Free chapter · Read without an account
34
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Under team yota's amazing pen
Page 3️⃣4️⃣
yanzu sun fi shekara 10 da aure amman har lokacin bata samu haihuwa ba sai dai tayi ɓari kusan sau uku
Muneef da Muneefa sun gama school har Muneef ya samu aiki ita kuma Muneefa na taɓa ƴan kasuwancinta agida
Adam da Hafeez sun gama school har Hafeez ya dawo amman shi Adam ya samu aiki a Company ɗin da Uncle Abdallah ke aiki kuma ya auri ƴar wajen shi Jannat
Lokacin Jannat da Adam sun haifi babban ɗansu Umar a lokacin itama Anty Zuhura da itama bata daɗe sosai da auren ba Allah be kawo mijin da wuri ba se yanzu bata ma fi 2 years dayin auren ba ta haifa Usman tsakanin su da Umar baifi 1 year Da ƴan kai ba
Itama lokacin anyi auren Juwaira da Yusuf babban ɗan uncle abdallah,Wanda hakan saida ya kusan haifar da wata fitinar wajen Sahura
"Nifah na lura kaf danginka sun fi jida ƴaƴan Harira taya za'a ce wai komai su, to wallahi bazai yiwu ba ai nima nawa yaran ƴaƴa ne, an yi auren Adam da Jannat bance komai ba dan haka sai dai Yusuf ya auri Muneefa, su kaɗai ne suke son auren masu kudi ai Nima yaran nawa suma mutane ne duk wani abun alkhairi da dangin ka suka dibo sai dai su ƙare akan yaran Harira, wallahi bazai yiwu ba"
Nan Uncle Abdallah ya mata tass harda cewa sai ya ijje manyantar su a gefe ya mata shegen duka dan yaga har yanzu kanta da motsi bata san ta girma ba, kuma shi ba da ƴarta yake son haɗawa ba da Juwaira yake so, in taga bazata Iya ɗauka ba tayi abinda ta saba kar hakan ya yiwu, ko wurin malamai dubu zata je, shi ba irin waɗanda zata kai bane gwara idan zata shiga tatitayin ta ta shiga ko ta gane kuren ta
Tsit tayi jin kamar yasan tana asiri ko kuma ma dai ita ta tsargu, ganin kamar idan ta cigaba da tura abin ita zata zauna ciki yasa tayi shiru, tunda ai bata faɗi ba yaranta har biyu na zaune gidan masu hannu da shuni
dama shi duk irin wannan abun da ke faruwa bai taɓa gani ba saidai a faɗa mai,
itama Juwaira bayan haihuwar Umar baifi watanni ba ta haifi Ahmad, suma a Cairo suke zaune shi yana aiki da wani Company daban but duk branch ne da wanda su Adam suke aiki da shi
Itama dai Shahida ta ɗan samu salama tsakanin ta da dangin mijin nata da harshi ma, tunda Umma da Hajiya Kursum suka je suka bude musu wuta suka ga masifarsu yafi nasu suka shafa mata lafiya
Ita kam Abida kusan shekara uku kenan baajin ta ba wanda yasan inda take saboda idan an je gidan ta na nan Kaduna ba'a samun ta, Mai gadin se yace wai suna Malesiya ita da mijin nata, saidai ko idan ta kira su a waya wanda se a fi wata shida ma ko umman bata nema ba
Shekara ɗaya da zuwan Abida gida bayan ta faɗa musu suna Malesiya ita da mijinta ya dawo da ita gidan su bata da lafiya dan ko iya zama bata yi saidai a kwantar da ita rufda ciki
Ashe mijin nata ɗan luwadi ne, kuma tun bayan zuwan ta gidan tasan da haka amma dayake son abun duniya da yafi na uwarta ya rufe mata ido ta take tunda yana bata maƙuden kudi, tun bata saba ba harta saba
Suna Nigeria Amma ba son kowa yazo yaci daga gare ta ke ba ne yasa tace musu sun bar kasar dan kawai kar wani ya more ta hatta da uwar ta,
Yanzu kuma da cuta ta same ta ta wurin, sai mijin nata ya fara gudun ta, kuma yaƙi yakaita asibiti gudun asirin shi karya tonu, sai dai ya kira likita ya zo gida ya duba ta
Ganin ba sarki sai Allah ya saka tace ya dawo da ita wurin mahaifiyarta tasan ita ba zata guje ta ba
Yana ko dawo da ita gidan su ya ajje ta ya tura mata maƙuden kudi wai akula da ita idan ta warke zai dawo ya ɗauki matar sa
Sanda Sabuwa ta ganta ya sha tofin Allah tsine tayi kuka iya kuka
Suma ƴanuwanta da suka ganta saida suka tausaya mata dan a iya watannin da basu gaza 4 da fara ciwo ba ta mugun lalacewa kamar ba ita bace in tazo take musu kallon basu kai ba tana musu kallon ɗaddaya hatta da ƴanuwan da suke ɗaki ɗaya
Papi ne yace dole sai ya sakar masa ƴa, da farko ƙin yarda yayi saida ya mai barazanar zai sanar da duniya tunda yayi suna, ya bata mai suna tukuna ya amince ya sake ta, daman basu taɓa haihuwa ba,
Saida aka kusan ƙarar da kaf dukiya da ta tara a gidan mijin nata kafin ta warke, koda ta warke aka sanar da ita yanda aka kaya dashi ga mamakin su
Sai ta hau balain daman sun tsane ta shiyasa suka ra bata da mijin ta da kuma daular da take ciki, hassada suke mata saboda tana cikin daula
Itakam Sahura abun yawa ya mata dan har ta fara abu kamar zararriya ko da aka kaita asibiti akace depression da jinin ta da ya hau ne to abune ya haɗe mata goma da ashirin ga Shaheeda yanda take shan wahala a gidan miji dan tun sanda ta bata wani magani ta barbaɗa ma mijin
Aka ka mata yace bazai sake ta ba Amman sai ta gwammaci kida da karatu ga kuma side din Abida
Bayan dawo war Hafeez wani zuwa da yayi gidan Papi lokacin su Adam da Juwaira sun kawo musu ziyara ne yaga Muneefa, da farko Sahura taso ta hana hakan amman ganin shi yanzu ba kamar da ba dan da uwar kudin sa yasa ta amince amma bawai dan tana so ba sai dan kudin da ta lura yana da su, duk da Anty Hadiza bata so ya auri yar gidan Sahura ba amman sanin halin Muneefa yasa ta amince dan a cikin rayayye ana fidda matacce haka zalika cikin matacce ana fidda rayayye
Rayuwa na tafiyar musu daidai komai alhamdulillah,wata mummunar rana tun suka wayi gari take jin gabanta na faɗuwa
Da misalin wajajen laasar wayar ta ta fara ringing numbern Juwaira na Nigeria ke yawo akan screen ɗin, ji tayi kamar karta ɗauka amma ta daure ta ɗauka
"Adda kina gida ne"
"Eh ina gida"
"To ina Kaduna, kuzo gida Yanzu"
"Meya faru da wani Matsala ne"
"A'a ba wata matsala ku dai kuzo"
Kallon Abhie tayi, duk yaji abinda suke faɗa dama shima tun tace mai tana jin gabanta na faduwa yaji shima dai jikin shi yayi sanyi
Wani kiran wayar ne ya ƙara shigowa, tayi mamakin ganin Shahida na kiranta, mutuniyar da idan ba wani abu kwakwara bane bata neman ta
"Innalilahi wa inna ilaihir raju'un!!!! Rukayya Papi ya rasu ɗazu!!..."
follow and like for more update please 🥺🥰
______________________
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***