Free chapter 路 Read without an account
Page 8
Hajja Kaka ta gama fada-ce-fada-ce, ta gaji. Ta tsaya a gaban MD, tana masa fada, tana cewa, "Kai Muhammadu! Wannan wane irin hali ne? Yara kake yi wa haka? Saboda ba naka bane ?" shi ko be sake tanka mata ba. Ya raba ta gefen ta, ya wuce, bai ko kalle ta ba. Kamar ba da shi take magana ba.
Wani irin harara ta bishi da shi, harara mai zafi, kafin ta fashe da kuka. Kuka mai karfi, kukan takaici. Ta ce, "Wannan wani irin yaro ne Gaddafi ya haifa ma kansa? Dan wallahi bani ya haifa mawa ba! Bakin cikin ka bazai kashe ni ba, wallahi! Katon banza, katan wofi! Yayi da, idanuwa a tsaye kamar kirjin budurwa!"
Kuka ta ke yi, tana goge hanci da zaninta. Gaba daya ta gaji da halin MD. A idonta, MD ya zama azzalumi.
Kai tsaye bangaren Mommy ta nufa. Ko sallama bata yi ba, ta shige falon. Babu kowa a falon. Sai karan TV da ke tashi a hankali, ga kuma dadda dan kamshin turaren *Albakhour na MRS CLASSY WRITE **** da yake tashi a falon, kamshi mai dadi da ke sanya gidan kamshi. Kara taji a kitchen yasa kai tsaye ta nufi kitchen din.
Dai-dai lokacin kuma da Mommy (Hassana) taji alamar motsi a falon, ita ma ta fito da himma, ta leka ta ga ko waye. Sai ko ta ga Hajja Kaka. Aiko cikin sauri, da girmamawa da fara'a dauke a fuskarta, take fadin, "Aa Hajja! Kece da kanki? Aida kinsa a kira ni, nima zan taho da kaina." Ta kare maganar tana fadin, "Ga wajan zama Hajja, bari na kawo miki abin sha, ko ruwa mai sanyi?"
Hajja Kaka ta harare ta, ta ce, "Aa zo zauna, ban ce ina bukata ba. Yanzu ke Hassana, kuna zaune kuna ji, kuna gani, yaron nan zai kashe muku yara ko? Shifa wannan mai sufan kafuran, be san zuro ba. Karki so ki ga yanda ya mayar da halittan yaran nan." Ta kare maganar tare da fashewa da wani kukan, tana goge hanci.
Mommy wani irin murmushi ne ya kwace mata. Murmushi na jin dadi. Tana fadin a ranta, "Alhamdulillah, yanzu na san wanda zai yi mata maganin su ya dawo. Badai basu jin magana ba. Ita yau tun safe da Jazzeelah ta zo ta gaisar da ita ta fice, to bata sake ganin ta ba. Halla wani laifi suka je suka tafka, to ae zakin nasu ya dawo, ga su ga shi nan a gadan."
Duk wannan tunanin tana yin, shine da murmushi a fuskarta. yayin da Hajja Kaka ta yi galala, tana kallon ta. Ita da ta zo ta fada mata abu dan su dauki mata ki, shine wato ta mayar da ita mahaukaciya? Wato tana mata magana, ita abin nishadin ya saka ta?
Ko to ae shikenan, ita ta lura gaba daya yanzu mutanan gidan basu da hali. Daman Hassanar ne take gani mai dan dama dama, to ashe ita ma yar'uwar danyen ne. Mikewar da Hajja Kaka tayi, tana gyara daurin zanin ta, shi ya farko da Mommy.
"Aa Hajja, ya akai kika tashi kuma, ko ruwa baki sha ba?"
Hajja ta ce, "Aa ki rike abin ki, harni Hassana. Zan zo ina miki magana, amma ki tasani gaba kina dariya, tunda ga mahaukaciya ko? To na gode, Allah ya saka da alkhairi. Kuma duk halin da ake ciki, ki saka shi ya kawo likita ya duba min jikoki, tunda na ga duk fadin gidan nan yafi shakkan ki. Idan ba haka ba, kotuce zata raba ni da shi."
