Free chapter · Read without an account

33. ... he's a vampire...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)




A tare muka shigo gidan da Roman dake saman mashin ɗinshi..naji zuciyata ta fara zallo a ƙirjina...ya riga mu parking ya sauka ya shige ciki...kamar in kira shi amma kawai sai na barshi... parking Khalil yayi muka fito... mutanen dake compound ɗin ya kira suka taya kwasar kayan da ya siya min zuwa sashen mu baƙar ledar nan kuma da kanshi ya riƙe ta muna tafiya tare...hankalina yayi wani wurin daban... babu wanda ke magana a cikin mu har muka iso ƙofar shiga sashen namu...miƙo min ledar yayi na karɓa

'' sai da safe'' ya furta babu murmushi a fuskar shi kamar koda yaushe..gyaɗa kaina kawai nayi ina mamakin anya lafiyar shi qalau kuwa?

***

'' me kake nufi daya daki mutanen ka Black and blue? Duk kuɗin dana baku?...'' Farzan ne ya shigo ɗakinshi tare da banka ƙofar da ƙarfi kamar zai karya ta 

'' You know what? Forget it!! You're a bunch of...'' naushi ne ya sauka a gefen fuskarshi daya sa wayar faɗuwa daga hannunshi,haɓarshi ta bada cracking sound... yayi baya baya zai faɗi yayi steadying kanshi da ƙyar....bai gama warkewa daga zafin naushin ba na biyun
 ya biyo baya saida ya jefar dashi saman kujerar dake bayanshi


'' Ahh! What the...'' cakumo collar shi Roman yayi towering over him... Like a devil,eyes dangerously cold,red glow ɗin dake ɗakin ya ƙara bashi wani irin dark aura...idonsu ya haɗu...goga haƙoranshi farzan ya shiga yi fuskar shi a yamutse,ƙirjinshi na sama da ƙasa...

'' your tricks are as dumb as you...and I absolutely hate...DUMB FU*CKS.. standing here with you is already enough insult but what to do...wasu mutanen daƙilai ne idan ba'a fito musu mutum a ba, they can't read the signs..the day i finally decide to even the scores,you won't survive!" Jikin Farxan babu abinda yake sai tsuma yake ji kamar ya soka ma Roman wuƙa a ƙirji har sai ya dena numfashi,sakinshi Roman yayi da ƙarfin daya sa kanshi haɗuwa da kujerar da yake zaune a kai ya nufi hanyar fita...Farzan ya miƙe ya rausayar da kanshi gefe...


'' want something new... careful what you wish for.. Brother!" buɗe ƙofar Roman yayi batareda ya juyo ba yace '' bring it on...Fallito!" Bed side lamp Farzan ya jefa ma ƙofar bayan Roman ya rufe...yasan ma'anar 'Fallito' mutumin da har abada bazai taɓa nasara ba!

Cusa hannayenshi yayi cikin sumar kanshi sai kuma ya fara buɗe button ɗin rigar shi ko iska zai rage mashi abinda yake ji a zuciyar shi....'' zaka gani...zan rikita rayuwar ka...ka daɗe daka shiga ɗakin hukunci ko...well, let's see ..'' faɗawa Farzan yayi saman gadon shi with a maniacal smile...

***"

Washe gari Litinin muna da jarabawa da ƙarfe biyu... da safe bayan na tashi nayi wanka na sauya kaya..ƙara komawa kitchen nayi da fatan zan haɗu da Roman amma har masu girki suka shigo babu shi babu alamun zai shigo...na fito na wuce sama..tunda har yanzu safiya bata iyarda waye ba na wuce lambu..ta rufin nake hango sama da alamu za'ayi ruwa...Black rose na tsinka da ƙyar bayan ta gama soke min hannu ban san da cewa tana da ƙaya ba...inata juyawa a hannuna ko ta waye?

Zagaye wurin na cigaba dayi ina kallon furannin masu kyau da ƙamshi...runtse idona nayi ina imagining nida Roman ne a wurin..ina a gaba yana tsaye daga baya na da murmushi a fuskar shi yace ' Abeedah ina sonki sosai' buɗe idona nayi na saki dariya...amma kuma murmushi? Ban taɓa ganin yayi murmushi ba ko sau ɗaya kuma bai taɓa kiran sunana ba...yasan sunana?

sosa gefen fuska ta nayi kafin na fita daga wurin zuwa ɗakinshi...wai nama taɓa shiga kuwa? sau ɗaya da daddare...

