Free chapter · Read without an account
Chapter 34
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 34
Sayyada barrister
***
YOTA 13
The five ink legends
Shirye-shiryen birthday party ya kan kama ba kakkautawa, ALAJA ta maida hankalinta kan yadda za a tsara taron, duk waɗan da suke cikin Tumbin Giwa sai da suka san eh lallai babban taro za ayi, tun la'asar ake sa ran fara shagali har 12:00 am na dare. Rabon da Alaja ta shirya irin wannan babban taro ya jima, yadda take rawan kai abin har mamaki yake baiwa ƴan Tumbin Giwa. Kowacce ta haɗa taro sisinta ta sayi suturan fitar taron.
Saura kwanaki biyu taron Bilqees tana zaune a restaurant, don ALAJA ta ce washegari da kuma ranan taron birthday party babu zuwa restaurant, a ranakun ba aiki, sai murna suke yi, za a huta na kwana biyu.
ALAJA ta aika aka kira mata Bilqees, ta iso ɗakinta dake restaurant ta taddata ɗauke da takarda list take dubawa, ta goge wannan ta rubuta wancen, ta zauna kusa da ita ta ce
"Ga ni Maa"
Ta ajiye ta ce
"Yawwa duba ki ga na sauya miki kayan da za ki saka, ya yi?"
Ta ɗauko doguwar rigar ta haɗu sosai, ɗauke take da ratsin pink and blue, ta matuƙar haɗuwa, ta ce ta yi, haka ma haɗaɗɗen takalmi da zata saka, sannan ta ce da ita
"Gobe za ki je saloon a gyara miki gashin kanki da safe za ki tafi fah do so nake ki yi kyau"
"To Maa da wuri zan fita"
"Yawwa, don ni ma ina so ayi min gyaran gashi kina dawowa zan fice"
"To Maa"
Ta taimaka mata suka ƙarashe abubuwan da take yi, sannan ta koma kitchen, har dare suna aiki. 8:00 pm daidai Dr Waahab suka shigo RESTAURANT kamar yadda suka saba, ya zauna a teburin sa, Bilqees ta kawo masa abincin daren sa, ta jera masa sannan ta yi masa sannu da zuwa, ya amsa tare da cewa
"Birthday girl"
Ta yi murmushi ta ce
"Yallaɓai likita"
Ya ce
"Gobe ne ko?"
"A'a jibi ne"
"Ok on Sunday za ayi"
"Eh"
"To ya yi kyau"
"Thanks"
Ta zuba masa shayin gargajiya sannan ta zuba masa Farfesun na jan nama da farar macaroni, yaji daɗin abincin ya ci sosai, ta dawo ciki ta haɗa masa fruits salad sannan ta kawo masa, ya kai ba ki ya ji shi ma daɗi, tabbas Bilqees yarinya ce amma ta iya girki, ga nutsuwa da sanin yakamata she is so special, he likes the way she treats people. she was very respected girl...
Ana washe gari taron birthday party Bilqees ta wuni a shagon saloon aka yi mata gyaran gashi, daman tana da yawan shi ga tsawo ga santsi, baki ne sosai aka gyara mata ya yi kyau, saboda shirye-shirye sai dare ta huta, Mamanta kuma bata ce ƙala ba akan taron don ta san bata isa ta hana ba, tun da Alaja tace za ta yi to sai ta aikata, bata soma baki ba ko ta yi wa Bilqees faɗa.
Ranar bikin birthday party da safe ƴan decorations suka iso aka gwangwaje sakiyan Tumbin Giwa da ado, abin gwanin sha'awa, in da Angel zata zauna aka zuba ballon pink and blue ya yi matukar kyau ga fararen kujeru da aka jera tare da teburin gwanin burgewa zuwa azahar aka fara shirya wajen. ALAJA ta fito cikin shiga ta uwaki Naira, ta ke ce raini, tayi kyau kamar ba ita ba, farin ciki ne kwance kan fuskarta. Karfe uku aka fara hallara kowacce ta sha kwalliya da wacce ya yi mata kyau da kuma wacce ya maidata biri, wani ko tsari babu, wasu kam da kayan jikinsu gara babu.
Babayo me bakin sigari, zee Dollers da Sadeebaby suka iso wajen, daga baya duk aka hallara, ana kallon yadda ALAJA ta zuba uban Naira wajen shirya birthday party, mamaki su ke yi duk da son kuɗin ALAJA amma ta iya zuba su a birthday party....
