Free chapter · Read without an account

BABI NA SHIDA

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

Kallon Yaya Hauwa nayi, da mamaki akan fuska ta “Yaya Hauwa ke likita ce?”
   “Yes, of course. Baki sani ba?” Kallon Zaid tayi “Zaid baka faɗa mata ba?”
Shiru nayi ina kallon Zaid ina sauraren abinda ze faɗa mata amma kuma nasan ba ze ce bata zama muna yin hira shiyasa bata sani ba. 
   “Abubuwan basu kawo min akai ba shiyasa ban faɗa mata ba” Zaid ya faɗa tare da kallo na. 
    “A good profession that is. Well respected in the community” nace, ina kallon Yaya Hauwa. Murmushi tayi tana kallo na “But really tiring.” Murmushi nayi ina jin idanun Zaid akaina se kuma ya juya ga Yayar shi yana kallon ta suna yin magana. 
   “Har yanzu baku ƙare kan maganar covern littafin ki ba?”
Ajiyar zuciya Yaya Hauwa tayi tace “Na gaji da mutanen nan. Basu so su min abinda nake so. Kawai fa nace a min zane a matsayin cover na littafin amma gani suke be yi fitting ba. Ba nice marubuciyar ba?!” tace cikin faɗa. Magana nake da Zara amma kuma hankalina na kan abinda Yaya Hauwa ke faɗa. 
   “Ki chanja wurin publication mana. I know someone here in Abuja that's good in that”
  “Basa so su rasa ni” tace tare da yin murmushin gajiya
  “Ana yin abu dole ne?” Zaid yace cikin takaici kuma ban taɓa jin yayi magana irin haka ba “Ki ce musu kin fasa ki zo na haɗa ki da wannan. Ya iya aiki fa” 
Zaman ta ta gyara tace “Ba haka kawai zan ce na fasa ba.” Wayar ta ta jawo ta danna ta ba Zaid tace “Kaga irin covern da nake so. Bana son hoto. Ina son covern ya zama painting. Nafi son painting”
   “Yayi kyau haka. Ki yarda ki zama rebellion, you have me”
Dariya Yaya Hauwa tayi ta amsa wayar ta hannun shi ta bani “Duba ki gani Hadiza. Wannan painting be yi kyau ba?”
Amsa nayi daga hannun ta na duba nace “Yayi kyau Yaya Hauwa. Dama kina rubutu ne?”
  “Eh, ina rubutu” tace tana kallo na “Yanzu haka na rubuta littafai uku wanda akayi publishing. Wannan shine na huɗu na”
   “Wow, that's impressive. Aikin ki yana bari kiyi rubutu kuma?” 
   “Eh, yana bari nayi rubutu na. Rubutu passion nawa ne. Medicine kuma shi nake so nayi a matsayin career na. So you see, they're two different things”
Nodding kaina nayi ina mata murna akan abinda take yi “Zan so na karanta littafan uku da kika yi. Sauran ɗayan kuma idan aka yi publishing mune na farko da zamu siya”
Kyakkyawan murmushi Yaya Hauwa tayi tace “Zaid yana dasu. Ya baki ki karanta ko kun fi so ki saye dai?”
Kallon Zaid nayi nace “Duk yadda kika ce haka za'a yi”
   “To kinga, Zaid yana dasu ya baki ki karanta”
   “Zan amsa daga hannun shi to”
    “Ke baki da wani passion?”
Murmushi nayi tare da tashi tsaye riƙe da hannun Zara “Bani da wani passion. Se de kuma zan iya cewa passion ɗina shine zama Barrister da kuma samun adalci ga wanda aka zalunta”
Nodding kai Yaya Hauwa tayi tana murmushi “I like this. I really like it”
Haɗa idanu muka yi da Zaid nace “Bamu fa dafa abinci a gidannan ba”
Kallon Zaid tayi se kuma ta kalle ni “Ba ku yin abinci ne a gidan? Naga yau na daga cikin ranakun hutu”
   “Ban samu nayi bane. Bana tunanin baƙi”
  “We're sorry, bamu faɗa zamu taho ba amma kar ku damu mun ci abinci a gida ban san ko Zara zata ci ba tunda se dare zamu tafi”
  “Yaya Hauwa dan Allah ki dena cewa haka. You'll always be welcomed here, da sanin mu da kuma ba sanin mu ba. Bari na shiga kitchen yanzu na ɗaura abinci” na faɗa kuma na lura da kallon Zaid da tayi. 
  “Mu tafi na taya ki” Yaya Hauwa ta tashi tsaye “Zara ki zauna nan tare da Uncle Zaid zamu shiga kitchen mu fito”
Nodding kai Zara tayi se na zaunar da ita a kusa da Zaid amma baya kallo na. 
  “Amma Yaya da kin zauna yanzu zan ɗaura na dawo”
   “Kar ki damu mu tafi” Yaya Hauwa tace tare da riƙe hannu na har muka isa kitchen. Bayan mun isa ne ta sake hannuna tana tambaya na me za'a dafa. Tsayawa nayi ina tunani. Nasan ba abinci nake dafawa a cikin gidannan ba. Zan ma iya ƙirgawa duk zamana matar aure a gidan Zaid, idan na dafa abinci sau biyar to ya kai. Be taɓa min magana akai ba ni kuma koda ya min magana zan nuna mishi ba zan iya ba kuma nasan ze ƙyale ni idan akan wannan abu ne. 
   “Let's make Zaid's favourite. Do you know his favourite?” 
Kallon ta nayi ta tsareni da idanun ta tana kallo na babu motsa idanu “Zaid's favourite. Do you know it?” ta ƙara tambaya na. 
Girgiza kaina nake so nayi amma ina jin wani iri akan haka. Cire idanun ta tayi akaina nasan tasan ban sani ba tace “His favourite food is rice with a very flavourful stew along with peppered fish. He never told you?”
Murmushi nayi na girgiza kai ina jin kaina very tense. Ba be taɓa gayamin bane ba, ni ce ban bashi damar faɗa min abubuwa game dashi ba. “Be faɗa min ba”
 “Ba kwa magana ne? Be faɗa miki Yayar shi likita ce ba kuma yanzu be faɗa miki abincin da yafi so ba. So, ku ba kwa magana ne? Ina nufin baku yin hira ne? Ko kuwa duk aiki kuka sa a gaba ne?” tace tana kallo na se kuma tace “Mu fara aikin mu”

