Free chapter · Read without an account

026

by Kansa'u Bello · MEERAH

*MEERAH*

     *026*


    Ƙarfe 10 da rabi Mamy, Jauhar da Fatima suka wuce airport don ɗauko Ajmal da jirginsa ke gab da sauka. Koda suka isa airport zaman nintunan da basu wuce 15 ba suka yi jirgin ya sauka.

   Cikin natsuwa da tsananin kamewa yake tako wa zuwa inda ya hango su Mamy, sosai yake jin farin cikin ganin Mahaifiyar tasa domin kuwa ya yi matuƙar kewarta. Rabon da ya ganta tun zuwan da suka yi duba shi ita da Abby a London.

   Jauhar da tunda ta hango sa jikinta ke tsumar farin ciki, tana jin tamkar ta ruga da gudu taje ta rungume sa ko zata ji sauƙin abinda take ji a cikin zuciyarta a game da shi.

   Sai dai kasancewar ta san halinsa tsaf zai yaga ta yasa ta kama kanta, don ta taɓa kwatanta hakan ya mata rashin mutunci. Tana wannan tunanin har bata san lokacin da ya ƙara so ba sai jin muryar Fatima ta yi tana masa oyoyo haɗi da rungume sa.

   "Barka da zuwa My Son, yaya jikin naka? Ina fatan dai ba abinda ke damun ka yanzu?." Mamy ta faɗa tana riƙe hannunsa.

   "Ina lafiya Mamy, fatan na same ku lafiya?." Ya bata amsa yana riƙo hannunta ya sumbata.

   "Lafiya lau Alhamdulillah." Ta faɗa cike da farin ciki. Matsowa Jauhar ta yi kusa da shi ta yi ƙoƙarin riƙo hannunsa tana cewa.

  "Barka da zuwa Ya Jam, na yi missing naka sosai!." Ta yi maganar cike da iya yi. Ajmal kuwa janye hannunsa ya yi bai bari ta taɓa shi ba ya amsa mata da cewa.

  "Barka." A taƙaice ya mayar da hankalinsa ga Fatima dake faɗa masa yanda ta yi kewar sa. Murmushi ya sakar mata yace.

   "I miss you more little Sis." Ya faɗa yana jan hancinta kaɗan, daga haka suka shiga mota suka wuce gida.


 *Kano* 

    *Nawaz....*
  
       Sai Azahar aka kammala yiwa Abba aikin sannan aka rubuta masa sabon maganin da zai ci gaba da amfani da shi, duka kuɗaɗen dake hannun Nawaz sun ƙare. Wanda suka rage bai fi na abin hawa da zai mayar da su gida ba.

   Don haka dole ya haƙura da sayen maganin ya bar shi sai idan sun koma ya nemi wasu kuɗin, hakan ya sa suka tattara suka wuce gida.

   Bayan sun koma Sallah ya fita yi sai da ya dawo sannan yaci abincin da Raihana ta girka kafin dawowar tasu, ɗakinsa ya shiga ya kwanta da niyyar ya ɗan huta kafin la'asar ya fita.

  Yana kwanciya kiran Meerah ya shigo masa, ɗauka ya yi da sallama cikin sanyin muryarsa wacce gajiya ta ƙara taimakawa wurin sanyaya ta.

   Ajiyar na sauke jin daukar muryar tasa a cikin kunnuwa na, lumshe idanu na yi na buɗe sannan na buɗe baki cikin ƙaramin sauti nace.

   "Har kun dawo daga asibitin ne?." Ajiyar zuciya Nawaz ya sauke sannan ya bani amsa da cewa.

   "Eh mun dawo, yanzu haka ma huta wa nake son yi kafin la'asar." 

   "Okay to ka huta, idan ka tashi sai muyi magana." Na faɗa da kulawa sosai.

