Free chapter · Read without an account

Chapter 26

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍

Chapter 26

Mujaheed.
    Kallon fuskar Mommah kawai yake yana yaba yanda ta ƙware a son zuciya, har mamakin ƙarfin halinta ya ke a wasu lokutan, kawai de baya da yanda zai yi da ita amma wallahi ta gama gundurarsa dan tana mahaifsa kawai ya saka yake ɗauke kai akan wasu abubuwan, kuma yana nan yana lissafin kwanakin da suka rage basu wuce biyu ba da ta ɗaukar masa alƙawari akan binciko ma shi inda Zunainah ta ke.
   "Mujaheed zauna mana kayi tsaye so kake jiri ya kwashe ka bayan kuma ba isashen ƙarfi gareka a jiki ba."
    Ta faɗa tare da kama kafaɗunsa ta taimaka ma shi ya zauna akan sofa.
     Yana jinta tana faɗin.
   "Yauwa bara inje insaka a haɗa maka abinci me sauƙi sai in haɗa maka ruwan ɗumi kayi wanka nasan zaka ji daɗin jikinka."
    Mujaheed kallon one siter kawai yake wasu memorie na zaman Zunaina a gidan na dawo ma shi, musamman yanda ta maida kujerar wajen zamanta.

***   ***
"Nikam dai na gaji da daurewa yau dole inyi tambayar nan karta kashe ni."
    Mujaheed ya faɗa yana tafa hannayensa ta bayan kujerar fuskarsa ƙunshe da murmushi.
     Da sauri ta juyo da kanta tare da wara ma shi manyan idanuwanta masu ɗaukar hankalin shi ta ce tana murmushi.
    "Kai Ya Muhjaheed ka kusa tsorata ni fa."
    "Thank god ban rigada na tsorata ki ɗin ba ai."
   Ya faɗa yana zagayawa ta bayanta tare tsayuwa agabanta ya harɗe hannayensa.

    "A'afa amma ai ka ɗauki alhakina idan kana so in hafe anjina ka kawo cin hancin ice cream manya raba uku."
    Duƙawa yayi tare da dafe hannun sofar still yana murmushi ya ce.
    "Ba za ki sha sanyi ba gaskiya salan mura ta kama mana ke ki barmu da jinya."
Da sauri ta ce.
    "Wayyo Yah Mujaheed ai ba ni kaɗai zan sha ba ni da Afnan da Mommah pleaseeee mana."
     Ta yi maganar tana ɗan shagwaɓe murya.
    Wani abu ne kamar ma shi ya caki zuciyar Mujaheed data gama ɗaurewa da tsananin soyayyar Zunaina.
     Cikin son abar zance saboda idan aka cigaba zai iya sakin layi, sai ya ce.
    "Ki bani amsar wannan tambayar, mi yasa kike son zama akan wannan sofar?."
   Ya faɗa yana dukan hannun sofar.
    Sai da tayi murmushi kafin ta ware hannayenta haɗi da buɗe duka girman idanuwanta sannan ta ce.
    "Ina son wannan sofa ɗin saboda nafi jin daɗin zama akanta ina jina cib da cib du ƙwaƙwar Afnan shafamin lafiya take idan na zauna akan kujerar nan, kuma ni haka kawai nike son zama akanta.".

****
Cikin ɗaga sauti Mommah ta ce.
    "Mujaheeddddddddd."
 A gigice ya dawo daga duniyar tunanin daya lula, nan yaji wani danshi kwance akan fuskar shi, kamar me tsoro yakai hannu ya taɓa kumatun shi aiko yaji sanyin ruwa alamun hawaye  ya ke yi ba tare da ya sani ba.
    A hanzarce ya goge tare da miƙewa tsaye yana ƙaƙalo murmushin yaƙe sannan ya ce.
    "Baa....ba..bakomu ai Mommah sanyin AC ne yayi min yawa shine idona ke ruwa an haɗa ruwan bara inje in watsa."
    Ya taƙaita zance ta hanyar bin gefenta ya wuce da sauri ya haura sama.

Wani abu me ɗaci Mommah ta haɗiya tare da janye dubanta daga hanyar sama inda ya haura ganin har ya ɓace.
     Zama wajen ta yi tare da kunna wayarta da ɓacin rai akan fuskarta dan tunda ta fahimci kujerar yake kallo ta gane tunanin Zunaina yakr dan ita ke yawan zama akan sofar.
    Danna kira tayi a number da aka rubuta Hajiya Zainab tare da kara wayar tana jira a ɗauka.
    "Assalamu alaiki Aminiyar yanzun nan nike shirin kiranki imbaki albishir me zafi."
     Da fara'a Mommah ta ce.
   "Wa'alaiki salam ƙawar alkairi maza shafa min nima nazo da nawa batun."
    Daga can cikin wayar aka ce kasancewar wayar a speaker take.
    "Nazliy na hanya yau kuma na fara shaida mata shawarar da muka yanke ni da ke to abi yazo cikin sauƙi ashema tasan shi Mujaheed ɗin tace tana ɗan yi ma shi magana kulata ke bai yi shine itama ta fita sabgar shi, daga jin yanda take min magana cike da ɗoki nasan tabbas ba zamu samu matsala da ita.
     To kema faɗa mib naki albishir ɗin."
     Da tsananin fara'a Mommah ta ce. "Kai ma sha Allahu abu yayu kyau, kinga dan Allah yanda tsarinmu zai tafi cikin sauƙi, gaskiya naji daɗin wannan batu Allah ya dawo mana da Dota lafiya haƙiƙa na yi murna.
    Yo dama nima kira nai intambayi sanda zata dawo dan ina son cikin satinan su haɗu ita da Mujaheed so nike ya manta da waccan mayyar yarinyar data lashe min kurwar ɗa, kingani nan na dawo gida sai yau aka sallame mu a asibiti."
Nan suka ci gaba da tattaunawa kamin daga bisani suka yi sallama da juna suka kashe wayar....

