Free chapter · Read without an account
Chapter 14
by Salis M Reza · MIJIN AMAL
Chapter 14
Mutumin ya amsa gaisuwar yana nuna shi da hannu. Ya ce "Kaman na sanka ko?" Yasir da gabansa ke cigaba da faɗuwa ya ce "Eh a'a um!. Sai mutumin ya kalli mutanen dake kusa da shi ya ce "Ku fara turo min shi idan na zauna". Daga haka yayi gaba yana sake waiwayowa yana kallonsa. Yasir ya koma ya zauna ba tare da ya bi ta kiran da Ali yake sake masa ba. Kowa sai kallonsa yake a gurin mata da maza, hakan yasa jikinsa ya sake mutuwa. Gabansa ke ta faduwa bai san mai zai faru ba. Ko ba komai wannan mutumin ya neme alfarma a gurinsa bai masa ba, gashi kuma shi yazo neman aiki gurinsa. Tabbas abun da kunya kuma da nauyi. Kaman ya kira Amal ya faɗa mata ko zata kwantar masa da hankali. Amma dai ya dake yana addu'a a ransa. Yana cikin haka kaman minti talatin kuwa sai gashi an zo an kira shi. Ya miƙe yana cigaba da addu'a a ransa har ya shiga da sallama aka amsa. Mutane uku ne a ciki harda mutumin. Bayan ya zauna suka amshi takardaun sa suka duba. Ɗaya daga cikin mutanen ya fara masa tambaya. Tambayoyi uku yai masa Kafin mutumin ya ce "Yasir ko?" Ya faɗa yana karanta sunan a jikin takardar tasa. Ya ɗaga kai kawai yana jin bakinsa na bushewa. Ya ce "Tun bayan abun da ya faru tsakanin ka da ƴata nake ta neman ka. Ban san ina zan sameka ba, saboda kayi abun da ba kowanne namiji ne zai iya ba, tabbas kai mutumin kirki ne. Naji daɗin ganinka a karo na biyu". Ya faɗa yana miƙa masa hannu. Yasir ya kalli hannun ya kalli sauran mutanen yana mamaki. Bayan sun haɗa hannun ne ya ce "Bayan chanchanta da kayi, kuma halayenka sun zama gadar zaran da ka taka ka samu wanan akin. Saboda haka congratulations again". Wani irin farin ciki ya mamaye shi. Ya fara godiya ya tashi zai fita yace "Zamu tura maka da saƙo ta email ɗin ka. Da Ranar da zamu neme ka da matsayin ka". Daga haka ya fita.
Burinsa kawai ya kai gida Amal ta fara jin wannan labarin mai mutukar dad'i wai ya samu aiki. Domin ko a waya ma ba zai faɗa mata ba. Zai fita daga kamfanin kenan wata farar Mota zata ta shigo. Hakan yasa ya tsaya domin ta ƙarasa shiga. Sai aka tsayar da motar a gabansa. Aka zuge glass. Sai ga Suhailait a gidan baya zaune tana waya. Ta kashe wayar tana kallonsa. Shima ita yake kallo bai ce komai ba. Amma tsaf ya gane ta. Sai yanzu ma yake ganin asalin kamar da take yi da mahaifinta Ta ce "Kai ne?" Ta faɗa tana nuna shi. Sai ya ce "Good morning". Ya faɗa yana ɗan risinawa. Ta tsayar da shi da hannu tana magana da dreban gamin da kashe wayar gaba ɗaya. Bayan ya ƙara gaba ta buɗe ta fito ta nufo gurinsa tana kallonsa cikin ido.
Ta na zuwa ta ce ",Mai kazo yi nan bayan abun da kayi mana? Kasan ina ne nan kuwa?" Ta faɗa tana nuna shi, abubun da yayi mata na sake dawowa akanta. Jin bai ce komai ba ta sake faɗin "Kai a tunanin ka badan ina da dalili ba, har ka kai wanda zai iya tsayawa a gabana bare har wani aure ya shiga". Ya ce "Hakan ne yasa na fasa, I'm sorry ban fasa dan wani abu ba sai dan kawai ke ɗin ba aji na bace". Ya faɗa a hankali yana haɗe hannu alamun roƙo, kuma fuskarsa da muryarsa ɗauke da murmushi. Ya ce "Kuma ina godiya saboda na samu aiki a kamfanin ku, wannan farin cikin ne bana so na rasa shi, zan je gida". Yayi gaba ya barta tsaye. Ta cire Glas ɗin idanunta bata san lokacin da ta bishi da kallo ba har ya ɓacewa ganinta. A fili ta iya faɗin "Aiki".