   "Alright sai na tashi ɗin, I love you masoyiya." Nawaz Ya faɗa yana lumshe iadanunsa da bacci ya fara cin ƙarfinsu. Murmushi sosai na saki ina jin daɗin yanda baya gajiya wa da furta min cewar yana sona.

  Zare wayar na yi daga kunnena don tuni ya kashe ta, tun bayan gama furta min kalaman da suka saka zuciyata a cikin farin ciki. Zame wa na yi a kwanta a saman gadon ina kunna daddaɗar waƙarsa mai taken "Ƙauna." Wacce duk cikin waƙoƙinsa ita nafi so.

   Domin kuwa tatattun kalamai ne masu cike da nutsuwa da nuna tsananin soyayya, wacce idan kana saurara baka sanin lokacin da kake tsunduma cikin shauƙin soyayya.
  
    Baitukan nake bi cike da shauƙin soyayya, yayin da zuciyata ke haska min hoton abin ƙauna ta a cikin idanuna, ina jin cewa na gama yin dace a soyayya. 

   Da haka nima bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ni, wanda ban tashi ba sai da aka kira sallar la'asar Momy ta shigo duba ni, jin shirun nawa ya yi yawa.

**** Knocking ta ɗan yi kaɗan sannan ta murɗa ƙofar ta shiga cikin ɗakin, Meerah ta hango kwance a saman gado ta rungume teady bear ɗinta tana bacci hankali kwance. Yayinda sautin waƙa ke tashi ƙasa-ƙasa a cikin wayarta.

   A hankali ta taka gaban gadon ta saka hannu ta ɗauki wayar, waƙar ta kashe sannan ta zauna kusa da ita ta shiga tashinta a hankali.

   "Meerah ki tashi, tashi mana Auta." Momy ta faɗa tana ƙwace teady bear ɗin da ta maƙal-ƙale tamkar wai jaririn da ta haifa take tsananin so.

 ****** A hankali na shiga buɗe idanuna da bacci ya ƙara musu girma da launi ka kaɗan na sauke a kan Momy.

   "Ki tashi ki yi salla ki shirya zamu wuce Gwangwazo duba Alhaji Babba da suka dawo yau." Momy ta faɗa tana miƙewa.

   "Okay Momy." Na faɗa ina tashi haɗi da murza idona, fice wa Momy ta yi bayan ta tabbatar min cewa kar na jima fa. Kasancewar nima ina son zuwa gidan Gwangwazo, (asalin gidan Kankanin su Dady) yasa ban ɓata lokaci ba.

   Alhaji Babba shine kakan su Dady wanda ya rage, mutumin kirki ne mai son zumunci. Ya tsufa sosai amma har yanzu hankalinsa bai ɓata ba don babu wanda baya gane wa a cikin zuri'arsa.

   Sannan duk lokacin da muka je gidan haka zai yi ta bamu labarin Masarauta da labarin asalin zuri'armu da alaƙar su da Masarauta wanda hakan ba ƙaramin daɗi yake min ba, domin kuwa ina son tarihi a rayuwa ta.

   Ya jima yana fama da jinya amma sai a kwanakin nan ne jikin sa ne ya matsa har aka fitar dashi waje aka yi masa magani, to yanzu an dawo da shi ne shi yasa zamu je mu duba shi. 

   Ban wani tsaya ƙaƙale-ƙaƙalen dana saba ba na yi wanka da alwala na fito, salla na fara yi kafin na shirya a gag-gauce kasancewar na san Mamy na jira na. 

    Kyakkyawar Abaya na saka ƙirar Egypt black color na yi rolling mayafinta na saka turare, na ɗauki jaka da takalmin da suka dace na fito cikin hanzari.

   Samu na yi Momy ita ma ta fito don haka fita kawai muka yi. Ya Sultan ne zai kai mu nuna fitowa muka samu shima ya fito shi da Ya Aryan da yace zai je shima. 

  Gaishe su na yi suka amsa min sannan muka shiga mota muka wuce, tare da rakiyar securities ɗin da Abba ya ajiye domin hakan.

