Free chapter · Read without an account

BABI NA BIYU

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 


KAMAR YADDA Zaid ya amsa min da eh har guda biyu akan aure na, haka yazo ya faru. Dangin shi sun taho har Kaduna sun nema mishi aure na kuma mahaifina ya yarda ya basu aure na bayan yayi binciken Zaid da mahaifansa domin ya san inda ze kai yarinyar shi kwara ɗaya da Allah ya bashi. Ina jin lokacin da Abba ya shigo cikin gida a ranar da aka taho neman auren, yana tambayar mahaifiyya ta sun tambaya ko za'a iya ɗaura aure?
“Me ze hana a ɗaura auren? Su ma an saukake musu wahalar ai tunda ba anan garin suke ba”
Nan take idanuna suka cika da hawayen da ban san dasu ba. “Haka kika ga yafi? Ko dai a jira asa rana?”
“Indai shawara ta kake nema akan wannan zancen, to kawai a ɗaura. Me ake jira?”
“To shikenan. Bari na tafi”
Fita daga cikin gida Abba yayi ya wuce. Nasan tunda Umma ta yarda da a ɗaura auren nan, nasan za'a ɗaura. Sauran hawayen da nake ji a idanuna nayi sauri ina son kar su zubo amma na kasa tsaida su. 
Bayan an gama ɗaura aure na da Zaid, Abba ya shigo cikin gida ya bani sadaki na Naira dubu ɗari biyu yana kuma maganar na shirya sun ce zasu wuce tare dani. Tsaye nayi ina kallon Abba saboda mamaki da irin haushin da nake ji.
   “Wane irin ta shirya kuma Yaya? An ɗaura aure da zuwa nema kuma yanzu ana cewa ta shirya? Ta ya zata shirya cikin ƙanƙanin lokaci?” Gwaggo na ta faɗa 
   “To me zata jira Maryam bayan an ɗaura mata aure? Jiran me zata tsaya yi bayan ta bi mijinta? Hakan ba ma yafi mata ba?”
  “A'a dan Allah. Auren nan da ake ɗaurawa daga zuwa nema ba haka ake yin shi ba. Idan aka ɗaura aure se bayan wani lokaci, wasu har kusan shekara ɗaya suna yi kafin ake tarewa”
Da mamaki Abba yake kallon ta yace “Shekara ɗaya Maryam? Ayi aure amma se bayan shekara ɗaya a tare a gidan miji? To menene amfanin shi auren Maryam?”
  “Eh nasan Hadiza ba zata yi shekara ɗaya ba kafin ta tare. Amma a bari har ta shirya tukuna ayi maganar tarewa. Kaga ko kayan da take so bata gama haɗawa ba kuma akwai wanda zata bada. Kuma fa kar ka manta aiki take yi”
   “Ban gane ba, Maryam. Akan aiki se taƙi zuwa garin mijinta? Dan Allah ki dena magana irin haka”
Gyara mayafin ta Gwaggo Maryam tayi tace “Yaya, a jira Hadiza dan Allah”
Shiru Abba yayi yana nazari shima yana gane abinda Maryam ke magana akai “Shikenan zan musu magana a bari har wani sati”
   "Yawwa, daidai ta gama gyarawa”

Gwaggo Maryam ta ja hannuna muka shiga ɗaki na. Bani da wani wanda zanyi kuka ya gane abinda nake ji se ita se na fara yikukan da ban gama sanin dalilin yin shi ba. Rungume ni tayi a jikin ta tana rarrashi na ba tare da tace wani abu ba. Nasan Gwaggo Maryam tana ƙauna ta kuma tana iya gane halin da nake ciki. 
Idanuna har sun chanja kala ciwon kai na kokarin mamaye ni. Gwaggo Maryam tace “Kukan ya isa mana Hadiza. Se kinyi haƙuri, ba komai ne yake zuwan maka a yanda kake so a duniyar nan ba. Haƙuri zaki yi. Kar ki wani damu kanki zan dawo na taya ki duk shiryawar da zaki yi na zuwa Abuja. Kar ma ki damu ai dani za'a je kai amarya. Ki dena kuka. 

DUK KWANAKIN da nayi a gida da auren Zaid, a ko wace rana yana kirana muyi Barka da kwana wa juna. Ba so nake ba amma babu yanda zanyi saboda bana so ya gano bana wani jin shi a raina haka dai na haƙura na aure shi. Yana jana hira sosai yana so yasan abinda yake faruwa a cikin rayuwa ta amma bana sanar dashi komai se de na amsa da eh ko a'a. Duk haka baya gajiya kuma baya nuna min ɓacin ran shi. 
A ranar juma'a daga filin jirgi na Kaduna muka sauka filin jirgi na Nnamdi Azikiwe Int'l Airport dake chan Abuja. 

