Free chapter · Read without an account
Chapter 28
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 28.
A washe gari lokacin da Ahmad yayo alwala ya buɗe gida da zummar zai fita masallaci sallar asubahi, turus ya tsaya jinin jikin shi na ƙafewa lokacin da idonshi ya sauka cikin hasken daya haskake unguwar sanadiyyar security light ɗin da Abdul ya saka a kusa da gidan shi.
Idon shi ya lumshe da wannan baƙar kalar da yake gani, kan shi ya sara cike da tsoron abinda kwanyar shi ke ƙoƙarin hasasowa.
"Innalillahi Daddynah kalla kaga gidan Abba wuta ce ko?." yaron shi Mujaheed daya biyo bayan shi ya faɗa.
Yana kyautata zaton maganar Mujaheed ce ta saka Halima fitowa, ba tare data saniba ashe Zunaina ta biyo bayanta lokacin ta tashi zata yi sallah itama.
Bin ƙananun ƙafafuwanta da kallon Ahmad yayi lokacin da ta fito tana gudu tana kiran gidansu da mahaifanta, babu ƙarfi sam a jikinsa dan ko motsi ya gagara yi Mujaheed ne yabi bayanta tare da riƙota duda irin tirjiyar da take yi tana ihun kuka....
A cikin hasken da yarin yayi tar Ahmad ke ganin gawarwakin Abdul da Zulaika kwance a ƙasa, wuta taci jikinsu amma hakan bai hanasu gane yankar dake jikunansu ba, ƙanƙame aka cirosu daga cikin wutar saide kuma babu gawar Maryam kamar yanda akaga tasu gawar, sai akabarshi wataƙila wuta ta cinyeta ƙurmus.
A can ƙasan zuciyar Ahmad bai yarda da hakanba, yasan Abduk nada ƙarfin hali ba kuma zai taɓa bari yana kallo da rayuwarshi wuta ta cinye ƴarshi Maryam ba, koda ace zasu mutu atare zaije inda take domin ya cetota, kamar yanda aka sameshi ƙanƙame da gawar matarshi Zulaika, saide kura rashin tabbas ya saka baice komi akai ba, kuma har lokacin baiyi wata magana ba hasalima daidai da sau ɗaya bai buɗe bakinshi ba, kamar yanda ƙwalla ko ɗaya bata fito daga idon shi ba, amma kuma yana iya jiyowa a gangar jiki da kunnen shi yanda wuta ke ci a zuciyarshi.
Ko bayanda aka kaisu makwancinsu na gaskiya bai iya cewa komi ba, kuma da hannayenshi biyu ya sassaka gawargakinsu a cikin rami ya kuma zama mutum na farko daya fara zuba ƙasa akansu, sannan ya zama mutum na ƙarshe daya fita daga maƙabarytar.
Ko a wajen zaman makoki zaune yake kurum yana bin mutane da ido baya iya amsar gaisuwarsu, hasalima gaisuwar na ƙara rura wutar da ke ci a zuciyarshi ne.
Yana a cikin wannan yanayin har aka yi addu'ar kwana bakwai, kowa ya watse aka daina shimfiɗa tabarma a ƙofar gidan, wasu daga cikin mutane har sun fara daina zancen sai idan antuna.
Daga ranar Ahmad bai sake lafiya ba, jinya yayi a asibiti bata wasa ba, jinyar da saida ta lashe dukanin abin da ya mallaka na dukiya, kafin aka samo kan shi dan saida aka haɗa da nemo rance.
Lokacin da ya tashi daga wannan jinyar bayada komi, a likacinne kuma komi ya sauya, sauyin da yakai rayuwarshi matakinda bai taɓa hangowa kan shi ba, hasalima baya saka rai a kurkusa baiƙiba idan aka ce nan gaba lokacin ya tara iyali sun girma sun tsaya da ƙafafuwansu.
Mafarin komi ya kasance ne daga ranar da Ahmad ya fara fitowa ƙofar gidan shi da aka aika ana sallama da shi.
"Assalamu alaika ya Ahmad."
Fari tas ɗin bayuren ya faɗa da murmushi kwance akan fuskar shi.
Haka ya gaisa sama-sama da shi da sauran baƙaƙen fata su biyu dake tare da shi.
Sosai ya buɗe kunnuwan shi yana sauraren bayanin da suke ma shi wanda ke shiga can cikin zuciyar shi kai tsaye yana sakar mashi da wani tunani daya kasa hana kan shi yi.