   Mun isa Gwangwazo asalin gidan Iyaye da Kakanninmu, gida ne mai tsohon tarihi wanda ba'a taɓa rushe sa ba duk arzuƙi da ɗaukakar da iyalan cikinsa suka samu kuwa.
   
   Sai dai duk bayan wani lokaci ana yi masa gyara da kwaskwarima irin ta zamani domin ƙara ƙawa ta shi.

   Su Baba Alhaji (Alhaji Mamman Basiru Gwangwazo Mahaifin su Dady.) sun so a rushe ko da wasu ɓangarorin ne domin yin gine-gine zamani, amma su Alhaji Babba da ƴan'uwansa suka ƙi amincewa da hakan.

   Suka ce kuma ko bayan ransu basu yarda a rushe musu gidan gadon su mai ɗauke da sirrikansu na gado ba, dole suka haƙura suka bar shi a haka sai dai gyara da ake masa duk bayan wani lokaci.

   Mun samu ƴan'uwa da dangi duk sun je tarbar su Alhaji Babba, don haka gidan a cike yake. Ɓangaren Alhaji Babba muka fara shiga muka gaishe sa da yi masa ya jiki, muka gaisa da duk manyan gidan da muka samu a nan.

   Mun ɗan jima ana hira da dangi kafin Momy ta kalle ni tace.

   "Auta ta shi mu ƙarasa ɓangaren Nene mu gaishe ta sai mu wuce."

   "To Momy." Na faɗa ina miƙewa bayan na sake yi wa Alhaji Babba fatan samun sauƙi. Gidan iyayen Momy muka nufa dake a cikin gidan, kasancewar Momy da Dady auren zumunci aka yi musu don Mahaifinta ƙanen Mahaifin Dady ne da suke uba ɗaya 

   Nene Mahaifiyar Momy ta yi farin ciki sosai da ganina saboda tana matuƙar sona sosai, nima ina sonta sosai saboda yanda take shagwaɓa ni, da biye min ta yi min duk abinda nake so.

  Yanzu ma ina zuwa ta bani haɗaɗdiyar fura da ta samu damu mai kyau taji nono da zuma, ga shi an saka ta a fridge ta yi sanyi. Rungume Nene na yi nace.

   "I love you Nene, Allah ya bar min ke ki daɗe ki yi lasting ki yi ta bani irin wannan damun ina sha." Na faɗa fuskata ɗauke da murmushi.

   "Ja'ira kyace haka mana tunda kin samu abinda kike so." Nene ta faɗa tana murmushi haɗi da kai min ranƙwashi kaɗan a kaina. Baki na tura nace.

   "Tunda kika rankwashe ni to na maki yaji wurin Baba Malam zan tafiya ta." Na faɗa ina miƙe wa na fice daga ɗakin. (Baba Malam shine Mahaifin Momy).

   "Idan kin je ma kya dawo ki neme ni da kan ki ai ƴar nema." Nene ta faɗa tana murmushi, ita dai Momy dariya kawai take yi domin kuwa in da sabo ta saba da damar mu ni da Nene duk lokacin da muka haɗu.

Sai bayan sallar magriba sannan su Ya Sultan suka dawo muka tattara wuce wuce gida cike da kewar mutanen Gwangwazo da tarin tsarabar da Nene da Baba Malam suka bani.....

  


  *Abuja...*

   A ɓangaren Ajmal kuwa lokacin da suka isa gida Mamy ta gabatar masa da duk abincin da aka shirya dominsa, bai ƙi ci ba duk da cewar dai ya riga ya yi breakfast a Kano kafin ya fito. Kuma ba wani lokaci bane aka ɗauka da zai buƙaci wani abincin.

   Sai dai ba ya son taji babu daɗi, hakan yasa ya daure yaci sannan ya zauna suka ɗan yi hira kafin ya wuce part ɗinsa don hutawa.

