Free chapter · Read without an account

chapter 27

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍

Chapter 27
    Parking ya yi a gefen hanya sannan ya buɗe murfin ya fito.
   "M.A" ya furta kalmar yana takawa aɗan hanzarce yayinda Naufar yabi bayan shi shima ganin dagaske Mujaheed ɗin ne.
     Mujaheed daya gama firgicewa tsabar shiga shock da wani irin ƙarfi ya kaiwa abokin shi Khamis wata iriyar runguma yana fashewa da kuka lokaci ɗaya yana faɗin.
    "Ya mutu Khamis na kashe shi duba ka gani."
    Da sauri Naufal ya matsa kusa da gawar yana duddubawa hankalin shi a matuƙar tashe.
    "A'a bai mutuba Khamis kuyi sauri mu kaishi asibiti da sauran rayuwar shi."
       Naufal ya faɗa yana ƙoƙarin cicciɓar mutumin amma ya kasa shi kaɗai.
    A hanzarce Khamis ya kama aka saka mutumin cikin motarsu, sannan ya dawo ya kama Mujaheed daya ruɗe yana rarrashin shi ya saka shi motar shi kuma Naufal ya ɗauki motar Mujaheed suka rankaya asibinsu da ke nan Malali basu sha wahalar dauko Police ba saboda asibitin ta mahaifin Khamis ce kuma shina Khamis din yana daya daga cikin manyan Doctors.
   accident and emergency aka wuce da shi kai tsaye tare da soma bashi tainakon gaugawa....

Jin shiru Mujaheed bai sauko ba ya saka Mommah zuwa dakin shi da kanta sosai ta yi mamaki ganin baya nan kuma ita bataga fitar shi ba sai tasa a ranta ko yaɗan zaga ne dan ya sha iska ya miƙe ƙafa, da haka ta koma parlor ta zauna tunanin abin da taga Daddy na shirin aikatawa ya tsaya mata a rai.
      Afnan ganin ambarta ita kaɗai a dinning tayi saving kanta ta cike ƙundunta tana gamawa ta koma ɗaki ta kwanta dama yanzu sam bata wannan surutun nata, idanma aka matsa mata da magana tofa fashewa take da kuka kafin kuma a samu ta yi shiru aiki ne ja.

       Mommah tana nan zaune ita kaɗai a parlor bata ankareba gar dare ya soma yi, kirane ya shigo wayarta ta saman screen taga har sha ɗaya ta yi nadare hakan ya zaburar da ita ta miƙe tare da surar wayar ta nufi hanyar fita.
   Tun daga compound ta soma kwalawa Yahaya da Idi me gadi kira.
    "Wai nikam Mujaheed ya fita daga gidan nan ne  yau da marice haka?." ta yi tambayar tana fatan amsar da zata fito daga bakinsu ta kasance a,a.
    Gyaran murya Yahaya driver yayi sannan ya soma faɗin.  "Ma sha Allah ai ɗazu..."
   "Malam banson wani dogon sharhi daga gareka just anser me." Ta katse shi kamar zata wanka ma shi mari tsabar haushi.

    Jin haka sai kawai Yahaya ya girgiza kai tare da ɗan matsawa gefe, Idi me gadi ya bayyana a bayansa.
     Tun kafin ta sake yanko musu wata maganar ya ce.
   "Ranki shi daɗe ya fita ai tun ɗazu, ko gaisuwar kirki bamu yi da shi ba ya fice a mota."
   Wani irin tashin hankaline ya rikitowa Mommah, ta ɗora hannu aka tare da kallon parking lot tana ƙarewa sauran motoci biyun da suka yi saura.
   "Na shiga uku, wai yau nike shirin faruwa da ni ne, daga wannan sai wannan yanzu da daren nan ta ina zan fara nemon Mujaheed, gashi shima wancan kuturu uban zuciyar ya fice ya bar gida."
    Ta faɗa tana danna kiran layin Mujaheed, sai de ko sakan biyar ba'ayi ba aka shaida mata ai layin a kashe ya ke.
   A gigice ta ɗora hannu a kai tare da soma zagaye kamar ƙaramar yarinya harda yarfa hannu ta ke, kafi  can ta zabura tacewa Yahaya.
    "To uban ganin ƙwam ka kafe ni da ido kamar maye, ni ɗauko mota ta zo mu fita kayi sauri please."  Ta faɗi tana hanzartawa ta wuce ciki.
Mayafi da key ta ɗauko ta kulle ƙofar shiba main parlor ɗin, kafin ta fito har Yahaya ya fitarda mota ya buɗe mata gidan baya yana jiranta.
   A 360 suka bar gidan har lokacin bata cikin nutsuwarta.
    "Ranki ya dade ina muka nufa ne?."
   Yahaya Driver ya tambaya sanda ya harba motar kan titi.
    Sai da taja uban tsaki "Mtwssss." tare da maka ma shi harara kamar idanuwanta zasu faɗo ƙasa sannan tace.
    "Kai kana da matsala wallahi, to ni ina zani a wannan daren daya wuce neman ɗana, maza muje gidajen abokansa du da kasani a garin nan."
   Baice komi ba ya ƙarawa motar gudu yaci gaba da tuƙi.