Daddare Mommah ce shirye cikin shigar ɗinkin material wanda ya ƙara fito da kyanta, da sallama a bakinta ta tura ƙofar ɗakin Daddy.
     Zaune ta iske shi akan study table gaban shi barbaje da takardu da alama dubawa yake.
    "Barka da dare Alhajina, aiki kaketa yi haka gashi har time ɗin dinne ya gabato."
     Ta faɗi tare da zama akan ɗayar kujerar dake kusa da shi tana kai dubanta kan wata takarda.
     Hannu ta saka ta ɗauka tare da  soma karanta takardar wani yanayi na bayyana yana korr fara'ar da tazo da ita.
    A fusace ta aje takardar tare da tashi tsaye cike da ɓacin rai ta ce.
    "Mi kake ƙoƙarin aikatawa haka wai Ahmad mi ya shiga cikin kanka kwana nan, wait wai ita wannan Zunainar ɗiyar Abdul ce ko kuma ɗiyarka ni bangane ma wannan abun ba koko ku biyu kai da shi kuka taru kuka haifeta ne bani da labari."
     Daddy da dama a  sama yake da ita ya miƙe tsaye ran shi a mugun ɓace ya soma faɗin.
    "Ki iya bakinki tun kafin imfaɗa maki abin da zakiyi danasanin sanina a rayuwarka."
     Sai kuma ya soma tattare takardun shi yana turawa a cikin wani Trolley yana gamawa ya datse harda saka password sannan ya fice yabar mata ɗakin saboda baya da lokacinta.

   Baki sake Mommah tabi shi da ido tana mamaki halin da yake nuna mata a kwanakin nan gaba ɗaya ya sauya mata kamar ba shi ba.
      Bin ɗakin ta yi da ido na ƴan mintuna sannan ta fice tana jin ɓacin rai akan rugujewar shirinta na yau....

Mujaheed tunda ya samu ya haye sama yabar Mommah kai tsaye ya shige toilet harda sakawa ƙofar key dan sosau yake da buƙatar space baya son surutanta da yakewa kallon borin kunya, yafi so yayi nesa da ita dan yasamu damar yin tunani ba tare da takurawarta ba.
     Ya jima yana gasa jikinshi da ruwan ɗumi da suka taimaka ma shi wajen warware gajiyar da kwanciyae asibiti da ciwo suka haddasa ma shi, ko bayan daya fito shiryawa yayi cikin ƙananun kaya masu rangwamen nauyi, tsaf ya  fito cikin kayan sosai suka yi ma shi kyau gami da haska fara tas ɗin fatar shi data ƙara haske saboda jinyar da yayi, key ɗin mota ya ɗauka ya sauka yana addu'ar karya haɗu da Mommah wacce ta maida shi Mamas boy ta ƙarfin tsiya, yayu sa,a kuwa bata nan da hanzari ya sauka ƙasa tare da ficewa daga ɗakin.
    Sama-sama ya gaisa dasu Yahaya driver ya shige mota ya bata wuta ya fice a ɗari bayan an buɗe ma shi get.
     Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya saki tare da furta kalmar "Alhamdulillah a fili yana jin kan shi kamar wanda ya fito daga keji, ɓat ya ɓace daga arear ya doshi hanyar unguwar Malali zai je wajen wani abokin shi da suka yi karatu a ƴar'aduwa tare da shi, kasancewar baya ƙasar sai yanzu ya dawo dama kuma ya daɗe yana son yaje su ɗan zanta shiyasa kai tsaye ya nufi can, yasan du nacin Mommah ba bata taɓa gane inda yaje ba tunda bawai sanin abokin nashi tayi ba sosai.

     Yana tsaka da driving kwatsam yaga mutum ya faɗo a gaban motar shi, du ƙoƙarin da yayi wajen danne burki abu ya gagara saboda tsabar rikicewar da yayi, rintse idon shi yayi hankalin shi a mugun tashe sanda ya tabbatar da ya banke mutumin, da ƙyar ya iya sarrafa kan shi ya danne burkin ya samu motar ta tsaya, a kuma daidai lokacin ne wata mota ta giftasu da gudun tsiya, daidai nan ya buɗe ƙofa ya fito a rikice tare da tunkarar gaban motar tashin hankali na kulle idon shi daga ganin wanda ke yashe a ƙasa.
 
     Zaune yake a mazaunin driver hakan ya bashi damar hango Mujaheed ta cikin glashin miro, a 360 ya take burki tare da faɗi a razane.
   "Dam it kamarfa M.A nike gani Naufal.
    Ya faɗa tare da karya kan motar dan ya koma baya....✍🏻

Tofa ko wanene wannan kuma Mujaheed ya bige?

Mu haɗu da ku a next page.

MARYAM STAR CE

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.