   Basu haɗu da Abby ba sai da magriba suka haɗu a masallaci, tun ƙarfe 5 na yanma Abby ɗin ya dawo lokacin shi kuma Ajmal na ɓangarensa yana hutawa.

  Tare suka fito har da Sulaiman da ya dawo daga makaranta shima, don lokacin da Ajmal ɗin ya dawo yana lectures ne.

   Kai tsaye ɓangaren Mamy suka wuce don yin dinner gaba ɗaya kamar yanda suka saba idan kowa yana nan, abinda yafi komai faranta rayuwar Mamy kenan taga zuri'arta wuri ɗaya ciki har da Ajmal ɗa ɗaya da Allah ya jarabe ta da mafificiyar soyayyarsa fiye da sauran yaranta.

   Sai kuma gashi a kansa kullum take shan wahala, don ta kasa dawo da shi ƙarƙashin kulawarta gaba ɗaya kamar yanda take buƙata.

   Lokacin da suka isa tuni an shirya table don haka can suka nufa suka fara cin abinci cikin farin ciki, bayan sun kammala zaman hira suka yi baki ɗayan su domin sukan daɗe ba su samu irin wannan damar ba da zai kasance kowa yana nan.

   A cikin hirar ne Abby da Ajmal suke tattaunawa a kan tafiyar da Ajmal ɗin zai yi zuwa Turkish da wasu ƙasashen, wanda yana dawo wa Companynsa zai fara aiki.

     Momy da take son yin amfani da wannan damar da ta samu ta gyara zama ta kalli Ajmal tace.

   "Alhamdulillah ka kammala karatu, yanzu zaka fara gudanar da Kasuwancinka kamar yanda ka buƙata. Yanzu abu ɗaya ya rage maka shine ajiye iyali, don haka nake ganin cewar da zarar ka dawo daga tafiyar nan da zaka yi komai ya fara tafiya a Company sai a tsayar da maganar aurenka da ƴaruwarka Jauhar, tun da itama Alhamdulillah ta kammala degree ɗinta." Mamy ta faɗa tana tsare Ajmal da ido.

   Daɗi sosai ya kama Jauhar jin maganar auren su da Mamy ta sako, don har ga Allah ita fa haƙurinta ya kusa ƙarewa. Don dama ta zuba ido ne tana jiran ganin abinda Mamyn zata yi.

   Ganin ya yi shiru bai ce komai ba yasa Mamy cewa.

   "Ka yi min shiru baka ce komai ba? Wato na sako maka maganar da kafi tsana ko Jamal?." Ta ƙare maganar cikin faɗa, don ta shirya a wannan karon dole sai ya auri Jauhar.

   Sabo da ba zata zuba ido tana kallo Laylah taci gaba da juya mata ɗa ba, bare har ta samu damar da zata liƙa masa wannan shagwaɓɓiyar ƴar tata da suke jinta kamar ransu ba. Ita ce zata zaɓa masa mace wacce ta dace kuma dole ya amshi zaɓinta.

   "Kiyi haƙuri Mamy." Shine kawai abinda Ajmal ya faɗa ya miƙe ya fice a ɓangaren baki ɗaya, da kallo Mamy ta bishi baki sake har sai da ya ɓace wa ganinta kafin ta dawo da kallonta ga Abby tamkar zata fashe da kuka tace.

   "Amma Alhaji kana ganin abinda yaron nan yake min ba zaka masa magana ba, shine zaka bar ni da shi in yi ta fama ni kaɗai ko?!." Ta ƙare maganar cike da takaicin halin Ajmal ɗin na manni.

  Don sai ka zauna ka yi masa dogon bayani amma ya baka taƙaitacciyar amsa.

   Allah ya sani shi Abby dariya ma abin nata ya ba shi, ya rasa yaushe Na'imatu zata gane cewar ba'a matsawa ɗan yau a kan abinda baya so. 