Daɗi naji akan abinda tace ko ba komai mun dena waccan maganar. Freezer na buɗe na ɗauko kayan miya tunda tace shinkafa da stew yake so kuma nasan shi za'a yi. 
   “Ki ɗaura shinkafa, zan gyara kayan miyar”
Nodding kaina nayi na ɗauko tukunya na kai a wurin sink na kunna. 
  “Muna magana dake. Ba kwa magana ne?” ta ƙara faɗa. Saura kaɗan nayi rolling idanuna akan tambayar ta. 
  “Muna yin magana dashi” nace mata tare da ɗauko tukunya daga sink na ɗaura akan gas na kunna. “Se de kin san yanayin aikin shi be cika zama a gida ba, shiyasa har yanzu muna kan sanin juna ne”
Tana gyaran kayan miya ba tare da ta kalle ni ba tace “Aikin shi ba ze hana muku magana ba. Se de idan baku cika magana ne ba”
Shiru nayi ban ce komai ba gaba-ɗaya naji ashe bana jin daɗin tahowar nan da Yayar shi tayi. Bana so kowa yasan abinda yake faruwa a cikin gidana amma daga gani Yayar shi observer ce kuma idan ta lura da abu bata yin shiru. 
  “A ina kuka haɗu? Be taɓa faɗa min ba. Na de san yana ƙaunar Hadiza”
Murmushi nayi na dole ina jin kaina very tense da yadda zan faɗa mata yaya muka haɗu da Zaid. Idan gaskiya zan faɗa, zata san ni ba sa'ar shi ba ce ba. Kuma ni ba maƙaryaciya bace ba. Kode zan yi ƙarya amma ba irin wannan ba. 
  “A makaranta muka haɗu”
   “Uhmm! Nasan ba jami'a ba” tace tare da ɗago kanta ta kalle ni da murmushi akan fuskar ta. Maida idanun ta tayi akan aikin ta.
   “A chan secondary a Kaduna”
   “Oh, lokacin da suka yi karatu a Kaduna. He was your mate?”
  “No. Muhammad Liman was my mate”
Ƙara ɗago kai tayi ta kalle ni da mamaki akan fuskar ta. Nasan Zaid duk be faɗa mata irin waɗannan maganganun ba tunda take tambaya ta. “Muhammad nawa?”
   “Eh, shi”
  “So Zaid was your junior and he fell in love with you. Is that?”
  “Unfortunately, yes”
Dariya tayi tace “Say fortunately rather”
Murmushi nayi ban ƙara cewa wani abu ba. Bana so tace kenan ba sa'an ki bane ba ko kuma tace kenan kin girme shi kodai irin yaran nan ne wanda ake yiwa jumping ko kuma wanda basu kai girman ajin da suke ba. 
  “I know he loves you. I don't know for you tho, but I know he loves you” tace, abinda ban yi tsammani ba amma kuma har kallona tayi ta kuma cigaba da abinda take. 
Shiru nayi ban ce komai ba. Ta cigaba da magana “Idan har dai ina gida, to zan dafawa mijina abinci. Kuma ina dafa duk abinda yake so se idan shine yace be san abinda za'a dafa ba” shiru tayi ta kuma sake ce “Kinsan ma'aurata suna da ....me zan ce....okay kaman crisis ne zan ce ko kuma wani abu dai akan abincin da za'a dafa a cikin gida. Shi miji be sani ba ya fita daga idea me za'a dafa itama matar bata san abinda za'a dafa ba shiyasa ma take tambaya. They're all out of ideas”
Murmushi nayi akan abinda tace ni ban san crisis din ba tunda ba abinci nake dafawa ba. 
  “And Zaid is a really good man” tace tana grating kayan miyan da ta gyara. Nace mata ga blender tace a'a grating yafi daɗi akan blending idan stew za'a yi. 
Bayan ta gama grating ta ɗaura stew ɗin akan gas sannan ta aza tukunyar kifi. 

Ƙamshi na fara ji yana tashi da freshness na kayan miya saboda naga jiya Zaid ya siyo ya kawo kitchen. Albasar da ta sa ta ƙara fitowa dashi ƙamshin fresh ginger da curry suna cigaba da haɗewa a cikin kitchen. 

   “Ina faɗa miki wannan mijin naki yana da kirki ta yanda baki zato. Ba fa saboda yana ƙanina bane ba. Ina cikin wanda suka yi raising nashi so nasan halin Zaid. Yana da kirki sosai. Kuma bashi da matsala. Ki yarda dani”
Murmushi nayi nace “Na yarda dake kuma nasan Zaid mutumin kirki ne” na faɗa kuma da gaske nake nasan mutumin kirki ne saboda da wani namiji ne nake yiwa irin wannan halayen, da tuni ya tura ni gidanmu ko kuma an mana namu zama asan menene matsalar. To matsala ta da Zaid shine auren da na mishi, na aure shi ne saboda shine kawai yake available ba wai son shi nake ba.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.