Free chapter 路 Read without an account
Page 6
Kamar kullum, yau ma da misalin karfe 6 na yamma, rana ta lafa, hasken rana mai launin gold ya ratsa cikin gidan, iska mai sanyi na kadawa, tana kada ganyen flowers din da suke compound Gidan ya yi shiru, babu hayaniya, sai karar ruwa a fountain din dake tsakiyar garden, da karar tsuntsaye a saman bishiya. Wannan lokaci ne da mutane da yawa suke Jin dadin shi.
A wannan lokacin ne Abidah da Jazzeelah suka tsaya a tsakiyar compound din gidan, gaba daya hankalin su a tashe yake, zuciyarsu na bugawa kamar ganga. Sun tsaya a bayan wata mota, suna leken gida.
Abidah ta rike hannun Jazzeelah da karfi, yatsun hannunta na rawa. Ta ce da murya kasa-kasa, kusan ra蓷a, "Jazzeelah, kina gani ko me nake gani? Wallahi kamar motar Hamma Muhammad nake gani a gate! Waccan bakar Toyota Camry din nan, tashi ce! Shike nan mun shiga uku! Mun mutu!"
Ta kare maganar tana kallon Jazzeelah, wanda fuskarta kadai ta nuna halin da take ciki. Duk jikinta sai wani irin sanyi-sanyi take ji, kamar alamar zazzabi ne yake son kamata, gumi na keto mata duk da iska mai sanyi. Musamman idan ta kalli kayan jikinta, wanda kwata-kwata Hamma Muhammad ya hanasu saka irin kayan nan, ko a cikin gida suke, balle a waje. Kuma dokan tafi tsanani a kanta, tunda itace duk gidan take ganin yafi tsanan ta mata, saboda shi mutum ne, mai tsananin kiyayiwa da kuma doka a kan kan nan shi. Zata iya cewa tunda take bata taba ganin dariyar shi ba,. Ko zata ga dariyar shi, to sai dai daga nisa, shi ma sai idan yana tare da su Baffa, ko kuma yana waya da abokansa.
Ta sake kallon jikinta, tana sake jin cikinta na murdawa, kamar wani abu na juyawa a cikinta.
Dan gwama Abidah, doguwar riga ta saka, pencil ce, an mata ado da duwatsu masu sheki, sai ta saka a baya transferred a sama, sai tayi amfani da mayafi a bayan sai takalmi ZARA Shoes & Bag sa tayi amfani sadu black
Ita kuwa Jazzeelah, skirt din roba ta saka, coffee brown, tayi amfani da top milk, sai ta daura abaya a sama coffee brown, ta nadan mayafin kayan a kanta. Wato, skirt din kamfanin Fashion Nova - Curve Lover Bodycon Skirt ne, skirt din ya matse, ya bayyana surar ta, top din kuma na Mango - Milk Cropped Top, abaya ta kuma na Zara Abaya Collection - Coffee Brown Open Abaya, sai ta nade mayafi na chiffon mai launin coffee brown a kanta, amma mayafin bai rufe komai ba, ya bari wuyan ta a waje. Takalmi da jaka milk na kamfanin Steve Madden - Madden Girl Heels masu tsini kadan, wadanda suka dace da kayan.
Kayan sun fito da surarta sarai. Yanzu ta lura da yanda shape dinta ya fita sosai a kayan, musamman hips dinta wanda suke tubarkalla. Dan duk da tana da kananan shekaru, yanzu suke da shekara 18, amma Allah ya mata wani irin halitta na manyan mata, halitta wacce mata da yawa ke burin samu. Akwai wadatan hips wanda ake kira da curvy, hips din da suka cika, ga kirjinta yana da cika sosai, amma kwata-kwata bata da waist, waist dinta karami ne, haka kuma cikinta a shafe yake, flat ne, kamar ba ta cin abinci. Sabanin Abidah da ita, Masha Allah, ba laifi tana da jiki, dan baza'a kira ta da ramammiya ba, amma kuma ita ma tana da cikan halitta ta nata, mai cika, amma Jazzeelah ta fi ta sura.
Kallon ta Abidah ta sakeyi, tana fadin, "Jazzee, zo mu shi ga kawai, mu yi addu'a. Dan naga kamar alamar gidan akwai baki, motoci da yawa a waje, sai mu lalaba mu shige Part din Aunty, wato Murshida, dan haka yaran gidan suke kiranta, shi yasa har yaran ta haka suke ce mata Aunty. Kinsan idan muka shiga part din Mommy, to ita da kanta zata mika mu wajanshi. Ni wlh na zance da aka ce zai tafi China, nayi tunanin can zai koma da zama, karki su ki ji dadin dana ji, nayi murna. Ashi an gudu ba'a tsira ba ne, gashi ya dawo." Ta kare maganar tana yatsina fuska, tana wasa da bakinta.