  Tun lokacin da ta nuna sha'awar haɗa wannan haɗin Ajmal ɗin ya nuna rashin amincewarsa.

   Ba wai fito na fito ya yi da ita ba, amma sai dai yanda yake share maganar da ƙin mayar da hankalinsa a kai duk lokacin da ta ɗauko ta ya isa ta gane cewar baya ra'ayi ne. 

   Sai dai daga ita har ƴar tata sun kasa gane wa su haƙura, kullum sai wahalar da kansu suke yi a kan hakan wan da suke yi domin san yana nuna bai ma san sunan yi ba.

   Ganin yanda ta fusata ne ya saka shi danne murmushinsa yace.

   "To ni miye nawa a ciki Mamyn yara? Wannan fa magana ce tsakanin ɗa da uwa, Allah dai ya zaɓa abinda yafi alkairi." Daga haka shima ya miƙe ya haye sama. Da kallon baƙin ciki ta bishi shima, don ta san cewar duka bakinsu ɗaya ne ɗa uban.

   "Ko kuso ko ku ƙi dole sai an yi wannan auren!." Ta faɗa cike da takaici tana gyara zamanta a saman kujerar da take zaune.

   "Amma Mamy me zai hana ki ƙyale Brother ya zaɓi wacce yake so da kan sa mana, tunda ya nuna baya ra'ayin Jauhar ɗin a ƙyale sa mana. She is not a child."

   Sulaiman ne mai wannan maganar, don yana mamakin yanda Mamy ta dage sai ta cusa wa ɗan'uwansa wannan mara kunyar yarinyar da babu abinda ta iya sai fitsara.

   "Tashi ka bani wuri Sulaiman kafin na kai maka duka a wurin nan, wato ni zaku haɗe wa kai a gidan nan ko?!." Ta ƙare maganar cikin ɓacin rai.

  "Allah ya baki haƙuri Mamy." Sulaiman ya faɗa yana miƙe wa ya fice shima. 

  Jauhar da ta gama kai wa wuya ta fashe da kuka tana tashi ta haye sama, da kallo Mamy ta bita ita ma tana jin zuciyarta a ƙuntace. Fatima ce ta matso kusa da Mamy tace.

    "Ki yi haƙuri Mamy ku sake bawa Yaya lokaci in sha Allah zai amince." Ta yi maganar cikin kwantar da murya. Murmushi Mamy ta yi tace.

   "Babu komai daughter je ki kwanta kema." 

    "Okay, good night Mamy." Fatima ta faɗa sannan ta miƙe ta haye sama ita ma. Mamy kuwa ta ɗan jama a zaune tana tunani kafin ta miƙe ta nufi ɗakinta ta yi shirin kwanciya sannan ta nufi ɗakin Abby.


****** A ɓangaren Jauhar kuwa lokacin da ta shiga ɗaki Mahaifiyarta ta kira a waya, cikin kuka ta shiga bata labarin abinda ya faru yau ɗin. 

   "Mimi ni dai na gaji da wulaƙancin da Ya Jam yake yi min gaskiya, kawai ki san yanda zaki yi ayi auren nan in dai kina son farin cikina. Don na lura Mamy ce kawai ke goyon bayan haɗin nan a gidan nan, amma tun daga kan Abby har Ya Sulaiman basa wani sona Mimi!." Jauhar ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan.

   "Kina jina ko Jauhar?." Mimi ta faɗa daga can ɓangaren.

   "To ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abinda zai hana Ajmal ya aure ki, domin Yaya ta riga ta yi min alƙawarin hakan. Kuma kema kin san halinta idan ta kafe a kan abu, ko su so ko kar su so dole sun amince da hakan." Mimi ta faɗa cikin son kwantar wa da ƴarta hankali.

  Ta jima tana rarrashinta da yi mata alƙawarin mallaka mata abinda take so, sai da ta tabbatar ta samu natsuwa sannan ta yi mata sallama ta kashe wayar.

 
  Bayan sati biyu.......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.