Free chapter · Read without an account
Page 17
by Ummu~Fadeela · JUYIN LAMARI
By
Ummu Fadeela
Page 17.
Arewapen: ummufadeela01
A hankali nake takawa. Duk takun da nayi sai zuciyata ta buga da karfi har jikina yana rawa. Lokacin da na iso ƙofar shiga bangaren, tsayuwa nayi na wasu mintuna ina shakar numfashi da mayarwa. Wani abu nake jin yana fitowa daga cikin cikina yana tokare kirji har zuwa makwogorona. Nayi karfin halin sanya hannu na bude kofar ba tare dana danna doorbell ba. Cikin sa'a ƙofar ta bude. Na cigaba da kutsawa cikin hadadden falon da bayyana girma da haduwarsa ma bata lokacine. Na taki sa'a kuwa, domin babu kowa a falon kasan.
Gidan ba bakona bane, duk da wariyar da ake nuna mana, amma babu bangaren da ba na shiga in kutsa inda naso a fadin gidanmu. Nayi nasarar haura stairs ba tare da na hadu da kowa ba. Kasancewar yau litinin Mom din Yaya Abdul da Anty Amarya dukkansu ma'aikata me, Mamy ce kawai yar kasuwa shiyasa gidan ya kasance shiru.
Handle na ƙofar bedroom dinsa na kama ina kokwanton in shiga kawai, ko inyi knocking. Ban gama tantance abunda zan yi ba, na jiyo muryar Momy tana haurowa sama. Wani irin zillo kirjina yayi, da wani irin sauri na afka dakin na turo kofa ba tare da sallama ba. Na jingina da ƙofar ina sauke numfashi sama-sama idanuna a rufe ruff. Tsanar da Momy tayi mini yafi na kowa muni. Idan ta ganni a dakin tilon danta bayan dogon layin data shata a tsakaninmu, tabbas ko zata kunna wuta ta jefani ciki.
Sai kuma na bude idon da sauri jin wani kamshi da bai yi mini dadi ba. na sauke su a kansa. Yana zaune a kan couch dake ɗakin, ya cire armless rigar ma daga shi sai gajeren wando mai dan fadi. Fatarsa tas sai sheki takeyi ga tarin gashi dake kwance lubb a jikinsa. Hannunsa rike da shisha yana zuka da fesarwa, idanunsa da ya kafeni dasu sunyi ja sosai yana lumshewa da budewa a hankali.
Jikina ya dauki rawa, tunda nake ban taba kallonsa babu kaya ba sai yau, hakan yasa na rikice na daburce na manta me ya kawoni.
"What do you want?" Na jiyo deep voice nashi. Na daga kai muka kara hada ido. Na tsugunna daga bakin ƙofar nace, "Iam sorry Yaya Abdul" "Sorry for what exactly Halima?" Ya jefo mini wata tambayar.
Sai na rikice, jikina yaci gaba da rawa nace, "A kan abunda ya faru, Wallahi ba da gangan bane Yaya Abdul. Taimakona kawai yayi..."
Maganar ta katse ganin ya kashe shishan da yake zuqa ya nufo inda nake. Na hadiye wani yawu mai kauri da kyar ina kwalalo ido waje lokacinda ya tsaya gaf dani har ina jiyo fita da shakar numfashinsa.
Wani karamin murmushi yayi ya kama hannuna ya zare wasikar da Mufidah ta bani yanzu ya bude. Kusan sau uku yana maimaita karatun kafin ya nade pepan yayi jifa da ita. Da sauri nace, "wallahi Allah Yaya Abdul babu komai a tsakanina dashi kawai taimaka mini yayi" a fusace ya daga hannu zai dauke fuskata da mari. Har na sadaukar na rufe idanu na ina jiran saukar marin. Ko me ya tuna ya kaiwa iska naushi da fushi yace, "Fuck*d your damn so called taimako, and fuck*d you Halima"
Sosai na tsorata, tunda nake ban taba kallon Yaya Abdul cikin tsananin fushi irin wannan ba. A hankali ya koma baya baya ya fada saman gadonsa yayi rigingine yana kallon saman POP. Na rumtse idanu da karfi, zuciyata tana bugawa nace. Yaya Abdul ba zan iya jure fushinka ba, zafin zai yi mini yawa. Baba yana fushi dani, kaima haka. Za'a iya wayar gari a tsinci gawata. Wallahi zuciyata bugawa zata yi. Sai na kara fashewa da kuka.