"Munzo ne daga compnyn Star gold inda akayi cinikin gold watanni biyu kenan aka kuma biya kuɗi akan za'azo a ranar a amsa, amma kuma shiru ba'azo ba, muɗan jira bayan lokaci nan shiru, sai muka yanke shawarar zuwa dakanmu mu kawo, amma da mukazo bayan munbi address sai muka samu labarin me siyen Alhaji Abdullahi ya rasu, shine muka nemi bayanan wanda ya wakilta wato kai amma sai muka samu bakanan kana jinya, yanzu dai muna so kazo muje can company ka saka hannu sai ka amsa shi kuma Allah ya gafarta mashi da rahama."
Haka suka ɗunguma zuwa company, wanda ya zama sanadiyar canza rayuwar Ahmad dama tafarkin da yake a kai.
Tun lokacin daya riƙe recipt ɗin gold da aga buga stam da sunan company yaga zunzurun kuli masu darajar da Abdul ya zuba wajen mallakar wannan me ƙololuwar darajar gold ɗin, lissafinsa ya kwace, tunanin yanda aka yi yana zaune Abdul ya mallaki wannan makuɗan kuɗaɗen suka soma dawowa ma shi.
"Baka da maida hankali ai kai, karka manta tun kana makaranta kana maida kanka baya, bayanda har wanda ke bayanka ya zo harma ya nemi wuceka, ina son ka tsaya kamar yanda nike bawai alfahari da kai ba niɗin inada maida hankali."
Sune maganganun da Abdul ke yawan maimaitawa idan wani abu nacigaba yazo, shi Ahmad yayi wasarairai da abin.
"Ba zaka gane lissafin bane, du abin da kaga na yi inada dalilina na yi, kuma du abinda kaga na bari shima inada dalilina na barin kaide kawai Allah ya datar datar da mu."
Ita ce amsar da Ahmad kan bawa Abdul a yawancin lokuta, yana ganin wahalhalun tarin aiyuka mabanbanta da Abdul ɗin ke yi bazasy barshi yayiwa kanshi abin kirkiba, komi Abdul ya hango zaiyi ƙoƙari su tunkari abun a tare, amma sam Ahmad baya bashi goyon baya saide yaje shi kaɗai yana tunanin sanar daya riƙe zata ishe shi yayi komi da yake son yi.
Ko bayan da Ahmad ya koma gida ya zauna agaban Halima ya buɗe gold ɗin saida ta razana da ganin shi, daya nuba mata recept ɗin kuwa saida tai suman wucin gadi, ta gagara furta koda kalma.
A kuma wannan ranar ne ya shiga tattaro du wasu takardu dayasan mallakin Abdul ne daya bashi ajiya, ya soma bincike akai, a ranar bai iya rintsawa ba sai da ya gama tsarawa kanshi canjin rayuwa.
Kamar yanda matar shi Halima itama ta gagara runtsawa, wani tsohon miki daya jima da ƙamewa a zuciyarta ya raunata ya dawo ɗanye juyi kawai take ido a rufe.
Daga wannan rana Ahmad ya tashi daga zallar sunan shi Ahmad ya koma Alhaji Ahmad, ya tashi daga unguwar tare da gina tamfatsetsen gida ya sayi miyoci ya tattare takardu masu yawan gaske da Ahmad ya bashi yaci gaba da more rayuwar shi, ya manta da wani Abdul ya shafe babin shi a rayuwa yaci gaba da wadaƙa da dukiyar da baisan baƙar wahalar da mamallakinta yasha wajen tarata ba, ya wancakalar da wannan yardar da Abdul yayi ma shi wacce ta saka shi bashi amanar dukiyarsa.
****
CIGABAN LABARI.
Hawayene kamar da bakin ƙwarya suka ɓallewa Alhaji Ahmad asanda yazo nan a tunanin shi, zuciyar shi ta ƙuntata danasani me girman gaske ya lulluɓe shi.
Daƙyar ya iya tashi ya kulle gidan bayan ya ɗauki jakar daya gama haɗa takardun ciki.
Kafe kangon jinin da ke gaba kaɗan da gidan shi yayi da ido memories ɗin daya gudana tsakanin shi da mamallakin gidan na dawo ma shi tar a ido yana jin zuciyar shi na ƙuna akan abinda ya aikatawa ɗan uwa kuma aminin shi.
