Free chapter · Read without an account
32. ...best day...🖊️
32.
awkwardly matar ta sakeni naja baya itama taja baya tare da share gashinta zuwa bayan kunnen ta...ɗayar tace '' wow... budurwar ka tana da kishi sosai!"
'' na sani ko? Amma taƙi ta yarda da hakan!" Khalil ya basu amsa idonshi a kaina..turo baki nayi...iska mai zafi yake fita daga hanci na...
'' sunana Isabella...wannan itace Eleira...'' doguwar ta miƙo min hannunta na karɓa muka gaisa ɗayar ma haka...
'' oh okay..see you again...'' Alewa tayi ma Khalil bye bye kafin su biyun suka yi gaba.. dama na ƙagu dasu tafi su bamu wuri....
'' waccan Alewa ɗin....''
'' sunan ta Eleira...'' juyowa nayi ina kallon shi kamar in mangare shi '' toh nace ka gyara min? ai ba iya kiran sunan ne banyi ba!!.." ɗage hannayen shi sama yayi alamar surrender yana danne dariyar shi,cike da takaici nayi gaba yana biye dani
wurin wasu dogayen riguna muka isa...yana ɗauka yana nuna min..ni kam basu mun kyau ba ko kaɗan sai banzar tsada
wata shegiyar riga ya nuna min daga baya a kware,gaban ma tsakiyar ƙirji an yanka,irin rigar nan da turawa ke sawa gaba ɗaya tsakiyar ƙirjinsu a buɗe...zaro ido nayi kafin na karɓi rigar na mayar da sauri...
'' rigar zata yi maki kyau...''
'' ka dena ban kunya...''.na faɗa ina rufe fuskata da hannaye na...waih,waya ga slippers
'' okay...'' matsawa gaba mukayi wurin su palazo,ya ɗauki barom zuba kaya yana turawa..
wani mai ƙyalli kalar ruwan toka ya ɗaukar min
'' beautiful as your eyes...but your eyes are more beautiful'' yayi maganar idonshi a nawa,kauda kaina nayi ina dariyar jin kunya
kafin inyi magana wasu maza biyu suka ƙaraso wurin '' bros...'' ɗayan su ya rungume Khalil duk da Khalil kamar baiyi farin ciki da kasancewar su wurin ba...
'' Kitten,go on..ina zuwa!" na karɓi wandon nayi gaba ina juyowa continuously kamar kada in tafi...yanda yayi maganar kamar a tilas take fitowa daga bakinshi idonshi sunyi irin duhun da ban taɓa gani ba...
'' who is she?''
'' I don't see how it concerns you Ameer!" Khalil ya katse baƙin gayen dake magana yana kallon Abeedah yana shafa gemu...
'' is that jealousy I'm seeing in your eyes?'' ɗayan mai haske ya faɗa yana ma Khalil kallon shaƙiyanci
'' koma meye kake gani it's none of your business'' Khalil yayi maganar coldly,his eyes shooting blazers,hannayen shi dunƙule daga gefen shi..taɓe baki su biyun sukayi
Khalil ya juya ya fara barin wurin
'' kasan da cewa har abada mun zama ɗaya Ibrahim '' Ameer ya faɗa yana yi mashi alamar heart 💜 da yatsun shi... Khalil bai juyo ba
Hankalina bai kwanta da barin Khalil da mutanen nan ba,gaba ɗaya basu yi kama da mutanen arziƙi ba,gashi har lokaci ya wuce bai dawo ba kodai sun yi kidnapping ɗinshi?...juyawa nayi zan koma ƙirjina na sama da ƙasa naci karo dashi...ɗagowa nayi idon mu ya haɗu,bai yi kama da Khalil ɗin dana sani ba...ga ƙunci nan bayyane a fuskarshi
'' lafiya kuwa...?''kalaman suka fito daga bakina kamar raɗa...da ƙyar yayi min murmushin yaƙe yana gyaɗa kai a irin yanayin daya tabbatar min da ba lafiya ba...
'' ko mu koma gida ne?" Na tambaya ina riƙo hannunshi abinda na koya daga gareshi batareda na sani ba...
'' ki gama sai mu tafi...'' da sauri na sake shi na ƙara ɗaukar wasu palazo guda biyar kala daban daban da rigunan da suka girmi jikina suma biyar nace
'' na gama!" Sai ya gyaɗa kanshi yayi gaba ina biye dashi na ɗauka fita zamuyi daga Mall ɗin a mamakina ya kawo ni wurin da ake sayar da kayan ciki...oh my God! Ji nayi kamar ƙasa ta buɗe ta haɗiye ni....