Bilqees ta iso wajen nan kallo ya koma kanta, ta yi kyau sosai cikin doguwar rigar da ta amshi jikinta, gashin ta an yi mata gyaran gashi ponytail ya yi wa kyakkyawar fuskarta kyau, da crown a kanta, ta koma little princess.
ALAJA tana gani ta shigo ta rungume su ka yi hoto, nan aka sha ɗaukan hoto cake ya iso me hawa biyar abin har mamaki yake baiwa ƴan wajen aka yi ta hoto nan DJ ya saki musu ƙida sai rakashewa ake yi, daga bisani aka raba abinci, Server's na ALAJA SPECIAL RESTAURANT ne su ka yi serving mutane.
Su Babayo me bakin sigari an samu na banza sai ci yake yi, da sauransu ya ba faɗa sai raya ciki kawai.....
****************
DR Waahab kasancewar yau Sunday babu in da zai je haka kawai yake fama da faɗuwar gaba, ya yi bacci ya tashi ganin la'asar ta yi yasa ya watsa ruwa ya ɗauro alwala ya isar da sallah wata zuciyar ta ce ya leƙa Tumbin Giwa ya yi wishing Angel happy birthday. Ya shirya cikin farar suit ya yi matukar kyau, sai ƙamshi yake yi, ya fito yana tunanin wane irin gift zai bata....
Shi bai cika shiga irin wannan taron ba, ko a KIRAWA'S FAMILY sai dai yaga ana yi, hayaniya ce baya so. Ya wuce babban shop dake bakin hanya yana ta tunanin wane irin kyauta zai saya mata amma brain nasa bai haska masa ba, daga ƙarshe ya sayo mata ƴar siririyar necklace a cikin kwantena me kyau da sada.
Ya ɗauko hanyar Tumbin Giwa, tun daga bakin titin yaji kiɗa na tashi, ya iso ganin ta main gate na Tumbin Giwa ake shiga yasa ya ɗan tsaya, a lokacin yamma ta yi sosai, ga motoci sun cika wajen da ƙyar ya samu ya daure ya shigo wajen, sai rakashewa ake yi mata da maza ya hango Angel zaune ta sha kyau kamar a sace ta sai murmushi take yi, a daidai lokacin aka dakatar da kiɗa don yanka cake, ALAJA ta karɓi min ta soma magana
"Yawwa yanzu za a yanka cake kowa sai ya yi wishing Angel birthdaynta"
Aka tafa mata, ta ci gaba da cewa
"Wannan unforgettable day ne, bayan an yanka cake an nutsu kuma zan sanar da muhimmin abu wanda zai bai wa kowa mamaki"
Nan ma aka tafa mata, sannan ta ce
"Yau ranan aci asha ne ba taro ba sisi aci na bati"
Dariya da shewa da tafawa aka yi, sannan aka yanka cake Bilqees ta sanya wa ALAJA a baki sai tafi ake yi musu, ALAJA tana rawa. Bilqees kamar an ce ɗago ta hango Yallaɓai likita a tsaye daga gefe Yana kallon ta, gani sai rawa ake yi ana cin cake yasa ta tako zuwa inda yake ta ɗan ɗaga rigarta tana takowa a hankali zuwa inda yake tsaye..
Bata yi tunanin zai zo ba, don ya ce baya zuwa irin wannan guraren, ta yi farin ciki mara misaltuwa, darajar sa da kimarsa suka ƙaro a idanunta, bata taɓa kare masa kallo ba sai yau, ya yi kyau sosai, Yallaɓai likita kyakkyawa ne kamar balarabe, har mamaki ma ta yi a lokacin da ya ce shi ɗan Nigeria ne.
Ya kura mata idanu yaga yadda ta yi kyau, ta koma kamar ƴar tsana, baby face nata ya fito sosai, kwalliyar ta yi mata amshi fuskar ta...