"Aa Hajja, insha Allah baza'ai hakan ba, ki yi hakuri, Allah ya huci zuciyarki," Mommy ta ce, tana rarrashinta. Tana ganin Hajja ta fita, ta koma kitchen, kafin ta dauki wayarta, ta kira Dr. Jameel.
Ringing daya, biyu, ya dauka.
"Assalamualaikum Mommy, barka da warhaka."
"Barka dai Jameel, ya ayyukan? Lafiya lau Mommy, ince dai kana kusa?"
"Eh Mommy, nazo ne, yanzu haka ina gida."
"Aa bangaren Hajja zaka duba, yaran nan, hankalinta ya kwanta."
Dan shiru yayi, yana tunanin wasu yara, dan shi kwata-kwata ya manta da punishment din da Lion (MD) yayi musu, Jazzeelah da Abidah.
Jin yayi shiru yasa Mommy tace, "Ko baka jina?"
"Sorry Mommy, wasu yara kuma, kawai?" Sai kuma ya tuna, ya ce, "Subuhanallahi! Wallahi na manta su Jazzeelah! Wayyo, suna nan bangaren ki ne?"
"Aa suna can bangaren Hajja Kaka."
"Okay tom Mommy, shi kenan, bari naje yanzu nan." Ya yanke wayar, yana sauke ma MD harara, wanda shi bema san me yake yiba, gaba daya hankalin shi ya tafi kan system din shi da yake aiki a kai, laptop din sa.
Mikewa yayi Jameel, kafin ya dauki akwatin agajin gaggawa (First Aid Box) ya fice daga part din.
Ko daya karasa part din Hajja Kaka, zaune ya same ta akan dadduma, da alama sallah ta idar, amma har yanzu bata daina mita ba. Tana ganin shi ta mike, tana fadin, "Ina azzalumin? Kuma Jamilu, kai ko a rayuwan ka, kaji haushi, kana tare da mutum bazaka dinga gaya mishi gaskiya ba? Ayi mutum ba, abin daya iya sai bakin hali da nukufircin tsiya. Yayi da k'ira kamar Samudawan farko. Nidai wallahi, duk a yayana babu mai irin wannan halitar, sai dai idan a can dangin uwarshi ya dauko shi!"
Shi ko Jameel, ka rasawa yayi, bai tanka mata ba, kafin ya fara ciro kayan aiki, yana duba su, dan shi ma ya tausaya musu, ya duba gwiwowinsu. Barin ma yanda ya ga yaran suna ta kuka, gwiwowinsu sunyi kumburi, jajir. Allurori ya musu, kafin ya basu magunguna, tare da man zafi da za'a dinga shafa musu.
Da daddare kuwa, da misalin karfe 11 na dare, Abidah da Jazzeelah suka farka da zazzabi mai zafi. Zazzabin ya kai 39 zuwa 40 digiri. Suna rawar sanyi, suna kuka, suna hargowa. Abidah ita bata surutai, ita ko Jazzeelah fadin take, "Wayyo kafa na ciwo! Kafa na ciwo! Ko tafiya bana iya yi, Hajja, cinyoyina ciwo suke min Hajja!" Zuwa safi kuwa, dole sai da Aunty Amarya (Murshida) ta zo ta taimaka ma Hajja, saboda basa iya komai, sai an taimaka musu. Ko bandaki ma sai an taimaka musu.
Duk tsawon dare, Hajja Kaka na tare da su, a nan dakin ta kwana da su. Ta kasa bacci. Tana zaune a gefen gadon, tana daura musu jikaken towel mai sanyi a goshi, tana musu addu'a, tana shafa musu baya.
"Abidah, me ya sa kuka je da irin wannan kayan? Na fada miki, Muhammadu baya so. Yanzu kin ga abin da ya faru?" Ta ce.