Ya taso daga kwanciyar da yayi ya matso ni kamar mayunwacin zaki cikin fushi yace. "Meyasa zuciyarki zata buga dan ina fushi dake? Ba tambayar ce ta hana ni amsa shiba, kusancin da muka samu sosai ne yasa nakasa magana. Dakyar na iya fadin, "Babu komai".
"So get out,"
"Yaya Abdul plsss."
Na fada ina hade hannayena waje daya.
"I said get out!" Ya fada da karfin amon dake nuna zallar bacin ransa. Kusan a guje na fita dan tsoron daya bani. Na tsaya ina sauke ajiyar zuciya. Da sauri na nufi fita daga bangaren ina share hawayen da suka ki tsaya mini, gefe daya kuma ina tausayin kaina. Na sauko falon kasa. Saura kadan numfashina ya dauke sakamakon hada idanu da mukayi da Abban Abdul zaune a falon shi da wasu bakin mutane turawa su biyu. Kudine shimfide a gabansu, daloli da nairori mint mint, suna shiryasu cikin manyan ghana must go guda uku dake ajiye kusa dasu. Kudine na tashin hankali da tunda Umma ta ta haifeni ban taba ganin kudi masu yawa kamarsu ba ko a cikin film. Da ace na san zan hadu da Abba tabbas da ban sauko ba sai dai Yaya Abdul ya yi mini illah.
Ya mike a fusace yana nuna ni da yatsa yace, "Me kika zo yi a gidana. Au ho ubanki yaji labarin na shigo da kudi shine ya turoki ki yi masa sa ido tunda baki da kunya ko?"
Na zaro idanu jikina yana makyarkyata nace, "Wallahi Abba ba haka bane kayi hakuri".
Ya kara fusata yace "Idan ba haka bane me kika zo yi mini a gida". Na kara rikicewa, bakina yayi mini nauyi. Ta yaya zan fara sanar dashi cewa wajan Yaya Abdul nazo" Tuna hakan yasa wani irin zufa ya yanko mini. "Wajan Mufidah nazo karbar wannan" Na samu kaina da furtawa ina nuna masa pepan hannuna. Na dora da fadin, "Aikin makaranta ne." Na karisa ina kikkifta idanu tamkar tsohuwar yar jari hujja.
"Fice, kuma kada in kara ganinki a gidan nan" Ya fada da karfi har Mommy ta sauko daga sama tana tambayar abunda ya faru.
Da sauri na fita har ina karo da ƙofar palon. Ban damu da buguwan da goshina yayi ba, domin zafin dake cikin zuciyata ba zai barni jin zafin ciwon da naji ba. Cikin sa'a na shiga bangarenmu ban samu Umma a tsakar gidan ba. Na shige dakina, na fada saman katifata na matse filo gam a kirjina na saki wani marayan kukan da wacce ke cikin irin soyayyata ce kawai zata fahimce halin da zuciyata ke ciki. Ashe ban sani ba kuka yana gaba. Ban sani ba na bar baya da kura a fitar da nayi. Haka na kwashe wannan yinin cikin kunci. Innani da iyalinta sunyi nasarar mayar da bangaren Baba Gadanga tamkar kufai. Muna raye ne Kawai, amma babu dandanon farin ciki a zuciyar mu, Ni Halima Ummata da Kuma Baba.
Washegari misalin karfe bakwai na safe muka jiyo wani irin ihun daya rikita dukkan gidanmu. Ba ihun ne ya bada tsoro ba. Muryar mai ihun ne ya tsorata mu. Duk da rashin karsashin da muke ciki. Dukkanmu muka fito babban compound din. Kusan kowa ya fito manya da yara as usual idan wani abu ya faru a gidan. Abbansu Ya Abdul ne yayi ihun. Muna fitowa yayo kan Baba gadan-gadan ya shakesa yace, "Gadanga fito mini da dukiyata daka sanya yarka Halima taje ta sace daren jiya.
Tofah mai karatu. Wannan shine tirka tirka. Lallai akwai babbar matsala.