Free chapter · Read without an account
Page 13
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 13
Washegari bayan sun gama karatun safe ya nufi gidan Mami.
Mami dake fitowa daga part ɗin Daddy sanye da dogon hijab tayi murmushi tace"Faruq ka shigo?"
Ya ɗurƙusa yace"ina kwana".
Tace"lafiya ƙalau ya karatu?"
Yace"Alhamdulillah".
Mami tace "Masha Allah, lafiya jiya ka dawo da abinci?"
Yayi shiru kanshi a ƙasa don bai san abinda zai ce mata ba.
Mami ta sake cewa "tambayarka nake,me yasa ba ka ci tuwo ba jiya?"
A hankali yace"ki yi hakuri,ban iya cin tuwo ba".
Da mamaki Mami ke bin shi da kallo,can ta gyada kai tace"ba ka iya cin tuwo ba?"
Ya gyada kai a hankali not looking at her.
Tace"ai da ka yi magana,to me ka ci jiyan?"
A hankali yace"babu komai".
Tace"shikenan,ban san ba ka cin tuwo ba,ka zauna zan aiko a kawo maka abinci yanzu".
A hankali yace"Nagode".
Yana zaune a wurin Zarah ta fito riƙe da bowl ɗin jiya da cup,ta ajiye kusa dashi ta koma ta zauna.
Da mamaki ya ɗan kalleta,tayi murmushi tace"Daddyna ya dawo jiya".
Ya shareta tamkar ba da shi ta ke ba,can ta sake cewa"kaima kana da Daddy,me yasa ka ke sa old clothes?"
Sadauki da ya fara gajiya da maganarta yace"tashi ki bar nan".
Ta miƙe tsaye da sauri tana kallon shi,nan da nan idonta ya cika da hawaye tace"me yasa ka ke min ihu?"
Da mamaki yake kallonta don bai san yaushe ya mata ihu ba.
Za ta sake magana ta hango Sudais tsaye a gaban apartment din shi yana kallonta,ta ruga da gudu tana dariya tace"Ya Sudais".
Tana zuwa ta rungume shi tace"i miss you ya Sudais,ina ka je?"
Ya riƙo hannunta suka zauna kan kujerun dake wurin yace"babu inda naje,me kike a wurin wancan,kamar almajiri ne ko?"
Ta juya ta kalli Sadauki da ya bita da kallo tace"Mami tace ba almajiri bane,she said his name is Faruq".
Ya gyaɗa kai yace"oh I see,so how are you?"
Cike da iyayi tace"I'm fine ya Sudais,yau ba ka kawo min chocolate ba?"
Yace"I'm sorry ban fita ba Zarah,maybe later".
Sadauki ya buɗe abincin ganin masa ne da miya sai tea dake cikin cup.
Ya karasa bakin pampo ya wanke hannun shi ya koma ya zauna,sai da yayi bismillah sannan ya fara cin abincin.
Da zai tafi Mami ta bashi sabulai da omo na wanka da wanki,ta haɗa mishi da dubu daya tace ya aske suman kanshi.
A haka ya cigaba da zuwa wurin Mami,idan ta nada aikin da zai iya mata ta kan bashi,wani lokacin ta aike shi kasuwa,har wanki da guga ta kan bashi time to time idan mai musu guga bai zo ba.
Ba tare da sanin shi ba ta sha gwada shi in different ways kuma kowanne sai da ya tsallake,harta saƙon kasuwa da take bashi cikin gwajin da take mishi ne.
Akwai ranar da tayi wani kasada,ita kanta ta san abinda tayi was nothing but risk,dubu ɗari ta sa cikin envelope ta miƙa mishi tace yaje kasuwa wurin wadda take siyayyan kayan abinci a wurin shi za'a bashi kayan da ta siya.
A ranar da wani mai son zuciyar ne babu abinda zai dawo dashi gidan,amma haka Sadauki ya dawo mata da kayan ko Naira biyar dinta bai yi ciwon kai ba.
Wani lokaci cikin kayan wanki ko guga haka zata bar kuɗi amma zai dawo mata dashi.
Sosai Sadauki ke jin daɗin alaƙarsa da Mami,tunda ya haɗu da ita ya daina kwana da yunwa,abinci yake samu sau uku a rana kuma ya ci ya ƙoshi,idan kuma tayi tuwo sai ta samu wani abin ta bashi koda snacks ne kuwa,bata ɗauke shi almajiri ba,kamar yadda za tayi treating ɗan cikinta haka take treating Sadauki,sabulun wanka da wanki kuwa baya yanke mishi.
