Free chapter · Read without an account
Chapter 30
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 30.
Kuma koda Sanata ya kama hannun shi suka shiga cikin gidan,sam hankalin shi bai kwanta ba wannan ɗaurin kuɗaɗen daya gani sababbi dal sai gizo suke yi ma shi a ido.
"Minene matsalarka da sauran mutane ba iya yau ba a kullum idan muka je wajen malam ina ganinka ware kana rayuwa kai kaɗai bakada abokai ne?."
Sanata ya jefa ma shi tambayar lokacin da Audu ya gama lashe kwanon abincin da aka dire ma shi.
Kallon shi yayi da jajayen idanuwansa sannan yace babu alamar shakka ko tsoro.
"Ni bana rayuwa cikin mutane, ni kaɗai nike rayuwa muna faɗa ne du sanda zan zauna cikin su ko tare da almajirai ƴan uwana."
Ya faɗa yana kaiwa ayabar gaban Sanata cafka ya ɓare bayan ya cinyeta yana jin tsakinta na ratsa bakin shi.
"Amma mi yasa haka suna kyamatar halittarka ne?." Sanata ya faɗa yana girmama zubin halittar Audu sam baida kyau ko kaɗan fuskarnan kamar ta birai ga jajayen idanuwa kuma manya.
Tsare shi da ido Audu yayi maganganun shi na taso ma shi da wani miki wanda ya jima da binnewa a ran shi.
"Ba iya halittata ba hatta da zuciyata baƙaƙirin take, bani da kyau ciki da bai du yanayin da kake kallon fuskata to a yanayin zuciyata ta ke."
Wani makirin murmushi Sanata ya saki yana ƙarewa baƙin fuskar Audu kallo yana hasaso duhun da zuciyar shi take da.
Daga wannan rana akuma wannan lokacin rayuwar Audu ta sauya ta sanadiyyar Sanata, wanda ya canza ma shi rayuwa da wata manufa da buri.
Gadan-gadan Audu wanda ya koma Abdullahi ya fara bangar siyasa, shine sara da suka, shine kunna speaker da karaɗe unguwa yana cashewa ya kuma tara yara suyita hayaniya suna rawa, cikin shekaru biyar ya zama cikakken tantarin marar kunya baya tsoron kowa bakuma ya shakkar kowa, har kuma wannan lokacin bai daina halin shi na sace-sace ba inde ya gani tofa sai ya ɗauko sai de du abin da zai faru ya faru, kuma idan akai jajaye kai tsaye yake cewa yana so shiyasa ya ɗauka babu kwana-kwana bare jin kunya da zarar mutum kuma ya yunƙura da niyyar magana ko faɗa zai kafe shi da mayun idanuwansa tare da zaro wuƙar shi daga wando yana jiran akawo farmaki ya farke mutum.
A WATA RANA.
A wata rana bayan cikar shekarun samartakar Abdullahi wanda zuwa lokacin muni da ƙirar shi ta Samudawa ta kuma haɓɓaka domin kuwa lokaci ɗuda ya kowa wani irin narkeke shirgegen ƙato me ban tsoro, ya zama abin da Sanator ke so wanda kallon shi kaɗai yana saka ma shi alfahari.
Dafa kafaɗun shi Sanator yayi wanda a lokaci ya sauya muƙamin daga Sanator zuwa Dupety Governor saboda ƙwarewar shi a kutsa kai a siyasa, komi zaka same shi a ciki indai ya shafi siyasa.
Cike da alfahari ya dafa kafaɗun Abdullahi tare da faɗin.
"Wanene Audu a baya, sannan kuma wanene Abdullahi a yanzu??."
Sai da Abdullahi ya saki wata arniyar dariya sannan ya ce.
"Audu a baya wani raunanen Almajiri ne wanda ya taso a gidan marayu cike da tsana, ƙyara, da tsangwama a cikin yara ƴan uwan shi, yaro ne da ake kallon munin fuskar shi a yanke ma shi hukunci akan abin da bai aikata ba, yayinda daga baya kuma ya kangare ya soma aikafa ɓarnar da ake dangantata da shi sai tsanarsa ta linku a idanuwan al'umma ya zamana abin ƙyama na ƙarshe wanda ake damganta muninsa da munin zuciyarsa.
Abdallah a yanzu kuma wani matashin sardidin ne da ake damawa da shi a sabgar rashin ji wanda yayi suna ya kuma yi fice wajen cika aikin da yasaka a gaba, baya shayi baya shakkar kowa yana rayuwar shi cike da ƴanci wanda riƙe makami da kuma tantirancin shi ne sular samun zaman lafiyar shi."