'' yallaɓai sannu da zuwa...Meye size ɗin budurwarka....'' numfashi naji ya dena fita na wucin gadi...naji kamar ana hura min wuta a fuska,idona sun kasa komawa dai dai
'' kitten...ki zaɓa...'' idon mu ya haɗu as he said those words...sai kuma ya matso kusa,bugun zuciya ta har kunne na,yayi ƙasa da murya bakinshi saitin kunne na yace
'' You look cute when you blush...''
ya kashe min ido sannan yayi gaba da murmushi a fuskar shi...a wannan lokacin ya dawo sak Khalil ɗinshi...naji daɗi amma kuma hakan baisa kunyar dana shiga raguwa ba...
'' this way Ma'am!" Matar taja ni tana nuna min kayan ciki,su breziya da pants...
wata farar singlet mai dots baƙaƙe na ɗauka..da kuma sauran masu kaloli daban daban guda biyar dan dai bazan da breziya ba wallahi,na ɗauki pants da guntayen wanduna suma biyar...har zan tafi ta nuna min inda ake sayar da su pad...na danyi jim..idan na ɗauka dole Khalil zai gani kuma dai gaskiya...girgiza kaina nayi...tayi murmushi kafin ta sake jana muka isa reception...
A nan muka haɗu da Khalil matar take faɗa mashi wani abu da banji ba,kawai naga ya gyaɗa kai,fara kwasar kayan akayi ana kaiwa mota...bayan ya biya mukayi gaba,har zamu shiga mota muka sake ganin wa'yannan mutanen suma zasu shiga tasu motar...fuskar Khalil ta sauya... har ina jiyo numfashin shi
'' hello beautiful lady, what's your name?'' mai hasken yake waving hannun shi a gaba na,kallon Khalil nayi naga yana taune leɓenshi kamar yana controlling kansa...
na sake dawo da kallona akan biyun,yanda suke kallona kamar zasu haɗiye ni da idonsu yaban haushi
'' Read the sign and understand ba'a maraba daku!'' saboda su yanayin Khalil ya sauya,su suka ɓata mashi rai and I dislike them for it!...sunyi kama da kwaɗin dake ƙwara ƙwara da uwar safiya.... fuskokinsu sukayi duhu
'' feisty....I like Fe...'' yake Maganar tare da matsowa zai taɓa Ni,riƙe hannunshi Khalil yayi '' don't!" Ya furta with a dangerously calm voice sai ya kalle ni yace in shiga cikin motar badan naso ba na sake barinshi dasu...
Matsowa Ameer yayi yana kallon motar da Abeedah ta shiga ciki ya kalli Khalil murya ƙasa yace
'' Ibrahim ka bani ita wallahi na kamu da sont....''
wani irin wawan naushi Khalil ya sauke mashi a fuska daya sashi yin tangal tangal zai faɗi...bakinshi ya fashe...gayen nan mai haske ya saki baki, Khalil ya kamo collar shi numfashin su biyun na mixing,idon Khalil sun yi mahaukacin ja
'' idan ka sake kallonta with those holes on your face, you'll see the absolute worst of me!" the air was thick with tension, maza biyun suka kafe juna da ido.. roughly Khalil ya saki collar gayen,jikin shi na wani irin tsuma
ya juya zai shiga mota,wani yaron mall ya kawo wani abu cikin leda ya miƙa mashi, literally wasge abun yayi kafin ya shiga motar...huffing angrily
Ya kwantar da kanshi akan steering ɗin yana numfashi da sauri sauri...
Yanayin Khalil ya tsoratar dani,ban taɓa ganin shi haka ba,kullum daga murmushi sai tsokana da dariya..amma yau harda kaima wani naushi...shiru nayi tareda maƙewa akan kujerar da nake zaune ina numfashi ahankali kamar ina gudun ya sauke fushin shi a kaina...
ya figi motar da gudu muka bar mall ɗin...
duk da a tsorace nake da irin gudun da yake shararawa ban ce ko uhm ba amma dai zuciya ta ta kusa faɗawa cikin cikina...
fuskarshi na kalla da take a tamke wannan murmushin wasar babu alamun shi ko kaɗan...'' Khalil...'' na kira a tsorace.. somehow hakan yayi tasiri kamar ya manta dani kiranshin dana yi yasa ya tuna rage gudun motar yayi ya parka gefe tare da Juyowa sashen da nake
'' Oh..kitten, I'm so...'' banyi tsammanin akwai ranar da zan yi hakan ba,kafin ya gama sentence ɗin daya ke shirin faɗa na rungumeshi sosai...naji yanda jikinshi yayi tensing kafin a hankali ya zagayo da hannayen shi a ƙuguna.. hugging me even tighter
anya kuwa nice? ƙila dai an canja ni...
