Free chapter · Read without an account
THE DAY SHE CALLED BLACK
by Saddiqah M · NURI
She had no one da zai bata amsar abinda ke going in her mind, don haka ta ture tunanin gefe tana qarasa abinda ta fara. Bayan ta gama ta koma dakinsu ta zauna tana daukar wayarta data fara gajiya da ita.
"Me kk yi ne awajen?" Mami ta asked her ganin yadda ta shigo dakin tana sauke ajiyar zuciya.
Kai ta girgiza mata tana cewa "bbu komai." Ba dai aiki kika je kika yi ba ke da baki da lafiya? "
"Ba shi nayi ba Mami.." badan ta yadda da ita ba ta rabu da ita tana binta da kallo.........
Nuri bata nunawa Mami damuwar auren nan ba sai bayan sun kwanta bacci ne ta kasa baccin saboda damuwar da take ta dannewa like kawai gani take za tayi rayuwa ita kadai ne babu kowa nata a tare da ita ba. Juyawa side din hagunta tayi ta sauke idonta kan Mami dake bacci tana iya jiyo saukar numfashinta daga inda take tunda katifar nasu dududu ba wata babba ce ba suna maneji ne kawai.
Dan hasken wutar dake waje ya ratso ta window ya haske mata kadan daga fuskar Mamin. Hakan yasa ta kafeta da idanu tana jin kwalla na cika mata idanu. If she could recall correctly, she had heard Inna say that the wedding would take place in 11 days. That meant she only had 10 full days left with her Mami.
She then started thinking of ydd za tayi rayuwar kuma ita kadai ta duba ta ko'ina taga rayuwa da Inna kamar shine worst life experience din da za tayi facing bayan babu Mami. And she wished zata iya bin Mamin can inda za'a kaita sai dai bata taji an ambaci hakan ba in banda alqawarin da Inna tayi na zata riqeta.
Ganin kamar tunanin yana shirin haddasa mata ciwon kai yasa tayi tunanin barinsa tana son tuna wani abu da zaiyi making dinta away from that thought and suddenly, Fu'ad came to her mind.
Time din har ta rufe idanunta amman tunawa da Fu'ad kawai makes her open her eyes tana dan waresu kan ceiling din dake dakin da ya gama jin jiki. She saw no reason for her heart to keep bringing that man's thoughts to her when he had only helped them. Hakan yasa ta qarfi da yaji ta yakice tunaninsa daga ranta. Ganin kamar baccin ne yake gudunta yasa ta miqe tsaye ta fita waje ta dauro alwala ta dawo ta tada sallah. Bata san nawa tayi ba kawai yi ta riqa yi tana kai kukanta wa Allah mujibud du'a har sai data ji bacci sannan ta shafa Addu'ar data dade tana yi ta miqe taje ta kwanta gefen Mami bayan ta sake sabuwar addu'ar bacci.
WASHEGARI
Same routine da ta saba yi kamin ta tafi mkrnta su tayi duk Mami tace ta barshi sai da tayi kamin taci abinci ta sha maganinta ta tafi mkrnta. Ji take kmr ta hqra da mkrntr sbd fashin da take zabgawa. Ba'a taba yin semester data taba yiwa kalar fashin nn ba har kunya taji take ji. Tun Fauzah qawarta na nemanta har ta watsar abinka da dama ba don Allāh take son qawancen da ita ba.
Tana zuwa ta tarar ma test za'a shiga hankalinta ya bala'in tashi sanin bbu uwar data sani bare ta rubuta amman hkn dai ta daure ta shiga fuskarta yana nuna karaya. And gradually, she had started losing interest in her studies altogether, especially since they began facing one misfortune after another. Duk sai taji komai ya fara sare mata kamar dai tayi loosing interest daga karatun.
Koda aka bata test din tabi questions din da kallo taga dagske fa bata sani ba. She was broken, amman haka ta daure ta hada ideas kawai daga dan abinda ta fahimta kuma immediately tana gamawa tayi submitting kar ma taje ta soke wani abin ko ta fara kokonto. Wuri taje ta samu ta zauna kan concrete chairs kawai ta zuba uban tagumi. Alokacin ji tayi kamar duk damuwar duniya yana kanta.
Jakarta ta bude ta dauko wayarta ta fara duba pdfs dinsu da da tana dan dubawa amman ynzu sam ina ma taga lokacin. It hurt her even more when she started reading and realised that her ability to understand what she read had significantly declined. She could read, but nothing seemed to stay in her head. Hakan yasa kawai ta mai da wayar jaka ta zauna shiru. Gashi sam ta dena engaging kanta cikin mutane tunda Fauzah ma ta yada ita sai take ganin halinta zai sa kowa ya yar da ita kawai dai zata gaisa da course mate dinta sama-sama shikenan.