Haka zalika bai da matsala da ƴaƴanta tun daga kan Zeenah har Zarah,shi dai matsalarsa da ita surutun tsiya gashi ta takura mishi.
Ɓangaren Hajiya Mama da ƴaƴanta kuwa sai abinda suka manta ne ba su mishi,tunda ta fahimci almajiri ne shi ta tsiro da sa shi aiki,sai da Mami ta rufe ido tace babu ruwanta dashi tunda ba ita ta samo mata shi ba,ranar kuwa ba ƙaramin tashin hankali aka yi ba don a ranar ma Daddy ya ga Sadauki ido da ido duk da ya sha jin labarin Sadaukin a bakin amaryarsa.
A hankali sabo ya fara shiga tsakanin Zarah da Sadauki duk da korata da yake,amma saboda tsabar naci ko sau ɗaya bata taɓa fushi ba,idan tayi kuka a lokacin zuwa anjima zata koma.
Ana haka ta hau bori tace Sadauki take son ya fara koya mata karatu,da farko duka taci a hannun Mami tsabar takaici,amma kullum aikin kenan sai ta zauna ta hau birgima ita babu islamiyyan da zata je sai dai shi ya koya mata.
Da Daddy ya ji abinda ke faruwa ya ce Mami tayi hakuri ya fara koya mata karatun a gani.
Sai da aka sa CCTV camera a parlourn ba tare da sanin duka yaran ba sannan Mami ta sanar dashi.
Cike da ladabi ya amsa mata, washegari ya shigo har parlourn ya zauna a kan carpet, Zarah ta fito sanye da dogon hijabinta riƙe da Alqur'ani ta zauna can nesa dashi.
A haka suka fara karatun kuma sosai take ganewa,dama barta dai da wasa da shiririta amma bata wasa da karatu.
Wani lokaci Zeenah da sauran ƴan uwanta kan shigo ayi karatun dasu amma karatun yafi ƙarfi da Zarah,duk abinda ke faruwa a parlourn Daddy da Mami na gani a haka har aka shekara ɗaya,ko sau ɗaya ba'a taɓa kama shi da wani mugun hali ko wani ɗabi'a mara kyau ba.
Ana haka watarana Daddy na zaune a garden dinshi dake baya yana aiki a system ya jiyo hira tsakanin Sadauki da Iliya mai gadi.
Iliya yace"ka ji labarin sace mutanen da aka yi jiya a hanyar Zamfara?"
Sadauki yace"subhanallah,wallahi ban ji ba".
Iliya ya gyara zama ya hau rattaba bayanai tamkar a gaban shi abin ya faru.
Yace"ai abun sam babu daɗin ji wallahi,ance kusan su goma sha takwas ne a motan,lamarin ƙasar nan kullum ƙara muni yake. Sace mutane ake tamkar kaji. Babu tsaro, mutane na rayuwa cikin fargaba,Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu".
Sadauki yayi shiru yana kallon Iliya,ya sauke numfashi yace"Allah Ya kawo ranar da za a samu mutanen da za su tsaya su kare ƙaarsu ko da hakan zai jefa rayuwarsu cikin haɗari. Da zan sami dama, zan so in kare ƙasata da duk ikon da Allah ya ba ni."
Iliya yayi dariya sosai jin zancen Sadauki.
"Anya ka san abinda kake faɗa kuwa?"
Sadauki ya kalle shi cikin natsuwa ya ɗauke kai.
Iliya ya sake cewa"Lalacewar kasar tayi yawa Sadauki,mugaye sunyi yawa,masu gaskiyar cikin su kaɗan ne,kana ganin mutum ɗaya zai iya canza wannan ƙasar?"
Sadauki yace"Ban ce mutum ɗaya zai canza ƙasar ba,idan kowa ya ce ba zai yi komai ba saboda ƙasar ta lalace, wa zai gyara ta?"
Iliya yace"kai yaro ne Sadauki,ba lallai ka fahimci abinda nake son ka fahimta ba".
Daddy da tunda suka fara magana ya bar abinda yake yayi shiru yana sake nazartar maganganun dake fitowa daga bakin Sadauki.
Tun daga ranar ya sake sa ido sosai akan Sadauki,duk wani movement din shi na cikin gidan har waje yana sane dasu ba tare da sanin sa ba.
Ranar ya sa Mami ta shigo dashi har babban parlourn shi dake ƙasa,ganin hoton Daddy sanye da uniform ya sa ƙirjin shi wani irin bugawa ya kafe hoton da ido,bai taɓa sanin mutumin gidan soja bane sai ranar.