'' kana lafiya?" Na tambaya da damuwa a murya ta naja baya daga jikinshi hannuna a kafaɗarshi...idon mu ya haɗu...
'' naji sauƙi...'' ya faɗa na gyaɗa kaina ya cigaba da faɗin
'' after you hugged me...I think your hug is a form of therapy...ya kamata ki dinga bani wannan daga lokaci zuwa lokaci!" Yana shafa haɓarshi daba gemu yayi maganar
'' haha..kai wannan Khalil ɗin...!" na kira a kunyace '' I'm serious...'' ya furta... tare da kashe min ido...
Na mayar da fuska ta gefe ina cigaba da murmushi '' kina jin yunwa?" Ya tambaya
Na gyaɗa kai
tada motar yayi da murmushi a fuskokin mu biyun..ina bashi direction har muka iso tsohuwar anguwar mu...inda akwai masu sayar da abubuwan bakin hanya lokacin har rana ta soma shigewa..
Fitowa mukayi daga motar ina gaba yana biye dani...wurin na motsi da rai da maganganun mutane,ga rumfuna nan jere da jere kowa da abinda yake sayarwa...kuma a gaban kowane runfa akwai table inda customers zasu zauna, babu abinda ke tashi sai ƙamshin soye soye da abinci kala kala..wurin bakin titi ne dan haka wucewar motaci ya ƙara ma wurin rai...sai dogayen bishiyoyi dake bayan runfunan...
akwai mutane da yawa ciki da wajen wurin, abubuwan da ake sayarwa harda gasassar kaza,kifi,nama,suya,gurasa da dai sauran street foods na Nigeria
Mutanen sun sanni dan haka suna ganin na suka fara kiran suna na...ina yi ina waigowa inga ko Khalil na bayana
'' meyasa kike waigowa?"
'' kada ayi gaba da kai ban sani ba...''
'' I'm an addult...''
''.manya nawa ake sacewa a irin wannan wurin?" yayi bam da bakinshi kwanar bakin a ɗage...yake kallon mutanen wurin kamar sun zama abun kallo a gareshi...Nima dai naga banbanci... kyakkyawan ɗan gaye ya ɗau wanka sai ƙamshi yake vs mutane daƙun daƙun kowa da irin wari ko ƙamshin da yake...
Yan matan dake wurin sai kallonshi suke.. kamar in tsone masu ido...
' a'a kuzo kuga tuwo tazo da saurayinta...'' wani tsoho mai sayarda sharare.. kifin da aka soya da ƙwai ko flour ya faɗa...sunan shi saminu amma ana kiranshi Baba saminu...nakan tara kuɗi da yawa inzo nan in kashesu a wurin shi,harda mutane nake kawo mashi dan su saye abu a gurinshi dan yana ban tausayi
murmushi nayi sai ga mutane sun taru sun zagaye mu nida Khalil, dole na riƙe hannunshi a nawa kamar ina gudun a sace shi...'' iyye tuwo kin iya zaɓe..'' wani mai sayarda masa ya faɗa...
Nikam dariya kawai suke ban..mazan suna miƙa mashi hannu su gaisa kamar ba ɗan uwansu ɗan Nigeria ba...
Khalil sai murmushi yake yana miƙa masu hannu.. mutane sai sun goge hannun kafin suke karɓar nashi...
daga ƙarshe dai kyauta muka ci komai...da farko masa aka fara bamu muka zauna ƙarƙashin wani rumfa amma Khalil yaƙi ci...ina faɗa mashi akwai daɗi amma ko saurarena bai sonyi...Yana tsaka da magana na tura mashi masa a baki...zaro ido yayi na fashe da dariya..daga ƙarshe dole ya haɗiye Masar ..aka ƙaro mana plate ɗin sharare wannan kam da kanshi yaci...
daga runfa zuwa runfa muke tafiya kowa yayi farin ciki da ganina..nima kaina nayi farin ciki sosai kuma ban taɓa sanin ina da masoya har haka ba...ada nayi roƙon a soni,a ganni amma yanzu batareda na wahalar da kaina ba,mutane suna nunamin so...abun ya daɗaɗa raina ba kaɗan ba...