Time ta duba taga lokacin wani lecture din ya shiga sai ta miqe ta wuce ammn instead of ta zauna a front seat yadda ta saba sai ta samu can baya tayi zamanta tana bin malamin da kallo. At first, she understood what he was teaching, but gradually, her thoughts drifted away from the lecture and returned to her own life. The thought of Mami getting married in the next nine days was all she could think about.
Tunaninta daya ne kawai, wanne kalar rayuwa za tayi tare da Inna. Inna never loves her duk da jininta ce, is it was like she's afraid of Mami leaving her with Inna alone. Bama ta karatunta data lura gaba daya yana gargada sbd komai has change, ba tayi registration ba, sannan ita akanta duk ya fice mata akai. Ita da ada bata da burin daya wuce taga ta maida hankali tana karatu yanzu komai is now a turn over.
Bata ankara ba sai gani tayi ana fita which meant the lecture had ended, and the lecturer had already left without her even realising it. Miqewa tayi ta fita haka nan ta samu kanta da kama hanyar fita daga mkrntar gaba daya saboda it was boring to her, ba iya karatu ba ahalin da take ciki yanzu komai haka take ji akansa even her life. She started thinking that kamar dai itace bata da sa'a a rayuwa sbd it quietly occurs to her that kowa was leaving her including her Mami.
Around 2 ta koma gida hakan yasa Mami bin ta da kallo sanin sai yamma take dawowa idan taje makaranta watarana ma kamin ta dawo gida anyi Maghrib.
"Yau da wuri kuka gama lectures dinne?" Ba tare data kalli Mami ba ta amsa mata da "eh Mami.." da kallo Mami ta bita ganin yanayinta za tayi magana sai tayi shiru kawai sanin tasan ba zai wuce maganar aurenta ba. Ita kuma she had nothing to do da zai yi saving karatun Nuri apart from the marriage.
Tana shiga daki ta ajiye jakarta sannan ta fito ta debi ruwa ta daura alwala tazo ta tayar da Sallahr Azahar. Bayan ta idar ta samu kanta da kasa tashi anan tayi zamanta kawai tana bin dakin da kallo.. da za'a saka mata wuqa a time din ace tunanin me kike Nuri ita kanta bata sani ba. A haka Mami ta shigo ta sameta ta tsaya kallonta fin minti biyar ammn still Nuri bata san ta shigo ba.
Kusa da ita taje ta zauna tana dafata wanda yasa tayi firgigit ta dago tana kallon Mami "Tunanin me kike yi?" Kai ta girgiza za tayi magana Mami ta riga da "don't say no.."
Ba tayi musu ba tace "tunanin duniyar kawai nake yi Mami naga duk ka gama wannan struggle din aqarshe duk mutuwa kowa zai yi.."
Mami na kallonta with emotions da yawa ta gyada mata kai. "Eh that's life. Babu wanda yazo duniya don zama.. kowa baqo ne acikinta lokacinsa nayi zai tafi ko ya shirya ko bai shirya ba..."
"Ko Ina Abba? Ko yana raye Mami?" Zancenta hits Mami sosai, Mami bata so ake mata zance irin haka wai Abba ya mutu she's always positive akan haka har tana assuring kanta zai dawo musu.
"Stop it Nuri. Abbanku yana nan araye zai dawo mu cigaba a inda muka tsaya.."
"I hope so Mami.."
"Jeki zubo abinci kici."
"I'm not hungry bacci nake ji."
"Okay then sleep well idan kin tashi sai kici abincin."
Miqewa tayi ta cire hijab din jikinta ta ninke sannan ta qarasa ta karkade katifarsu ta kwanta tana rufe ido hoping baccin yazo mata don ba bacci take ji ba ta fadi haka ne saboda bata jin yunwa ko ta zuba abincin tasan ba zata iya ci ba.
THE DAY SHE CALLED BLACK!!
Time never waits. The day Nuri had never wished to see had finally arrived.
Ba ita kadai ba hatta Mami haka suka tashi da wani sanyin jiki ranar plus garin ranar babu wani zafi duk da ba'a yi ruwa ba amman weather din garin sam babu zafi. Tun bayan asuba babu wanda ya koma acikinsu kowa yana zaune with different thoughts running in his mind. Mami ce ma take lura da ita yadda ta takure awaje daya. Suna haka gari ya gama wayewa amman aka kasa samun wanda zai tashi daga wajen.
A haka Inna da ta kasa zama ta shigo ta same su. Binsu da kallo tayi duk da ta lura they're down amman wannan ba damuwarta bane, for all she cared was that Mami should leave the house so she could receive the huge amount of money.
"Bintu na ganki azaune?"