Cigaba da kiran layukan abokai da wanda tasan Muhajeed na gaisawar ko zuminci dasu Mommah tayi, tana tambayar koya zo, amma kowa sai yace ya ɗauki kwanaki bai gan shi ba, gashi sai kiran wayar Daddy take yi amma shima bai amsa mata ba gaba ɗaya ta firgice kamar Mujaheed ɗin yaron goye ne....


Shiru Alhaji Ahamad yayi yana kallon tarin takardun dake gaban shi wanda ya kammala saka hannu, gaba ɗaya gumi ya jiƙe rigar jikin shi duk kuwa da akwai iskan fanka a ɗakin.
    Ɗaga idon shi yayi yana ƙarewa ɗakin kallo, wanda daga gani basai amfaɗa ba kowa yasan tsohon gini ne abinda yasa bai lalace ba saboda mutane na rayuwa a ciki.
      Nan take ya soma tunano ranar shi ta ƙarshe da Abdul rabuwarsu ita ce abu na ƙarshe da bai hasasaba a lokacin da Abdul ya damƙa amanar dukiyar ƴaƴan shi gare shi, sai a yanzu yake tunani akan abin da ya kamata ace tun farkon faruwar komi ya hasaso.
       ****  ****  
CIGABAN LABARIN AHMAD DA ABDUL

A ranar da Abdul ya damƙawa Ahmad dukiyar shi bayan sun rabu wajen ƙarfe takwas na dare, saiga Abdul ɗin shi da matar shi da yaran shi biyu sun je gidan Ahmad.

   "A'aha ko kayi mantuwa ne?."
    Ahmad ya faɗi bayan ya buɗewa Abdul ƙofa sanda ya ƙwanƙwasa.
     Matar Ahmad Zulaika ce ta fara shiga bayan sunyi gajeruwar gaisuwa ita da Abdul ɗin ta wuce ciki wajen haliya Halima.

    "Lafiya dai naga yanayinka ya sauya miya faru ne?." Ahmad ya faɗa yana janyo hannun Abdul ya shigo da shi cikin gidan ya mayar da ƙofar ya rufe.
    Da damuwa a muryar Abdul ya miƙawa Ahmad Zunaina dake kwance akan kafaɗun shi sannan ya ce.
    "Ga Angel nan ta ɗan zauna wajenka zamuje asibiti ne Zulaikace bata jin daɗi ga Maryam itama zazzaɓi take yi bata sanar min ba tun ɗazu sai bayan dana koma gida, na siyo musu magani amma baiyi aiki ba shi ne nace tunda dare ne bari inbaka Zunaina idan muka dawo zan biyo in karɓeta." Ya faɗi yana zaro wasu takardu daga aljihun shi ya miƙawa Ahmad ɗin bayan ya bashi Zunaina.
    "Ashashsha abu baiyi daɗi ba itama dai Zulai ko yaushe zatabar wannan  zurfin cikin nasu na fulani ta ina mutum zaiyi shiru da ciwo, to shikenan Allah ya bada lafiya ko inzo muje tare ne asibitin."
    Ya faɗa yana shiga cikin gidan Abdul na biye da shi a baya.
    "A'a ka zauna a gida ka taya Madom tayi mana girki please bata samu damar dafa komi ba yau."
     Sallama suka yi tare da shiga cikin ɗakin inda Halima da Zulaika ke zaune suna ɗan fira sama-sama kasancewar Zulaikar bata jin daɗi sosai ƙarfin hali kawai take yi.
     "Oyoyo ga tawan, tafisu wallahi su zabaya sai sun jira."
    Halima ta faɗa tana karɓar Zunaina dake barci akafaɗar Ahmad.
    "Ai ƴar yaki barci take yau tasha gajiyar School shiyasa muka kawota nan idanma munyi dare kawai kubarta anan ta kwana."
 
Abdul bai jira anyi wata fira me tsayi ba yayi musu sallama bayan ya amshi Maryam daga hannun Zulaika ya kama hannayenta cike da kulawa suka fice daga gidan tare da rakiyar Ahmad.

     Wannan ganin shine gani na ƙarshe da Ahmad yayiwa aboki kuma aminin shi Abdul wanda ya zama tamkar ɗan uwansa na jini, daga wannan haɗuwa basu sake haɗuwa ba, daga wannan maganganun masu sake magana ba, wannan ranar ita ce ta zama rana mafi baƙin ciki ga Ahmad saboda rashin ɗan uwa amininshi ɗaya tilo.

Ahmad baida masaniya akan asalin abinda ya faru, kawai de yasan ya kirawa wayar Abdul ɗin wajajen shaɗaya na dare, lokacin yana jin barci sosai ya tambaye shi ko sun kusa dawowa, sai yace.
   "Anya kuwa gamunan dai ana ƙara musu ruwa, jikin Maryam ɗinne sai a hankali ammadai sunce za'a sallame mu yau, ni kaina nafi so mu dawo gida wallahi agajiye nike sosai."  daga wannan maganar bai sake jin sautin muryar Abdul ba.

Washe gari.....✍🏻

MARYAM STAR CE.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.