Shima Khalil da ganin shi kasan yana farin ciki it's radiating daga jikinshi..tsaye muke gaban wani mai runfar suya nikam har na gama cin tawa..shine dai da duk ya ɗan ciza sai ya tsaya yayi shhh saboda yaji kafin ya ƙara ciza...abu kamar dole mutanen sai dariya suke amma bai ko damu ba....
Koda na kalli sama har rana ta faɗi duhu ya fara sauka...sanyi da iska sun ƙara ƙarfi...duk da wurin akwai mutane dake magana da murya sama...nake ji kamar duk wannan surutun yayi nesa dani...daga duniya ta... it's just me and Khalil...shi ɗin...ban ma san yanda zan faɗa ba
Mun daɗe a wurin kafin mukayi musu sallama zamu tafi Saida Khalil yabi duk wa'yanda suka bamu kyauta ya dinga basu kuɗi har wurin baba Saminu...tsohon yayi mana godiya da addu'a kamar ba gobe...
Muka bar wurin da nishaɗi muna tafiya cikin shiru mai natsuwa can yace '' me yasa kowa ke kiran ki tuwo?" Ɗage kafaɗa nayi '' wani bayarraben Malami ne a makarantar mu yake so yace Abeedatu..sai yake cewa Abeedatuwooo..shine yan makaranta suka mayar dani tuwo yan unguwa ma suka ɗauka...''
'' huh..ashe kina da mutane har haka?"
''.nasani ko...nima nayi mamaki...'' na bashi amsa da murmushi...zama nayi a wuri na shima ya zauna a driver seat,na ɗauka gida zamu amma a waje mukayi sallar maghrib da isha'i...ya kaini inda ake sayarda wayoyi.. wata tsadaddar waya mai kyau ya siya min...da yar ƙarama irin wacce ta faɗa cikin ruwa ɗazu...irin farin cikin dana tsinci kaina baya misaltuwa...sky blue pouch mai ƙyalƙyali na ɗauka ya biya muka tafi...
Sanda muka fito daga shagon sayarda wayar ƙarfe tara dai dai..babu mutane da yawa a wurin sai hasken fitilun gefen titin da kuma orange lights da suke fitowa daga shagunan dake kusa,muna tafiya gefe da gefe iska mai sanyi da daɗi na kaɗawa...Khalil was so happy yana bani labari abinda yafi maimaitawa shine '' wannan itace rana mafi kyau a rayuwa ta...'' sai murmushi nake...hasken gefen titin dake faɗawa saman fuskarsa yake ƙara mashi kyau...har muka iso motar muka zauna a seats ɗin mu...shiru nayi ina jujjuya wayar a hannu na da wani irin farin cikin da kalamai bazasu iya faɗa ba
'' Khalil....'' Juyowa yayi sashena yana min wani irin kallon da yafi na koda yaushe zurfi...nima na tsinci kaina da mayar mashi da irin wannan kallon
'' Nagode!" Na faɗa daga ƙasan zuciya ta...Juyowa yayi muna fuskantar juna da kyau,hasken single light ɗin dake gefen motar mu ya sauka a gefen fuskarshi,ga ƙamshin turarenshi dake tashi sosai kamar a lokacin ya fesa shi hakan ya haifar da wani irin abu a ƙasan ciki na...
'' honestly...you don't have to thank me! Zan iya bada koma nawa ne to live those moments again...TARE DA KE!" yayi maganar with a low deep voice dayasa naji butterflies na wasa a ƙasan cikina wai meya ke damu na? His gaze deepens on me,sai nayi ƙasa da idona ina tsananin jin nauyin shi,ga bugun zuciyata da yaƙi zama dai dai
'' yaune mafi kyawun rana duk tsawon rayuwa ta!"
'' kai Khalil,faɗi gaskiya ka amshi Naira biyar!" nayi maganar kaina a ƙasa,Dariya mukayi a tare bayan na faɗi hakan
'' I'm serious Abeedah...I have never been as happy as I'm today...Nagode!" yanda ya kira sunana naji wannan shine the best way da aka taɓa kiran sunan...and I loved it...ƙila in faɗa mashi ya dinga kiran sunana koda yaushe
Ɗauke kaina nayi gefe kumatuna sukayi zafi...na kasa dena murmushi..ban san me yake damuna ba a duk sanda nake tare da Khalil ɗin nan