Kuma haka aka yi. Da daddare, da misalin karfe 11 na dare, Abidah da Jazzeelah suka kwanta a daki daya, a gado daya, suna za
Aunty Amarya (Murshida) ce ta kwana a dakin nasu. Saboda Abidah 'yarta ce, ta kasa bacci. Tana zaune a gefen gadon, tana musu borin ruwa a goshi, tana musu addu'a, tana shafa musu baya. Tana kuka, tana cewa, "Abidah, me ya sa kika je da irin wannan kayan? Na fada muku Muhammadu ba Imani ne da shi ba, kuma baya so kuna irin saka wa'innan kayan na yaran zamani mara amfani. Yanzu kun ga abin da ya faru?"
Abidah ta ce cikin zazzabi, tana rawar murya, "Hajja, Dan Allah ki yafe mana, wallahi ba zamu sake ba. Kafa na ciwo, Hajja, kafa na ciwo."
Jazzeelah ma tana fadin, "Hajja wallahi ba zamu sake ba. Dan Allah ki ce Hamma Muhammad ya yafe mana."
A part din Hajiya Aisha Miemie, labari ya isa cewa yaran sun yi zazzabi, ko tafiya basa iya yi. Kuma Hamma Muhammad taji musu ba dadi, amma duk da haka gwara su akan su Firdausi. Dan akwai ranan da sai daya sumar mata, har yanzu da suke da aure, har da yara, suna shakkan shi wani lokacin.
Bahayurah da ke zaune, ba ta ji tausayin su ba. Sai ta tashi da sauri, siririyar jikinta yana bayyana a cikin karamar *ZARA Crop Top* dinta, ta ce da turanci, "Oh my God! They have fever? Like, seriously? Because of frog jumps? Oh my God, MD is so strict! I love it! Like, a real man! So dominant! I love dominant men!"
Miemie da idanu kawai take binta, dan Hajiya Jumai tunjiya ta bi jirgi ta koma Abuja, amma ta ce zata bar Bahayurah saboda a samu su hadan kansu, su daidaita, kafin ta koma a fara shirin biki.
Bahayurah ta ce, "Miemie, yes! It's so hot! I'm going there, I want to see him! I want to see MD! Maybe he is there!"
Ta dauki wayarta, ta nufi part din Hajja Kaka da sauri, tana takawa da takalmi mai tsini, hips dinta babu komai amma tana girgiza su, ita a dole ga mace.
Miemie ta kalle ta tana fita, ta girgiza kai, ta ce, "In ba da ina da manufa akan auran nan, yarinyar nan kwata-kwata a ajin Muhammadu bace."
Bahayurah ta shigo, ta tsaya a kofa. Ta ga MD sanye cikin wata shadda *ash color*, ba karamin fitinan kyau shaddar na yi mishi ba, kanshi sannye da hula, tangaran fura shigo wanshi kenan gidan, ya taho part din Hajja Kaka ya same damamiyar furar da ba'a raba ta da shi, ya sha, dan kusan zai ce a wajenta ya samo kaddarar shin fura, indai bai sha ba ya kan ji bashi da sukuni. Ta tsaya cak, zuciyarta na bugawa.
Ta yi murmushi, ta cije lebe, ta ce, "Hi, MD... Like, I heard what happened... I brought perfume for them... but... you look so handsome in that shadda... Like, so handsome..."
MD ya daga kai, ya kalle ta. Ya ga siririn jikinta, Zara shirt din da ya nuna cikinta, wandon *Jean Palazzo*, mayafin da bai rufe komai ba ta daura a kanta. Fuskar sa ya kara hadewa, yana jin gaba daya ya tsani yarinyar, har wani tashin zuciya yake ji idan ya ganta. Dan haka ya mike cikin izzar nan tashi, ko kallon sashin inda take be yi ba, ya fita daga falon, yana tafiya, yana jin bacin ranshi na sake tashi.
Bahayurah ta rufe idanu, tana shakar kamshin *Oud* dinsa da ya rage a iska, ta ji wani irin sanyi a jikinta, ta fada a ranta, "Oh my God! Wallahi ko duniya ce zan bayar domin ka, MD, zan bayar! I will do anything! Anything for you! Even if you say I should die, I will die for you! I love you!"
Hajja Kaka ta juyo, ta gan ta tsaye a kofa, ta ce da tsawa, "Ke kuma me kike yi anan? Wannan wace irin shiga ce? Wace tarbiyyace Uwarki ta baki? Fita! Fita daga falona!" Ta kare maganan tana sakar mata harara!
