Free chapter · Read without an account

BABI NA HUƊU

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 
 
82 Division Army Barracks, Abakpa, Enugu. 

A KOWANE lokaci idan Megidana baya nan Barikin soji a tare dani da ƴaƴanmu, hankali na baya kwanciya a duk inda ya tafi. Inaso na koyawa zuciyata yarda da abinda ya ɗaukarwa kanshi na irin wannan aiki wa ƙasar shi, amma ba zan iya ba. Inaso na koyawa zuciyata haƙuri da juriya da nuna ban damu da duk wani abu da ze iya faruwa dashi ba idan suka fita aiki amma ba zan iya ba. A duk inda aka tura shi aiki, muna samu muyi waya ko sau uku a sati ne amma yau gashi sati biyu bamu yi waya ba. Nayi zuwa yafi a ƙirga a ofishin soji dake nan cikin bariki ina tambaya akan lafiya Megidana har yanzu be kira gida ba, duk lokacin da na tafi cewa suke inda suke babu network shiyasa har yanzu be kira ba. 
  “Ki dena damuwar kanki akan shi, nasan duk inda yake suna lafiya rashin network ɗinnan ne da suka faɗa miki. Da wani abu ne ya faru ai zamu sani ko a labarai” Babban yaro na, Ahmad ya faɗa. Ahmad ɗan jami'a ne anan jami'ar University of Nigeria, Nsukka dake Enugu State. Yana kan scholarship ne a makarantar shiyasa abubuwa suke taho mana da sauki. Ƙanin shi kuma, Baffa, yana zuwa jami'ar shima nida mahaifinsu muna ƙoƙari akan kuɗin makaranta saboda tsadar dake gare ta tunda ba indigine ne ba. Ƙanwar su kuma, Farida, tana zuwa nan secondary school dake cikin Barrack na Abakpa na Enugu. Muna iya kokarin mu domin mu ga sun samu ilmi sosai wanda zasu yi alfahari dashi kuma su taimakawa kansu. 
  “E don tey wey I dey tell her that o” Baffa yace yana kallon Ahmad
  “Make i just go and ask them again. Na damu da irin wannan shirun daga mahaifin ku”
Babu wanda ya ƙara ce min komai har naja mayafi na na wuce. Ko yanzu da na tafi haka suka faɗa min suna cewa ya kusa dawowa ma. “Maman Farida, ki kwantar da hankali naki. Nothing has happened to your husband. Na internet matter wey dey stop am from calling home but they'll soon be back”
Fuskata na ɗauke da damuwa naji duk ta saki jin maganganun Captain John. Yana jin Hausa ba sosai ba saboda zaman da yayi a Arewacin Nijeriya wani lokaci. “Wetin i go do, Captain? Dole zan damu saboda shi ɗin rayuwar mu ne”
Cikin kulawa yana kallo na yace “I understand Maman Farida and your husband is okay”
“Thank you Sir” na mishi godiya tukuna na wuce. 

Muna cikin wani irin babban bariki ne a Abakpa Barracks dake nan Jihar Enugu, a kudancin Nijeriya. Komai ana saidawa a ciki kama daga kayan miya ne, da duk wasu abubuwa na buƙatocin rayuwa. Da akwai makaranta ta yaran Bariki a ciki kuma anan ne Farida ke zuwa. 

NI DA MEGIDANA mun kasance haifaffun garin Sokoto dake Arewacin Nijeriya. Ya kasance yana sha'awar zuwa aikin soja tun kafin mu haɗu dashi kuma ya kasance wanda ya cika aikin soja tun kafin mu haɗu. Bayan ya samu ne ya dawo daga training ya fara zuwa ganina. Da farko mahaifina be yarda da auren soja ba se daga baya ya amince ya bar wa Allah komai zaɓin rayuwa. Tun lokacin da muka yi aure aka fara kai sojoji gari mabanbanta suna aiki aka kawo megidana kudancin Nijeriya kuma yanzu shekaru har ashirin da takwas bamu yi retire ba bamu koma gida ba. Mu kan je akai-akai domin ganin gida kuma mu kan yi wata ɗaya har biyu a gida saboda jimawar da muke bamu tafi ba. 
Megidana, Ibrahim, warrant officer ne mukaminsa, duk da jimawar da yayi a gidan soji saboda da secondary certificate ya shiga aikin soji. Albashin da ake mishi ma ba wani me yawa ne ba saboda takardun shi. Haka muke lallaɓawa da rayuwa da kuma ƴaƴan mu da muke so su samu ingantaccen ilimi. Ba ƙaramin jin dad'i da alfahari da ƴaƴana nake ba da suka samu gurbi a cikin jami'ar Nijeriya ta Nsukka. Nasan ko mu iyayen bamu samu ba, ƴaƴa na maza biyu zasu yi kokari su ga ƙanwar su ta samu ilimi kamar yadda suka samu nasu. 