Daddy dake saukowa daga stairs ya kafe shi da ido with many thoughts running through his mind.
Yana ganin Daddy ya sauke kai ya gaishe shi,Daddy ya zauna kan kujerar dake facing Sadauki yace"ya sunanka?"
A nutse yace "Sadauki".
Daddy yace"sunan yanka nake nufi".
Sadauki yace"Umar".
Daddy ya jinjina kai yace"daga wani gari ka ke?"
Yace"Bauchi,sunan kauyen mu Rafin Dawa".
Daddy yace"that's good,mene nne sunan mahaifinka?"
Wannan karon sai da ya ɗan ɗago ya kalli Daddy,ya sunkuyar da kai yace"Mallam Muhammadu,shine limamin ƙauyen mu".
Daddy ya gyaɗa kai alamar gamsuwa yace"ka taɓa karatun boko ne?"
A hankali yace"eh,ina JSS 3 aka kawo mu makaranta".
Daddy yayi shiru for some seconds kafin a nutse yace"kowa na da buri a rayuwa,na san ba zaka rasa wani buri a ranka ba,menene shi?"
Sadauki yayi shiru yana wasa da zanen carpet dage gaban shi,yana da buri,amma wannan burin zai cika kuwa?
A nutse yace"babban buri na shine in zama soja,lokacin da nake karami hakan sha'awa kawai yake bani,sai yanzu na fahimci abin yafi ƙarfin haka,so nake in kare ƙasata,inyi maganin azzalumai da suka mamayeta,inyi yaƙi tsakanin karya da gaskiya,ko da hakan zai sa na sadaukar da raina domin ƙasata ta samu zaman lafiya da adalci."
Cike da wani irin burgewa Daddy ke bin shi da kallo,wani hope da natsuwa yaji yana shigar shi.
Yayi murmushin da ba kasafai aka saba gani a kan kyakkyawar fuskar shi ba yace"I'm really impressed Umar Sadauki,za ka iya tafiya".
Sadauki ya mishi sallama ya fita Daddy ya bishi da kallo.
Cikin sati ɗaya Daddy ya gama bincike tsaf akan Sadauki,har can kauyen su sai da ya sa aka nemo masa information.
Hakan bai mishi wani wahala ba kasancewar akwai wani abokin aikinsa ɗan garin.
Ranar wata asabar bayan ya gama karatu dasu Zarah ya aika a sanar dashi yana neman sa.
Bayan ya amsa gaisuwarsa yace"Sadauki!"
A nutse yace"na'am".
Daddy yace"kana son cigaba da karatu?"
Da sauri ya ɗago don bai zata wannan tambayar zai masa ba,Daddy ya gyaɗa kai ganin kamar bai yarda da tambayar da ya masa ba.
Ya sunkuyar da kai a hankali yace"ina son karatu sosai".
Daddy yace"burinka ya kusa cika Sadauki,da yardar Allah zaka zama abinda kake fata,ka shirya ka zo nan ranar Monday ƙarfe bakwai na safe,amma zan so yin magana da malaminka saboda ya san abinda ke faruwa".
Da sauri Sadauki yace"idan ya sani ba lallai ya amince ba".
Daddy yayi shiru yana kallon shi,a hankali yace"to shikenan babu damuwa,za ka iya tafiya".
Sadauki bai yi wani baccin kirki a wannan daren ba,gani yake kamar mafarki yake,bai taɓa tunanin akwai mutane irin Daddy da Mami a wannan duniyar ba.
Mami sosai ta nuna farin cikinta bayan Daddy ya sanar da ita shawarar da ya yanke,ita kanta tana da hakan a rai sai ga shi ya rigata.
Ranar Monday da sassafe ya shirya cikin kayan da Mami ke siya mishi time to time ya bar makaranta bayan sun gama karatun safe,Daddy na tsaye kusa da mota sai su Zarah dake tsaye a gefe sanye da uniform,cike da girmamawa ya gaida Daddy.
Daddy ya amsa da ɗan kulawa yace ya shiga mota su tafi,driver ya taso da gudu Daddy ya dakatar dashi yace"koma ka zauna Musa,na hutar da kai yau".
Musa yace"Yes Sir".
Daddy ya shiga driver seat Sadauki ya zauna a gefen shi,su Zarah su ooka shiga baya.
Har cikin makarantar ya shiga bayan mai gadi ya wangale masa gate, ya samu gefe daya yayi parking su Zarah suka wuce classes ɗinsu, cike da girmamawa ake gaida shi har suka shiga office ɗin principal.