Abuja tana da wani irin yalwa da kuma natsuwa ba irin sauran wasu garuruwa da suke da hayaniya ba. Mutanen cikin ta basu yi kama da wanda suke yin gaggawa ga abubuwa ba. Tituna masu kyau da manyan motoci suna yawo akai. Kowa yana yin abinda ya shafe shi a rayuwa ba tare da kulawa ko kuma nuna ɓacin rai ga abinda wani yake yi ba. Kowa rayuwar shi yake yanda yake so. 
A gidansu, da yake babban gida me shukoki a ko ina da alamun yawalcen ruwan da yake ɗauke dashi, muka isa. Fuska ta a rufe take amma ina iya gano irin waɗannan abubuwan saboda greenery da nake ji da kuma alamun ruwa a ƙasan interlock ɗin su. A wani babban parlour aka mana iso me ɗauke da ƙamshin turaren Sandal Flakes wanda ya sanya naji sanyi da natsuwa a tattare dani. Duk irin natsuwar da nake ji be hana naji zuciya ta na duka ba saboda nasan wannan gidansu Muhammad Liman ne. Matar dake ciki muka gaida da Gwaggo Maryam da ta rako ni ɗakina. Amsa mana tayi cikin murna da nuna farin ciki tana mana ya gajiya. Ta kuma taso ta yaye mayafin dake rufe da fuska ta. Saukar da idanuna nayi a ƙasa sosai bana son ta ganni. Murmushi tayi tace “Amaryar Zaid me kunya. Gashi shi fa bashi da kunya.” Murmushi Gwaggo tayi se kuma aka bani ɗaki na zauna a ciki kafin anjima akai ni gidan Zaid. 
Wuraren ƙarfe uku akayi knocking a ɗakin kuma aka shigo. Cikina har ya ɗau ɗuri azatona Zaid ne se naga mace, me haske ba dayawa ba, fatar ta kamar caramel irin na Zaid amma ita nata da haske sosai. Saukar da idanuna nayi da sauri ina kallon dogayen yatsun hannuwana. 
  “Assalamu Alaikum, amaryar Zaid. Na shigo inda kike ba tare da izini ba. Kin san amarya tana da farin jini sosai. To ya tafiyar ku? Kun zo lafiya?”
  "Alhamdulillah” na amsa ta cikin girmamawa daga gani zata girme ni a shekaru.
   “Yayar Zaid ce, Hauwa. Hala ko kinji labari na daga wurin shi ban sani ba” ta sanar dani 
 Murmushi nayi wanda take iya ji na ɗan ɗago kai na kalle ta kuma na sauke. Tana da kyau irin kyawun da ake cewa mutum yana dashi “Eh Zaid yana maganar ki”
    “Ma sha Allah, ki huta lafiya anjima zaki tafi ɗakin ki. Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a nagari” ta mana addu'a kuma ban ce komai ba se murmushi da nayi. 
Fita tayi daga ɗakin ganin ban sake sosai ba. Ta ya za'a yi na sake a gidan nan?
Bayan ta fita se kuma ga wata ta sake shigowa. Ta faɗa min sunan ta Shahida kuma itace auta a cikin gidan. Ta faɗa min ita student ce a University of Abuja tana karatun Bsc. Nursing. Ta kuma ce tana makaranta shiyasa bamu haɗu ba da zuwa na se yanzu. Ta ɗan jima muna magana da juna kafin itama ta fita daga gidan. 
Babu abinda nake tunani se haɗuwa da Muhammad. Ban ga wani matsala ko kuma nuna alamun na girma Zaid a gidansu ba. Se nayi tunanin ya dai faɗa musu kuma abin be dame su ba ko kuma be ce komai ba akan tazarar shekaru biyu na haihuwa dake tsakaninmu. 

Ina nan zaune, Gwaggo na tana shigowa ganina akai akai har ƙarfe takwas tayi ina jin dad'i Zaid be shigo ba. Wata shiryawa na ƙara yi daban za'a kai ni gidan Zaid. Bayan an gama shirya ni cikin riga da skirt na atamfa da mayafi wanda ya rufe fuska ta, aka kai ni wani parlour daban wanda nake tunanin na mahaifin su ne saboda yanda naji presence na wasu maza. Zama nayi a ƙasan carpet na gaida wanda na zauna daura dashi wanda nake tunanin shine mahaifin Zaid. Amsawa yayi cikin wani irin yanayi da zaka iya jin farin cikin shi. Magana ya fara wanda yake kama da nasihar aure. 
   “Zaid bashi da matsala nasani” naji muryar Muhammad Liman. Da farko ji nayi kaman na gudu se kuma na daidaita kaina. Nasan ko ban buɗe duka mayafi na ba, watakila Muhammad ze iya gane ko wace. 
   "Nasan ko ƴa ta bata da wani matsala. Allah ya basu zaman lafiya” Abban su ya ƙara cewa 
    “Dukan mu bamu da matsala Abba. Amin ya Allah” naji muryar Zaid yace ba tare da na lura da yana wurin ba.
    “Kinga dama na faɗa miki wannan mijin naki bashi da kunya kuma gashi ya nuna a wurin Abba” muryar matar ɗazu naji wacce ke nuna alaman itace mahaifiyar su se suka sa dariya. 