Kallonta Mami tayi kamar mai jiran qarin bayani. Inna kamar ta fahimta sai cewa tayi, "eh ke da zaki tashi ki fara shirya kayanki nifa banga kina wani shiri ba kuma kinsan yau za'a daura ki tare ko?"
"Inna wanne shiri bayan wanda nayi ko ince kika yi? Ai an gama hada komai."
Nuri dai bata kulasu ba, don yadda take ji akan auren nan was clear kowa yasan bata so. Babban abinda ya qara mata tsanar auren was duk abin nan da ake shi wanda Mami zata aura bai taba zuwa sunga juna ba, sai yau idan an daura auren zai zo ya dauki Mami ya tafi da ita wai babu mai kaita shi zai dauki abarsa kuma duk sun yadda. Daman ba taro za'a yi ba sai maqota da qaiqayin bakin Inna yasa ta sanar musu ne ba'a dade ba suka fara dan leqowa tunda goma za'a daura auren kuma immediately ana daurawa zai tafi da Mami.
Duk mitar Inna kan Mami ta tashi ta shirya haka suka yi banza da ita sai Maman Hanif ce ta dan lallaba Mami kan ta tashi ta shirya lokaci baya jira yanzu zata ga sun qaraso tunda time din is past 8 tara ta kusa.
Ita Mami hankalinta da komai nata yana kan Nuri ne da har lokacin tana nan zaune a inda ta idar da sallar asuba bata miqe ba sannan babu wanda ta kalla ko ta kula. Kallon Nuri da Mami tayi Maman Hanif tayi kamin ta dawo da kallonta kan Mami tace "kiyi haquri Maman Nuriyya ki tashi ki shirya kinsan dole za taji wani iri ko don saboda babansu ki daure ki tashi kije kiyi wankan..."
Masifar Inna dai ita ta saka Mami ta tashi taje tayi wankan wanda ta mugun dade tana abu da sanyi kawai taji komai ya fita akanta bata son barin yarinyarta ita kadai.
Time din data fito ta tarar Inna da maman Hanif sun fito mata da kayan da zata saka wanda Inna da kanta ta siyowa Mami da kudinta wai na biki ta kai aka dinka mata. Mami ba tayi musu ba ta amsa ta saka sai dai still hankalinta yana kan NURI da har yanzu bata tashi a inda take ba kuma babu wanda take kallo kanta ma yanzu ta saukeshi qasa.
Time din da agogo ya buga qarfe goma daidai yayi daidai da daura auren Mami da akayi a kofar gidan with few people as witness da basu wuce biyar ba kuma duk yan sa ido ne masu neman labarin da zasu dorar.
Sallamar Rabe yasa Inna yin wuf ta fice ta sameshi bakin qofa yasha wata koriyar shadda data mugun fito da baqinsa zak mutumin qauyen daya zo binni bai waye ba.
"Ta fito kinsan baya son jira.." tana washe baki tace "to to to.." sai ta koma dakin da sauri tana cewa "maza tashi Bintu ga mijin naki ya qaraso..."
Yadda kalmar mijin nan ya daki Nuri daban sai taji kamar an soka mata mashi ne haka a qirji amman still bata motsa ba. Mami ta kalli Nuri da sauri jikinta yana fara rawar data rasa daga ina ne.
"Bintu ki fito baya son jira fa.." bata kalli Inna ba ta nufi wurin Nuri ta tsugunna sai kawai taji kalaman bakinta sun qare ta rasa me za tace wa Nuri. Yanayin yadda Nurin tayi yasa taji kamar kunyarta take ji don haka kawai ta bita da kallo ta kasa magana har fin minti uku.
Inna ce ganin zasu bata lokaci kuma ita bata son a batawa Alhaji Labaran rai ko lokaci yasa ta qarasa wajen Mami ta dagota tana cewa "sai kace guduwa zakiyi ki barta bayan kinsan ina nan.." sai a sannan hawaye ya fara bin fuskar Mami ta damqe hannun Nuri da sam ba tayi hawayen ba kuma har sannan bata dago ta kalli Mami ba saboda abinda take ji was beyond imagination.
Jan Mami Inna ta fara yi tana cewa "bafa wai rabuwa kuka yi ba zata ke kawo miki ziyara kema kuma zaki ke kawo mata ziyara..."
Inna bata bawa Mami option ba ta jata har bakin kofar fita dakinsu sai sannan bakin Mami ya bude da kyar saboda hawaye ta furta "Allah ya albarkaci rayuwarki NURI...."
My dear Nuri fam, mu gyara zama don ganin what will happen next. This is just half of the story more is coming.
Thank you so much for reading, commenting and supporting me. Jazakumullahu khairan.
To be continued...
#like
#comment
#share