Free chapter · Read without an account
Chapter 1
╔══════════════════════╗
🌺🌺 *KOWA DA RABONSA* 🌺🌺
╚══════════════════════╝
🌺 A Story Filled With Lessons, Destiny and Love🌺
✍️
> BY MARYAM USMAN MAMYY WRITER (FULANIN JAJIRTATTU)
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🏆 JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
✨ FIVE STAR WRITERS✨
📞 ***
📚 BOOK 1
📖 Page 1
━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
Bismillahir Rahmanir Rahim.
~Wane lokacin kaddara ce take zaɓa maka rabonka, wani kuma rabon nasa ne kaddara. Duk abin da ya zama rabonka dole ne ka yi haƙuri da shi.~
> NOTE: Ban yarda da wani ko wata su yi amfani da littafina ba. Ban yi littafin nan da wata ko wani ba. Duk abin da kuka gani mallakina ne, bana so wani ya yi min copy ba tare da sanina ba.
━━━━━༺🌺༻━━━━━
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un!"
Shi ne sautin da ya fito daga bakinta tare da zabura. Tana kallon fuskarsa da yake murmushi cikin farinciki marar misali.
Rawa jikinta ya fara, hawaye na zuba daga kyakkyawar fuskarta. Tana kokarin fahimtar abin da Abbansu Nadiya yake fada.
Cikin kamala da kame fuska yake sake jaddada mata auren da aka daura mata jiya da MAMUB. Wanda yake tamkar uba a gare ta, ko ta kira shi da uba ma gabadaya.
Cikin tashin hankali da firgici take kallonsa. Abin da yake fada a bakinsa tana ganin masifa ce babba a rayuwarta. Domin ta san ta gama rayuwa daga yau din nan.
Tsayawa zuciyarta ta yi da aiki. A lokaci daya tana ganin sama da kasa na juyawa, idanunta na rufe wa, numfashinta na kokarin tsayawa.
A lokaci guda hankalinta ya fita daga jikinta. Tunanin makomarta ne ya saka ta fashewa da kuka. Hakika tana cikin wani hali da bata san waye zai fitar da ita ciki ba.
Amma duk halin da take ciki, Abbansu Nadiya farinciki ne kwance a kan fuskarsa. Har wani tattausan murmushi yake yi yana sake kallonta.
Suna cikin wannan yanayin ne suka ji ihun Mummy ta na cewa,
"Inna Lillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! Na shiga uku! Me kake fada min haka M. Madawaki? Me ya sa za ka yanke wannan danyen hukuncin?"
Ba ta ƙarasa maganar ba, ta yanke jiki ta faɗi.
Da gudu duk suka fita zuwa inda suke jiyo ihun Mummy. Kwance a kasa suka ganta a sume, M. Madawaki na tsaye a kanta.
Jiri ne ya ɗebeta ko taku ɗaya bata yi ba ita ma ta faɗi a sume, masu aikin gidan ya kira, suka saka masa Mummy a mota. Shi kuma ya dauki Shatu a kafadarsa. Yana fitowa, Security guards ɗinsa suka yi saurin bude mota.
Da mugun gudu suka fita daga Madawaki Dynasty. Mintinan kaɗan ne suka kaisu Madawaki Special Hospital.
Security na Hospital ɗin na ganin motocin M. Madawaki suka bude Gate tare da zagaye motar suna jiran fitowarsa.
A. Maina ne ya fara fitowa yana kiran nurse. Kafin ya rufe baki, nurses ɗin asibitin suka fito da gadon daukar marasa lafiya.
Mummy aka fara shiga da ita, sannan M. Madawaki ya fito da Shatu a jikinsa wacce take sume.
Taimako gaggawa aka fara basu. Wasu daga cikin nurses ɗin suna mamaki abin da ya saka uwa da 'ya suma a lokaci guda.
Cikin kwarewa aka ceto rayukansu tare da kaisu dakin hutu.
M.Madawaki ne ya bukaci a raba musu daki. Umarninsa suka bi na abin da ya bukata.
Dr. Nadraa ce ta yi wa A. Maina bayani, domin ta san shi ɗaya ne yake iya fada wa M. Madawaki magana ba tare da an ji kansu ba, musamman akan zuciyarsa wato Shatu M Madawaki.
━━━━━༺🌺༻━━━━━
Fita M. Madawaki ya yi daga office ɗin. Yana shiga dakin da aka kwantar da Shatu, ya jima a tsaye a kanta, ya zuba mata idanunsa masu kaifi.