Tun da Yasir ya fita take tunanin abun da zata dafa musu da rana, saboda babu komai a gidan. Dubu biyu ta ɗauko a cikin kuɗin da ta fasa ɗazu ta bashi uku. Sai ta fara aikin gida tana yi tana lissafin yadda dubu biyun nan zata koma abinci. Kichin ta shiga ta sake duba komai, amma daidai da kishiri babu. Harda ledar shinkafar ma ko ƙwaya ɗaya bata fado ba. Ta ɗauki waya ta nemo number Nana. Kira ɗaya ta ɗaga. Ta ce "Kina ina?"
"Ina tare da mijina mana Anty" Ta amsa da saurinta.
Amal ta sauke hajiyar zuciya ta ce "Tom ki gaida shi. Amma zaki iya zuwa gida na yanzu dan Allah?"
"Anty muna da nisa fa, kuma yanzu muka zo, ki bari idan mun dawo, kuma ban ma sani ba ko a cen zamu kwana". Ta ƙarasa da alamun tana cikin farin ciki.
Amal ta ce "Nana kwana fa, har kina faɗa mi?"
"To Anty zan miki kariya ne? Kuma ina ce dai mijina ne ba yawon banza naje ba?"
Afusace ta ce "Idan haka yake so to ku tare mana, mai yasa baki da hankali ne, dole ne sai ya gama ginin ne, ko haya ya kama miki mana. Wannan wani irin aure ne na zubar da mutunci. Ke yanzu ya miki dad'i a dinga yawo dake kwararoro-kwararoro kamar wata mara gata, da anyi magana kice Mijinki miji, haka mijin yake?" Ta ƙarasa da ihun da rabonta da tayi har ta manta. Nana ta ce "Yanzu so kike idan ya kira kar na je kenan?" Da karfi ta ce "Dan ubanki ke ba mace bace, baki san yadda zaki ƙwaci mutuncin kanki ba, har sai kin masa haka. Wallahi Nana idan baki dawo cikin hankalinka ba kina biye Mama ko..." "Sai an jima". Ta katse mata wayar. Amal ta bi wayar da kallo baki a buɗe. Ta ajiye wayar tana kawar da batun a ranta amma ina wallahi bata yarda da aure irin wannan ba. Tunani tayi akan ta sayo ko taliya ce guda daya, sai ta haɗa musu jajjage. Kuma gashi ba yara. Ta saka hijjabi ta nofo waje. Ta kai minti biyar a bakin ƙofa bata ga ko yaro ba. Har zata juya ta hango yaron shagon su yana nufowa gidan a ƙafa. Hakan yayi mata daɗi ta koma ciki ya shigo. Bayan sun gaisa. Ya ce "Oga ne yace da anyi ciniki nayi sauri na kawo miki wannan na cefane". Ya faɗa yana bata dubu uku". Ta amsa tana faɗin "Yauwa dama ina so na samu wanda zan aika ne". Ta masa lissafin abun da take so. Taliyar ma ta sayo guda biyu. Wake gwangwani huɗu.
