Free chapter · Read without an account
Page 14
SAWU BIYU
BY
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 14
Bayan an tashi driver ya zo ya ɗauke su ya mai da su gida,Mami da dawowarta daga wurin aiki kenan ta kai shi har apartment ɗin Sudais mai ɗauke da ɗakuna huɗu kowanne da toilet a ciki.
A gyare yake har da karamin gado da wardrobe.
Bayan ta gama nuna mishi ko'ina tace"daga yau nan ne ɗakinka,idan ka kwana a can makaranta sai ka zo nan ka shirya ka wuce School."
Sadauki yayi shiru kanshi a ƙasa,anya akwai abinda zai iya biyan mutanen dashi?
"Nagode Allah ya saka da alkhairi..."
Mami tayi saurin dakatar dashi tace"babu godiya tsakaninmu Faruq,kai ɗana ne,abinda muke so da kai shine kayi karatu sosai,mun yarda da kai,kar ka watsa mana ƙasa a ido".
Tun daga ranar idan an gama karatun safe zai bar makaranta da wuri ya shigo gidan ya shirya cikin uniform din shi su wuce makaranta.
Sai washegari ya san Sudais makarantar yake kuma ajinsu ɗaya.
Kamar yadda bai kula shi ba shima ko kallon inda yake bai yi ba.
Kusan ko wani lokaci suna tare da Abduljalal,duk da zuwan Sadauki ya sa ya rage wani shiriritar.
Babu komai tsakaninsa da Zarah sai gaisuwa duk da yadda take shige mishi,babban abokinta shine Sudais,ya kan biyewa duk shirmenta ba tare da ya gaji ba.
Sai dai duk lokacin da ta nemi faɗa wurin Sadauki take zuwa direct,gashi sosai ake shakkar shi a makarantar ba don komai ba saboda yanayin kamewarsa,bai da hayaniya ko kaɗan.
Akwai waɗanda ko muryarsa basu taɓa ji ba balle dariyarsa.
Ranar suna karatu tare da Abduljalal ta shigo kamar an jehota,kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai.
Tana zuwa ta riƙe hannun shi tace"Yaya F,ka ga wata yarinya ta zage ni wai gani kamar jan ƙosai".
Ya watsa mata wani kallo da yasa tayi saurin sake mishi hannu tana turo baki.
A hankali yace"shine sai kin riƙe min hannu?"
Abduljalal yace"kai wannan kanwar taka akwai rigima catalyst,ke baki gajiya da faɗa ne?"
Zarah ta wani harare shi ƙasa ƙasa, Sadauki dake lura da ita yace"ke me kika mata,haka kawai ba za ta nemi faɗarki ba".
Ta turo baki tace"don nace mata goshi kamar jirgi".
Ya watsa mata harara yace"bar nan".
Ta fashe da kuka ta bar wurin,Jalal ya fashe da dariya yace"Allah ka shiryi Zarah,kullum cikin neman magana take".
Sadauki yayi ƙaramin tsaki ya cigaba da karatun da yake.
Daga wurin Sadauki class ta shiga ta sanar da Sudais zagin da yarinyar ta mata,da sauri ya riƙe hannunta yana share mata hawaye suka tafi har wurin yarinyar.
Yana jin abinda yarinyar tace ya juya yana kallon Zarah yace"ke kika fara zaginta Zarah,why?"
Ta turo baki ta ɗauke kai don itace ba ta da gaskiya,ya ba yarinyar hakuri suka bar wurin
Duk abinda suke Sadauki na kallonsu,ya ɗauke kai ya cigaba da abinda yake.
A can makaranta babu wanda ya san rayuwar da yake a waje,duk da Sadiq ya so ya fahimci wani abu amma kasancewar he is very smart yasa koda wasa bai taɓa kawo wani abu a ransa ba.
Akwai ranar da ya shigo yaji kamshin turare mai ƙarfi sosai,ya kalle shi da kyau yace"ina ka samo turare mai kamshi haka Sadauki?"
Da ɗan mamaki yace"turare kuma,ina zan sami turare balle mai kamshi ni da nake almajiri?"
Sadiq ya gyada kai cike da gamsuwa don ya san abu ne mai wahala almajiri dake neman abin kaiwa bakin salati yasa turare mai kamshi haka.