A. Maina ne ya shigo tare da zama gefen gadon ya shafa fuskarta.
"Rigimar yau ta da ban ce, ina tausayawa M. Madawaki."
Lumshe idanunsa ya yi tare da juyawa ya fita daga ɗakin, ɓangaren Mummy ya nufa.
Bai jima da shiga ba ta farka tana kuka sosai. Dago manyan idanunwansa ya yi yana kallonta, sannan ya dauke kai yana mike wa zai fita.
Da sauri Mummy ta riƙe hannayensa za ta yi magana. Cire hannunsa ya yi daga nata ya fita ba tare da ya ce wani abu ba.
Dama ta san ba magana zai yi ba, da gudu ta fita tana tambayar ina Shatu take, wata Nurse ce ta nuna mata dakin da aka kwantar da ita.
Da karfi ta bude kofar, babu kowa a ɗakin sai Shatu M. Madawaki da take kwance. Ido a rufe Mummy ta fara dukanta!
Wahala ce ta farfaɗo da Shatu. Ganin Mummy na dukanta ya saka ta fashewa da matsanancin kuka. Dama ta san sai Mummy ta yi alajinta duba da irin yadda Mummy take kishin mijinta.
Cikin fitar haiyaci Mummy ke dukanta tare da cewa sai ta kasheta kowa ya huta.
Nurse ɗin da ta shigo ce ta ga abin da yake faruwa ne ta koma da gudu tana sanar da A. Maina da suke magana da M. Madawaki. Cikin hanzari suka shiga ɗakin.
Cikin karamin sauti ya furta,
"Assagafirullah."
Tare da kamo hannayen Mummy ya fitar da ita daga dakin. Dr. Nadraa ya kira ta sake duba Shatu wacce ta sake sumewa.
Hauka Mummy ta fara yi masa a Hospital ɗin. Yusuf ne ya kawo masa wayoyinsa da ake kira cikin girmamawa.
Da ido ya yi wa A. Maina magana yana so a maida Mummy gida, fahimtar abin yake nufi ne, A. Maina ya kira Baba Jamila da suka zo tare, bayanin komawar Mummy gida ya yi mata tare da haɗa su da Yusuf.
Duk haukan Mummy sai da aka maida ita gida. Shi kuma ya zauna har Shatu ta dawo haiyacinta.
A lokacin A. Maina ya koma gida. Tun farkawarta take kuka marar sauti ganin iya M. Madawaki ne a ɗakin, duk rigimarta tana tsananin tsoronsa. Duk Madawaki Dynasty babu wanda take shakka irinsa.
Sautin kukanta ne ya fara damunsa ya kira Dr. Nadraa ta sallamesu.
Dr. Nadraa wayeyar mace ce, tana jin daɗin aiki da M. Madawaki shi yasa take masa biyayya sosai. Murmushi ta yi tare da rarrashin Shatu da take kuka.
Taimaka mata Dr. Nadraa ta yi tana kama hannunta domin raka ta mota. Kamshin turaren M. Madawaki da ta ji ne, a kusa da ita ta yi saurin ɗago da kanta.
Ganin irin kallon da yake wa Shatu ne ya saka ta matsawa gefe.
Cak ya daga Shatu yana fita da ita kamar yar bebe. Yusuf na ganin fitowarsu ya yi saurin bude mota.
Yusuf ne ya jan motar suka fita daga Hospital ɗin. Tun da ya shiga motar ya fara amsa wayoyi, yana magana cikin karamin sauti. Ko Shatu da take gefensa bata jin abin da yake fada.
━━━━━༺🌺༻━━━━━
A compound ɗin gidan Yusuf ya faka motar. Cikin fargaba da tashin hankali Shatu ta fito jikin a sanyaye.
Baba Isa mai gadi ne ya karaso bakinsa a washe yana cewa,
"Shatu sannu da jiki ai yanzu Inayaa ta fita tana kuka..."
Shiru ya yi dalilin M. Madawaki da ya fito. Ita ma da gudu ta karasa cikin babban falon gidan.
Madawaki Dynasty ne gabadaya a falon zaune da alama magana suke mai mahimmanci. Shigowar Shatu ne duk suka zuba mata ido kowa yana kallonta.
Cikin sanyin jiki ta tsaya daga bakin ƙofa tana mai jin tsoron shiga.