Kafin ya dawo har ruwanta yayi zafi. Ta zuba waken, tana yi lamarin Nana da wanda take kira da miji na dawo mata. Ta ce da yaron anjima yazo ya ɗauki na shi. Yayi godiya ya fita. Yauma waka ta kunna tana yi tana girkin ta. Kuma tana tunanin mijinta Allah yasa an dace, Allah yasa ya samu wannan aikin. Ita a ranta ma tana jin kawai ya samu wannan aikin in sha Allah. Bayan ta kammala girkin ne kaman yadda ta saba ta juye. Ta samu karamar kula ta zubawa yaron nasa. A fili ta ce "Allah yasa ya iya ci ba kifi ba nama". Ta gyara komai na gurin ta kawo Palo. Ta ɗauki waya domin ta kira shi ganin kusan karfe ɗaya. Har zata kira ta fasa kar ta dame shi a gurin neman aikin. Ta kunna data. Sai ga messages masu yawa daga group ɗin makarantar su. ganin sunan Hafsah na ta yawo ne yasa ta shiga tana faɗin yanzu haka rikici ta kwaso. Ta fara bi tun daga farko. Har dai ta gano abun ne nasu na yan mata wato faɗa akan saurayi. Kuma gashi ba nata saurayin bane amma ta ari fadan ta yafa. Idan ma baka tsaya ka bi a hankali ba, zaka ce da ita ake. Tana kokarin yin magana sai taga sunanta anyi tagging da wani rubutu mai tsayi na Turanci yanzu an turo. Hakan yasa ta fara karantawa. Sai kawai dariya ta zo mata. Ta fara yin reply kenan taji bugawarsa. Ta ajiye wayar ta kalli kanta. Batayi wanka ba, kuma ya kamata ace tayi. Sai dai ta nufi gurin tana faɗin
"Waye?"
ya ce "Yaron gidan ne?"
"Yaya sunansa?"
"Kamalu". Ya faɗa shima sunan na bashi dariya.
Itama dariyar tayi tana faɗin "Kuma a gidan nan?" Ta faɗa tana buɗewa.
Ai cikin ƙasa da second ɗaya yayi sama da ita. Dama gata nan dai ba auki ba. Yayi cikin da ita da yana faɗin "Albishirinki?" Tun farkon maganar su, ta gane an samu nasara, hakan kuma ya sake tabbatar mata. Ta ce "Goro fari tass-tass". "Tom alhamdu Lillah, an bani aiki". Ya faɗa yana sauketa. Take ta naimi yunwar da take ji ta rasa. Ta rungume shi tana faɗin "Alhamdu Lillah!.
Da sauri ya ciro laptop ɗin sa daga chaji ya kunna. Ya ce "Bari ma na sake yin bincike akan kamfanin, kin san ban fa san komai a game dasu ba, kawai abokina na faɗa min na tura musu". "Ta ce "Ko ma dai aikin menene mun riga mun samu". Ta maƙalƙale shi ta ce "Kasan irin farin cikin da nake ciki kuwa? Ji nake kamar fa umara ka biya mana ni da kai haka nake ji". Ya juyo ya kalleta. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki. Zaki je umara, kuma zamu je birnin London wato Ingila mu kalli wasan Chelsea a cen". "Amma idan mun dawo daga umara ɗin ko?" "Eh daga cen ma zamu wuce". Ashe zamu je indiya ganin Alu Arjun, da kuma Aliya Bhaat ko?" Ya ce "Duk suna cikin tanadina" Tsaf ya gama duba komai na aikin yaga babban kamfani ne, kuma ba laifi suna biya mai kyau, har ma sai ka kai ɗan manya kake samun aiki a gurin. Dan har da gurare ya gani suna da shi a kasashen tsallake.
Ta kawo abinci ya ce shi dai wallahi ya koshi, ba zai iya cin komai ba Yau. Itama tace ta ƙoshi sai dai su bari zuwa dare ko safiya. Tasa ya ɗauki waya ya kira yaron aikin nasa. Ta kara masa ya ɗauka ya tafi. Daga nan kuma aka buɗe fagen hirar duniya, irin burin da suke da shi na rayuwa. Daga karshe aka ɓuge da kallo. Har sai bayan isha aka turo masa da gurbin aikin nasa, da kuma adadin albashin sa. Gaba ɗaya sai da sukayi sujudur Shakur a tare. Ya rungumrta sai addu'a yake yi. Suna cikin haka yaji ana kiransa. Yana dubawa yaga number abokin nasa ne. Bayan ya ɗaga yake faɗa masa cewar an ɗauke shi, Allah yasa shima ya samu. Nan suka taya juna murna suka kashe waya. A wannan daren barcin farin ciki sukayi mai cike da burin rayuwa mai kyau har karshen rayuwa.