Bahayurah ta fita, amma a zuciyarta tana jin gaba daya ta tsani tsuhuwar nan.
MD na zaune a garden, cikin rigar *mai hannu singlet* da *gajeran wando*, sai *silifas mai taushi* da yake sanye cikin kafafuwan shi. *(Kayansa na kamfanin Nike - Nike Dri-FIT Singlet, da Nike Shorts, da kuma Adidas Soft Slides)* wanda suke kamar ka cinye su danye, shi kadai, yana tunani, maganar Miemie na maganar aure, baya jin zai iya auran yarinyar nan, dan kwata-kwata bashi ba. Idan ko Miemie ta matsa, to sai dai ta nimo wata, amma ba dai wannan yarinyar ba.
Safiya ta yi. Misalin karfe 5:30 na asuba. Gidan ya yi shiru, sai karar tsuntsaye, compound din ya hadu da gasken asuba, ga kuma hasken fitillun da suka haska gidan, sai iska mai dadin sanyi na asuba dake kadawa.
Hajja Kaka ne ta tashi, dakin da suke kwana, dan ta tashe su suyi sallah. Karasawa tayi gaban gadon, Abidah ce a farko, sai data dan bibige ta, tana kiran sunan ta, kafin ta bude ido.
"Abidah," ta ce da murya kasa, "Ya kike ji yanzu? Zazzabi ya sauka?"
Abidah ta bude ido da kyar, muryarta na rawa, "Hajja... da sauki Hajja."
"To tashi ku yi sallah," Hajja Kaka ta fadi, tana shafa kanta, ta sake jin tausayin su, "Shhh, ki yi shiru, to a tashi a yi sallah."
Jazzeelah ma ta bude ido, ta ce, "Hajja..."
"Na'am yar albarka, kin tashi? Ku tashi ku yi sallah..."
Misalin karfe 6:00, aka kira sallar asuba a masallacin kusa da gida. MD da Jameel suka fito daga part dinsu, suna cikin *jallabiya*, sun yi alwala, suka nufi masallaci. A kan hanyan su na dawowa daga masallaci, suka gaisa da iyayen nasu maza, Baba da Baffa, dan Daddy shi baya ma kasan.
Hajiya Aisha Miemie ta tashi da wuri, har ta shiga kitchen, ta fada ma Inna Asabe abin da za'a dafa musu na breakfast, amma Bahayurah na kwance a daki, tana bacci, bakinta a bude, gashinta ya bazu a kan pillow, sakamakon *syrup din* da ta sha na yau, mai karfi ne, dan daker da samu Kure Dani ya kawo mata jiya, ta san dabaran da tayi ta je ta karbo.
Miemie ta shiga dakin Bahayurah, ta tada ta, "Bahayurah! Tashi! Karfe 7 ya yi! Ba zaki tashi ki yi sallah ba ne, amma kina bacci har yanzu?"
Bahayurah ta mike da kyar, kirjinta yana bayyana a cikin karamar *nightie*, ta yi hamma, ta ce da turanci, "Miemie, what? Like, why are you shouting? It's too early! I was dreaming about MD! Oh my God, I was dreaming he was holding me!" Duk wannan maganan da take yi bata san me take fadi ba, saboda har yanzu syrup din be sake ta ba.
Miemie ta ja ta, "Tashi ki yi wanka! Ki saka kaya ki yi sallah kafin raina ya baci!"
Bahayurah ta tashi, ta shiga wanka, ta fito, ta saka wata karamar riga ta *bodycon red*, wacce ta kara nuna siririyar jikinta, da skirt mai dan fadi, mayafi ta saka. Ta fesa turare mai tsada, ko sallah bata yi ba, ta fice.
---
Masu bukatar a musu tallah zaku iya tuntubana ta wannan number 馃憠*** MRS CLASSY WRITE nagode馃檹
鉁嶏笍 Mrs Classy | Author of RABO DA
KADDARA 馃挃
Hausa Romance & Kaddara | Read on ArewaPen 馃憞