Mummy ce ta fito da wani katon sanda a hannunta za ta rafka mata. Cike da bacin rai Daada ta ce,
"Kina dukan Shatu M. Madawaki a bakin auranki ko M. Madawaki bai sake ki ba sai na sake ki yau ɗin nan..."
Fashewa Shatu ta yi da kuka tare da zubewa a kasan wajen, za ta fara sana'arta ta, wato rigimar banza. Tana ji shigowar Abbanta cikin rawar jiki ta tashi tare da goge fuskarta.
Shiru falon ya yi. Kowa yana kallon fuskar M. Madawaki da ya zauna ba tare da ya yi wa Shatu magana ba.
Baba Malam ne ya kamo hannunta yana goge mata fuskarta cikin sanyin murya kamar yadda ya saba yi mata magana ya ce,
"Shatu M. Madawaki......"
Dariyar Aminu H. Madawaki ce ta saka Baba Malam shiru yana kallon gefenshi da yake cewa,
"Sai yau sunan ya zama cikakke...."
Ganin kallon da Baba Malam ya yi masa ne ya hana shi karasa maganar yana murmushi.
Zaunar da ita Baba Malam ya yi a kusa da shi. Suna zama suka ji cikakkiyar muryasa wacce a kowane lokaci take saka Shatu cikin nutsuwarta ya ce,
"Ko da wasa bana son jin ko ganin irin hakan ta faru."
Sai da ya dan huta sannan ya cigaba da cewa
"What is really bothering you? Are you the first woman to have kishiya? Shin ke kadai aka fara yiwa kishiya a duniya? Listen to me very well, I will not tolerate any nonsense from you. Bazan lamunci wani rashin hankali ba, kin ji ko?"
Farinciki ne ya bayyana a kan fuskar Madawaki Dynasty sosai. Wasu daga cikinsu ma dariya suke yi suna hararar Mummy.
Cikin ɗaga murya Mummy ta ce,
"Wai kana da bakin magana Muhammad Madawaki? Ni zaka cuta yarinyar da rike ita zaka auro min? To wallahi baku isa ba daga kai har shi shegen Uban nata. Ashe ma saboda haka ya baka ita? To wallahi sai dai ka zaba ko ni ko ita dan ba zan zauna da yarinyar cikina ba."
Fashewa Shatu ta sake yi da kuka domin tun da take da Iyayenta, bata taɓa ganin sun yi fada ba sai yau. Kuka take sosai ganin suna irin wannan maganar kuma Baba Malam ya yi shiru ga Daada ma bata saka baki ba.
Tsayawa ta yi da kukan sakamakon wata mummunar kaddara da ta ji tana fita daga bakin Abbanta. Cikin bacin rai ya ce,
"Za ki iya tafiya, but Eshaa is now part of Madawaki Dynasty She is mine, babu rabuwa a tsakaninmu. Try touching her again and you will see the other side of me."
"Ni zaka saka a kanta? Wai wane shegan ne ya baka shawara auranta?"
"Nothing. I just need it to be so."
Yana gama fadar haka ya tashi tare da nufar hanyar bangarensu. Sake fashewa ta yi da kuka tare da rungume Daada.
Cikin bacin rai Mummy ta bi bayan M.Madawaki. Baba Malam yana mata magana, amma ko juyowa bata yi ba.
━━━━━༺🌺༻━━━━━
Tun bayan fitar M. Madawaki daga falon, Daddy Meerah yake ta rarrashin Shatu. Amma saboda rigimar da take da ita, ta ƙi saurarensa. Har bacci ya dauke ta tana cikin kuka.
"Alhamdulillah, yau M. Madawaki ya nuna wa matarsa cewa shi cikakken Madawaki Dynasty ne."
Baba Malam ne ya jinjina kai alamar ya gamsu da abin da ya faru. Abubakar Madawaki ne ya kalli Shamsudeen da sauran yaran da ke zaune a gefen Daada, ya ce su koma dakunansu.
Magana suka yi iya manyan Madawaki Dynasty sai matansu, waɗanda ke mamakin abin da M. Madawaki ya yi wa Hajarah na aure da ya sauke.
> MAMYY WRITER CE ✍️
> Ku biyo NI domin jin cikakken labarin KOWA DA RABONSA 🌺
> Wai meke faruwa a cikin littafin KOWA DA RABONSA ne?