Tura ƙofar parlorn nayi ta buɗe Batareda ƙara ba...na kalli ko ina dake a tsabtace ban taɓa ganin masu aiki a sashen shiba...ƙofar ɗakinshi na tunkara..zan ƙwanƙwasa aka buɗe ƙofar na firgita sosai nayi gaba zan faɗi..matsawa gefe yayi kada in faɗo mashi shi mugu...kuma bai ko taro ni daga faɗuwar ba...kamar abinda yake fata shine in faɗi ɗin....

Da ƙyar na samu na riƙe gefen ƙofar na tsayu da kyau....na ɗago idon mu ya haɗu fuskarshi a ɗaure yayi kama da vampire...ga laɓɓanshi da suka ƙara ja kamar yasha jini... kodai jini yasha? Kodai vampire ne?idan na gani dakyau kamar harda ratsin fari a cikin gashin shi....kuma vampires idan basu sha jini ba sai su fara tsufa gashin su yayi fari ƙarfin su ya ƙare 

'' Me kike yi anan?" Muryar shi bata ɓoye jin haushin shi na kasancewa ta a sashen Shiba...'' you're an unwanted guest kin sani ko?" ya sake furtawa...ɗauke idona nayi daga kallonshi na haɗiye iska sannan nace '' xama unwanted guest shine abinda yafi nishaɗantar dani...kai Vampire ne? Inga haƙoranka...'' 

Hannun shi dake motsi akan ƙofar na kalla Nasan abu na gaba shine ya rufe ƙofar a fuskata ƙasa nayi na shige cikin ɗakin...ya juyo da sauri lokacin har na kai tsakiyar ɗakin nashi mai faɗi da kyau .. komai baƙi sai bangon dake gabas glass ne daga sama har ƙasa an kwashe baƙin labulen daya kasance kamar shamaki...


'' xoki fita...i don't like ppl invading my space!" Juyowa nayi na ƙare mashi kallo saye yake da guntun wando da riga mai guntun hannu baƙaƙe kamar yanda vampires koda yaushe suke saye da baƙaƙen kaya,gashinsa har saman idonsa na hagu

Dawowa nayi na tsaya gaban shi,duk da inada tsawo yafini tsawo sosai.. na koma wata yar ƙarama gabanshi na ɗago idona ina kallon shi'' kai Vampire ne?like a high breed vampire?" Sai kuma na mayarda kallona akan wani cup dake ɗauke da jan abu kamar jini...jinina ya daskare... idona suka fito

Matsowa ya farayi ina matsawa baya '' idan ni vampire ɗin ne..kinzo ki bani jinin kine?" haɗuwar bayana da bango ya kawo ƙarshen matsawa baya... runfa yayi min da ƙaton jikinshi yana kallona kamar mafaraucin daya ga abinci... tsananin tsoro ya shige ni...'' uhmm?" yayi humming


'' Uhmm..ai kai...uhm ba vampire bane " Na faɗa confidently..ai vampires suna da haƙori zago zago ina nashi...?

'' how so..?" yayi ƙasa da kanshi gefen wuyana kamar zai cije ni '' I can...smell your blood... yana sani ina jin yunwa ...'' yayi maganar yana shinshinar wuyana kamar yanda Vampires suke yi..ture ƙirjin shi nayi jikina na rawa...ƙafafuna sunyi sanyi sosai '' Uhmm...ina... haƙorinka nnn...na vampire?" na tambaya ido gwalale

dawo da fuskarshi yayi daidai tawa... zuciya ta kamar zata fito ta baki...ya buɗe min bakinshi..na gani..shima yana dasu...farare tass! Ya akayi ban taɓa gani ba? Wayyo Allah na... shi yasa yake amfani da turare masu tsananin ƙamshi ashe abinda yake ɓoyewa kenan?

'' yanzu..xan iya sha?" girgiza kaina nayi idona suka ciko da hawaye...idan fa ya shanye min jini na mutu?

'' a'a dan Allah kayi haƙuri...'' nayi ƙoƙarin matsawa daga kusa dashi...dawo dani yayi ya ƙara trapping ɗina tsakanin shida bango,mugun turaren shi na neman shaƙe ni kafin shi ya iyarda aikin ta hanyar shanye min '' No..." Ya furta yana jan hijabina, idonshi cikin nawa corner bakin shi a ɗage.. Innalillahi wallahi kamar sheɗan, harda ƙaho na gani a saman kansa..riƙe ƙarshen nayi ina kuka wiwiii

'' dan Allah ban so in mutu...kayi haƙuri...'' 

