fara zuwa gobe in sha Allah". Ya faɗa daidai yana kai lauma bakinsa.
Wallahi duk yadda take addu'a da neman aikin nan sai taji Kamar bata so, kawai sai ma ranta ya ɓaci. Ta ce "Ka amshi auren kenan?" Ta faɗa itama tana kai abincin da ya fita daga ranta baki. "Wai wani aure ne ne naga tun ɗazu kina ta min habaici, lafiyar ki kuwa?" Ya faɗa a fusace har yana buga chokali a cikin abincin. Sai ta sunkuyar da kai ƙasa kawai, tana addu'ar Allah ya hana ta magana a daidai wannan lokacin saboda ba zata musu dad'i ba, wato ita zai rainawa wayo. Ya ce "Wai mai yasa ku mata daga namiji yayi niyyar aure shikenan sai ku ɗauki hakan a matsayin wulaƙanci ko kuma cin amana, bayan Allah bai haramta ba". Ta ɗago da sauri jin dai magana ta tabbata. Kawai innalillahi wa innalillahi rajiun take ambata yadda taji ƙirjinta ya mata nauyi. Tana ta maimaita kalmar har taji ta fara dawowa daidai. Kafin hawaye suka fara zubo mata na tabbatar da ta rasa mijinta.
ta ce "Aure zaka ƙara?" Sautin Muryar Tata kamar macen da take kokarin koyar magana kuma bata da kalmar R.
"Hafiz yaji jikinsa yayi wani irin sanyi ya mutu gaba daya jin da irin yadda tayi magana, yayi zaton zata hayayyaƙo masa ne, wani irin tausayinta da kuma jin kamar bai kyauta mata ba. Ya ce "Am Hafiza ki saurare ni, wannan abun nufin Allah ne, wallahi ban taɓa kawo haka a rayuwata ba, ita ɗin mutuniyar kirki ce, sannan bata da wata damuwa. Dama ina so na faɗa miki ne idan abun yayi nisa, amma dan Allah ki fahimce ne ba ina nufin komai a tare da ke ba". Ta ce "Na fahimta Hafiz. Allah ya bada zaman lafiya". Tana faɗa ta bar gurin da gudu ta shiga ɗaki. Sai kuka mai sautin da ta kasa sarrafa shi, tana tunano maganganun mutane da suke faɗa mata cewar ta rage irin wannan son da takewa mijinta, su maza ba'a musu haka. Amma ita tace nata Mijin ya sha banban da na kowa. Ta daɗe tana kuka kafin ya shigo ya fara bata baki. Sai taji duk magana ɗaya haushin sa take ƙara ji, idan ba hali irin na namiji ba, mai ta rage shi da shi a duniya. Haka dai ta kwana tana tunani shi kuwa ya sha barcin sa. Da safe kuwa ya shirya tsaf. Bai ko tsaya batun abinci ba, ganin bata ɗora ba. Yana sauri da zumuɗi fara aiki yau yayi mata sallama ya fita. Yana fita kuwa ta lalubo waya ta kira Hadiza. Tana ɗagwa ta ce "Dan Allah kina ina kizo gida na zamu yi magana". Ta faɗa cikin muryar da ake neman agaji". "Bayan kin koreni, harda cin mutumci akan na faɗa miki gaskiya, yanzu hala kin tabbatar ne ko?" "Kiyi hakuri dan Allah kizo, wallahi maganar ki ta tabbata ne". "To yanzu dai ina hanyar Adamawa sai gobe zan dawo, idan na dawo zan kira ki". "Adamawa kuma, mai kika je yi haka?" "Munje kai amarya mana, kin manta ƙawatq tayi aure ne?" Ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin "Ke dai da tarkcen ƙawaye kawai. To dan Allah kina dawowa kizo". Haka suka sauke wayar tana sakin tsaki. Zama tayi a palon tana ƙoƙarin yin tunani. Amma hankalinta ya karkata kan karatun ta. Sai ta kunna wayar ta shiga decommt ɗin. Har zata fara sai ta tashi ta duba ƙofar gidan ta ganshi a buɗe. Ta zauna a palon. Bata ko karya ba bare wanka da gyaran gidan, saboda a ranta tana jin zata iya samo mafita a cikin labarin.