Tun daga ranar ya sake kiyayewa, idan ya tashi a School ya wanke uniform din shi yayi wanka sai ya maida kayan da aka san sa dashi a makaranta.
Sosai yake karatu with all his life,wani lokaci Abduljalal ya kanzo har gidan suyi karatu tare,kuma koda wasa bai taɓa kawo Sadauki ba ɗan gidan bane.
A ɓangaren Hajiya Mama kuwa tun ranar data kyallare ido taga Sadauki a part din Sudais ta hau masifa.
Har bedroom ta sami Daddy tace ita ba ta yarda yaronta ya zauna tare da almajiri ba.
Ko kallonta Daddy bai yi ba,a ƙarshe da ya ga abin nata bana ƙare bane yace"idan gidanki ne ki kore shi Maimuna".
Daskarewa tayi a tsaye tsabar shock,bata taɓa tunanin zai faɗa mata wannan maganar ba.
Da jan jiki ta koma part ɗinta ta zauna kan gado, Jidda ta matso kusa da ita tace"Mama me Daddy yace,yace zai kore shi?ni wallahi na tsane shi Mama,gashi ko gaisuwa bai iya ba sai ji da kai kamar ɗan wani mai kuɗi,gaka almajiri ɗan talakawa".
Mama tace"miƙa min wayata Jidda".
Da sauri ta miƙa mata wayar ta koma ta zauna kusa da ita.
Har wani dishi dishi take gani tsabar masifa,tayi dailing numbern babbar ƴarta Maryam dake aure a Katsina.
Tana ɗauka ta sanar da ita abinda ke faruwa,sai da ta jira ta gama sannan tace"Mama ki dinga haƙuri dan Allah,tunda yaron nan ba'a kanki zai zauna ba ai shikenan,kuma ke ma kin san Daddy ya miki kawaici sosai akan Sudais tunda ba shi ya haife shi ba".
Cike da ɓacin rai tace"ba shi ya haife shi ba amma ai ɗana ne ko,wai Maryam wani irin magana kike haka?"
Maryam ta sauke numfashi tace"Mama,ki yi hakuri idan maganar da nayi ta ɓata miki rai, honestly bana son wasu abubuwan da kike,ita Mami da kike damuwa da ita bata san kina yi ba, Daddy ya riƙe Sudais tamkar ɗan da ya haifa,bai kamata ki ɗaga hankalinki ba".
Mama tace"dama na san ba za ki goyi baya na ba Maryam,ke da Sudais tamkar bani na haife ku ba,ai shikenan".
Maryam tace"dan Allah Mama ki yi hakuri ba haka nake nufi ba".
Hajiya Mama ta kashe wayar rai ɓace, tun farko bata san dalilin da yasa ta kirata ba.
Da yamma bayan ya dawo daga makaranta yana ƙoƙarin shanya Uniform dinsa da ya wanke Hajiya Mama ta zo wucewa,ya sauke kai a nutse yace"Ina wuni".
Ta juyo cike da wani irin ɓacin rai da masifa ta nuna shi da yatsa tace"kar ka sake,ko da wasa idan ka ganni kar ka sake gaishe ni,bana buƙata,ka cigaba da gaida Hafsah ita ke da buƙatar gaisuwar ka,kai ko shadow dina ka gani kayi gaggawar canza hanya babu abinda ya haɗa ni da ɗan maula,mai bara a kan titi yana neman abinda zai ci,muna nan da Hafsah watarana sai ka basu kunya sau nawa a ka yi?a dauko ku daga rana a kai ku inuwa daga ƙarshe ku watsawa mutum ƙasa a ido ku kaishi rana tsundum".
Mami da isowarta wurin kenan tace"babu abinda zai faru sai alkhairi, Faruq wuce ka shiga ciki".
Ya maida rigar hannun shi cikin bucket ya juya ya shiga ciki.
Hajiya Mama ta watsa mata kallo cike da tsana ta bar wurin.
A hankali Mami tace"Allah ya min tsari daga sharrin ki".
Ta ɗauki Uniform ɗin ta shanya mishi ta koma ciki.
Ko da ya fito ya tarar da kayan a shanye murmushi kawai yayi ya koma ɗaki.
Yana kwance Zarah ta shigo part ɗin,jin tana knocking ya sa ya zuro jallabiya ya fito.