'' ai ba kashe ki xanyi ba... kaɗan zan sha...'' yanda yanayin shi ya canja ya sake sani a tsoro...babu shakka wannan mutumin vampire ne,ƙasan idonshi yayi ja...sauran jikinshi fari kamar paper...gaske yake sa turaren mai nauyin ƙamshi ashe yana rufe ƙarnin jini ne ..

'' dan Allah...'' kafin in gama ya karkatar da kanshi gefe going for my neck,zago zagon haƙoranshi a bayyane

'' KHALIL!!!!!!!!" na kira da ƙarfi ido rufe na ture shi da duk ƙarfin da nake dashi na sheƙa da gudu ban tsaya ko ina ba sai sashen Khalil dake fitowa daga ɗakinshi...muka ci karo...ƙanƙame shi nayi jikina na rawa sosai...

'' Oh... KITTEN meya faru?" yake ta maimaitawa ganin yanda na rikice, cikin kuka na ɗago Fuskata nace '' Romo ne yace... zai shanye min jini..ashe vampire ne...'' 

Zaro ido Khalil yayi '' shi Roman ɗin?" na gyaɗa kaina...riƙo hannuna yayi '' muje in gani...'' da ƙarfi na fisge hannu na '' wallahi baxan tafi ba...''

dariya Khalil ya saki '' come on...wasa yake maki ba vampire bane..'' girgiza kaina nayi''ya nuna min haƙoranshi suna da tsawo kuma ƙasan idon shi yayi ja fatar shi kamar paper...''


Dawowa yayi ya zaunar Dani akan ɗaya daga cikin kujerun ya bani ruwa insha bayan na gama ya zauna can ɗayar kujerar yana kallon yanda jikina ke mazari...

'' mutum ne fa...wannan...canine teeth nima ina dashi kin gani...'' buɗe bakinshi yayi na gani shima yana da irin haƙorin Roman...a firgice na tashi zan tsere ya damƙo hannu na...'' come on...ba cizon ki zanyi ba ..nima mutum ne kin gane...ba dole vampire kaɗai keda canine teeth ba kema kina dashi...''

Jana yayi zuwa ɗakinshi muka tsaya gaba madubi...'' buɗe bakin ki kigani...'' buɗewa nayi ya nuna min wai kenain tit...taya ni ban taɓa ganin wani mai shiba sai su?

'' kin ga naki basu da tsawo...'' 

'' oh...amma ai naga jini cikin wani cup a ɗakin shi...''


'' he's an artist kitten... ƙila painti ne ba jini ba!" na gyaɗa kaina...tare da sauke numfashi...'' kawai ya sani kuka a banza a wofi...''naja tsuki

Daga ƙarshe tare da Khalil na karya daga lokaci zuwa lokaci yake kallona ya tuntsire da dariya...na turo baki..bayan mun gama na tafi ɗakin Diyaam mukayi karatun civic education Dan shi muke dashi yau...har ƙarfe ɗaya sannan ta biyoni part ɗin mu na shirya muka tafi tare...kafin nan munsha kallon banza da alamu itama ba sonta suke ba


Dana tambaye ta meyasa cewa tayi dan kawai itama yar aiki ce amma Roman ya kaita sashen masu gida take samun gata fiye dasu shine yasa...



Yauma kamar koda yaushe,duk da sauƙin jarabawar mutane sun biya a basu amsa...can naji wasu malaman suna hira wai pepopin da mukayi mutane da yawa sun faɗi... gabana ya bada dum! idan fa nima ina cikin wa'yanda suka faɗi ɗin? ya zanyi...har lokacin tashi gaba ɗaya raina ba daɗi kamar inyi kuka...yau ni kaɗai na dawo abina ban jira Diyaam ba..nabi wata doguwar hanya...tunani na duk akan idan na faɗi jarabawa ne..hakan ya haifar da fargaba da ƙunci a raina... ƙarƙashin bishiya na zauna nayi abinda na daɗe banyi ba...na daɗe ina kuka kafin na tashi na cigaba da tafiya nayi rabin hanya aka tsuge da ruwa...hakan ya ƙara ma kuka na ƙarfi danaga Ni kaɗaice a hanyar...a da abinda nake ƙorafi akai kawai shine halitta ta, amma akwai wani ciwon da zuciya ta ta ɓoye wanda take tsananin tsoro...na farko idan fa ni a matsayin mutum ban isa ba?(not good enough) idan fa bayan duk ƙoƙari da addu'a da komai na faɗi jarabawar? Idan fa har ƙarshen rayuwata duk wani abu da nake addu'a akai bai faru ba? Ya zanyi? Idan fa abubuwan da koda yaushe nake tsoro suka dinga faruwa despite my efforts?