Ta ce "Ina jinka, kenan da gaske ne baka son aihuwar?" Yasir ya ce "Eh da gaske ne, saboda na san da mun aihu zaki ɗauki duk wani irin son da kike min ki ɗora a kan yaron ko yarinyar. Zai zama bazaki bani kulawa ba sosai, komai zai koma kan yarinyar. Ni kuma hakan nake tsoro shi yasa da naji batun kina da ciki sai na shiga damuwa". Amal ta kwashe da dariya mai mutukar tsayi tana riƙe ciki. Shi kuma ya tsaya yana kallonta har ta ɗan sassauta tana nuna shi tana cigaba da yi. Ta ce "Wai abun da mata ne suke faɗin hakan, amma yau kaine kake faɗa. Ai bari kaji, su maza ne suke ɗauke soyayyar matan su bawa yara, sai kaji suna cewa abun cikin ƙwai yafi ƙwan daɗi". Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Bafa wasa nake ba, wallahi da gaske nake Amal, bana son komai ya shiga tsakanin mu ne, ki min alkawarin ba zaki fifita yaron ko yarinyar ba?" Ta sake fashewa da dariya. Sai ya haɗe rai. Ta ce "I'm sorry, wallahi abun naka ne fa akwai abun dariya, kana da rigima mara dalili". Au rigima ce ma nake yi kuma mara dalili ko?" "Eh mana! Ina ba haka ba, ta yaya zan so wani abu a duniya da zai wuce kai, kai ɗin fa, aljanna ce Ubangiji ya mallaka min irin ta gidan duniya". Ya ce "Ham! Har kin sa na ɗan samu salama. Amma kawo hannunki". Ta kawo ƙaramin ɗan yatsa kamar yadda tayi. Suka kulla alƙawari. Tayi dariya ta ce "To yanzu dai za'a iya aihuwar yau ko gobe ko?" Ta faɗa tana kanne masa ido ɗaya. Sai ya kalleta ya ce "Allah ya kawo mai hankali kamar ki, da kyawu kamrki, da natsuwa da haƙuri kamar ki". Ta ce "Amin wacce ta fini hakan ma. Kuma mai sona kamar ka, mai tausayinmu kamrka, mai natsuwa da kame wa mai tsoron Allah kar ka. Mai son addini kamar ka". Yayi murmushi yana tashi ya ce "Kafin muyi barci yau muna da aiki fa. Zan yi transfer na komai dake cikin wannan laptop ɗin zuwa wannan. Sannan ga batun kayan mu da zamu ƙarasa na cikar shekara biyu". Ta ce "Bari kuma mu buɗe wannan wayar muga meye a cikinta". Nan ta shiga buɗewa. Taga babbar tata ce ga komi na sabuwar waya. Ta kalleshe ta ce "To ai babbar ta hannunka ce". Ya ce "Eh, ribar taimakon miji kenan, sai Allah ya saka miki da wacce ta fita". Ta ce "Na gode Ubangiji ya kara wadata da arziki. Amma da zaka amshi wannan ɗin ka dawo min da tawa da zanfi jin dad'i". Ya ce "Kin riga kin bayar da wannan. yanzu dai kije ki saka a chaji. Bari na fara duba wannan ɗin".
Daga haka ta ɗauka tasa a chaji tana ta murna. Ta tashi ta shiga kichin tana haɗo kan kayan abun nasu. Shi kuma yana ta kokarin kwashe komai na wannan laptop ɗin da yake ya kai an gyara ta, kawai dai ba zata cigaba da aiki kamar da bane, tana yi tana tsayawa, ga kuma gefe ɗaya ya yi baƙi. So yake ma ya fita da ita gobe ya sayar. Sai da ya gama tass, harda hotunansu tun na aure da na bayan aure. Sannan ya goge komai na ciki. Ya nufo kichin ɗin. Dama tun yana aikin yake jin yadda ta kunna wakar Umar tana ji. Yana shiga ya bi bakinta suna bin wakar mai suna ke nafi ƙauna cikin matan duniya. Haka suka cigaba da yin wakar yana taya ta haɗawa har suka gama. Suka jere a ƙasan palo. Ya zauna ya ɗauki ɗaya ya sa a baki yana juya kai kamar kadangare. Ta ce "Yaya daga ɗari zuwa sama maki nawa na samu?". Ya ce "Ba'a ganewa daga lauma ɗaya. Let me nayi kamar biyar haka". Ya sake kaiwa ɗaya baki. Ya sake haɗawa da wani. Tana tsaye tana kallonsa. Sai ya ce "Na baki 99%". "To mai ya cinye ɗayan?" Ta faɗa a shagwaɓe. Ya ce "Wai kar ace nayi sankai ne ai". Tayi dariya tana faɗin "So so ne, amma na kai yafi". Duk yadda taso da tai masa batu akan fara sana'a sai ta hakura sai zuwa gaba, saboda ganin yadda farin ciki ya dawo gidan nasu. Haka washegari ya tattara laptop ɗin nan ya fita da ita ya sayar. Taci gaba da aiki da samuwar wayar shi kuma tsohuwar suka ajiye wacce ta fashe ɗin. Ya dinga tafiya shago a ƙafa, yace ya haqura da neman aiki. Suna dogara da abun da yake samu a shago. A bangaren Mama kuwa lokacin da ta kai mata wannan kuɗin a karon farko da tai mata godiya tana faɗin To a ce duk bayan sati tana kawo mata irin wannan da wa zaiji kansu. Ta ce mata ai Yasir ne ya bata ta kawo. Ta ce to tai masa sannu.