Bayan sun gaisa don akwai sanayya sosai tsakanin su ya sanar dashi abinda ya kawo shi.
Principal ya kalli Sadauki yace"da farko zamu bashi exams,idan Allah ya sa ya ci shikenan,zai rubuta Junior WAEC don sun kusa rubuta shi in sha Allah,daga nan sai mu san what next".
Suna zaune aka yi typing questions aka mikawa Sadauki,ya kai shi empty seat dake gefe ya miƙa mishi pen ya koma wurin Daddy suka cigaba da hira.
Bayan minti arba'in ya miƙe ya kawo mishi script din, principal ya cire glasses din shi ya ajiye ya sake kallon Sadauki.
Da mugun mamaki yace"you attended Rafin Dawa Government Day Secondary School?"
Sadauki ya sunkuyar da kai yace"Yes Sir".
Ya jinjina kai yana kallon Daddy yace"I'm so impressed with his performance Sir,hakan ya nuna zamu iya ajiye shi a SS 3 kamar yadda ka buƙata saboda yanayin shekarun shi,yanzu zai karbi exercise book da textbook da zasu taimaka masa wurin karatu,zamu bashi Uniform yanzu sai ya shiga class kawai tunda babu abinda za'a jira."
Daddy yace"Nagode sosai Sir,sai dai zai dinga zuwa late due to some personal reasons,ayi mana haƙuri da hakan dan Allah".
Principal yace"we don't accept late coming Sir,sai dai tunda kayi magana I'll speak to our securities and discipline masters,that won't be an issue".
Daddy yace"I really appreciate Sir".
Daga nan yayi payment aka ba Sadauki duk abubuwan da zai buƙata aka kai shi changing room ya canza kayan shi zuwa Uniform.
Principal da kanshi ya kai shi class,ya kalli Chemistry teacher dake ciki yace"you have a new student here, introduce yourself Umar".
Sadauki yace"Good morning Sir,my name is Umar Muhammad Sadauki".
"You're welcome Sadauki,were very happy to see you".
Ya nuna seat dake tsakiya yace"you can sit next to Abduljalal,I pray he doesn't disturb you".
Sauran ƴan class suka fashe da dariya.
Wanda aka kira da Abduljalal ya wani daure fuska,teachern yace"if you can only be this serious Abduljalal".
A haka period dinshi ya ƙare ya musu sallama ya fita.
Yana fita class ya hargitse da surutu,Sadauki ya juya inda Abduljalal ke zaune ya ga wayam,can cikin sauran student ya hango shi ana hira.
Ya ɗauke kai ya cigaba da duba takardun dake gaban shi,shigowar maths teacher yasa class din yayi tsit kowa ya koma wurin zaman shi.
Bayan ya fita Abduljalal ya mike zai bar seat din Sadauki yayi saurin tsai dashi ya tambaye shi sauran abubuwan da su kayi.
Yayi dariya ya koma ya zauna,a nutse ya fara mishi bayani daki daki,da taimakon Abduljalal da yawanci ake kira Jalal ya fara rubuta notes.
Yana jin karan bell yayi saurin rufe books ɗin yace"gaskiya yunwa na ke ji,ka bari idan mun dawo sai mu cigaba".
Ba don ya so ba sai don nacin Abduljalal suka fita, Zarah dake tsaye a School Shop ta waro ido da sauri ganin shi cikin uniform,da gudu ta ruga kusa dashi tace"Yaya F".
Abduljalal yace"kin san shi ne?"
Tace" Ai,yayana ne".
Abduljalal ya wani yarfe hannu yace"don Allah ya ku ke da wannan parrot ɗin a gida,she talks too much for crying out loud".
Zarah ta wani turo baki tace"kaima you talk too much Abdul".
Ya waro ido yace"really?"
Ta murguɗa baki ta ɗauke kai tace"Yaya F,ka daina kula shi ka ji?ya cika surutu da yawa".
Sadauki har ga Allah kanshi ya fara ɗaukar ɗumi,bai cika son yawan magana ba gashi Allah ya haɗo shi da mutane masu surutu.
A ranar Sadauki ya gama sanin waye Abduljalal,mutum ne mai son wasa ga yawan fara'a,bai cika daukan abu serious ba kuma a haka shine Head boy,yana da ƙoƙari sosai don shi ke daukan first position,idan ka biye mishi tsaf zai kai ka ya baro don ba zaka taɓa ganin yana karatu ba,zai biye ka kuyi wasa amma duk abinda aka koyar nan take yake shiga kanshi.
Oum Rijalain
***