"Yaya F,homework na kawo ka min,Ya Sudais is not around".
Calmly yace"fita waje".
Ta waro ido tace"Yaya F,idan ban yi homework ba Aunty will flog me".
Ya watsa mata harara yace"ai gara ta miki duka tunda ba ki jin magana,ban hana ki shigowa part ɗinnan ba?"
A hankali tace"ka hana".
Yace"then taurin kai yasa ba ki ji ba kenan,get out".
Ta juya tana turo baki ya maida kofar ya rufe.
Tana isa compound ta ji motsi a bayanta,tana ganin shine tayi murmushi ta share hawayen da ya wanke mata fuska.
Wurin empty chairs dake compound ɗin ya wuce ya zauna,da sauri ta zauna ta buɗe School bag ɗinta ta fito da books ɗin,tana JSS One zata shiga two.
A nutse ya dinga mata bayani harta gane ya mike ya koma ciki.
Daddy dake zaune a balcony ya bishi da kallo.
A haka suka fara shirin rubuta WAEC,karatu suke sosai shi da Abduljalal.
Sai ya gama karatu a gidan kafin ya koma makaranta,tsakaninsa da su Bala da Tanko sai dai kallo don tunda daɗewa suka fita hanyar sa.
Sosai Sadiq ya sa masa ido don ji yake bai yarda da shi ba,kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin kwanciyar hankali.
Duk abinda yake Sadauki na lura dashi,ba wai yana tsoron Sadiq ya san abinda yake ɓoyewa bane,bai son abinda zai kawo mishi cikas a cikar burin shi ne.
Bayan watanni biyu suka fara zana jarabawar barin Secondary School,abinda Sadauki bai taɓa tunanin zai yiwu ba.
Bayan sun gama rubuta exams suka koma zaman gida,a halin yanzu baida babban aboki kamar Abduljalal,duk da akwai tazara mai faɗin gaske tsakaninsu,na farko Abduljalal ya kasance ɗa ɗaya tilo a wurin mahaifinsa,babban ɗan kasuwa kuma mai faɗa a ji a ƙasar,na biyu mutum ne shi mai yawan fara'a da wasa saɓanin Sadauki da magana wuya take masa wani lokacin.
Abota ce da aka gina ta tsakani da Allah babu wata karya,ranar da Sadauki ya sanar da Abduljalal matsayinsa a gidan ba ƙaramin mamaki ya sha ba,kuma hakan bai sa ya ji a ransa Sadauki ba sa'ar sa bane.
Wani abu da ya ƙara ƙarfafa alaƙarsu kuwa shine burin da suke dashi iri ɗaya,a duniya babu abinda Abduljalal yake da burin zama kamar soja, sai dai mahaifin shi yaƙi yarda,so yake yayi karatun da zai cigaba da kula da dukiyarsa,shi kuma yace idan ba soja ba babu abinda zai yi sai dai ya zauna a gida babu wani karatu da zai yi.
Ba tare da sanin sa ba Mami ta shirya musu tafiya can Rafin Dawa.
Cikin satin da za'ayi tafiyar ta sanar dashi.
Kasa ɗaga ido yayi ya kalleta,a duniya bai san abinda zai yi ya sa Mami farin ciki ba,matar ta kaunace shi ta nuna mishi kauna a lokacin da duniya ta kyamace shi,a ranar da wani ya nuna mishi ƙarfin dukiya yaso ya wulakanta shi a ranar ta rungume shi ta shigo da shi gidanta ta rike shi tamkar ɗan da ta haifa a cikinta.
A hankali yace"ban san da bakin da zan miki godiya ba Mami,Nagode Allah ya saka miki da alkhairi".
Ta miƙe tsaye tace"ba ka ɗauke ni uwa ba kenan tunda godiya ka ke min Faruq,idan ka shiga makaranta ka sanar da malaminku za ka tafi gida ranar asabar".
Haka kuwa aka yi,bayan ya koma ya sanar da Malam batun tafiyar,ya masa addu'ar sauka lafiya.
Ranar asabar suka ɗauki hanya,yana zaune a gaba tare da driver sai Mami da Zarah a baya,don har da birgima ita sai an je da ita.