Ido a rufe ya faɗa motar shi dake fake a wajen yana fizgeta da ƙarfi har tayoyin na cin ƙasa suna tada ƙura ya fice a 360.
Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya saboda gudun daya sharara ya wuce ƙima.
Duda bai cikin cikakkiyar nutsuwar shi saida yayi mamakin ganin babu motoci har biyu a parking space, hakanne ya tilasta ma shi kunna wayar shi ya duba time, ƙarfe 11:40pm na dare, da mamaki ya kalli Idi driver dake yi mashi barka da dawowa sannan ya ce.
"Idria lafiya naga babu motocin gidan?."
Cike da kadabi yace.
"Ranka ya daɗe ɗazu da marice ne Alhaji ƙarami ya fita to ashe Hajiya bata saniba shine wajajen ƙarfw goma ta fito tana tambayarmu ko mun gan shi nan muka sanar mata ya fita, yanzu dai sun fita nemo shi ita da Malam yahaya."
Wani ƙulu-ƙulun takaicine ya kume Alhaji Ahamad ya doka tsoki cike da takaicin Mommah ya soma faɗa.
"Shi Mujaheed ɗin yaro ƙarami ne da zata fita neman shi cikin wannan dare, na rasa miya shiga ƙwaƙwalwar kanta da take wannan shirmen na banza da wofi."
Ya faɗa yana lalubo wayar shi ya kamo lambarta ya danna mata kira.
"Na shiga uku Daddy wallahi ina cikin tashin hankali Mujaheed ɗina ya..."
"Idan kika wuce mintuna goma baki dawo gida ba karki kuskura ki sake takomin cikin gida ki san inda dare yai maki tunda ke shashasha ce bakida tunani sam, shi Mujaheed ɗin Afnan ne ko jinjirin goye?."
Ya faɗa cikin katseta daga maganar data soma yi, ya wuce cikin gida ran shi na daɗa ɓaci.
Nan ma wani ɓacin ran ya tarar ta kulle ƙofa ta key ga kukan Afnan yana jiyowa ta ciki.
Rintse idon shi yayi da ƙarfi yana ƙoƙarin tausar kan shi kada ya sauke ɓacin ran da yake ciki akan Mommah.
"Na shiga uku ni Halima wannan wace iri ɓaƙar rayuwa ce, kamar dai wacce ta zagi sama daga wannan sai wancan daga uban har ɗan suna so mayar dani ƙwallo sai buga ni suke san ransu."
Mommah ta faɗa cikin muryar kuka sai kuma ta zabura tare da faɗin.
"Na shiga uku Yahaya dan girman Allah taimakeni mu juya gida wallahi Alhaji minti goma ya bani inkoma."
Yahaya daya soma gajiya dama kuma yana kusa sa unguwar sai ya saki murmushi yana jin yanzunne daidai lokacin daya dace ya rama abinda tai ma shi yau.
Rage gudu yayi yacigaba da tafiya a slow tare da kunna karatun ƙur'ani yaci gaba da tafiya kamae mejin kashi.
(Hhhhhh da alama yau ta gama ƙarewa Mommah wannan wuta haka, gadai shalele Mujaheed ya tsere ga kuma Alhaji ya ƙirga maki mintuna a gefe kuma da driver dake ƙule da ke, sai muce Allah yasa ki wanye lafiya."
*****
JUNAID
Da ƙyar ya iya tada motar ya soma tuƙawa a slow yana fatan ya iya kai kan shi gida saboda azaba ciwon da kan shi ke yi.
Ba tare da sanin shi wata ƙaddarar na gab da aukuwa wacce bai isa ya tsere mata ba, kusan rayuwarshi ta rana ra tafiya tare da cakuɗuwa ne da wannan ƙaddarar dake zamab jiran cikar lokacin wanzuwarta.
A daidai round about lamarin da bai tsara faruwar shi ba a yinin ranar ya auku.
Da wani irin azama ya take burkin motar tare da yunƙurawa ya fito jikinshi na makyarkyata, fatan shi ɗaya ace bata mutu ba kamar yanda yaga jini yayo tsalle daga bakinta daidai sanda hancin motarshi ya daketa....✍🏻
TOHWA WACCE ƘADDARA CE KUMA KE BIBIYAR RAYUWAR JUNAID HAKA.
Kuci gaba da kasancewa tare da ni domin jin yanda zata kaya, karku manta ku taya ni share mutanen arziƙi ina matuƙar godiya.
MARYAM STAR CE