"Princess Angel"
Murmushi ta yi sosai dimple nata ya lotsa, ya kurawa ramin idanu, ta ce
"Uncle sannu da zuwa"
"Yawwa ya taro"
"Ga shi muna yi"
Ya kalli crown dake kanta da kuma gyaran gashi da aka yi mata, ya yi kyau, sai dai ya ji babu daɗi ƙarti suna ta kare mata kallo, ya karewa mutan wajen kallo yaga taron ba marabar sa da club sai rawa ake tikawa. Angel ta sudda kai ƙasa tana wasa da zoben dake hannunta ya sauke numfashi ya ce
"Happy birthday cutie wish you Allah's khair"
"Thank you Uncle"
Ya ciro sakar da yazo da ita ya miƙa mata kwantenan tare da envelope ya ce
"Ga gift nawa, Allah ya karo shekaru masu albarka"
Ta kalle shi yaƙi sakin jiki, wajen bai yi masa ba, ta ce
"Uncle da baka wahala ba zuwan ka ma ya wadatar"
"Ko dai bai yi miki bane?"
Ta girgiza kanta ta ce
"A'a na gode sosai"
Ta karɓa, taga sarƙa ce ta yi murmushi saboda ta haɗu, ya ce
"Ki saka"
Ta buɗe ta fiddo da ita, silver color ce siriri da kwalliyar heart, tana ƙoƙarin sakawa ta kasa ya karɓa, cikin kulawa ya ce
"Kawo"
Ta miƙa masa, ya ce
"Zan saka miki"
Ta sudda kanta ƙasa ya saka mata, ta dace da wuyarta suna kallon juna ya ce
"Kin yi kyau"
"Na gode"
Ta faɗa sannan ta sake cewa
"Bari na baka wajen zama"
"A'a tun da mun gaisa zan koma"
"Uncle ba za ka ci abincin birthday na ba?"
"A'a ba haka bane a ƙoshe nake"
"To ina zuwa"
Yana tsaye yana kallon mutan wajen suna ta chashe wa, ya sauke numfashi yana mamakin kansa wai duk ya sauya lokaci guda akan Angel, in ba don ita ba, ba zai shigo wannan wajen ba...
"Uncle ga shi"
Ta miƙa masa take away, ya karɓa don kada ta yi fushi amma ba ci zai yi ba, bai san waɗan da suka girka ba, ya ce
"Thanks"
Ta janyo masa kujera ya zauna ta miƙa masa cake na birthday a ɗan ƙaramin disposable plate ya karɓa ba laifi ya ɗan kusura ya ce
"Na ci saboda ƙaran shekaran Mommie nah"
Ta yi murmushi ta ce
"Na gode"
"Yaro ya girmi Mommie nsa"
Ta yi murmushi a lokacin aka kira sunanta ana buƙatar ta a wajen, ta ce
"Ina zuwa Yallaɓai"
Da sauri ta koma filin sai rawa ake yi masu bada gift suna ci gaba da bata, ALAJA ta watsa mata kuɗaɗe, cen ALAJA ta shiga sakiyan wajen tana tikan rawa mazaunanta da na shanunta sai sama da ƙasa su ke yi ko a jikinta sai ma zage damtsi da tayi tana ci gaba da rawa.
Abraham ya shigo wajen cikin shiga ta irin na ƴan yahoo ya cika wuyarsa da manya manyan sarƙa ya soma zubawa Alaja kuɗi shi ma yana rawa, suka riƙe hannu suna chasewa abin su.
Sai dariya yake yi, sannan ya iso inda Angel ke zaune ya kura mata idanu kamar ya lashe ta, ya ce
"Wow my Angel, you look like take away"
Nan ƴan neman gindin zama suka ce ai sai ka ɗauketa ka tafi, ya karɓi gift da ya kawo mata ya ajiye kusan kala biyar, a ranta ta wa ya sanya shi..
ALAJA da ta gaji don kanta ta karɓi mic ta soma kura jawabi
"Na yi farin ciki da nuna ƙauna, kowa ya yi ƙoƙari ya nuna ma Angel bajintarsa, ba zan manta da wannan ba. To akwai wani gagarumin surprise da zan baku yanzu, na san za ku yi farin ciki da shi"
Kowa ya yi shiru ya zuba mata na mujiya yana kallonta da kuma kasa kunnuwa, ta ci gaba da cewa
"Kamar yadda ku ka sani Angel ƴa ta ce, kuma kowa ya shaida yadda nake sonta, na zauna na yi tunanin zaɓa mata miji da kaina don inganta rayuwarta"
Angel ƙirjinta ya bada tas, miji kuma wanene wannan?..
Da mamaki Dr Waahab yake kallon Alaja, jin abin da ta ce yasa ya miƙe tsaye yana kallonta, miji kuma wa Angel, a yau!