Duk wannan surutun, Jazzeelah bata ce komai ba, zuciyarta na wani waje, kunnenta na jin bugun zuciyarta kawai, sai da Abidah ta kai karshan maganar ta kafin ta ce, "Please, kina ganin motar Hamma Jameel a wajan?" Cewar Jazzeelah,
"Gaskiya ban ga motar shi ba, babu motar Hamma Jameel a waje, ita kadai motar Hamma Muhammad ce a waje," Abidah ta bata amsa., ganin tsayuwan bazai musu ba, kuma duhu na fara yi, yasa kawai suka kama hanyar part din Aunty, suna takawa a hankali, suna jan kafa, suna addu'a a ransu kada a gansu.
Duk wannan abin da sukeyi, MD (Muhammad) na zaune cikin kujerun da suke cikin garden din dake gidan. Garden din yana da kujeru na roba masu kyau, da table a tsakiya, da hasken wuta mai launin yellow. Kallo daya zaka mishi, ka san ranshi a bace yake, fuskar shi a hade, goshin shi a hade. motsi kadan yake, shafa kanshi tare da wani irin huci mai karfi, numfashin sa na fita da karfi, ga idanun shi da suka canza kala, sunyi ja,. Hannu shi rike da goran ruwa, wanda Jameel ya miko mishi. Dan tunda yaga yayi irin wannan fitowar daga falon, da sauri ya bar falo, ya fito garden, ya san ran yan maza ya baci, shine ya dauko ruwan ya biyo shi da shi. Yana zuwa ya mika mishi, aiko ya kafa kai ya shanye shi tass, gaba daya, ya rike roban a hannun shi da karfi har roban ya dan murkushe, yana sauraran yanda zuciyarshi take wani irin bugawa, wanda ya rasa gane dalilin hakan, bugun da bai saba ji ba.
Jameel na tsaye a gefe, yana kallon shi, yana mamakin abin da ya faru, Muhammad ga matar da zaka aura yarinyar a miniyatace Bahayurah dan haka ina so ku samu lokaci ku tattauna dan mu ajiye maganar biki, Jameel dake tsayi yake tuna maganganun Miemie a falo tana fada ma Muhammad, wanda bayan gama zaman ne Muhammad ya fito yazo ya zauna a garden, to bama Lion da yake murdadin ba ko shi baya tunanin Aunty zata mishi irin wannan Karan tsayan a zauna lafiya, Amma dole zaiyi zama dashi yayi hakuri yayi biyaya saboda Miemie kaifi daya ce,
Ganin Abidah da Jazzeelah zasu shige part din Aunty, Jameel yana mamakin ina yaran nan suka fito da yamma cin nan. Ba ma wannan ne abin dubawan ba, irin shigarda take jikin su kuma abin da ya sake bashi mamaki. Har da Jazzeelah, da Abidah ce ya gani ya San za'arina, yaran da ya haramtawa fita da irin wannan kayan, kasa hakuri yayi kafin ya bude baki,
"JAZZEELAH!"
Wani irin murdawa taji cikinta yayi, kamar hanjinta ya yanke, nan take taji jikin ta ya fara rawa, kafafun ta suka yi sanyi, kamar zata fadi a wajan. A fili take fadin, "Shikenan mun mutu! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
To ba ma ita ba, hatta Abidah ji tayi jikinta na rawa, juwa tayi dan kanin waya kira su a kan Jameel, idanuwan ta suka sauka, ta kalli kasa. Hakan yasa ta danji sanyi-sanyi a ranta, ta san zasu sha fada sosai, Amma zanyi hakuri.
Juyawa tayi ta nufi garden din, Abidah na biye da ita, wanda tun farkon kiran da aka musu, idanuwan ta suka sauka a kan dukansu su biyun. Hakan yasa taji daker take iya daga kafafun ta, kamar kafafunta sunyi nauyi,ta ja da kyar sunyi nauyi.
Jazzeelah kuwa, sai da suke gab da shiga wajan, ta lura da ubanganyan da yayi zaman sarakuna, kafa daya kan daya, hannu daya a kan kujera, daya rike da gorar ruwa, da alamama baci yakeyi, fuska a hade,. Ji tayi gaba daya ta kasa motsi, ta tsaya a wajan, sai da Abidah ta tura ta suka karasa kusa. Cirko-cirko
Harara ya sakar musu, harara mai zafi, kafin ya ce, " tsayuwan na mecece"
Ai tun kafin ya karasa magana, suka zube akan kafafuwan su, suka durkusa sosai, tsananin tashin hankali yasa sun manta aya suke, sun manta komai,.