Anan ne kuma na haɗu da ƙaninsu wanda yace min sunan shi Khalifa ya kuma faɗa min student ne a University of Abuja yana karatun Software Engineering. 
Ɗazun ma da ina ɗaki wata yarinya ta shigo a ɗakin da nake zuwa kwasan kwanuka. Na ɗauka itama yar gidan ce naji ta gaishe ni da aunty amma kuma da na maida hankali na se na gano yana yiwuwa yar aikinsu ce. 

Bayan an gama duk abinda ake muka wuce gidan Zaid tare dani dashi kaɗai. Gobe Gwaggo Maryam zata shigo sannan kuma ta koma gida Kaduna. 
Yana tuƙin mota bamu cewa juna komai ba. Ya tsaya ya siya nama da yoghurt da babban five alive. 

Gida ne babba madaidaici wanda yake isar fiye da mutum biyu na ma'aurata zama a ciki. Shima shukoki ne dashi masu yawan gaske na daga mabanbantan kaloli. Naga har ɗawisu a cikin gidan guda uku masu kyau da kuma girma. A cikin parlour wani carpet ne me laushi akai haɗi da kyau me kallon birgewa. Hannuwana biyu na rufe tare da juna na zauna a kujera ash da sauran kujerun ciki suma ash. A cikin parlourn akwai wasu ice guda biyu na artificial plant wanda ya ƙara ƙayata shi. 
   “This is your home, Hadiza. You should get up and take a look at the kitchen and the bedrooms and everywhere else. Duk abinda be miki ba se ki faɗa za'a chanja” Zaid yace yana kallo na.
Kallon shi nake ban ce komai ba ko gyaɗa kai na kasa yi. Yana nufin idan ma wuri be min ba, nayi magana za'a chanja. To kuma rashin hankalin da nake ɗauke dashi be kai har haka ba. 
     "Kinji?" Yace, bayan yaji nayi shiru 
Gyaɗa mishi kai nayi dryly inaso na tafi na kwanta duk da babu gajiya a ciki na. “Ina zanyi bacci? Ina jin bacci” na sanar dashi tare da tashi tsaye na taho kusa dashi ina ƙara ganin yanda tsawon shi yake. He's tall and looks extremely healthy a jiki da alama yayi workout wani lokaci na rayuwar shi. Wannan caramel skin ɗin shi da nasani yana ƙara fitowa. Sajen fuskar shi gyararre har yanzu yana da irin ko ma fiye da kyawun da na san shi dashi a chan makaranta. 
   “Let me show you to our room“ haka naji ya faɗa. Ba ɗaki na ba, ɗakin mu. Ban ce komai ba se bin shi dana yi sanin be yi kuskure ba da yace ɗakin mu tunda mu yanzu ma'aurata ne dole muna kwana a ɗaki ɗaya. 

A ɗakin, gadon dake ciki babba ne jikin shi fari amma chan kan gadon yana da kwaliiya na kalar ash kamar irin kujerun mu. A gaban gadon, da akwai wani rug me laushi sosai. Ɗakin yana da duhu amma ba duhun da za'a ce ba za'a iya gani ba saboda bedside lamps ɗin shi a kunne suke. Wardrobe dake ciki babba me kyau har cikin ɗakin da akwai artificial plant wanda ya ƙara bani sha'awa a cikin ɗakin. 
Zaid ya juyo gare ni yace “Muyi sallah kafin kiyi bacci ko?”
Tsayawa nayi ina nazari ko nace mishi bana yi amma kuma nace “Shikenan, muyi sallah.”
Banɗaki na shiga na ɗauro alwala tukunna na fito. Dama ɗazu Gwaggo ta taho ta jera min kayana se na duba wardrobe. Hijab na ɗauko na zauna ina jiran shi ya fito mu yi sallah. Be jima ba ya fito ya ja mu muka yi Sallah. Bayan mun gama yayi addu'o'i ina amsawa da amin saboda ya zama wajibi a gare ni. 
   “Ba zaki ci komai ba zaki kwanta, Hadiza?”
      “A'a na koshi. Naci abinci a gida”
Gyaɗa kai yayi ya fita daga ɗakin na ajiye wata irin ajiyar zuciya tukuna na tashi na shiga banɗaki nayi wani wanka nasa wata rigar bacci me kaiwa har ƙasa na. Se bayan har na kwanta akan gadon, nasan bacci ba yanzu ba, amma idanuna na rufe, naji alaman an kwanta akan gadon. Ban buɗe idanuna ba saboda bana son wata magana ta haɗa ni dashi. Shima be ce min komai ba kuma bana tunanin yayi bacci.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.