Ta wahala kam,don tunda take bata taɓa tafiya mai nisan wannan ba,da anyi tafiya kaɗan zata ce a tsaya tayi amai, gabaɗaya tayi laushi jikinta ya saki kafin su isa Bauchi.
Yamma lis suka isa,dai dai kofar gida driver yayi parking.
Sadauki ya sauko ya budewa Mami ƙofa yana kallon Zarah dake kwance jikinta.
Mami ta ɗan taɓa ta jin jikinta da zafi tace"za ki iya tashi kuwa Zarah?"
Ta ɗan girgiza kai a hankali.
Mami ta kalli Sadauki yace"Faruq taimaka ka dauke ta dan Allah,ta zama ƙatuwa ba zan iya daukarta ba".
Ta turo baki jin Mami ta kirata ƙatuwa.
Sadauki ya miƙa hannu a hankali ya dauko ta,jikin yayi zafi sosai alaman zazzabi ke son kamata.
Gabadaya mutanen gidan na tsakar gida idan ka cire Baba,Umma na tattare bakin ƙofar ɗakinta da tsintsiya.
Inna Yalwati kuma na kokarin hura wuta lami na zaune a gefe tana yanka kuɓewa,jin murya kamar na Sadauki ya sa duk suka juya da sauri.
Da farko Umma kallon shi ta tsaya yi ganin yaronta ya koma saurayi cikkake,a kalla zai kai shekaru shida rabon shi da gida tun kafin ɓacewar Sani.
Sai kuma ta zubawa hannun shi ido ganin shi riƙe da yarinya,bata gama wannan tunanin ba Mami ta shigo.
Tuni Inna Yalwati ta miƙe tana gyara ɗaurin zaninta dake ƙoƙarin kwancewa.
Umma ta nufi Mami cike da fara'a duk da yadda ƙirjinta ke bugu ganinta yar gayu tace"sannu da zuwa".
Ga mamakinta Mami tayi murmushi tace"yawwa sannun mu".
Umma ta nufi ƙofa tace"bismillah shigo".
Ɗakin na gyare tsaf sai tashin kamshi yake ta shiga Mami ta bi bayanta,a kan gadon Umman su ka tarar da Zarah Sadauki tsaye kusa da ita.
Ganin Mami na ƙoƙarin zama kan tabarma ya sa tayi saurin nuna mata bakin gado tace"ki yi hakuri kar ki zauna a ƙasa dan Allah".
Mami tayi murmushi tace"nan ma yayi".
Umma tace"ki yi hakuri dan Allah,ba don hali na ba".
Dole Mami ta koma kan gadon, Umma ta buɗe cikin tsohon wardrobe ɗinta ta fitar da sababbin cups ta fita ta wanke ta dawo ta buɗe randar ruwanta ta ɗebo ruwa ta ajiye kusa da Mami.
Ba tare da damuwa ba Mami ta ɗauki ruwan ta sha,hakan ba abin mamaki bane a wurin Sadauki,don shi shaida ne da kyawawan halayyar Mamin.
Tun shigowar su Umma ta fahimci wacece bakuwarta,don Sadauki ya sha bata labarinta idan ya sami damar magana da ita a wayar Kawu Buhari.
Nan da nan ta hura wuta ta ɗora tukunya,ta sa Sadauki ya yanka mata ƙaton zakarar da ta jima tana kiwonsa.
Ta sake hura wani wutan ta ɗora naman ta haɗa mishi kayan kamshi ta rufe ta koma ɗaki Inna Yalwati ta bita da kallo ƙasa ƙasa.
Tana shiga idonta ya sauka a kan Zarah dake lafe jikin Mami kamar mage,da sauri ta karasa wurin gadon tace"subhanallahi,lafiya kuwa?"
Mami ta girgiza kai tace"lafiya ƙalau muka bar gida,to da yake bata saba doguwar tafiya ba maybe shine dalilin da yasa ta koma haka".
Lokaci ɗaya Umma ta rikice,ta riƙo hannun Zarah tace"sannu ƴan mata, bari in aika a samo miki magani".
Mami tayi murmushi tace"kar ki wani damu,akwai magunguna na taho dasu yanzu zan bata".
Umma tace"Sai ta sha magani ba tare da ta ci komai ba?hakan ba zai yiwu ba ai,ina zuwa".
Oum Rijalain
***