Zama nayi na dafe goshina ina tunanin Ibrahim. 
  “Make you sha stop thinking about that man ooo” na tsinkaye muryar Baffa yana fitowa daga ɗakin su. Ɗaga kaina nayi na ɗauki pillown dake kusa dani na jefa mishi. Chapkewa yayi yana dariya yace “Ah you wan kill yourself with man thinking”
  “The man na your father no be my own father oo”
    “I dunno wetin carry you marry soldier toh”
Wani irin kallo na mishi ina mamakin maganganun shi. Shi Baffa daban yake a cikin yarana. Babu damuwar komai a cikin ranshi ko kuma yadda nake ganin yana nunawa. Ko wace irin damuwa zan shiga idan na mahaifin su ne ko na wani, baya nuna damuwarsa. Ahmad kuma a kodayaushe idan yana nan yaga ina damuwa sosai akan abubuwa, shine yake kwantar min da hankali na. Idan na ɗaga hankali ga abinda zan ɗan bashi yaje dashi makaranta, ya kan ce na dena damuwa. Da kanshi ma yake fita yayi aiki da hannayen shi ya samu ƴan kuɗaɗen shi yayi sayayyar makaranta ya tafi. Shima Baffa yana ɗan taɓa yin abubuwan neman shi suna taimakawa junansu. 
   “Suppose you know you go worry yourself no good, then why carry yourself marry soldier? Him no tell you the kind of danger wey he put himself so?”
   “Zan ci ubanka fa Baffa” 
Wata dariya ya ƙara yi ya zauna gefe na. “Sun ce lafiya fa. Network ne babu”
Zaman shi ya gyara yace “Ahmad ya faɗa miki ai. Kene ba zaki yarda ba se idan kinji muryar masoyin ki”
  “Hmm. Baffa dai. Baka san irin damuwar da nake ciki ba”
  “Kene kika ɗaurawa kanki wannan damuwar”
      “Tashi ka tafi”
   “Na tafi kuma? You no like my company again?”
     “Yes, I don't like. Oya go”
“Okay oo. Make i go start preparing myself for today's match”
        “Na you know”

                                              
                 ________



Ina cikin gida na gyara kayan miya kenan har na ɗaura miyar naji ana kwala min kira “Maman Farida” “Maman Farida” naji ana kiran sunana. “Maman Farida” na ƙara jin Mama Alex ta kira sunana. Gabana ya fara faɗuwa. Da sauri na fito daga ɗakinmu ina yin sauri naji abinda ke faruwa. “Maman Farida oo” naji ta ƙara kiran sunana ba a cikin firgici ba. Hankali na ne ya ɗan kwanta ina fitowa daga gidanmu. Koda na fito na samu wasu daga cikin mazajenmu da suka tafi kwantar da wata matsala ta tsaro dake addabar ƙasarmu. 
     “These men are back oo” ta faɗa cikin murna marar misaltawa saboda itama mijinta na cikin wanda akayi tafiyar tare dasu.
Murmushi ne ya samu wuri a fuska ta ina kallon su nace “They are back. And they look healthy. Alhamdulillah”
   “Praise be to God oo, hallelujah!” ta faɗa cikin farin ciki mijin ta na fara tahowa muka gaisa dashi suka wuce cikin gidansu. 
Ibrahim ne yake tafiya irin wacce ya saba yi nayi tsaye ina kallon shi maimakon na tafi na rungume shi kamar yadda muke yi duk ya tafi ya dawo. Ibrahim dogo ne kyakkyawa koda bayan tsufan da yayi yanzu yana nan da kyawun shi. Irin mazan nan ne wanda daka gan su zaka ga alamar ƙarfi a tattare dasu. 
Yana isowa wuri na ya kalle ni cikin idanu ya kai hannun shi a kunci na “Look at you” ya faɗa. Hannun shi na jenye akan kunci na ban san lokacin da na fara zubar da hawaye ba. Rungume ni yayi muka shiga cikin gidanmu. 
Lokacin Baffa ya fito daga cikin ɗakinsu. Ahmad dama tun shekaran jiya ya wuce makaranta hostel suke zama. 
“Lovebirds” Baffa ya faɗa yana so yayi dariya 
   “Zaka ci ƙaniyar ka a cikin gidan nan” Ibrahim yace ya ƙara rungume ni ina kuka. 
   “Ki dena kuka fa. You're seeing how Baffa is teasing you”
Kukan nawa yaƙi tsayawa duk da ina son na dena kuka. Be san wani irin sauƙi ne nake ji a cikin zuciya ta ba da ganin sa ya dawo lafiya ƙalau. 
Zama muka yi yana rungume dani. 
  “Ki dena kuka fa Umma. Ki tashi ki duba mijinki ko yana lafiya”
  “Ba zaka wuce ba Baffa? Get out my friend” Ibrahim yace
“Okay, lemme leave you two to yourselves”
“Ya isa mana Maryam. Ki dena kukan nan” Ibrahim ya faɗa yana ƙara rarrashi na. Ƙoƙari nayi na tsaida kuka na na ɗago kaina ina kallon shi cikin idanu “Kasan ka kusa kasamin hawan jini Ibrahim?”
“Dan Allah kiyi haƙuri Maryam. Gaba-ɗaya inda muke babu network shiyasa ban kira ba”
“Ko kaɗan babu network? Ko ɗan text ɗinnan Ibrahim. Koda sau ɗaya ne nasan kana raye”
“Ah ah Maryam. I told you babu network. Da da akwai kinsan ba zan je har na dawo ba muyi magana ba koda kuwa text ɗin ne”
“To shikenan. Ya hanyar ku da kuma aikin?”
“Toh Alhamdulillah. Na dawo da gajiya sosai”
Tashi tsaye nayi nace “Bari na haɗa maka ruwan wanka se kayi kaci abinci ka huta”
“Yawwa nagode Maryam”

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.