A washegari gaba ɗaya wanda aka ɗauka ɗin kowa yaje aka nuna masa ofis ɗin sa. Sannan aka basu kafin alkalami na fara shiga ofis ranar Litinin. Wanda matsayinsu ya kai harda Mota aka bashi. Wanda ma harda gida aka basu. Wasu ma daga ciki ba'a nan Nigeria zasu zauna ba. Yasir dai yana daga cikin wanda suka samu kyautar Mota ta kamfani domin zuwa aiki kan lokaci, wannan kyauta ce ga duk wanda ya samu wannan aikin. Ko daga ganin ofis ɗin da aka bashi yasan ba karatunsa bane ya kai shi. Saboda shine mataimakin CEO na kamfanin, wanda zai dinga taimaka masa Kamar yadda aka ce masa an sauya wancen ne saboda an kama shi da ha'inci. Sosai ya godewa mutumin nan har sai da ya rasa bakin magana.
Lokacin da ya zo gida da motar kuwa Amal tsalle take yi tana drewa. Ko kasheta baiyi ba, yasa ta ɗauko hijabi suka tafi ɗani. Basu yi nisa sosai ba suka dawo. Ya kira Ali ya faɗa masa, haka ma Yaya. A cikin kuɗin da aka fara bashi kuwa kayan abinci ya jido masu yawa kuma na ƴan gayu. Dama Yasir muddin yana da kuɗi to fa ko abincin da suke ci na masu kuɗi ne. Hakan yasa yanzu ma yaje ya sayo komai da komai. Wani abun ma sai ya dawo zai tuna. Amal ta ɗauki waya ta fadawa Nana. Ai kuwa a ranar sai gata tare da Mama. Amal na ganin Mama ta rungumrta tana faɗa mata cewar Yasir ya samu aiki har ma ya sayi Mota". Mama ta gwasaleta da faɗin "To sai me? Ke ina taki?" Ba Amal ba, har Nana sai da ta tsaya tana kallon Mama. Ganin haka ta ce "Ina nufin kiyi murna a hankali kar ki rasa sauran idan aka saya miki taki, kuma yanzu ne zaki ci ribar aure idan kina da hankali. Komai ya dawo hannunki, fita da shigar kuɗi duk ki sani". Amal ta ce "Mama yanzu dai zauna a kawo muki abinci". Tana faɗa ta shige kichin. Mama ta bita ciki tana girgiza kai. Ta ce "Eh lallai ba shakka, su Amal an yi kuɗi, yanzu ko zaki samu kiyi auki". Daga haka Mama ta fara jidar kayan abinci. Amal bata ce mata komai ba har ta gama.
Wannan samun aikin shine mabuɗin gaddarar rayuwar Amal da mijinta ba tare da sun sani. Wata rayuwa mai mugun ciwo da raɗaɗ ne ke biyo bayan cikar wasu burunkan. Haka ya fara aikinsa lafiya ƙalau har aka bashi albashi na farko mai kyau. Ya ɗauke ta suka je sayayya ya faɗa mata adadin kuɗin da zata kashe rabin albashin nasa. Da yake ita ma tasan mai take yi sai ta raba kuɗin biyu ta kashe rabi ta dawo da rabi gida. Suna cikin buɗe kayan ne amai yazo mata. Kafin ma ta kai toilet ɗin ya zubo. Da yake ranar Lahadi ne, ya kira sabuwar likitar da ya sauya. Sai tace suzo asibiti. Tuni ya sunkumota izuwa mota. Ko tari tayi sannu yake mata, haka tun da suka shiga mota yake riƙe mata hannu ɗaya. Gashi tace masa ba komai kawai tashin zuciya ne, amma yaƙi yadda. Ita kanta likitan na ganinsu ta fara dariya ganin yadda yake mata. Bayan ta tabbatar da ciki ne na wata guda. Ta kalleshe ta ce "Malam Yasir wannan ciwon farin ciki ne, matrka na ɗauke da juna biyu". Ta ƙarasa tana murmushi. Da sauri ya toshe baki tsabar farin ciki da murna, ita kanta bata san sanda ta mike tsaune ba tana shafa cikin nata...📝
Muje zuwa a page na gaba