Tsawon Wata ɗaya kenan abubuwan sun tafi daidai wasu kuma sun chakuɗe. Yanzu kayan abincin da ya sayo sun ƙare. Ga shi yanzu basa samun wuta sosai, abubuwan duk basa tafiya. Kuma ga yanzu son yin kallonsa ya ƙaru dan ma suna da Pawabang. Tai masa maganar sana'a ya ce bai yarda ba, ta bari yana da wani tanadi akanta. Hakan yasa ta kawar da maganar. Yanzu dai dole ya sake kaɗe takardun sa zai fara cigaba da neman aikin. Bangaren Ali kuwa dole suka sake jonewa saboda bai da aboki kamar sa. Sai kuma Nana da tun da aka ɗaura auran har zuwa yanzu ba'a tare ba, kuma ba'ayi tafiyar ba. Sai dai yazo ya ɗauke ta su fita yawo, wani lokaci ma har kwana suke yi. Ranar ma har gidan ta suka zo. Ita dama tun kafin ta ga mijin sam bai mata ba. A lokacin tai masa batun tarewa, sai tayi wuff ta ce ai sai sun dawo daga tafiya. Amal ta ce "Mai zai hana ku tare tun yanzu kafin ku tafi?" Ya ce "Ai gidan ne ake karasawa". Haka dai ita Nanar ce ma mai kare shi. Shi yasa ta yi shiru. Ya ajiye mata 10k suka fita. Tun daga nan bata sake ganinsu ba, sai dai labari da yake iso mata cewar an ga Nana a hotel kaza an ganta a kaza. Hakan yasa ta wanke ƙafa ta je gurin Mama domin ayi wanda za'ayi, saboda sam hakan bai dace ba, ko haya ne ya kamata a ce ya kama. Sai dai daga karshe ranta ne ya ɓaci, wai mutum da matarsa ma sai an masa shisshigi. Haka ta dawo gida da baƙaƙen maganganu. Dan har gorin dubu goman nan da ya bata sai da akayi, tana mamakin ma aina Mama ta san sunje gidantta har ya bata dubu goma. Kaman tai wa Yasir batun ya taimaka wa Nana saboda bata yarda da mutumin ba, amma dai tana tsoron maganar ta kai kunnen Mama a ɓallo wani ruwan. Haka dole ta hakura da faɗa masa. Yanzu basa da komai a ƙasa, kullum sai ya dawo daga kasuwa yake zuwa da abun da zasu ci gobe. Ranar da ba ciniki ma bredi zai sayo su sha ruwan bunu.
Yau ma abun da suka sha kenan yana ta sauri domin tun shekarn jiya suka tura da takardun su, kuma yau aka naimi da suzo ayi gwaji. Wani abokin karatunsa ne ya turo masa da address ɗin wani babban kamfani suna ɗaukar ma'aikata. Farko kamar ba zai jarraba ba, amma dai da yayi mata hirar tace kawai ya tura bai san ina ne rabon nasa yake ba. Shine fa ya tura ba tare da da rai ba. Sai gashi an kira harda dhi. Shine yake so yaje ya gwada sa'ar sa. Tun jiya shi da ita suka ta addu'ar samun aikin nan. Ko a sallar asuba gaba dayansu akan addu'a ɗaya suka barta. Haka yanzu ma da zai fita. Dama tun jiya yake ce mata bashi da ko kuɗin mashin ɗin zuwa gurin. Ta ɗauko dubu uku a cikin dubu goman nan ta bashi. Tun ma Kafin ya tambaya ta faɗa masa ta inda suka shigo. Yayi godiya ya ce "Kisa a ranki bashi kika bani. Ta rike masa hannu kaman wani yaro, tana faɗin "Bashin masoya ko". Da yake itama tana da tsayi. Ta kama kansa. Ya sunkuya ta fara addu'ar nan tata a fili. "Ya Allah yasa wannan itace ranar nasarar da muke ta jira. Allah yasa karshen neman wannan aikin ne yazo. Allah ya kawar da duk abun da zai hana ka samun wannan aikin. Kuma yasa alkairi ne, ya nisanta da sherri komai yawansa". Ya amsa da amin yana haɗe jikinsu waje ɗaya wani irin sanyi na shigar sa na natsuwa. Yayi mata kisa a goshi da kumatu da baki. Ta fito da wani turare da bai san da shi ba. Da yake ƙananan kaya ne a jikinsa. Ta feshe masa su a jiki daga ita har shi ta ce "Fatan nasara jarumin mijina ni ɗaya". Daga haka ya fita yana jin wani irin ƙwarin guiwa da farin ciki na shigarsa. A cen gurin suka haɗu da gayan nasa wanda har ya riga shi zuwa. Bayan ya hau layi ya zauna yana ta tunanin matarsa. Sai yaji wayarsa na ƙara. Yana dubawa yaga number Ali. Ya ɗaga da sallama, yana ma so ya faɗa masa cewar yana gurin neman aiki ne. Jin baya ji ne yasa ya tashi da nufin fita waje. Daidai lokacin sai ga mai kamfanin an buɗe masa ya shigo. Nan gaban Yasir ya faɗi yana cire wayar daga kunnesa tsabar tsoro da firgici. Shima mutumin ya tsaya yana kallonsa rike da takarda a hannu. Nan ake ta kallon-kallon kusan na minti guda Kafin Yasir ya iya ƙarfin halin gaida shi yana jin shikenan baida Sa'a...📝
To fa! Da wa Yasir ya haɗu ne anan gurin? Ko yaya ne, ko mijin Suhailait na da.