Ya faɗa yana murmushin da ke ƙarawa munin shi muni.
"Da kyau Audu Abdullahi Mafakan ƴan siyaya, ko ince Makafa na domin kuwa da kai nike tinkaho ina fakewa a bayanka, yanzu rayuwarka zata ƙare sauyawa, yanzun tsoronka da iko zasu sake tunbatsa a idon al'umma da zuciyoyinsu shin zaka amshi tayin da zanyi maka da hannu bibiyu kamar yanda na saba yi maka tayi akan sauyin rayuwa, ka shirya zama shaharare maɗaukaki da al'uma zasu yi alhafari da kai??.
Kallon shi Abdullahi yayi tare da faɗin.
"Aini ko iya haka rayuwata ta tsaya na cimma nasara, ba dole sai na tara kuɗaɗe ba kuma ba dole sai mutane sun soni ba, ni nafi so suci gaba da nuna min ƙiyayya tare da ƙyamatar halittata, ni kuma in saka ƙarfi in ƙwaci du wani abu da nike da buƙaya a wajensu oga Ƙwaro."
Ya faɗa yana murmushi.
"Baka fahimce ni ba, shin baka son ace kana sama da kowa baka so ace kai ke juya kowa da kowa, ko baka so ace yau kaine me kuɗin da babu kamarka, baka son ka mulki al'umar da suka kasance ƙalubale agareka?."
"A gaskiya bani da wannan ra'ayi iya wannan rayuwar da nike gudanarwa ta ishe ni oga Kwaro."
Sosai Ƙwaro ya fusata da wannan maganar ta Makafanshi amma bai nuna ba a fuska, sai de a zuciyar shi ya ƙuduri aniyar aiwatar da abin da ke ran shi, domin kuwa ƙiri-ƙiri Makafa ke neman jaza ma shi asara.
A tsakiyar daren wannan ranar Abdullahi ya tashi idon shi cike da barci, ya soma yana sauraren kiran da ake yi ma shi da wata iriyar murya me firgitarwa, kasancewar sam baya da tsoro ko shakka ya saka shi laluben lafceciyar addar shi ya buɗe ɗakin shi tare da hayewa can sama inda yake jin sautin kiran na tashi.
Su uku ne sanye cikin baƙa ƙirin ɗin shiga, Mansur Ashiru (Ƙwaro), sai kuma Alhaji Laminu da kuwa Aminu Dutsi manyan mutanen da suka kasance masu mulkar ƙasa a lokacin, su Abdullahi ya gani suna zagaye wata jar tsoka me kama da zuciya hannayensu riƙe da sarƙoƙi baƙaƙe suna wulwulawa tare da jefawa asaman zuciyar bakunansu na furta wasu kalamai daya zaga gane ko mi suke faɗa, Amma dai yana iya jin haruffan sunan shi a ciki.
Sakin addar ya yi tare da duƙewa ya tallabe zuciyar shi, jini ya soma tsartuwa daga bakin shi kafin daga bisani ya soma yo amai wanda ke cike da wasu abubuwa marasa kyawun gani, nan ya kwanta a wajen mina-mina cikin ficewar hayyaci yana jin wata irinar mummunar azaba a ƙirjin shi kafin daga bisani komi nashi ya tsaya cak ya tafi doguwar suma me tsayi wacce ta ɗauke shi tsayin kwanaki masu yawa bai farko ba.
Wannan kenan.
A ranar wata alhamis Abdallah ya buɗe idanuwan shi da suka sake komawa jajaye abin tsoro, kan shi yayi ma shi nauyi ba irin na ciwo ba nauyi irin na wanda wani sabon wabu wanda yafi ƙarfin shi ya baibaye shi.
Babban abin da yafi bawa Abdullahi tsoro bai wuce yanda daga inda yake ba yake isa hango wasu abubuwa kamar irin abubuwan da ke faruwa a waje, sannan kuma yana ganin wasu abubuwan da abaya baya iya gani a tare da mutane, ga wata hayaniya da aka soma yi ma shi me ƙoƙarin tarwatsa kan shi ya kuma rasa daga inda take fitowa, sai kawai ya dafe kunnuwan shi tare da fasa razananniyar ƙara a maimakon ya ambaci sunan Allah.
Ƙwaro ne ya bayyana a gaban shi cikin abin da bai wuce daƙiƙa biyu ba, abin da ya kuma firgitar da Abdullahi kenan domin yana jin hucin shi ya ɗaga kai tare da kallon shi sai yanayin da Ƙwaro ya shigo ta hanyar biyo bango ya bayyana a idon Abdallah yanayin daya sake ɗimauta shi kenan.