"Ni ALAJA SA'ADEEY EMMANUEL ABRAHAM na bai wa ɗana ABRAHAM SOLMON JEMES auren ANGEL wato Bilqees, yau kuma za ayi baikon auren, yanzu zai sanya mata zoben alƙawari kamin lokacin bikin"
Nan aka soma murna ana ihu, ban da Bilqees da ta yi mutuwar zaune, me Alaja ta ke shirin aikatawa ne? Abraham a matsayin miji...
"Don haka nan da wasu watanni za ayi shagalin bikin"
Abraham don murna ya rungume mommynsa yana washe baki ya ce
"Thank you my lovely Mom, i love you so much"
"My son zan yi maka fiye da haka ma, burina shi ne ka yafe min"
"Na yafe miki tun da na kusa na mallaki Angel"
DR Waahab dake tsaye jiri ka soma ɗebarsa da ƙyar ya dafe bango, ya matuƙar kaɗuwa da jin wannan al'amarin, Abraham kuma zai auri Bilqees, ta yaya? Ƙarar sake sautin da aka yi ne ya sake sanya masa ciwon kai, numfashinsa yana sama, da ƙyar yake iya sauƙo da shi...
Bilqees dake zaune kamar an shukata ta haɗa uban gumi a lokaci guda, daman taron baikonta da Abraham ALAJA ta yi, no wonder shi ya sa ta kashe makuɗan kuɗaɗe...
Maman Bilqees dake zaune a verender tana jin duk abubuwan dake faruwa, a lokacin da taji muryar Alaja tana cewa ta baiwa Abraham auren Bilqees ta mik'e zunbur kamar wacce aka yi wa alluran sojoji, yau za ayi yaƙin da ba a taɓa yin irinsa ba, yau hakurinta ya ƙare, sai ta nunawa ALAJA iyakarta...
Fuuu ta yafa mayafi ta tunkaro wajen, ta hango ALAJA tana rawar murya, ta girgiza kanta ta san da walakin goro a miya, ALAJA ce zata kashe kuɗi babu riba, ai tun farko tasan da wata a ƙasa, tayo cikin wajen kai tsaye amma ALAJA ta tare ta tare da cewa
"Yi min magana a hankali yadda zan maida miki a hankali, muddin kika ɗaya min murya to zan faɗi abin da zai girgiza ki da kuma ƴarki"
Da ƙyar Maman Bilqees ta sauke ajiyar zuciya, idanunta suka kaɗa su ka yi ja ta nuna Alaja da yatsa ta ce
"Wannan karon ba za ki yi galaba akai na ba, ba zan ɗauki cin kashe da kike yi min ba, na gaji dole mu kawo ƙarshen komai"
Yadda ta yi magana a hankali yasa ALAJA tunsirewa da dariya ta ce
"Ashe kina da hankali, to ki sani wannan auren babu fashi sai an yi"
"Ba zayyu ba, Bilqees ba zata auri Abraham ba, yaron ki ba, ko da musulmi ne"
Murmushi ALAJA ta yi ta juya tare da cewa
"Sai mu gani"
"ALAJA"
Cewar Maman Bilqees da ƙarfi, ta juyo tare da cewa
"Ko ki amince ko karki amince sai yarona ya auri ƴar ki"
"Ba ki isa ba, kin yi ƙarya anan na rantse..
"A'a dakata Malama, riƙe rantsuwarki yau za ayi baikon aurensu, da albarkan ki da rashin sa ba damuwata bace, amma muddin ki ka ce za ki hana, yanzu sai na sanar da duniya wacece ke? Zan fallasa musu asalin fuskarki, ƴarki zata san komai, za ki rasa ta, za ta guje ki, har ta mutu kuma za ta ci gaba da tsine miki"
A hankali Maman Bilqees ta soma dawowa da baya² tana kallon Bilqees dake zaune akan kujera ta hango tashin hankali da ruɗewa da damuwa tattare d ita. Da ƙyar ta kawo kanta ɗaki ta rufe ƙofa ta fashe da wani matsanancin kuka, ta ɗora hannu akanta tana ji ina ma duk waɗannan abubuwan a mafarki suke faruwa yanzu tana ji tana gani za ayi baikon auren ƴarta da wanda ba musulmi ba.......
Ayi hakuri da typing errors, bana samun lokacin editing ne.
Comment and share fisabilillah