"Daga ina kuke?" Jameel ya fadi, yana kare musu kallo, yana kokarin rage fushin, amma shi ma fuskar sa a hade take, saboda ya san abin da suka yi ba daidai ba ne.
Shiru kake ji, babu amsa, sai kukan Abidah kadai, da na Jazzeelah mai karfi.
Cikin tsawa, murya mai karfi, Muhammad ya ce, "NACE DAGA INA KUKE?"
Abidah ta firgita, cikin rawar murya tace, "Hamma, daga wajan walima kawar mu muke, walimar kawar mu Farida."
"Okay! Daman da kayan da ake zuwa wajan party ake zuwa walima? Da irin wannan kayan? Shiru kake ji, ba magana. Ba magana nake muku ba?" Ya fadi yana zabura kamar zai tashi daga kujerar, hannu ya kai kamar zai dake su. Wani irin kuka ne Jazzeelah taji ya kwace mata, kuka mai karfi, cikin kuka tace, "Hamma Dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zamu sake ba, kayi hakuri,."
"Ba hakuri na tambaye ku ba, daga ina kuke?yana kallon su kamar zai cinye su.
"Dan Allah kayi hakuri, daga gidan su Farida muke, yau tana birthday, shine ta gayyace mu, kuma wallahi mun tambayi Daddy," ko Abidah ta kare maganan tana kallon Abidah, ita ma cikin sauri ta daga mata kai, tana goyon bayanta.
"Okay, birthday kawa kuka je, shine kuka fita da irin wannan shigar? Kuma da alama ba driver bane ya kai ku? Driver ina yake? Waye ya baku izinin fita" Ya kare maganar yana dafe kan shi, kamar kan shi na ciwo, kafin ya ce, waye ya Kai ku? "
Cikin sauri Abidah tace, "Wallahi Hamma, Napep muka hau, lokacin driver baya nan, mun nemi driver bamu ganshi ba, sai muka hau Napep."
Kallon su Jameel yayi, kallo mai zafi, kafin ya girgiza kai, ya ce, "Wato duk fadan da ake muku bakwaji ko? Duk yanda aka kai da saka muku idanuwa a banza ko? Da yake fitina a cikin jinin ku yake ko? Musamman ma ke Abidah, ke ce babba, amma kece kike jawo ta. To wallahi wannan ya zama na farko kuma na karshe, idan kuka sake fita haka, ni kadai nasan mezan muku. Ku tashi ku bani waje kafin na kakkarya ku,!"
Ai cikin sauri suka yunkura zasu tashi, kafafun su na rawa, suna kokarin tashi, kafin su kaji wannan muryan nashi mai karfi da kaifi,, mai ladabtar da fitsarare har cikin kawunan su, haka sukaji saukarta, kamar wuka a kunnensu.
"Idan kun tashi daga nan, JUMPS TO THE WATER TANK! 20 frong yana mai nuna tankin ruwa mai nisa, nisan da ya kai kamar mita 50
Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a fuskokin su, musamman ma da suka sake kallon nisan guri da kuma adadin da ya fadi zasuyi. Idanuwa suka juya suka zuba kan Hamma Jameel, suna rokon shi da ido ya ce musu wani abu, ya taimaka musu, wanda shi ma ya dauke idanuwan shi akan su, ya kalli gefe, saboda ya san Hamma Muhammad idan ya fada, ba ya can zawa.
Ganin babu mafita, yasa suka fara tsallen, suna kuka, gwiwoyinsu na ciwo, amma babu wanda ya isa ya ce musu su tashi, saboda MD ne ya bada umarni. Shi kuma yana gama fadin haka, ya mike Saboda kiraye kirayen sallah da aka fara a masallatai, yawurgar da gorar ruwan a kasa, yana tafiyan nan nashi cikin kasaita, kafada a bude. kallo daya zaka mishi, ka san akwai namiji a wajan, namiji mai kwarjini da cika ido. Ganin haka yasa shi ma Jameel ya bishi a baya, saboda akwai maganar da zasuyi a ciki, idan sun fito sallah
Masu bukatar a musu tallah zaku iya tuntubana ta wannan number 馃憠*** MRS CLASSY WRITE nagode馃檹
鉁嶏笍 Mrs Classy | Author of RABO DA
KADDARA 馃挃
Hausa Romance & Kaddara | Read on ArewaPen 馃憞