Dafa kan shi kawai Ƙwaro yayi tare da furta wasu kalmomi nan take komi na Abdullahi ya tsaya tsak ciki kuwa harda numfashinsa.
Samun kan shi yayi da bin bayan Ƙwaro suka fice daga ɗakin asibitin ta cikin bango suka bi iskar wajen suka ɓace bat basu bayyana ako ina ba sai a cikin gidan Ƙwaro a cikin main parlor inda su Aminu Dutse ke zazzaune gaban su cups ne da aka cike da wani jan abu.
Zaunawa Ƙwaro yayi tare da furta wasu kalamai nan take Abdullahi ya dawo cikin hayyacin shi, wannan yahaniyar da ihu suka dawo.
Yunƙurawa yayi da azama tare da kaiwa cups ɗin wawaso, saide kuma Ƙwaro ya hana shi isa garesu yana sakin murmushin samun nasara ya kalli su Aminu da suma suke sakin murmushi.
"A'a please ina da buƙata zan iya mutuwa idan baka bani ba." Abdullahi ya faɗa yana jan numfashi a wahale.
Ta shi Ƙwaro ya yi tare da soma zagaye shi yana faɗin.
"Ba iya na yau ba na kullum ma zan dinga baka idan kayi alƙawarin bin dukanin umarnina."
A wahale ya ce, "Na ɗaukar maka alƙawarin zama bayanka zanbi dukanin umarni da tsarinka."
Wata arniyar dariya Ƙwaro ya saki sannan yace, "Kace kai shege ne da yaro kenan baka san wuta ba sai ka taka."
Abdullahi kamar zai zauce haka yake ji kafin Ƙwaro ya bashi jinin ya sha, sanda kuwa ya miƙa ma shi ɗaya daga cikin kufunan dake aji, jikin shi na mazari ya amsa tare da kafa kai ya soma kwankwaɗa, wanda bai saniba hakan na tare da shiryayyar ƙaddarar da aka cakuɗa da manufa da son zuciya haɗe da zalunci, ya shnaye kofi ɗaya aka ƙara ma shi ɗaya ya zamana biyu kenan aka kuma ƙara ma shi wani ɗayan yasha na uku sannan yayi zaman daɓaro tare da soma sauke ajiyar zuciya a wahale.
"Abdulllahi ina son kaje ka samo min jinjiran yara sababin haihuwa guda uku sannan ka ciro min zuciyar yara biyu da idon tsoho ɗaya."
Ƙwaro ya faɗi cikin bada umarni, a wani irin zabure Abdullahi ya miƙe tsaye abin mamaki a maimakon ya miƙe akan ƙafafuwan shi sai ya miƙe akan iska lokacin daya yunƙura da zummar yakawa sai kawai ya ɓace a cikin isakar.
"Wow amma nayi mamaki yanda aikin nan yaci cikin sauƙi haka wannan ai shine shafshaf ɗin."
Laminu ya faɗa yana mamaki.
Bushewa da dariya Aminu Dutse yayi tare da faɗin.
"Hummm kana wasa da baƙin tsafin, shin kuwa kassan mi ake nufi da ƊAURIN ZUCI wannan tsafi ne da ake yi a ɗaure zuciyar mutum ta hanyar tsafi sannan a yi yi abin da baya so ta ƙarfin tsiya, du wanda aka ɗaure zuciyar shi da baƙar sarƙar tsafi zai tsinci kan shi a wata rayuwa ta dabban kuma babu wanda ya isa ya dakatar da shi akan dukanin abin da ya saka gaba, makarin wannan baƙin tsafin ɗaya ne rak kuma yanada wahalar gaske hakan yas ake ma shi laƙabi da gagara karaya domin kuwa tsayin shekarun da aka ɗauka ana tsafin har yau ba'a samu wanda ya taɓa karya shi, hasalima a littafin sirrin tsafi an ruwaito bazai taɓa karyewa ba har abada sai idan wasu mutane masu kamanceceniyar ƙaddara sun wanzu tare da haɗu zuciyoyinsu waje ɗaya sannan zasu karya wannan tsafi, yayinda duniyar tsafi ta tsunduma laluben waɗanan mutanen domin yin rigakafi tun gabanin wanzuwasu ba zamu taɓa rinsu su rayu ba kamar yanda baƙin tsafi zaici gaba da wanzuwa yana bamu kariya haka muma zamu ci gaba sa kare shi tare da toshe ko wace iriyar ɓaraka."....✍🏻
MARYAM STAR