wata motace ta wuce ni da gudu ta fallatsomin ruwan datti,farin hijabina ya rine da sauri ya zama brown haka ma wani sashe na rigata... idanu na suka ƙone da hawaye na cigaba da tafiya ruwan na ƙara jiƙani suka wanke wani sashe na uniforms ɗin nawa...wata baƙar mota ce tayi parking daga can gefe da sauri wanda ke baya ya fito riƙe da lema ya iso inda nake ya riƙe lemar ta saman kaina

Juyowa nayi... Khalil ne fuskar shi da damuwa..shi bai samu shigowa ba ruwan jiƙe shi suke ta baya amma bai damuwa ba sai magana yake min... bana jin abinda yake faɗa... idona suka fara ganin duhu duhu... kafin suka rufe ruf!!

*****

Buɗe idona nayi suka saukan akan farin ceiling..jikina ba ƙwari na juya gefen da aka kwashe labule... kamar sauran ɗakunan transparent glass wall ne,ina hango bishiyoyin tsakar gidan... kallon ɗakin nayi ya haɗu sosai da komai na ciki pink harda bedsheet da blanket sai wani pink paint daga can saman gado.. carpet ɗin shima pink...sai yellow Lights dake kunne da kuma candle dayasa ɗakin ɗumi duk da ruwan da ake shakakawa a waje..ga wani daddaɗan ƙamshi dake tashi


Kallon kaina nayi na ganni saye cikin fararen kaya riga da wando harda farar singlet irin ta maza... gwalalo ido nayi... zuciya ta na bugu da ƙarfi waya canja min kaya? 

Tashi nayi na isa gaban mirror dake ɗakin... kaina babu ɗan kwali...kalabar da Diyaam tayi min ta sauko har saman wuyana alamun gashina ya ƙara tsawo...nayi murmushi Batareda nasan cewa bala'i zai cimma gashin ba...
For now wannan ba shine abu mai muhimmanci ba,waya canja min kaya? Idan Khalil ne sai na dafa shi na cinye shi ɗanye...

Autumn: taya zaki dafa shi kuma kici shi ɗanye?

Abeedah:Bakisan figures of speech ba? oxymoron,paradox...oho... anyways

Ina tsaye ina tafasa sai gashi ya shigo ɗakin ya sauke ajiyar zuciya '' Oh.. Kitten thank God...me kike tunani da kike tafiya cikin ruwa?" Ya riƙo fuskata a hannun shi tsantsar damuwa bayyane a fuskar shi..

'' me nake tunani? Result ɗin jarabawar mu...ba wannan bane mai muhimmanci..''

Na kaɓe hannun shi daga fuska ta '' waya canja min kaya?" nayi tambayar ina tapping ƙafafuna a ƙasa,hannu a ƙugu...

'' ehmm...'' sai ya sosa ƙeya tare da ja baya...abinda nake tunani ne kenan..

'' KHALIL!!" na kira da ƙarfi ina hararar shi tare da matsowa.. shima yana ja baya...sai kuma ya juya ya fara gudu...ina biye dashi muka zagaye ɗakin '' ka tsaya mana...'' yana dariya yace '' a'a...''

'' tambaya kaɗai zanyi..'' na furta sai ya tsaya bayan mun gama mayarda numfashi nace '' waya canja min kaya?" Muna haki sosai nayi tambayar

'' Meye ma sunan ta? fauziyya.. Hansa'u ?yeah!" 

'' MEYE?" Maganar ta fito da ƙarfi idona waje

'' you look disappointed...kinyi fatan ace nine?" kunnuwana sukayi ja taya za'ayi inso ace shine...

'' wai ma ..'' na Harare shi inaja baya...yake matso wa '' oh really? Meyasa kika turo baki kamar hakan bai maki daɗi ba? Anyways i was going to do it but I decided against it..." Yayi maganar da murmushin gefen baki,kaina a ƙasa duk zafi yasha min kai duk da sanyin da ake makakawa 

rasa abun faɗa nayi '' kai wannan Khalil ɗin...'' nayi ƙoƙarin barin wurin da gudu ɗauke ni yayi sama yana jujjuya ni yace '' ke wannan Abeedah'r...'' 

Ina dariya nace '' kada fa kasa mu faɗi...''


'' ai zan iya riƙo ki kafin ki kai ƙasa.... I'll always do that...''


🍁🍁: are you sure you're not a two timer Khalil Roman?

Abeedah: multiple timing.. besides I can't help it da Khalil.. it's just different ina jina free... 


***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️










































Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.